Showing 18001 words to 21000 words out of 136985 words
ta inda zata bullo har ya gaji dai ya tambaya, don ita kanta Innar ganinta da yayi sai a hankali yasa ya zargi ko sun k'ara kwatawa ne da Dijen shiyasa yaji Gidan shiru alamun bata nan, Inna kam bata so sanar dashi ba har sai ya ci abinci don tasan muddin yaji ba k'aramin d'aga hankalinshi zai yi ba, sai dai dole ba yanda ta iya saboda yanda ya matsa mata da tambayar ina Dijen taje har lokacin bata dawo Gidan ba?.
Kai tsaye ta ce dashi tana ciki bata da lafiya, hankalin Baffah a tashe ya garzaya d'akin Innar inda Dije take kwance cikin zazzab'i sharkaf sai nishin marasa lafiya takeyi, aiko tana ganinshi ta fashe da sabon kuka gwanin ban tausayi, cike da fad'uwar gaba Baffah ya zauna bakin gadon ya rik'o hannunta yace
"Meke maki ciyo?"
Dije ta share hawayenta cikin rawar murya tace, "jikina gaba d'aya ciyo yake yi man ga raunukan sai zafi suke yi man Baffah, WALLAHI saura kad'an a kashe maka ni yau da baka zo ka sameni ba"
Baffahn ya zaro Ido waje yace,. "Wanene da wannan danyen aikin gareki halan?, Ashe ko yau ba zan saurarawa kowa a gidan nan ba tunda har abun ya zo da cin zarafi irin haka, ki yi gaggawar sanar dani wa ya dake? tashi zaune ki fad'a man don in san irin matakin da zan d'auka kan mutum ko ma wanene"
Dije ta yunkura dakyar ya rikata ta tashi zaune cikin kuka ta fara nuna masa raunukan da Safwan ya ji mata ciyo, Baffah kam ganin jikin Dije duk shatin bulalar yasa ya fara zuba ruwan fad'a bakinshi har kumfa yake yi saboda tsabar b'acin rai, Inna kam ganin yanda ya hau da yawa yasa ta fayyaace masa komi da aka fad'a mata ta sanar dashi, akan wanda ya dake tan tare da dalilin da ya janyo ya yi mata dukan.
Baffah cikin tsananin b'acin Rai ya ja talkamanshi sai Gidan Maigarin, inda kai tsaye ya fara nuna rashin dacewar abunda BAK'ON Malamin yayi wa 'yarshi, Maigari da sauran mutanen da ke wurin Suka dinga bashi hak'uri sannan cikin tattausan kalami Suka nuna masa aibun abunda Dijen ta yi masa wanda Sam Sam bai dace da tarbiyyar dalibi ga malaminshi ba, tun yana ganin laifin Safwan har ya kai ya gano ashe rabin laifin duk na Dijenshi ne, sannan Maigarin da mutanen Suka fahimtar dashi sosai akan ya tsawatarwa Dije akan sake faruwar wata hatsaniya tsakaninsu, daga k'arshe suka bashi hak'uri akan abunda aka yiwa Dijen , sannan ya baro wurin ya koma gida inda dakyar da jib'in goshi ya samu tasha yan farau faraun fura sannan tasha pracetamol ta koma ta kwanta, cikin dabara Baffah yayi ta kwantar mata da hankali akan muddin Safwan d'in ya sake dukanta ta zo ta sanar dashi don wannan karon shi da kanshi zai rama mata, ba ko Malami yake ba ko hukumar ce da kanta sai dai idan an rufeshi mabudin ya b'ace.
Sannan Dije ta rage bak'in cikin da ke cin zuciyarta, amman fa tasha alwashin sai yasan da ita yake zancen, haka ta kwana tanata wassafa irin muguntar da zata yi masa, cikin ikon ALLAH kwananta biyu ta warke Masha ALLAH,a rana ta uku da komawa Makaranta ne ta ci alwashin sai taje school d'in ko don labarin da su Jummala suke ta bata kullum akan yanda suke gane karatunsu, duk da dai shi Safwan d'in ba hausa yake yi masu ba amman dai ba laifi suna dan fahimta sama sama.
Aiko ranar Alhamis tun da sassafe ta shirya cikin uniform d'inta, ta yi sallama da su Baffah cikin natsuwa ta nufi Makarantar, don shi Baffah har so yayi ta daina zuwa Makarantar a cewarshi tunda ba ta ALLAH ba ce, don dai ita Dijen ta nace tana son karatun ne yasa ya amince amman ya ja kunnuwanta da kyau akan ko kallon Safwan d'in kada ta sake yi don gudun wata sabuwar fitinar, sai da ta yi masa alk'awali sannan ya barta akan zata koma d'in, don tun lokacin da tasha dukan ta zama wata so silent da ita ko rashin jin cikin Gida duk ta daina yi, saboda kwata kwata ko walwala daina yi ta yi a gidan kullum tana d'akin Inna dunkule kan gado, don duk masifar da take yiwa akuyarta idan ta zubar da abinci ko abinsha, a lokacin duk ta daina don acen baya har bulala take sakawa ta yi ta dukan akuyar tana yi mata fad'a da kashedi kala kala, har wani zubin sai Inna ta yi mata fad'a akan zalin d'in akuyar da take ci sannan take kyaleta, amman sai gashi Safwan yasata zama kurum kurum dolenta.
Aiko tafe take kanta a duk'e tun da ta hangosu daga nesa ta Sha mur tare da saita natsuwarta, don ko da ta zo ta gabansu sai da ta dan rankwafa sannan ta gayar dasu sai dai bata jira sun amsa ba tayi gaba abinta, Safwan ya bita da wata jar harara yayi kwafa yace
"Mumu kawai black cat"
Lawi ya kyalkyale da dariya yana dafe bakinshi don kada Dijen ta jiyo dariyarshi, amman duk da hakan bai hanawa kunnuwanta ji ba sai dai ko kad'an bata waigo ba har ta shige cikin class dinsu.
Dan lokaci a tsakani sai gashi ya shigo ajin yana wani cin magani ya jefa mata chalk tare da nunata yace ta goge allo, ta mik'e ba tare da ta yi gardama ba ta goge black board d'in tass ta koma ta zauna, daga nan ya fara karatunshi mai cike da zallar turanci tsintsa don mugunta duk ya zo tambaya sai ya tambayeta saboda kawai ya kureta,
Wani lokaci ta bashi amsa dai dai wani kuma idan bata iya ba ya kirata jahila, haka ya k'are darasin nashi cikin isa da gadara ya koma tambayoyin cikin tambayoyin ne kawai sai ga wani bera tun daga cen saman rufin ajin ya fado tsakiyar class d'in saboda rufin ajin gaba d'aya duk ruwa sun canye rabin, aiko ba shiri yayi wani tsalle cikin tsoro yace
"Oh my gosh"
Bera ko kamar ya san tsoronshi yake yi garin gudun neman mafaka ne ya nufi wurinshi, aiko sai ga Malam Safwan da yin wani uban tsalle ya dale window yana sambatu irin na tsoro, ganin hakan yasa duka Yan ajin suka fara dariya k'asa k'asa, Dije kam fuskarta a had'e tamau tamau ba alamun ma zata yi dariya, bayan beran ya wuce ne a gurguje ya kammala karatun ya fice, Dije ta kalli Yar paper'r da ke hannunta ta fara karanto abubuwan da duk yayi ta fad'a mata kalmomi kanana na turanci kamar haka
Illiterate.
Black cat.
Urgly girl.
Village girl
Sai maimaitasu take yi amman ta kasa tantance fassararsu bale tasan ma'anarsu, a ranta ta kudurta zata tambayi abokinshi domin ya fassara mata su fillah fillah, Aiko kai tsaye ta fito ajin aka yi dace ta hangoshi cikin wani class yana karantarwa, aiko taje da sallamarta cikin ladabi tace dashi wurinshi ta zo, ya yi Yar guntuwar dariya ya d'auki excuse wurin Yan class d'in ya fito, cikin sakin fuska tace dashi don ALLAH wata tambaya take son yi masa in da Kai tsaye ta fara zayyano sunayen a kanta da ta samu ta hardace su cikin kanta.
Lawi yayi shiru yana tunanin amsar da zai Bata wadda ranta ba zai b'aci ba, don zuciyarshi ta bashi cewa duka kalmomin daga bakin Safwan suka fito zuwa gareta don yasan k'aramin aikin abokinshi ne wannan, aiko dai ya koma class ya dauko wani littafin kalmomin turanci da fassararsu cikin harshen hausa ya mika mata yace taje ta duba da kyau zata gano fassarar kalmomin duka a ciki, cike da jin dadi Dije ta karb'a tana murna har ta juya zata tafi ta waigo tace
"Don ALLAH ka ara man shi nan da kwana Uku zan maido maka"
Yana dariya yace,
"Na baki sati d'aya ma amman ki sani akwai tambayoyin da zanyi maki idan lokacin ya cika kin kawo"
Cike da jin dad'i tace ta amince ta koma class dinsu zuciyarta cike fal da murna, tare da tunanin hanya mafi sauk'i da ta gano wadda zata rama abunda Safwan d'in yayi mata cikin dan kankanin lokaci.
Har aka tashi Makarantar Dije bin littafin take yi d'aya bayan d'aya shafi bayan shafi har ta gano abunda duk yake nufi da miyagun kalmomin da ya yi ta jifarta da su kala kala.
Tsawon kwana biyu Dije tana kamun beraye tana sakawa kwali tana b'oyewa don har da abinci da ruwa take ajiye masu, don kuwa ta kama bera yafi ashirin irin bakake d'in nan manya manyan, kullum Inna da Baffah sai dariya suke yi mata suna fad'in
"Dije Kuma aikin kiyon beraye kika koma yi ??"
Sai dai tayi dariya amman bata nuna masu cewa wani nufi ne a ranta ba, sai ko gashi tun da sassafe zata je Makarantar Allo ta yi dubarar fita da k'aton kwalin berayen, bata zame ko'ina ba sai Gidan Maigarin cikin nasara ba kowa a wajen ta yi dubarar ajiye kwalin ta je k'ofar d'akinsu Safwan ta leka, sai ko gashi shi kad'ai a d'akin yanata baccinshi hankali kwance.
Dije ta d'auko kwalin ta shigo bakin d'akin a hankali ta kwantar da kwalin ta budeshi Aiko sai ga Beraye suna ta fitowa daga ciki suna shigewa cikin d'akin sai da ta juyesu duka sannan ta fito da kwalinta ta janyo k'ofar ta rufe ruf da kwadon da ke makale jikin k'ofar, sannan ta tafi da key din ta cillashi cikin ciyayi cikin sauri ta tafiyarta zuwa Makaranta zuciyarta cike da tsantsar farin cikin rama abunda ya yi mata .
Ku taimaka kar ta yi kisan Kai😳🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
Akafta🤣
D/AUTA CE✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*BAKINA YA YI KAD'AN YA NUNA DINBIN GODIYATA ZUWA GAREKU BA MASOYA BOOK D'IN DIJE K'ARANGIYA, AMMAN KU SANI INA YINKU SOSAI INA MAKU GASKIYAR SO FISABILILLAH💃🏻*
*Lamba ta 13*
SAFWAN kam cikin Bacci ya fara jin abu yana hawa jikinshi, wani jarumin beran ma cikin k'warewa da mugunta ya cafko masa farcen k'afa da k'arfi sai ga Malam Safwan a zabure tare da kwallah k'ara, idonshi suna kaiwa kan berayen ya fasa wata arniyar k'ara ya nufi k'ofar fita, sai dai mamakinshi rufe take gam gam ba alamun zata iya budewa, SAFWAN kam ya fara tsalle yana ihu Berayen suka firgice suma su ka dinga gudu suna neman maboya, wurin gudun ne wasu Suka yo kanshi aka yi sa'a wani zai hau sama ya kuskure sai gashi ya fado jikinshi, cikin firgici ya fasa wata arniyar k'ara tare da yin tsalle sai ga bera ya shige cikin rigarshi, Safwan ya ci gaba da ihu yanata tsalle har ya samu ya fito rigar da k'yar, amman duk da hakan bai daina zuba ihun ba don kafin kace me k'ofar d'akin nasu ta cika fam da dan Adam, don kuwwar da yake yi iya karfinshi ta janyo hankulan Mutane da yawa ciki kuwa har da Lawi da ke dawowa daga wajen kiran wayar da yayi da mutanen gidansu, kai tsaye aka fara k'ok'arin buge kwadon don a samu k'ofar d'akin ta bud'e, sai dai kafin ma a sami sa'ar budewa tuni Malam Safwan ya some saboda tsabar tashin hankali da firgici da tsoron da ya kamashi, don daman cen shi babu abunda yake tsoro a duniya face b'eraye, akan bera guda d'aya sai ya hargitsa d'aki kaf wajen nemanshi don kuwa muddin akwai bera a d'aki to kam sam shi bashi ba bacci a ranar har sai ya kasheshi sannan ne hankalinshi ke kwanci, to gashi yanzu ya janyo Dije ta yi masa gudunmuwa da manyan zaratan lukutayen kosashin Berayen kauyensu.
Aikuwa ko da aka samu sa'ar bud'e d'akin kwance yake a sheme tsakiyar d'akin tsilla tsillan berayen sai hawa suke yi kanshi suna ta wasa, ganin Berayen yasa Lawi firgicewa saboda yasan yanda Abokinshi yake tsananin tsoronsu, cikin zafin nama ya dauko ruwa ya kandama masa, sai gashi da sauke k'atuwar ajiyar zuciya ya mike a zabure ya fito d'akin yana ihun kiran wayyo a taimakeshi beraye zasu kasheshi.
Mutane kam sai kumshe dariyarsu suke yi ganin wai shi duk akan bera ne yake wannan firgici da tashin hankali har da su suma, Lawi kam sanin wanene abokin nashi da beran ya nufi wajenshi yana ta bashi Baki, sai dai ganin babban farcenshi na k'afa yana zubar jini yasa ya gano ba k'aramar barna Berayen suka yi masa ba, uwa uba fuskarshi da wuyanshi da ya yi jawur ga sawun yagar beran nan ya fito a jikinshi kasancewarshi farin mutum wurin yayi jawur, da kyar ya ciyo kanshi ya daina haukar da yake yi ya samu natsuwa ta ziyartoshi, ya jashi ya kaishi gindin iccen da ke k'ofar gidan Maigarin ya zaunar dashi, maigarin da sauran mutanen kowa sai yi masa sannu suke yi.
Maigarin yasa aka fito da Berayen d'aya bayan d'aya anata kashesu, amman duk da hakan Safwan kafewa yayi akan shi ba zai sake shiga d'akin ba, don ko wunin ranar ma duk a waje yayi komi saboda tsoron shiga d'akin da yake yi, lokacin da dare yayi ma Dole sai d'akin wasu samarin yaran Maigarin aka kai shi ya yi bacci, amman duk da hakan motsi kad'an zai sa ya zabura haka ya kwana zuciya ba natsuwa.
Ko da safiya ta waye tun da sassafe ya nufi Makarantarsu Dije don ko karyawa bai jira ya yi ba saboda gaba d'aya zama gidan ya gundureshi, aka yi dace itama Dijen ta yi sammakon fitowa don kusan ma itace ta biyu ko uku da zuwa Makarantar duka, tana hangoshi saman baranda kanshi duke yanata tunani ta fara kumshe dariyarta, ta yi k'ok'arin saita kanta ta isa wurinshi ta tsaya gabanshi cikin jarumta tace
"Toch me toch fire live me live dengerous your cross the bala'i kaddara your business for nown you tunani in kwakwalwarka"
Tana kare maganar ta gyara zaman Jakar fatar da ke rataye a kafad'arta ta yi masa wani kallo ta wuce fuuu abinta zuwa class dinsu, don tsoron ya sake yi mata irin dukan da yayi mata ranar, Safwan kam binta yayi da wani kallon tafi cen sakarai yana wani mere sai cen Kuma ya tuntsure da wata arniyar dariya, don a iya zamanshi garin ko Murmushi bai tab'a yi ba amman sai gashi yau da kyakyatawa kuma duk a sanadin abokiyar fadan nashi Dije, yarinyar da yake jin tsanarta har cikin zuciyarshi tsana irin wadda bai tab'a yiwa kowa irinta ba.
Yabi bayanta da kallo yana dariyar takaici yace, "crazy girl"
Dije kam murna kawai take yi shima yau ta wankeshi da turanci don ya gano cewa ita d'in ba jahila bace kamar yanda yake kallonta, taji matuk'ar dad'in samun aron littafin da Lawi ya bata don kuwa dashi ta ke kwana a saman kanta tana hardar kalamai tana had'a wannan da wancen ta yi magana cikin turancin duk da ba dai dai take yi ba amman ba laifi tana kamo hanya.
Har aka tashi school Safwan bai da wata natsuwa Dije kam sai jinta take yi cikin nishadi, don tasa a ranta duk ya kuskura ya sake yi mata wani abun abunda zata yi masa a gaba sai yafi wanda ta yi masa a yanzu.
Safwan kam kalamanta sun saka ya zargi cewa ko itace ta yi masa wannan horon da Berayen?, Sai dai ya sa a ranshi zai binciki kawarta d'aya idan har da gaske ita din ce to shi ko sai ta yabawa aya zakinta, aiko safiya tana wayewa ya yi sammako kamar yanda ya yi jiyan sai gashi ko Mune da su jummalo sun zo zasu wuce ya kira mune ta k'araso wurinshi cikin ladabi ta gayar dashi, sannan ya yi mata tambayar cewa
"Kawarki ta gaya maku cewa ta saka man beraye a d'aki ko?"
Mune ta fara waige waige tace, "A'a ba Ni ta fad'awa ba su Jummala ne ta fad'awa"
Safwan ya had'e fuska yace,. "Au da gaske kenan itace ta saka man?"
Mune ta rufe bakinta da sauri tace,. "Ni ma ban sani ba na dai ji tana fad'awa su jummalar don ni yanzu ko magana na yi mata bata amsa man gaba take yi dani"
Ta k'are maganar cikin taruwar kwallah a idonta, Safwan ya bita da kallon mamakin ashe zarginshi ya zama gaskiya ita din ce amman Lawi ya tsaya Kai da fata yanata kareta tare da wanketa tas da soso da sabulu, cikin k'ara tsuke fuska yace
"Me ya had'aku da har take gaba da ke?"
Mune tana shirin bashi amsa ne ta hango Dije tafe tana tsallen jin dad'i tana yan wakokinta, ta yi saurin dafe k'irjinta tace
"Na shiga Uku don ALLAH kar kace Ni na fad'a maka WALLAHI dukana zata yi in taji"
Cikin rawar jiki Mune ta bar wajen da sauri har da su gudunta ta shige ajinsu, Dije Kam duk da ta hangosu amman ko kallo bai isheta ba ta dage kanta sama ta shige aji, sai ko gashi ya shigo class d'in yayi masu karatu saboda takaicin Dijen ko tambaya d'aya bai tambayeta ba, don ko ta d'aga hannu da nufin bada wata amsar sai ya basar da ita ya zab'i wata, haka yayi ta yi tun Dije bata damu ba har ta zo wuya itama ta daina d'aga hannun.
Ko da aka tashi ya sakata kamun kunne cikin rana tsoron ya daketa yasa ta kama kunnen, tun tana juriya har ta kai ta fara kuka tana fad'in jininta zai dawo ta kai zubowa zai yi k'asa idan taci gaba, ya ce ta koma yin kneel down ta d'aga kanta sama ta kalli rana hannuwanta duka biyu ya d'ora mata duwatsu masu dan girma yace kuma ta yarda suka fad'i jikinta ya gaya mata.
Dije tsawon minti sha biyar tana kallon ranar da taji azaba ta Kai mata karo ta fad'i sheme alamun aljanun sun zo, Safwan ya dauko bulala zai daketa ta yi saurin tashi tana fad'in
"Don girman ALLAH Malam ka yi hakuri yunwa nike ji ka bari in je gida"
Yace da ita suna nan har marece sai ta fad'i uban da yasa ta saka masa beraye a d'aki, Dije ta fara rantsuwar ba ita bace