Showing 63001 words to 66000 words out of 136985 words

Chapter 22 - DIJE ƘARANGIYA

09 Apr 2026

1074

ga yanda ake yi"

Dije ta turo baki tace "Don Allah Inna ki bari kawai Surry ta koya man, tunda naga itama watarana tana shiga ta yi girkin idan saurayinta zai zo fira, sai dai kuma su fa da wata ƙatuwar akwati suke sanwa a kai, baki ganshi ba da murhun ɗora girki ya kai shida ko bakwai fa, to ni har yanzu ban ma san ta yanda ake kunna abun ba, saboda da wutar lantarki ma naga ana aiki da shi"

Inna tace "To ki dinga koya kinji kinga abincinsu daban da namu, idan baki iya ba sam ba zaki ji daɗin zama cikinsu ba, kuma kinga Mijinki ɗan gayu ne yana buƙatar ace komi kin iya irin nasu, idan kuma ya ga baki iya komi ba sai ya auro wata matar wadda ta iya abubuwa irin nasu, kin ga shikenan sai ta karɓe mijin ta barki sake da baki tunda baki iya komi ba"

Dije ta yi shiru sannan tace,. "Ai ni Inna ko don renin hankalinshi ma dole in koya kafin ya dawo, amman fa gaskiya in yace zai auro wata bayan ni yasin sai naci Uban ko ma wacece inna"

Inna ta zaro ido waje tace, "saboda mi? Ko ance maki ke kaɗai ce ALLAH ya halastawa ya zauna da ke? To kul kar in fara jin wannan shirmen gareki, don jikina yana bani yanda yake ɗan birnin nan ba zai zauna da ke ke kaɗai ba matuƙar ba kin iya komi na yan birnin ba, don haka idan har baki son ya ga wata ya sake aurowa to ki natsu da kyau ke ma ki zama yar gayu kamar su, ki dinga wanka kamar yanda suke yi, ki iya girki irin nasu, ki iya kwalliya irin ta su ke tafiya ma idan kin so zaki iya maidata irin tasu, saboda kawai ki zamo dai dai da mutanensu don kawai ki ƙwatowa kanki ƴanci, ki rage yawan surutu da faɗi ba'a tambayeki ba, ki zamo shiru shiru sannan ki dinga komi cikin natsuwa ba rawar jiki ko ƙiriniyar da kika saba yi anan ba, sannan kar ki yi wasa da ibada kamar yanda kika koya tun nan gidan, idan ma da hali ki dinga yin azuminki na Litinin da Alhamis don samun nutsuwar zuciya"

Dije ta yi shiru tana ta wassafa duk abubuwan da Inna ta faɗa a ranta, sai cen ta yi ajiyar zuciya tace

"Ai Inna na fara koyar wasu abubuwa, kinga ko kwalliyar garinmu da nake yi acen yanzu duk na daina yi, saboda Surry tace in ina yi mutane zasu gano cewa wai daga ƙauye na fito su rena ni"

Inna tace,. ,"To ki yi ƙoƙari ki yi ta koyar abubuwa irin nasu kafin Mijinki ya dawo, saboda kawai idan ya zo ki yi masa bazata don na tabbata ba ƙaramin so yake yi maki ba, tunda har ya aureki a yanda ya ganki bayan akwai ƴanmata da yawa a cen birnin, amman duk ya tsallake kowa ya aureki"

Dije ta cire tagumin da ta yi tace, "Ni WALLAHI sai in ga shi baya sona ma kamar Malam Lawi, don yafi sona da shi nesa ba kusa ba, don dai shi baki ga yanda yake ta hantarata ba komi na yi ya yi ta gwasaleni yana katsa man tsawa, watarana ma har dukana yake yi fa"

Inna ta yi saurin faɗin,"Ni kaina da na haifeki ai idan kika kaini bango watarana ina dukanki ko kin manta ne?, To shikenan don kinyi laifi na dokeki sai ace ban sonki? Saboda haka idan kina son ki ƙwato ƴancinki gareshi to ki zama mace kamar sauran matan garinsu kafin ya dawo, in da hali ma har ki fisu natsuwa da kamun kai har ma da gayun gaba ɗaya, ke ko ki ga yanda zai dawo yana lallaɓaki don gaban kowa baya shayin nunaki matuƙar kika zama yanda yake so, sannan kika zamo dai dai da yanda na lissafo maki, amman idan kina wannan shirmen me zai hana ya jibgeki ko?, tunda ke kanki kinsan kunnuwanki ba jin magana suke yi ba"

Haka Inna ta yi ta cusawa Dije ra'ayin son abunda zai sa ta ƙwato yancinta wajen Safwan, saboda a matsayinta na Uwa ta fahimci cewa har yanzu ba wani abu da ya shiga tsakaninsu na auratayya, kuma har ga ALLAH tana son su Hajiyar su ji daɗin zama da Dijen, kamar yanda ta ga ita Dijen hankalinta ya fara kwantawa da su, saboda kyawawan dabi'unta da zata nuna masu su zai sa ta samu matsayi fiye da yanda ta samu yanzu garesu, musamman shi uban tafiyar wanda take so ta zamo tauraruwa a wajenshi fiye da duk wasu mata da zai aura bayanta.


Suna cikin firar ne suka jiyo sallamar Ladiyo, Dije ta yi saurin washe fuskarta da fara'a tace

"Ladiyooo!"

Ladiyo ta zauna kusa da Dijen tana gayar da Inna, sannan ta kalli Dije ta ɓata fuska tace

"Yanzu Dije ki zo garin nan ki kasa zuwa wurina?"

Dije tana dariya tace, "na so zuwa fa Inna ce ta hanani wai......"

Kallon da taga Inna tana yi mata ne yasa ta yi shiru ba shiri, Ladiyo ta zubo da wasu hawayen takaici tace,. "Banga laifin Inna ba tunda har Bala bai ji kunyar karɓar kuɗi a madadinki ba, WALLAHI ki godewa ALLAH ma da bai zamo Mijinki ba, don yanzu haka ba yanda banyi da shi ba akan ya barni in zo in ganki yaƙi baki, yanzu haka ma bai san na fito ba saboda Duduwa bata gidan yana fita nima ta fito abuna"





To fa🙀🤣🤣😂





Akafta😝






D/AUTA Ce✍🏻


*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Ku yi haƙuri da rashin mayar da reply akan comments ɗinku wani lkc amman duk wanda ya yi ina group ɗin na gani duka kuma na gode sosai ALLAH ya bar ƙauna.*




*Lamba ta 41*


Inna ta yi saurin faɗin

"Haba Ladiyo wannan hali ba halin macen da tasan haƙƙin aure bane, don na tabbata ke ma kin san cewa abunda kika yi ba kyautawa bace, saboda haka sawunki a likkafa ki tashi ki koma gidan Mijinki, kuma ki yi haƙuri tunda har bai amince da ki zo ba, insha ALLAHu Dije zata zo har gidan naku sai ku gaisa"

Ladiyo ta miƙe tana matsar ƙwallah tace, "Don Allah Inna ki barta ta zo taje gidan kowa fa ni kaɗai ce bata zo wurina ba"

Inna tace,. "Yi sauri ki je kada ya dawo ya taradda baki nan insha ALLAHu zata zo tunda nace maki zata zo"

Ladiyo ta fice da sauri tana faɗin,. "Sai kin zo Dije ina jiranki kinji?"

Dije ta ce "kar kiji komi tunda har Inna ta bari ai zaki ganni, daman cen don ta ce kada in je ne shiyasa......"

Inna ta yi saurin buge mata baki da bayan hannunta tace,. "Shikenan ke ba za'a yi sirri da ke ba? To ni ba wai bana son ki je bane don wata manufa, tsoron nike ki je ki ɓallo muna wani aikin azo kuma ace ke ce mafari, amman yanzun ma ko da zaki je ban lamunta da inji wata mummunar maganar Bala ta shiga kunnuwan Ladiyo ba, ke shi kanshi ma ban amince da ki tankashi ba idan kin ganshi matuƙar ba gaidashi zaki yi ba"

Dije ta turo baki tace,. "Cabɗi ai WALLAHi Inna ban iya gaidashi lalle ma kam yaji daɗi nai"

Inna ta yi saurin kai mata wani mangari Dije ta miƙe cikin sauri ta bar wajen tana dariya tana faɗin,. "Wai ke Inna yanzu duk abunda Bala ya yi man baki ga laifinshi ba?"

Inna ta ce "ai mu godiya ma ya kamata mu yi masa ba muji haushinshi ba, don ke ma da kina da hankali da kin fahimci cewa hakan da ya yi taimakonki ne ya yi, don in banda shi da yanzu baki je makarantar da kike da gurin zama likitar ba"

Dije ta yi saurin faɗin

"Haka ne kuma Inna in don wannan kuma da wannan gaskiya, shege Bala shine ya ƙi yi man bayani tun farko in zo inyi masa godiya?"

Inna ta maka mata harara tace,. "Ke tafi cen sakarya sai aka ce dole shine zai yi maki bayani ba kece zaki hankalta da abun alkhairin da ya yi maki ba?, To yanzu dai gobe idan ALLAH ya kaimu kije gidan ki gayar da Duduwa har shi ma Balan ki gaisheshi ki yi masa godiya"

Dije ta washe baki tace, "aiko WALLAHi zan yi masa godiyar don na fahimci ba ƙaramin taimakona ya yi ba, yanzu ga shi ta sanadinshi na je birni na shiga makaranta idan ALLAH ya cika mani gurina shikenan sai in zama babbar Likita, kai Balan Duduwa dole ne inyi maka godiya yasin, Inna ko ma in je yanzu in dawo da wuri kafin ayi magriba?"

Inna tace,. "A'a ki dai bari sai goben yafi"

Haka ko aka yi goben tana yi bayan ta yi wankanta Inna ta ce ya saka tufafinta waɗanda suka fi kowane kyau cikin kayanta, sannan ta ɗauko kuɗi sababbi yan ɗari bibbiyu cikin waɗanda Hajiya Mama ta baiwa Dije wai ko da zata kasa idan ta buƙata, tace da ita ta je da su ta baiwa Inna Duduwa ɗari huɗu ta baiwa Jummala ɗari shida, ta ɗauko dubu ɗaya guda biyar ta ce idan ta ga Balan ta bashi ta ce ya yi cefane, sannan ta yi masa godiya, cikin hikima Inna ta dinga koya mata yanda zata yi da abunda zata faɗa, aiko Dije ta riƙe komi a kanta tana harda.

Sai ko ga Lanti da Mune sun zo suka taka mata suna ta yaba irin kyawon da ta yi, sai taɓa lesin da ke jikin Dijen suke yi suna jinjina kyawonshi, Mune ta kasa haƙuri sai da ta ce

"Lalle Dije ke kam kinji daɗi kin tako arziƙi wannan gayun haka ai ko birnin ma iyaka kenan"

Dije ta washe baki ta ce,. "Ai wannan ba komi bane idan kuka ga waɗanda aka saka man cikin kayan lefena"

Lanti da ta yi tagumi ta ce,. "Kinji daɗinki ke kam amman ko wannan ai ba ƙaramin kyau ne da shi ba"

Haka suka yi ta zuzuta Dije suna ƙara koɗata tana jin kanta a sama har da wani canza tafiya tana yanga kamar bata son taka ƙasa, har suka je gidan basu daina wasata ba.

Shigarsu gidan kai tsaye ɗakin Duduwa ta nufa, cike da fara'a Inna Duduwa ta fara tarbonta tana faɗin

"Lale marhabin da mutanen birni sannunku da zuwa, ashe muma zaki zo ganinmu? da har na fara yiwa Gambo ƙorafin rashin zuwanki ashe kina hanya?"

Dije ta yi ɗan murmushi tace, "eh daman ina da ƙudurin zuwa mu gaisa, yanzu kuma ga shi na zo na wanke laifina"

Duduwa zata yi magana sai ga Ladiyo aguje ta shigo tana wasar baki tana faɗin

"Sannu da zuwa Dije ashe da gaske kece kika zo?"

Dije tana dariya ta ce

"Nice kuwa ba wata ba to ya kika ganni"

Ta yi wani rawa da ido tana kallon kanta Ladiyo tace,. "Ai Dije ko kamshinki kawai aka ji ai ansan ke ɗin mai tsada ce balantana anyi arba da kyakkyawar fuskarki, ke ma da kanki kinsan kinyi kyau masha ALLAH da ke, ki godewa ALLAH birni ya karɓeki WALLAHi"

Duduwa ta miƙowa Dije kwanon faraufaraun da ta haɗo mata tace,. "Karɓi ki jiƙa maƙoshinki kar ki biye wannan uwar surutun"

Dije ta karɓa tana dariya ta ɗan kurɓa kaɗan ta miƙawa Lanti kwanon, tana goge bakinta da hankacif ta buɗe zif ɗin jakarta ta ciro ɗari biyu guda biyun ta miƙawa Duduwa tace,

"Gashi a siye goro Duduwa"

Duduwa jikinta yana rawa saboda tsabar farin ciki ta karɓa, sai zubawa Dije godiya take yi tare addu'a ba ƙaƙƙautawa, ƙarshe ma sai gata da ɓugewa da yiwa Dije kirari sai kace wata mabanya.

Dije ta riƙo hannun Ladiyo da ke ta wasar baki tace, "muje ke kuma inga ɗakin naki Ƙawata"

Ladiyo cike tsakanin jin daɗi ta ƙanƙame Dijen tana tsalle suka shiga sashen nata da aka keɓe da katangar da ta raba tsakaninta da Duduwar.

Dije tana zama Ladiyo ta fara jero mata kayan ƙurasa kala kala waɗanda suka haɗa da danginsu, Fara, kwai da kwai, ƙamƙam, ɗantamatsitsi, hanjinligidi, da soyayyiyar aya, saboda su ne sana'arta da take saidawa, Dije kam duk da kwaɗayinta gaba ɗaya ba abunda ta ci saboda jan kunnen da Inna ta yi mata, ganin haka yasa Ladiyon ta zuzzuba mata kowane a leda ta baiwa Lanti ta riƙa mata, sannan suka ci gaba da fira na ɗan lokaci kafin ta fiddo kuɗinta itama ta bata, Ladiyo cike da jin daɗi take ta yi mata godiya, sannan ta miƙe tana yi mata sallama Ladiyon ta rakota bakinta bai daina yi mata godiyar ba, Duduwa ma ta biyota sai godiya take yi mata sai gashi ko suka yi kiciɓis da Balan, yana ƙoƙarin zagayeta ya wuce don yi yayi kamar ma bai ganeta ba, Dije ta faɗaɗa fuskarta da fara'a tace

"A'a Malam Bala abun ba ko magana?, Ai sai ka tsaya mu gaisa ko?"

Bala ya fara sosa kai yana faɗin, "a'ah Dije ce? ai ban ganeki ba naga kin zama wata babbar Hajiya shi yasa"

Dije ta yi masa wani kallo tace, "ai dole in zama Hajiya Bala saboda ina tare da alhazawan, nan gaba kaɗan ma zan zo yi maku sallama idan zamu ta fi Saudiyya, ai dole ne in yi maka godiya akan abun alkhairin da ka yi mani, na gode sosai ALLAH ya ƙara lafiyar aljihu"

Ta saka hannu ta ciro kuɗin a jaka tace,. "Ga wannan ba yawa a ƙara ayi cefane"

Bala da gaba ɗaya kunya ta kasheshi cikin muzanta yace, "Da kin barsu kawai ai don har yanzu da sauran na cefanen"

Duduwa ta yi masa wani mere tace, "da dai ka karɓa don kada ta tafi ka dawo kana cizon yatsa"

Bala ya sosa ƙeya yace, "Ayi haka? "

Dije ta mazge tace

"Karɓi kawai ai an zama ɗaya Bala idan basu isa ba ka faɗa kawai sai a ƙaro maka ai, don insha ALLAHu zakkar da za'a badawa idan an tashi ka tsimayi zuwanta, ko don saboda Ladiyo ai ba'a rabu ba ana tare"

Bala ya zura hannu cike da jin nauyi ya karɓe kuɗin, ya fara godiya Dije ta ce

"Ai Ni ce da godiya WALLAHi na gode sosai ALLAH ya biyaka ya saka maka dai dai da taimakon da ka yi"

Duka suka rakota har bakin gida sai godiya suke zubawa, har ta yi nisa Bala ya biyota cike da ladabi ya rusuna yace

"Afuwa nake nema nasan nayi maki laifi ki yi haƙuri ki yafe man don ALLAH"

Dije ta waigo tace da shi

"Zan yafe maka kuma zan ci gaba da kyautata maka matuƙar ka riƙe Ladiyo amana, ka kyautata zamanka tare da ita kuma ka gyara halayyarka ta son kuɗi ka daina kiranta ɓarauniya, sannan ka gyara duk wata mu'amalarka da ita, to da ka yi hakan ka ɗauka cewa tamkar ka sami alkhairina da na Maigidana ne, amman muddin na ji cewa baka zama da ita yanda ya da ce to ka ɗauka tamkar ka datse igiyar alkhairanka garemu ne, saboda haka idan ka gyara ka ga da kyau a aljihunka, idan kuma ka ɓata to shikenan ka lalace komi, ni ka ga tafiyata kuma ka sani zan saka masu kula da komi, don kada ka ga bana nan to ina da idanuwa ta ko'ina a garin nan"

Bala baki washe ya ce

"Ai Insha ALLAHu alkhairi ma zaki ji amman itama zan turo ta wajenki ki ja kunnenta akan abubuwan da take yi mani, da ta gyara shikenan matsala ta kau gareni da yardar Allah"

Dije tace, "tace wannan ba damuwa bace sai ta zo kawai ALLAH ya sa mu dace dai gaba ɗayanmu ya bamu zaman lafiya"

Yace "Ameen Ameen ranki ya daɗe ai ke kin haye saura mu kawai"

Dije ta so ta yi dariya ta mazge tace, "kai m ka kusa hayewar matuƙar na dawo garin nan na ji labari mai daɗi"

Bala sai duƙe ɗuke yake yi yan faɗin, "kar ki ji komi insha ALLAHu komi zai daidaita"

Haka suka rabu Dije sai ƙumshe dariyar da take cinta take yi, su Lantin ma sai da ta basu ɗari biyu tace su raba, suka tafi gida suna ta jin daɗi.



Hannuna ya yi sanyi yasin😩





Akafta😆




D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*INA YINKU ALL MY FAN'S INA GODIYA🙏🏻 DA ADDU'ARKU GARENI KU DAƊE KU YI LASTING MUTANENA👍🏻*



*Lamba ta 42*


Dije kam tana cin kayan ƙwalam ɗin tana kyalkyatar dariya, tana baiwa Inna labarin abunda ya faru don ko da su Baffah suka dawo gidan ranar labarin ne kawai take ta basu ana dariya.

Haka Dijen ta ci gaba da ziyarar yan uwa da abokan arziƙi don har wani ƙauye suka je da Inna inda ainahin tushen iyayenta suke, kowa ya yi sambarka da auren Dijen don kuwa su ma sun sheda ta sanadiyyar tsarabar Dijen da Inna ta kai masu.

Satinta biyu dam a ƙiriu Direban da ya kawota ya zo ɗaukarta da uwar tsarabar ƙauyensu niƙi niƙi suka lula yola, bayan tasha kukan rabuwa da Inna da sauran ƙawayenta da yan uwa da abokan arziƙi, kowa da kalar tsarabar da ya bata ta kaiwa surukarta Hajiya Mama, don Maigarin kanshi galan ɗin manshanu lafiyayyen suya ya bada akai masu, Baffah da Inna kam babu ce kawai basu bayar ba don tsakanin tsintsiyar laushi, kuka, daddawa, guro, kayan yaji maburki, busasshiyar rama, gero, dawa, wake, niƙaƙƙen garin waken na ɗanwake lafiyayye, manja, manƙuli, soyayyar gyaɗa, kai kayan ƙwalam na Ladiyo ma ba'a barsu a baya ba, don kuwa kaf maƙulashenta sai da ta yo wa Dije tsarabarsu saboda takanas Bala ya bada kuɗi aka haɗa mata kayan.

Tafiyar wuni biyu ce ta kai Dije Yola cikin tsananin galabaita saboda rashin sabo da tafiyar, Ba Surry da Hajiya Mama ba har Fiddo kanta sai da ta nuna jin daɗin dawowar Dijen, saboda himilin kayan tsarabar da ta zo masu da su, Hajiya Mama baki har kunne sai godiya take zubawa saboda tsananin jin daɗin karamcin da su Baffah'n suka yi masu.

Kasancewar hutunsu Dijen ya ƙare kwananta biyu a gidan aka yi mata provision ta koma makaranta, ita kanta cike take da ɗokin ganin mutanenta sis Aysha da kuma ƙawarta Hannatu, saboda sunyi kewar juna ba kaɗan ba.

Kwanci tashi asarar mai rai sai ga Dijen Baffah ta shiga jerin sahun kowace mace a duniya, don kuwa ranar farko da ta fara ganin baƙon watanta duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login