Showing 102001 words to 105000 words out of 136985 words
ɗigon pinck a jikinshi, an mata ɗinkin half bubu ta ji aiki sosai a gaban rigar, sannan ga ɗaurin ɗankwalin da suka yi mata irin na wayayyun ƴanmata, sai gata da fitowa sharri! Masha ALLAH sai pics ake yi mata tana jin kanta wata shegiya, sannan su ka ta yi tare da ƙawayenta suna iya shegensu, duk da ita kam ƙarfin hali ne kawai ta ke yi tana wayancewa cikinsu ana ta sharholiya.
Bayan sun yi break ne Safwan ya zo suka gaggaisa tare da yi masu godiya akan ɗawainiyar da suka yi, sai dai da yawa wasu daga cikin ƙawayen nata sun ƙyasa sosai akanshi, wasu ma har kwatantawa suke yi ina ma ace sune suka sameshi, wasu kuma suka ga gaskiyar Zee da ta nace sai shi duk cewa shi kanshi Aminun ba abun kushewa bane, amman ko kaɗan ba za'a haɗashi da Man ɗin Zee ba, saboda Safwan ƙosasshshen ingarman namiji ne cikakke mai cikar haiba ta ko'ina, saɓanin Aminu da yake siriri sosai sai dai daga ganinshi zaka gano cewa shima jarumin gaske ne.
Bayan fitarshi ne Zee ta samu keɓewa da wasu amintattun ƙawayenta biyu Ruma da wata Sadiya, inda ta sanar da su irin abunda Safwan ɗin ya yi mata, Ruma ta yi shiru sannan ta ce
"Ke fa mace ce don haka ki bi shi da taki kalar salon kissa don ki samo kan Mijinki, saboda irin wannan renin hankalin WALLAHI ba kowa ce mace ce zata iya jura ba gaskiya, don ance yana son Matarshi ai ba sai ya nuna maki ba tunda dai ke ma ɗin yanzu Matarshi ce, don ko an ƙi ko an so ke da ita duk matsayinku ɗaya a wurinshi, to cin zarafin kiran sunanta a gabanki na minene?"
Sadiya ta yi saurin faɗin
"Wa ya ce matsayinsu ɗaya? Don Allah ki daina ragewa Zee martaba Rumasa'u, ai ko makaho ya shafa Zee ya shafa waccen matsiyaciyar Uwargidan tashi duk da bamu santa ba WALLAhi kinsan Zee ta fita nesa ba kusa ba"
Ta dafa kafaɗar Zee da ta yi tagumi tana saurarensu ta ce, "ke mrs Man buɗa kunnuwanki da kyau ki ji Ni, WALLAhi ki zage damtse ki fatattaketa da kyau a zuciyarshi don ke ma ki sami matsugunnin da ya fi na kowa a wurinshi, in ba haka ba WALLAhi kina ji kina gani zata ƙwace maki mijin ta barki da cizon yatsa, kallarki da kyau mace har mace son kowa ƙin wanda bai samu ba, don haka ta ƙarfin tsiya ke ma ki mamaye ko'ina na zuciyarshi, ke in da hali ma kada ki bari ko kaɗan ta raɓeshi ki kama abunki ki riƙe gam gam tunda dai ba wani abu aka fiki da shi ba, kyau kuɗi iya soyayya da hali mai kyau kowane ALLAH ya baki ai, saboda haka ya rage naki ki ƙwaci Mijinki tun kafin kwaɗo ya yi maki ƙafa kina ji kina gani, don WANNAan tsadadden mijin naki ko wace mace a duniya tana son irinshi idan zata samu"
Ruma ta yi ƙarfin halin cewa "Haƙiƙa kam tun kafin ki aureshi ƙanwarshi da kanta ta sanar da ni yana bala'in son Matarshi, saboda haka Ni ina ganin tunda har karatu aka ce tana yi me zai hana ku tattara ku bar ƙasar ku koma school abunku ke da shi, kin ga daga cen sai ki cusa masa kanki ta yanda ko sunan wata mace ma ba zai so a faɗa ba bayan ke, kin ga duk lokacin da ku ka dawo ba wani power da ita waccen matar tashi zata fi ki a wajenshi, saboda kin riga da kin mallake komi dole ta yi haƙuri don kin fita a wurinshi, tsorona ɗaya ne kada ace itama sai ta biku kun je tare, don a gaskiya idan aka yi maki hakan za'a wargaza komi"
ZEE ta yi saurin faɗin
"Ba ma za'a je da ita ba WALLAhi, haka kawai in dai ba salon mugunta ba ai tun cen tare aka ganmu ita kuma tana nan, To yanzu kuma akan me za'a ce ta bimu? lalle ma ai WALLAHI da taga rashin mutuncina kuwa don sai nasa ta dawo gidan ubanta ba shiri, saboda sai na nuna mata cewa ita ƙaryar asirin farauto zuciyar miji take yi, da salon Soyayyata zan sakashi ya manta uwar da ta haifeshi ma ballantana ita ƙaramar ƴar iska"
Ta ƙare maganar cikin huci, Sadiya ta dafa kafaɗarta ta ce
"Cool down Zee Sani wannan faɗan fa duk mai sauƙi ne idan kin so ki sauƙaƙawa kanki shi, yanzu dai miji a hannunki yake to ki yi iya ƙoƙariinki wajen ƙwamuso abunki ya dawo hannunki, Saboda ke ce amarya mai sabon muhallin shiga har ana ihu musamman idan kina gyara jikinki, to ko uwarshi kika ce kada ya kalla bai isa ya kalleta ba bale wata aba kishiya cen, wadda idan kika so cikin ƙanƙanin lokaci zaki saita mata hanyar zuwa gidan ubanta ba tare da ta shiryawa zuwan ranar ba"
Daga Zee har Ruma suka ƙyalkyale da dariya har da su shewa, ZEE tana dariya tace
"Daɗina da ke ƙawata baki da sanya, WALLAhi tunda har ya tsiro da wannan renin hankalin to Ni kuma sai na nuna masu cewa ba a banza aka haifoni duniya ba"
Haka suka yi ta zuga Zee tana hawa tare da sanar da ita wasu salon kissoshi da bata san da su ba, sannan aka yi masu sha tara ta arziƙi suka tattara yanasu yanasu suka koma Gombe, tare da yi mata fatar zaman lafiya da mijinta.
****
Amarya Zee kam sannu a hankali ta dinga nutse Angonta cikin tafkin kogin ƙaunarta, saboda ko kaɗan bata gajiya da buƙatarshi akan hakan ta sami matsayin da ko kaɗan bata yi tsammani ba, saboda salon kissar da ta mamayeshi da ita wadda ko kaɗan bata nuna masa jin haushinta akan damuwar rashin Dijen da yake yi, illa ma haƙurin da take ba shi duk da har lokacin bata san asalin labarin ba, saboda ta tafi ne kawai a zuwan makarantar da take yi ne baya so a sanadin hakan ta haifar masu da matsala, shiyasa ya shiga irin wannan damuwar ta yi amfani da damarta ta saka shi nanuƙe mata kullum, saboda ba laifi ta tsayu da kyau wajen gyara jikinta a ƙokarinta na son fin kowa a wurinshi.
Bayan sati biyu da aurensu ne suka yi sallama da kowa suka kama hanyarsu ta zuwa London, zuciyar Zee cike da jin daɗin ganin Safwan ɗin ya zama nata ita kaɗai kuma mallakinta, saboda ko kaɗan Hajiya Mama bata nuna cewa sai an tafi da Dijen ba, don ganin yanda Zee take ta rawar kai da Safwan ɗin, kuma ta fi son duk lokacin da Dijen zata dawo gareshi ya zamto itama ta zamo mace dai dai da kowace mace mai ji da kanta, wanda a lokacin ita da kanta zata ƙwaci ƴancinta a hannunshi ba tare da ta nemi taimakon kowa ba.
*****
Dije kam tun tana damuwar rabuwa da su Hajiyar tare da kewar Mijinta har ya zamo ta saki jikinta ta fara zuwa Makarantar da aka sakata ta fara daga class five waton ss 2 wadda ta zamo jeka ka dawo ce kullum da mota ake kaita a dawo da ita, babu inda take zuwa daga gida sai makarantar sai kuma idan zasu je yawon buɗa idanuwa wurin shaƙatawa kala kala ko kuma idan zasu shiga shaguna siyayyarsu ko ta gida, sannu a hankali idon Dijen Baffah ya fara buɗewa ta fara jin kanta itama wata aba ce mai daraja, musamman idan ta ga ta yi wanka ta sade cikin ƴaƴan Aunty Ummin ba wani banbanci sai fari da zasu nuna mata, don idan ma aka ce za'a tantance take yanke za'a ce ta fisu, saboda cikar ƙirjinta da suka ƙara fitowa ɓul ɓul ga kuma hips ɗinta da ya buɗe tare da tudun duwawunta masu gantsarwa da suka turo, don ko hijabi ta saka dole ne ma sai sun fito ballantana tana cikin shigar ƙananan kaya, fatarta ta murje sosai sai sheƙi take yi haka ma jikinta ya mulmule ta ko'ina ba rama.
Ga cima irin ta yangayu da take ci ga zama wuri ɗaya da hutun ya ratsa jikinta, tubarakallah masha ALLAH Dijen Baffah kam, don kuwa duk mai son mace ya ganta ya zo ƙarshen nema.
Duk da jin daɗin da take yi hakan bai hanata yin kewar Mijinta ba, don kuwa lokaci zuwa lokaci tana tsintar kanta cikin wani sabon yanayin buƙatuwa da mijinta, amman dole take ɓoyewa don bata son Aunty Ummi ta ganota, sai ga shi watarana tana dawo wa daga school ta taradda wayar Aunty Ummi tana ta ɓurari soke da caji, ta ɗauka ta nufi ɗakinta bata nan ta dawo ɗakinsu Husnah babbar ƴar Aunty Ummin da nufin ta tambayesu ita, suka sanar da ita ai ta fita wataƙila mantawa ta yi da wayar ta fita ta barta, sai ga kiran ya katse aka sake bugowa Husnah ta karɓi wayar tana ganin numbar ta gano Safwan ne, cikin dariya ta miƙa mata wayar ta ce
"Aunty Khady ki ɗauka mana maybe uzurin babba ne shiyasa ake ta kira"
Kasancewar number ce kawai ba suna shi yasa ta yi saurin ɗauka ba tare da ta ce ƙanzil ba ta ji ya ce
"Plss Aunty Ummi don ALLAH ki tayani roƙon Hajiyarmu ta dawo man da matata WALLAhi a takure nake sosai da rashin sanin inda take, don ALLAH Aunty ki ce ta bani matata WALLAhi buƙace nike da ita kamar in kuwata"
Dije ta yi saurin cire wayar a kunnenta ta goge kwallar da ta sauko mata ta miƙawa Husnah wayar cikin sanyin jiki ta fice ɗakin ta nufi ɗakinta da aka ware mata ita kaɗai, Husnah ta bita da kallon tausayi ta kara wayar a kunnenta saboda maganar da yake ta yi yana kiran sunan Aunty Ummin cikin magiya, cikin wata muryar tausayawa dukansu ta ce
"Auncle Mummy bata nan ta fita idan ta dawo za'a sanar da ita ka kira"
Cike da jin haushinta ya ce, "uban wa ya ce ki ɗauki wayar kin san bata nan?"
Ta yi saurin faɗin
"Sorry Auncle....."
Kittt ya kashe wayar cike da jin haushinta, Husnah ta sauke wayar ta yi shiru tana nazari sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Dijen, sai dai kukan da ta ji tana yi ne yasa ta yi saurin isa wurinta tana faɗin
"Plss Aunty Khady ki yi haƙuri ki yi shiru ki sanar da ni abunda kike wa kuka, Ni kuma insha ALLAHu zan taimakeki ko don ki sami farin ciki"
Da ƙyar ta shawo kanta ta yi shiru sannan Dijen ta miƙe zaune tare da share hawayenta ta ce, "kin yi alƙawalin ba zaki faɗawa kowa ba?"
Husnah ta yi mata kallon tausayi ta ce, "ki faɗa kawai Auntynmu ni nace da ke zan taimakeki in dai hakan zai sakaki farin ciki"
Dije ta ce
"Ya zanyi in dinga communicate da Auncle ɗinku ba tare da ya gano ni ce ba?"
Husnah ta yi shiru sannan tace, "ki bani yau zuwa gobe zan samo maki number'rshi da yake using da ita yanzu, ke kuma sai a buɗa maki whassapp ki dinga yi masa magana a ɓoye amman fa plss kada ki bayyana masa inda kike, har sai lokacin da Hajiya Mama ta sanar da shi da kanta, don WALLAhi Mummy tasan da Ni a wannan lamarin kinsan zan ci Ubana ne a hannunta"
Dije cike da jin daɗi tace "na amince My Husny don ALLAH ki taimakeni WALLAHI da kinyi man haka kin gama man komi don sai naji daɗi sosai, kuma kin ga ke ma ai zaki sami lada"
Husnah tana dariya ta ce "ai naji haushin da wayar Mummy take da security na fingerprint WALLAhi da yanzun nan zamu samota"
Dije ta dafe goshi tace
"Ai shiyasa ma kika ga bana taɓa wayar Aunty saboda ba abunda zaka iya yi da ita idan ma ka ɗauka"
Haka suka yi ta shawarwarinsu har dare lokacin da Aunty Ummi ta yi bacci, sannan Husnah ta je ta lallaɓa ta saka yatsanta da ta yi lock ɗin da shi ta cire securityn, sannan ta yi saurin shiga wayar ta ɗauki number'r Safwan a wayarta ta ajiye wayar ta fito cikin sanɗa, sannan ta dawo wurin Dijen da ke ta tsumayin jiran fitowarta, kai tsaye ta bata numbar ta yi saving a wayarta, sannan ta nuna mata duk yanda zata yi da yanda zata shiga da fice cikin whassapp ɗin, sannan ta yi mata sai da safe ta shige ɗakinsu.
Dije kam cike da tsananin farin ciki ta shige nata ɗakin ta dantse, sannan ta haye gado cike da murna ta fara shiga contacts list ɗinta sai ga number'r Safwan ta fito raɗam tare da hotonshi da ke dp, inda ya sha ƙananun kaya sun fito da kyaunshi sosai sai dai ƴar ramar da ya yi, amman duk da hakan sajenshi da ɗan ƙaramin gemunshi sun ƙawata fuskarshi gwanin burgewa, ya fito bafulataninshi na usuli mai cikar zati tare da tarin kamala da ke tattare da fuskarshi.
Dije ta yi zooming hoton sosai tana shafo fuskar sannan ta kai bakinta ga hoton ta yi mai kiss ba shiri ta rufe fuskarta tana dariya alamun jin kunya, sannan ta shiga ta fara yi masa sallama, aka yi dace yana online amman bai kula da ita ba ma balai ya duba yaga ko wace ce, saboda ganin baƙuwar number Kuma daga Nigeria, don in da sabo ya Saba da gayyar mata da maza masu son cuso kansu gareshi ta ƙarfin tsiya, shiyasa bai cika damuwa ma da ire irensu idan ya gani ba, Dije kam ganin bai amsa ba yasa ta sake turo masa emoji na kuka mai ɗauke da ƙwalla kamar haka😢ta sake ce wa
_Salam!_
Amman nan ma shiru cike da jin haushi ta shiga gallery ta Ciro wani pic ɗinta Wanda daga ita sai guntuwar t.shirt baƙa ba ɗankwali sai dai ta yi cropping ɗinshi ta cire fuskarta ta bar ƙirjinta kawai tare da jelar gashinta da ta sauko a kafaɗunta har gaban ƙirjinta, sai da ta tabbatar da hoton ya shiga sannan ta yi offline zuciyarta cike da jin daɗin ganin photonshi.
Dijen Baffah banda jan rai hwa🙄
Akafta😝
D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Na gode sosai da addu'o'inku gareni i luv u all my guys💋*
*Lamba ta 60*
Sai dai ƴan mintuna a tsakani ta kasa haƙuri ta dawo abun haushi har lokacin bai duba ba, cike da takaici ta kashe datar ta kwanta abunta tare da ƙarewa pic ɗinshi da ta ɗauka kallo, haka ta kwana cikin begen Mijinta tare da mafalkinshi kala kala.
*****
Malam Safwan kam sai da ya kammala uzurin da ke gabanshi zuciyarshi ta ƙawata masa duba sauran text's ɗin da ake turo masa da numbers mabanbanta, cikin nasara ya kawo kan na Dijen Baffah cike da mamaki ya bi massages ɗin da kallo
_Salam_
_😢_
_Salam_
Sai hoton da ta turo wanda idonshi a kan dukiyar fulaninta da suka cika ƙirjim fam kamar za su fasa rigar su fito, ba shiri ya haɗiyi wasu yawu da suka tsinke masa, sannan ya sake yin zooming ɗin pic ɗin haka kawai ya tsinci kanshi da faɗin
"I like it"
Amman a zuciyarshi ya ce _ita kuma wannan wacece take son janyo hankalina da abunda na fi so a jikin mace??._
Haka kawai ya ji ya kasa ɗauke kanshi daga pic ɗin sai ga shi da tsintar kanshi cikin wani yanayi marar misaltuwa, cikin wata kasala da ta sauko masa ya mayar mata da reply kamar haka
_wslm plss wace ce?_
Sannan ya kashe wayar yana ta ƙarewa pic ɗin kallo duk da wani sashe na zuciyarshi yana yi masa kashedi da kallon pic ɗin, kuma ta shawarceshi akan ya goge hoton sai dai kuma ya kasa baiwa zuciyarshi haɗin kai, saboda ba ƙaramin kyau suka yi masa a ido ba.
Dije kam ko da safiya ta waye tana gama SALLAHr asuba ta janyo waya ta duba cike da zumuɗi tare da fatar ya ga massages ɗinta, ai kuwa sai ga shi ta ga ya duba har da su reply, cikin rawar jiki ta mayar masa da amsa kamar haka
_"Am the one how was the day??"_
Sannan ta sake ɗauko wani pic ɗin wanda daga ita sai rigar bacci mai siririn hannun vest, ga shi ko bra babu a jikinta sun fito sosai masha ALLAH ta yi crop ɗinshi ta cire fuskarta, sannan a ƙasan photon ta rubuta
_Good morning my life partner._
Sannan ta sauka ta nufi kitchen ita da su Husnah da wasu ma'aikatan gidan biyu suna shirya abun break fast, Bayan sun ƙare ne ta dawo ɗakinta da nufin yin wanka, amman zuciyarta ta ƙawata mata ta duba ta ga in ya ga saƙonta, sai dai ganin bai hau online ɗin ba yasa ta yi saurin shigewa toilet domin ta yi shirin zuwa school.
Dije har ta je makarantar ta dawo tunaninta yana kan wayarta, saboda son ganin wane saƙo ne ya turo mata, aikuwa cike da ɗoki ta duba wayar sai ga reply ta gani kamar haka
_"Idan ba zaki buɗe fuskarki ba kada ki sake yi man magana"_
Cikin daburcewa Dijen ta yi shiru tana nazari sannan ta yanke wata shawara ta sake ciro wani photon wanda ta yi daga ita sai wata doguwar riga half gown ta kanti da wani wando skin tight baƙi, inda ta juya gefen fuskarta kawai ya fito don gaba ɗaya ma bayanta kawai aka ɗauka sai gefen fuskarta ga gashinta ya zubo har gadon bayanta, sannan a ƙasanshi ta rubuta
"Good bye"
Aka yi da ce shima yana online saboda ya kasa natsuwa zuciyarshi sai hasko masa fuskar Dije take yi a matsayin mamallakiyar photon, shiyasa ya ce idan ba za'a turo fuska ba kada a sake yi masa magana saboda kawai ko wacece ta bayyana kanta, sai ko ga shi wannan photon da ta sake turo masa na ƙarshe ya tabbatar masa da lalle Khadijarshi ce, saboda ko a mafalki ya ga gefen fuskarta sai gano ita ce bale a ido biyu, sai dai kuma kokwanton da ya ke yi akan anya zata iya aikata hakan gareshi,sai ga shi da tsintar kanshi cikin wani tsantsar farin