Showing 231001 words to 234000 words out of 244033 words

Chapter 78 - AJIYA A DUHU COMPLETE

11 Jul 2025

75251

Harda su system Winsa ta aiki duk ya tattara ya haWe dana Daddy sannan ya fito. Sashen Hajiya Basariyya yaje, ya taSa ?ofa a rufe nan ma, sai ya zagaya ta kitchen, bawan ALLAH sai zufa yake, cikin sa'a nan a buWe yake. Aiko ya shiga, kai tsaye bedroom Winta ya shiga. Ita kam bai san inda take ajiye abubuwanta ba sai da yasha wahala sosai kafin ya gano, aiko kaf ya tattaro harda sar?o?in ?anensa na gwal da nata, da takardun kaddaririnta da take tun?aho da su. Dana yaranta dan Daddy duka yayansa babu wanda bai mallakawa takardar fili ba da anan gaba zai amfana da shi. Sai da yay mata kat sannan ya shiga Wakin ?anensa nan ma yay kaca-kaca da shi sai dai bai samo komai ba sai takardunsu na makaranta, dan Hajiya Basariyya bata barin komai a hannunsu. Daga nan sashen Ammie ya nufa, can dai tako ina a kulle dan Sakina sai da ta rufe ko ina saboda tsoron halin Nazeerah sannan ta wuce. Harta window ya gwada shiga amma bai samu dama ba dole ya ha?ura ya siWaWa sashen Hajiya Yaya. Kai tsaye Wakinta ya nufa, tana barci motsinsa ya sakata farkawa. Da farko firgita tayi, sai da ta kunna fitila taga shine sai mamaki ya kamata. Ta shiga yimasa magana cikin faWa, kawai yazo yasa abu ya Waure mata baki, itama ya Waureta a jikin gado. Yanda hankalin Hajiya Yaya ya tashi ALLAH dai ya kiyaye zuciyarta bata bugaba. Dan ita kam a gaban idonta ya tattare komai da komai nata dana ?a?anta kasancewar yasan inda suke kuma itama bata barin yara da su anan take adanawa yay ficewarsa ya barta a Waure. Cikin matu?ar takaici ya hararari sashen Ammie da bai samu nasara ba. Sai kuma ya nufi sashen su Hameed. Tsaf ya hargitse komai amma bai samu ko atm ba kam ya fito cikin takaici. Babban Nazeerah ya kira yace gasu duk ya haWa, sai dai Ammie ta kulle sashenta nata ne kawai babu. Duk da Babban Nazeerah yaji takaici sai yace ba komai fito ka kawo min ina waje. Haka Yazeed ya buWe gate ya fita. Babban Nazeerah kam yana nan a mota yana jiran nashi, yayi mamakin samuwar komai cikin sauki dan bai san haka aikin zai zamo ba ai da tuni ya saka Yazeed Win yayi an wuce wajen. Koda ya amsa kayan sai ya amshe har wayar Yazeed. Sannan ya kallesa cikin gargaWi.
? ? ? ??  Kaga idan za'a kasheka kace nine na sakaka ka kawo min abubuwan nan sai na wulakanta rayuwarka. Ka Wauka bama ka taSa sanina a rayuwarka ba har abada. Kaje zan nemeka bayan na gama dubasu na tantance masu muhimmanci, zan saka kai min signing a Wanda kake da damar haka dan nasan kaine next of king na ubanka. Wanda kuma bakai bane Waya bayan Waya zan sace ku kuyi min signing. Na gama da ubanka kuma sai next, gidan Darma bye .
? ? ?? Yazeed kamar robot haka yayma Babban Nazeerah godiya ya juya cikin gida.......

??
? ? Tir?ashi>?? nama rasa abin faWa>?z?

________&
? ? ? ?
? ??? Dangin Mamy sune suka fara shirin wucewa. Koda sukazo yima Oum sallama kamar yanda ta saba ta haWa musu alkairi mai yawan gaske. Cikin su Ajwaad babu wanda ta gani tasan kowa na barcin gajiya. Balle ma Babban Yaya da Fawzan bai yiwuwa a kirasu, ya kamata a basu damarsu. AA ne ma mai Wan dama-dama yau dan haka ta shiga kiran tashi wayar....
? ? ? ?? Da ?yar AA dake rungume da Maanal ya iya buWe idanunsa ya Wauka wayar. Badan ringtone Win Oum bane ma bazai Waga ba. Shiyyasa ma shi yafi yarda da saka waya a vibration koma a silent gaba Waya saboda bai ?aunar damuwa. Wannan wayar ce kawai yake bari a buWe da Wan ring ?asa. Jin yanda yay sallama murya a sha?e Oum ta ce,  Oh sorry Auta baka tashi ba ne kaima .
? ? ? ?  Oum an gaji ne shiyyasa, amma yanzu na tashi ina kwana .?
? ??  Lafiya lau, ya Baby .
 Lafiya lau Oum ta tashi normal kamar yanda Uncle ya faWa .
? ?  To Alhamdullahi ALLAH ya kiyaye gaba. Dama ba?ine zasu wuce ya kamata a nema musu mota mai ?yau, nima banyi zaton tafiyar wuri zasuyi haka ba .
? ? ??  Okay Oum suyi ha?uri su jirani bara na Wanyi wanka.
? ?  Okay tom sai ka fito .
Ta faWa tana yanke kiran. Tana yimusu hakane dan su san muhimmancin dangin Mamyn a wajensu. Kuma Alhamdullah hakan yana yin tasiri sosai. Dan ita dai Mamyn ba damuwa tai ta sakasu suyi masu alkairin ba. Sai Maman Saheeba kawai da Aunty, Maman Saheeba Win ma tafi ci. Suko wannan itama Wan bata da yanda zata yi ne take yarda ana nuna su a ?an uwanta saboda talakawa ne. Idan ma sun yi musu alkairin idan ta amsa sai ta gadama take basu, gara ma Wan rabon azumi tana basu abinda ya samu sauran ta rabama wanda take so...

? ? ? Tunda ya fara wayar Maanal ta farka. Yana ajiyewa ta buWe idannunta. Dama barcin dole aka sakata bayan ya gama yamutsata, amma ita barci safe a yanzu dai sam bayinsa take ba. A hankali ya hure idanun data zuba masan. Sai ta lumshesu ta sake buWewa. Da muryarta ta barci ta ce,  Waye ya kira? .
? ? ? Cikin raWa yace,  Oum. Wai ba?i zasu tafi, nasan ?an jigawa ne ?an uwan Mamy .
? ? ?? Wai ?an uwan Mamy, ita dariya ma ya bata. Amma sai batayi ba itama cikin raWan tace,  Kai banda kai? . Kumatunta ya Wan matsa, bakinta tada cuna masa ya ?ara dan tsukewa waje Waya kamar yara na shagwaSa. Yay murmushi da sumbatar bakin ya ce,  Sarkin fassara zance ni bance ba . Idanunta ta Wan juya zuzu sai kuma ta murmusa tana janye hannunsa dake matse mata kumatu, sai ta kai yatsarsa cikin bakinta ta ciza kaWan .
? ? ??  Ouch! Besty wace mugunta ce haka? .
? ?? ?ar dariya tayi kaWan.  Sorry, ALLAH kawai jinai ina sha'awar in cijeka. In gani wajen yayi jini . ?in bata ta gani yayi sai ma ya Soyeshi yana Sata fuska. Ita kuma ta hau dariyar ?eta tana ?o?arin kamawa da tsiya. A haka suka rikice da ?ar kokawa, ta dage sai ta gani shi kuma ya?i. Ta koma saman jikinsa. Sai kawai ya shiga yimata cakulkule tana dariya sosai shima yanayi. Sai da suka gajiyar da kansu kowa idonsa ya ware daga barcin sannan ya Wauketa suka wuce bayi suna dariyar ?asa-?asa. Sun Wan jima kafin suka fito, dan a bayin ma ba'ai wankan kai tsaye ba. Da taimakon juna suka shirya. Sunyi ?yau kamar ka sacesu ka gudu. Ga wani sirrikan ?amshi mai ratsa zukata. Shi ya fara fita ita kuma ta gyara Wakin sannan tabi bayansa....
? ? ? ?? Ta sami su Umma a falo suna breakfast harda Ammienta da su Hajiya Basariyya, sai AA zaune a dining yana waya RK a kusa da shi yana shan abu a kofi shima. Oum na daga tsaye. Zuwa Maanal tai ta fara gaishe da su Umma sannan ta je ta rungume Oum. Cike da shagwaSa tace,  Oum yunwa cikina kamar anmin sata .
? ? ? Cike da kulawa Oum ta shafa kanta tana murmushi, yayinda RK ke mata dariya. AA kam kallonta yake kawai yana wayarsa. Oum da kanta ta haWa mata abinci, ta zauna tana ci AA ya kammala wayar yana kallonta yanda take cin abincin da sauri-sauri, sai kuma ya Wauke kansa ya maida ga Oum.  Oum su shirya gashi nan zuwa. Gashi babu kash a jikina na kuWi dole zan fita na samo .
? ? ?? RK yace masa nawa kake so? FaWa masa yayi. Shi kuma ya jefa masa key yana faWin,  Za'a samu a motata ka duba .
? ??  Yauwa thanks you Uncle .
?  Munafuki, ka dai nema Uncle Winka bani ba .
? ?? Murmushi AA yay yana tashi ya fice. Maanal da Oum kuma na musu dariya.........
'?



*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ?ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =??=?O?_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*

*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*


______________

......Koda AA ya Wiba kuWin a motar RK sashen Mamy ya nufa. Ya samu duk sun kammala shiri jira kawai suke. Ya gaishesu da girmamawa, tare da godiyar ?o?arin su sannan ya basu ha?uri na jinkirin daya sakasu. Yace ga wanda zai kaisu nan zuwa. Aunty ya bama kuWin yace ta basu. Aiko sunata godiya da sanya albarka. Tare da addu'ar zaman lafiya su da iyalansu. AA da addu'ar tasu tai masa daWi ya amsa da Amin yana mi?ewa da tambayar ina Mamy. Dan bata a falon. Shine aunty Babba tace masa tana Wakinta. ?an jim yay na mamaki, sai kuma baice komai ba ya haura saman. A falo ya samu Maman su Saheeba da Nuratu suna magana. Suna ganin shi sukai shiru. Shima kallo Waya yay musu ya wuce abinsa ko gaida Nana baiyi ba. Cike da takaici ta bishi da kallo, dan ta fahimci Wan iskan yaron nan fa ya daina gaisheta yanzu. Nuratu kam tamkar mayya haka take kallonsa zuru, wani irin sonshi na ratsa mata zuciya da Sargon jiki, jitake kamar taje ta rungumeshi wlhy....
? ? ? Knocking ?ofar Wakin Mamyn ya Wanyi, ta zabura daga tagumin data zuba abin duniya ya isheta. Musamman maganar Sille dake tsaye a ranta. Tana son ta?i bashi kuWin tana jin tsoron yazo ya mata tonon silili gida cike da mutane. Ko bai ce komai ba wani ya ganshi ya shigo mata ai sai ma ai mata wani zargin daban, balle gashi da suffar tantirai. Jin an ?wan?wasa ?ofar sai da gabanta ya faWi, sai ta dinga tunanin ko Sille Winne ma. Yana ?ara kwan?wasawa ta dirgo a gadon jikinta har rawa yake ta buWe kofar. Sai sukai ido biyu da Ajwaad. Wata irin ajiyar zuciya mai nauyi data bashi mamaki ta sauke. Sai kuma ta juya ta koma ciki. Bin bayanta yay ajiyar zuciyar tata na tsaya masa a rai. Koda ya zauna a cikin sofa sai da ya sake kallonta. Sai ramarta ta fito masa sosai yau a idanun. Gaisheta yay cike da kulawa, ta amsa masa sama-sama. Ya ce,  Mamy baki da lafiya ne wai? .
? ? ?? Shiru tai masa, kusan minti Waya sannan tace,  ?alau nake miya kawoka? .
? ? ? Shiru ya Wanyi jimm. Sai kuma ya girgiza kai da faWin,  Babu komai, kawai nazo gaisheki ne na kumayi sallama da ba?i da sukace zasu wuce .....
? ? ??
&&
? ? ? ? A nan sashen Oum kam bayan ficewar AA a bisa tsautsayi Nuwaira ta Wakko naman kai da taima RK farfesu dan yana sonshi, kawai tana gamawa sai ta Wakko tukunyar gaba Waya ta fito da ita ta ajiye a dining Win tana faWin,  Yauwa to Yaya naman kanka yayi . Maanal ta tsaya cak da cin abinci, Ammie dake daga falo ma tana jin furucin Nuwaira sai da ta Wan juyo ta kallesu, dan tabbas tasan in dai hasashensu gaskiya ne, kuma irin Waukar cikinta Maanal tayi to akwai matsala dan bata shiri da naman kai da soyayyan ?wai. Aiko tunanin nata bai kai ?arshe ba Nuwaira na buWe tukunyar ?amshin naman ya wani bigi kan Maanal dan anyi rashin sa'a ta inda take iskar ke kaWawa, ai da wani kalar sauri ta mi?e tana mai sakin spoon Win hannunta jikinta har rawa yake nason barin wajen. Duk kallonta sukai, Oum tai ?o?arin ri?ota tana faWin,  Subahannallahi Baby lafiya? Kuwa .
? ? ? ? Kai Maanal ke girgiza mata, idanunta sun wani kaWe sunyi jazur lokaci guda. Tana buWe baki zatai magana kawai sai amai.
? ??  Ya ARRAHIM .
Oum ta faWa tana ri?ota dan neman zubewa take ?asa. Duk mikewa su Mah-mah sukai suma suna nufo dining Win, Ammie kam ta fuske kamar bata san mike faruwa ba. Sai dai zuciyar nakan Maanal, dan tasan yau kam zata Wan Wana kuWarta, dan in ba sa'a akaci ba sai tai kwanaki tana jin ?yan?yamin abinci. Dan zatai ta tuna wannan ?amshin naman ne. A farkon ciki da wahala ka gane mata dan bata wani laulayi ko ciwo da sauransu, sai yawan barci da shagwaSa da neman rigima da bu?atar miji a kusa da ita matu?a, kamar dai yanayin Maanal. Amai ko wani zubar da yawu duk batayi. Sai dai duk randa taji ?amshin naman kai ko soyayyan ?wai babu zaman lafiya. Sai tai kwanaki tana fama. Sai ciki ya shiga irin wata bakwai Win nan take fara WanWana kuWarta. Bazata sake lafiya ba sai kuma ALLAH ya rabasu.
? ? ? ? Yanda Maanal ke amai kamar zata zubo da kayan cikinta waje sai da tabama kowa tausayi, ga kuka tanayi da faWin,  Wayyo Oum zan mutu sai wani ya sake yun?urowa sai ta rirri?e Oum Win. Gaba Waya hankalin Oum ya tashi jitake kamar tai mata kuka. Shi kansa RK duk ya daburce kamar ba likita ba. ?amshin naman dake shiga mata hanci yana hawar mata kai yasa aman ya?i tsayawa, su kuma kowa bai fahimci ?amshin naman ne bata so ba. Kamar ya tsaya Oum ta kamata ta mi?ar sai ya ?ara bugarta, ai da sauri ta koma ta sake du?ewa. Sai lokacin ne Ammie dake daga falo har yanzu bata taso ba tace ma Aunty Sharifah matar Uncle Modibbo.  Wannan naman ne ke sata aman, idan ta daina jin ?amshin zata bari .
? ? ?? Aiko cikin haushi Gwaggo Khadijah da taji Ammien ta fara mata faWa. Murmushi kawai Ammie tai ta ce,  Ayi ha?uri Gwaggo .
? ? ? ?  ?yace fa haka, dan rashin tausayi yarinya na wahala kin san miye matsalar sai kiyi shiru saboda ALLAH Asiya. Sai kace wata ?ar fari. Auta ce fa. Kawaicinki yayi yawa ALLAH sai kace wata bafulatana .
? ?? Ammie dai murmushi kawai tai bata sake cewa komai ba. Ana kuwa Wauke naman Maanal ta daina jin kanshi ta daina yun?urin aman. Sai dai tayi laushi gaba Waya ta zube a jikin Oum tana sauke wahallen numfashi ga hawaye sun?i su tsaya. Dai-dai nan AA ya shigo, dangin Mamy biye da shi zasuma Oum sallama. Ganinsu sun tattaru waje Waya yace,  Lafiya? .
? ? ? ? Meeno datai kwale-kwale kamar zatai kuka tace,  Yaya Auntyna ce keta amai .
? ? Yasan Maanal take cema auntynta. Gabansa ya faWi ya bi ta gefe ya shigo inda Oum take ri?e da ita tana hawaye da ri?e ciki. Gaba Waya idanun AA ya rufe, ita Win kawai yake gani cike da tashin hankalin halin daya ganta a ciki. Gabansu yazo ya tsugunna ita da Oum Win, fuskarsa na bayyana matsananciyar damuwa. Inte na gyara wajen da Maanal Win ta Sata. ?amshinsa kawai taji, sai ta Wago daga jikin Oum dake shafa mata baya kamar yanda RK yace a mata ta kallesa. Sai ta sake fashewa da kuka ta ce,  Besty cikina.
? ? ? ? Gaba Waya shima idonsa ya kaWe, ya ri?o mata hannu sai kawai ta shige jikinsa ta ?an?amesa tana sakin sabon kuka. Ina shi wlhy yama manta da wani batun iyaye a wajen, ya ?an?ameta idanunsa na sake juyewa. Yanda take kukan cikinta-cikinta yasa RK faWin,  Ajwaad Wauketa muje ciki ina zuwa . Ya fita da sauri. AA Win kuma ya mi?e ya Wagata cak. Sama ya nufa da ita bedroom Win Oum. Kukan da take na kekketa masa zuciya. Ammie ta girgiza kai kawai a zuciyarta tana ayyana (Indai haka za'ai renon cikin kowama zaiji jiki a gidan naku kenan).
? ?? Hajiya Basariyya ta kalla Maman Yaseerah, Maman Yaseerah ta kalleta, gulma fal cikinsu da hassada. ?asa-?asa Maman Yaseerah tace,  Tab Win, wannan fa daga gani ciki ne . Sosai gaban Hajiya Basariyya ya faWi, har taji ta gagara iya cema Maman Yaseerah komai.
? ? ? Bayi ya wuce da ita, da taimakon Oum suka Wauraye mata fuska da baki dan bata Sata jikinta ba. Kafin ya sake Wakkota suka dawo Wakin ya sata a gado, yanda ta?i yarda tabar jikinsa dole ya zauna a gadon shima tana a jikin nashi. A haka RK ya shigo, allura ya haWa ya bama AA yay mata. Sai kuma ya haWa wani Wan madaidaicin drip da wasu alluran. Da yake ba tsoron allura take ba lafiya lau akayi, shima ruwan AA Win ya saka mata a hannu bayan ya Wiba jinin da RK Win ya bu?ata duk tana lafe a jikin nasa. A hankali ciwon cikin ya fara raguwa sai kuma jikinta ya fara saki sai barci. AA dai na faman ri?on hannunta dan karta tunSuke ruwan. RK kuma ya mi?e yana faWin zaije asibiti ya dawo dan a gwado jinin.
? ? ? ?? ALLAH sarki ana gayoma su Abah suka taso suka fito, a karo na farko na tarihi yau Baba Sardauna da Abbu, da Baba har bedroom Win Oum sun shigo a dalilin Maanal. Sai yanzu ne AA yaji Wan nauyi dan gaba Waya Maanal Win a jikinsa take kwance. Oho su Baba Sardauna babu ruwansu,? cike da kulawa da nuna damuwa suke mata addu'a. Mamy ma dai dole ta fito jin gasu Baba Sardauna can a sashen Oum Win. Tsoron kar Abah yay mata wata ?ullatar dole ta fito tazo dubantan itama. Kamar an saita sai ga RK ya dawo abinka da masu abu yana zuwa asibitin abinda ya dace yayi. Yanda yake wani makirin murmushi yasa Uncle Mahmud yin magana.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login