Showing 30001 words to 33000 words out of 61296 words

Chapter 11 - NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE

10 Sep 2025

6003

matsalolinmu dan Allah." Banza nayi mishi da ƙyar ya iya nasarar shawo kaina na faɗa mishi abinda ya faru" Shiru yayi kamar ruwa ya cinyeshi yana riƙe da kumatunshi. Amman naga ranshi ya ɓaci ainun har jijiyoyin goshinshi sun tsaya.
"Yanzu kayan suna ina, ina shi Lekan ɗin?" Cikin rawar murya nace.
Kayan suna hannun Baban Nazifi, Lekan kuma Yaya Harisu ne ya koreshi." Numfashi ya ja dogo yace.
"Ina zuwa ki goya Kahinde da Taiwo zamu fita."
Gwadabe na kirayi sunanshi da gaggawa, kulawa ma yabawa dan ko juyowa bai ba. Ina zaune a bakin gado da goyo a bayana, sai na soma jiyo maganganu sama sama ina jiyo tashin muryoyi daga tsakar gida. Ni dai ban ko yi yinƙurin miƙewa ba, hayaniyar sai ƙara tsananta take yi, jin kamar ana titirniyar dambe ne yasa na fito da gudu, aikuwa ƙafafuna suka harɗe na faɗi rib cikina da Manana suka daku da ƙasa. Take wasu hawayen wahala suka wanke mun fuska. Abunka da mai ƙiba sai fa da dabara na miƙe ƙafata naji ta nai mun mugun zafi, a haka na daure na fita. Da'u Gwadabe ya damƙa yake ta kai mishi mahangurɓa, Yaya Harisu na riƙe da Gwadabe ta baya yana jayeshi, Ɗan fodiyo na riƙe da Da'u ga Auwal a tsakiya yayi musu iyaka. Baban Nazifi kuwa yana gefe yana sharce hawaye Yaya Haula tana rarrashinshi kamar wanda jaki ya kada shi da ƙasa. Su kuma matan gidan suna cure waje guda da yaransu maza da mata.
"Ni zaka duba ka ce matata ɓarauniyace, me aka kamata ta sata da za a ci zarafinta ita da ɗan uwanta? Kaya kuma ga kuɗin rigarki Haula ku bamu kayanmu" Ban san Gwadabe na da zuchiya haka ba sai yau. Ƴan uwanshi suka rufu a kanshi da zagi da cin zarafina. Baban Nazifi ne ya jefo mana bugun kayan ya sauka a ƙirjina tab, ba da ban ina da ƙiba ba da sai na faɗi. Yaya Haula kuma ta fisge kudin hannun Gwadabe.
"Gobe_gobe ku tattare yanaku _yanaku ku bar mun gidana, tunda ba da uwa da uban Iyabo aka haɗa kuɗi akasai gidan ba. Ku kuma ko wacce ta koma ciki ta ja ƴaƴanta"
"Kullo ɗakin mu je mu dawo kinji Iyabo?" Ya faɗa yana haki. Da ɗingishi na koma na kullo ɗakin muka fita. Amman fa har muka isa gidanmu babu wanda yace da wani komai. Acanma mun shiga mun samu kab matan gidan da samarin gidan a tsakar gida Iyaa tana ta faman kwakwaso da sababin abinda ya abku. Ai muna shigowa ta dira a wuyan Gwadabe da zagi, har kakan kakanshi sai da ta zaga. Mahaifiyata ta kaɗa kanta ta shige ciki, Gwadabe ya miƙo mun buhun kayan na shiga ɗaki na sameta, na baro Gwadabe na ba iyaa haƙuri amman kamar ƙara ma zigasu yake yi. Ina jiyo sanda Iyaa Kokodeen ta koreshi shima waje. Da ƙyar mahaifiyata ta yarda ta karɓi kayannan, shima sai ajjiyewa nayi a gefenta. Ina gunjin kuka na nufi hanyar waje. Muryarta na rawa tace.
"Jabu ki yi ma mijinki biyayya. Muddin shi yana ƙaunarki kar ki sake wannan rikice_rikicen banbanci ƙabila da aketa gwabzawa kice zaki kaso aurenki. Ko beyerabe kika aura ba tsira zaki yi ba. Dan a ƙarƙashin ko wacce igiyar aure akwai ƙalubale, in kika ji na wasu naki ba komai bane. Kice ina gaisheshi bamu samu damar gaisawa ba" Kasa amsata nayi na fice ina dingishi, a ƙofar gida na tad da Gwadabe idanunshi sun rine sosai. Haka muka rankaya gida, a daren dai ɓarawon baccine ya kwashemu muka wayi gari da labarin Baban Nazifi yace dukkansu zasu tafi Takai akwai meeting da za'a gabatar. Ni dai har Gwadabe yai mun sallama ya fita ina sharar hawaye. Ga ƙafata ta aune ta yi him. Tsabar ɓacin rai Gwadabe bai ga ƙafarba bai san ƙafar ta samu rauni ba. Haka na wuni ni dai sukuku ba laka, ƙafa fa kafin la'asar ta sake hayewa da ƙyar nake takawa. Ina zaune akan kujera ina kirɓa sakwara sai ga ƴan Takai sun yi sallama. Gwadabe na ƙura ma idanu sai naga har ya faɗa. Yana isowa ya cafe taɓaryar a ƙoƙarinshi na ganin ya kore damuwar dake cin ranshi. Ya hau dukan sakwara a turmi, dan da nan ya kammala tsab. Durƙusawar da zaiyi ya taya ni kai filas ɗin abinci ciki, sai yaga ƙafata a kumbure.
"Me ya samu ƙafarli ta aune haka, kuma kike zaune kina aiki? A'a taso muje maza_maza" Babu shiri muka fice a gidan.
"Ɗan iska na mamaji" Cewar Baban Nazifi kenan. Ashe targaɗe naji a idanun sawuna, mai ɗori ya gyara mun muka dawo gida. Bayan sallar isha muna zaune muna cin abinci yke bani labarin yadda akayi a takai.
"Abun babu daɗi. Babala dama kinsan sai dai ma ta daɗa kwaye mun baya, gashi Goggo Iyatu tana nan mahaifiyar Laila, itama tai ta kunnawa abun wuta. Mun tsaya akan dukkan abinda ya ɓace a gidannan kece kika sace kuma ni zan biya. Wallahi nayi iyakar yina dan in fahimtar dasu fur sunƙi. Ni dai roƙon da nake yi miki kiyi taka tsantsan kuma ki iya takunki, kisa ma Laila ido sosai, kinsan na faɗa miki ƙasurgumar ɓarauniyace." Kuka na fashe dashi.
Kana nufin a haka zanci gaba da zama tare da kai anai mun kallon ɓarauniya, harma duk abinda aka nema aka rasa sai na biya? Gwadabe haƙurina ya ƙare ni na...."
"Kul kika bari mala'ilun Allah su yi fishi dake, Allah yayi fishi dake. Iyabo wallahi dukkan wannan abun so akeyi a samu a ukun da da kanmu zamu ji mun haƙura da junanmu, abinda suke so kenan. Nayi duk iya iyawata in kare ki, abun yafi ƙarfinane bazan tsaya ina jayayya da Yaya Hambali ba, domin uba ne, a kafaɗunshi muka girma, Balle kuma Babala da goggo Iyatu. Kiyi haƙuri ni zan dinga biyansu duk abinda suka ce an sace musu."
Ya batun korarmu kuma da Baban Nazifi yayi, ba gara mu bar gidan ba, tunda in bana gidan ba mai cewa nayi sata?" Kanshi ya dafe kafin a tausashe yace.
"Babala tace ko bayan rants bata yafe ma duk wanda ya bar gidannan ba. Ashe Yaya Hambali da Yaya Harisu sun sai gidajen su Malam Audi, da gidansu Baturiya, wata mai kamawa ma za'a soma aikin fashe katangun a haɗe gidajen. Kinsan bikin Nazifi da Laraba ya ƙarato, nima fa duk yau nake jin labari. Nazifi zai zauna a cikin gidannan da matarshi. Itama Laraban a cikin gidannan zata zauna. Ai kinsan Ilum ɗakin Goggo mai Yaɗiya ko? To shi zata aura, Yaya Hambali zai ɗaukeshi aiki a kasuwa. Ni dai Iyabo abinda nake so dake shine kar ki sake fita tsakar gidannan sai in fita daga gidan zaki yi, ko ban ɗaki zaki shiga. Su girki, wanke_wanke wanki duk kiyi a ɗakinki, kiyi haƙuri damo.."
MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

NAMA YA DAHU...
ROMO ƊANYE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI


Lamba ta tara (9)




"Kinga can wajen tudun?" Gwadabe ya nuna mun da hannunshi. Wani dan tudune karami akayishi a falon kamar wajen cin abici. ( Daining )Amman bashi da girma, a wajen na saka kayan kallona.
"To ki fito da kayan kallon gobe zan siyo miki teburi da dirowar da zaki dinga zuba kayan abinci a ciki. Zaki dinga amfani da risho, ke ko gawayinne in kika kunna a ƙofar ɗaki daya ruru ki shigo dashi, ki sa labule wajen ya zama miki kicin. Iyabo bana so ki sake fita na kuma na jajjada miki. Kiyi haƙuri wata rana sai labari. Ki daure wallahi ba'a sona haka ke faruwa ba, naso mu bar gidannan muyi nesa da ƴan uwa Kuka babu irin wanda banyi ba, washe gari kuwa sai ga Gwadabe da tebur, da durowarshi gajera ta kicin ɗin ƴan gayu. Tare muka jera kayan tukwanena da ɗan kayan abinci da nake dasu, har randunana a cikin wajen na jera, Gwadabe ya hau ya kafa mun labele, Laila sai zirga_zirga take yi tsakanin tsakar gida da ciki. Bai fita ba sai da ya ciccika mun randunanan da ruwa tab, kana ya fice kasuwa. Ni kuma na shiga aikace, aikacen gidan. Bani na fita tsakar gida ba sai da na gama komai nawa na fito da ruwa bokiti uku na sheƙar a rariya, bokitin dana shake shi da wanki na fita dashi na je maƙota na shanya. Ina dawowa na yi komawata ɗakina.
Haka al'amuran rayuwar su kaci gaba da gudana yau fari gobe tsumma.
A kwana a tashi, gashi yau mun wayi gari jama'ar Takai suna hanyar shigowa Kano. Gidan namu shaƙe da matan anguwa suna ta faman taya mu aikace_aikacen biki. Dan Yaya Haula hantsice leƙa gidan Kowa, babu gidan da bata shiga, kowa a layinnan ya santa. Gida ya ɗau fenti, ga girma da gidan ya ƙara, sakamakon gidaje biyu na jere damu da Yaya Hambali ya siya, aka rushe katangun gidan ya ƙara girman gaske, kuma yasha gyara sosai. Ɓangaren Amarya Laraba da Ango Nazifi ya sha gyara na musamman. Wajajen la'asar sai ga ƴan Takai sun iso Bus biyu su da gayyar yara raɓe_raɓe, gida ya kacame da hayaniya, amman nifa babu wanda yazo daidai da ƙofar ɗakina . Washe gari aka shiga biki ka'in da na'in. Ranar ɗaurin aure tun duku_ duku muka game jallof ɗin shinkafa, da tuwon shinkafa, harda masa. Su Gwadabe kuma suka kama hanyar Takai dan acan za'a ɗaura auren kasancewar duk haɗin gidane. Ko akwatin Amaryar Nazifi baa'a kaiba, ance in aka kawota sai kawai a miƙa. Akwatuna masu taya suna nan a ɗakin Yaya Haula, ina dai gani matan waje sunata shigowa kallon kaya. Ni ko da nake gidan babu wanda ya neme ni da in zo in ga kaya, nima ban ɗaɗa kaina ba. Bayan azahar maza ƴan ɗaurin aure suka dawo tare da bataliyar maza ƴan Takai. Da yamma lis kuma sai ga jerin gwanon tsofaffi da Amarya an tawo da'iya. Harda Sakina aka tawo, suma sun sha ankonsu na Takai. Muma duk mun ci namu ankon na cikin gida, shaddace mai ruwan toka na iyaye, sai wani yaɗi haka na ƙawayen Amarya dai. A haka taro ya watse, duk da ina kaffa _kaffa sai da Yaya Halima ta ci mun mutunci a cikin mutane, daurewa nayi na shanye dan a ranar ma Takai zasu komai. A dangina babu wanda yai mun kara yazo, Uwani ce dai na matsama bata da yadda zata yi shi yasa tazo.
A kwana a tashi asarar mai rai. Wasa wasa ƴan biyu shekararsu guda, har suna dabo, Toye kuma yanata zuwa makaranta. Fitinar gidanmu kuma babu abinda ya ragu sai ƙaruwa, dan sau huɗu Gwadabe na biyan kayan da aka sata. Na huɗun ma har ƙarƙashin kujerata akazo aka saka mun, da suka shigo bincike suka zaro. Nayi imanin Laila ce ta aikata mun hakan ba kowa ba, dan tuggu da munafurci iri iri take haɗawa, tsaraicinta da aljanun ƙarya fa babu abinda laila ta dena, a wannan shekara guda ɗin abubbuwa masu dama sun faru. In baku mance ba nace ina yaye ƴan biyu zan bar gidan, to maganar tana ɗamfare a zuchiyata. Ga zawarawa kullum a cikin sallama da' Laila suke, tare da kawo mata ƙwalam da maƙulashe, amman mayyar tana kan bakarta ita sai Gwadabe. Gwadabe ne yaita bani haƙuri nima ganin na kusan yaye in barshi ma baki ɗaya shi yasa ma ban yi tafiyata ba na haƙura na zauna, na cire damuwar kowa da komai a raina.
Kamar wasa wata ranar juma'a sai ga Oga Lurwanu shi da karen motar Gwadabe sun riƙo gwadabe ko iya taka ƙafarshi bayayi, suka shinfiɗe mun shi a doguwar kujera.
"Gashi nan kin ganshi, mota ya shiga, amman wallahi sai zaro shi akayi ƙafa taƙi takuwa. Muna kyautata zaton sammu akayi mishi. Dama in dai a raba mutum da kafa ko hannune a harkar tuƙi ba kanshi farau ba. Sai ku dage mishi da maganin gargajiya" Hannu na ɗaura aka ina kuka, shima Gwadabe kukan yake yi yana girgiza mun kai halamar in yi shiru.
"Ki gode ma Allah ma, da ba haɗarin mota akasa yayi ba ya ragargaje ba. Dan shima anayi kana tsaka da tuƙi sai kaga zaki ko kura, kana ɗauke hannunka magana ta ƙare. Wasu kuma teku suke gani a gabansu duk sai su dibibice" Ni dai sai mamaki da tsoron sha'anin mutan Duniya duk ya kamani. Nera dubu biyar ya ajjiye mun.
"Mu kam zamu koma Gwadabe Allah ya ƙara sauƙi"
Su kai mana sallama suka tafi. Kifewa a jikinshi nayi ina kuka kamar fitar rai.
"Iyabo ki yi ta mun adda'a Allah zai bani lafiya, ta Allah ba dai ta mutum ba. Ni na ɗauka wannan jarabawace ubangijina ya jarabceni dashi. Bazan ɗaura hakkin akan kowa ba Allah yana madakata yana ji da ganin kowa. Ki yi ta mun adda'a. Kafin in amsa shi Yayyen nashi su kayo sallama suka shigo. Baban Nazifi yace.
"Gwadabe haka abun ya faru? Ni ina kasuwa ma shigowata kenan mata suke sanar dani wai an shige da kai a hannu baka tafiya, haɗari ne ya afku kome? Koma dai menene Allah ya kyauta gaba. Ke bamu waje ko?"
Ya juyo yana mun kallon tsana, ƴan biyu na kwashe dan kar su damu Babansu. Ina daga uwar ɗaki na kira Iyaa nake sanar mata halin da Gwadabe yake ciki. Halin ko in kula ta nuna, tsaki ma tayi ta kashe wayarta, sai Burodami kokodeen da Burodami Debisi na kira na sanar musu, sai ƙawar arziki Uwani. Su Baban Nazifi sun daɗe sosai a falon kafin daga bisani suka tafi, ni da yaran muka fito.
"Iyabo inaso zan ɗaura alwala, gashi ina jin fitsari ma. Zaki iya kuwa?" Murmushi nayi ina hawaye lokaci guda nace.
"Ai ko ɗaukarkane kacokam zan iya mijina. Nice a haƙƙu in yi maka duk abinda kake da buƙata" Miƙewa nayi na kai yara uwar ɗaki na kulle, falonma na kulle na tawo da ƙaton po mai murfi, cikin dabara na zamo Gwadabe izuwa kan po ɗinnan. Yayi fitsari na mai tsarki, na sake mayar dashi kan kujera. Daga ni har shi sai muka fashe da kuka na faɗa jikinshi.
Allah kenan mai yin yadda yake so da bayinshi. Mutum ya fita da ƙafafuwanshi amman yanzu jibeshi a kwance, abunda yafi ƙarfi yanzu ya fi ƙarfinshi. Su Baban Nazifi daya kamata ace su zasu mai duk wannan amman kowa ya tafi ya barmu.
Gwadabe kayi haƙuri kuka ba namu bane fa. Akwai Allah shi zai yi mana sakayya. Ka rungumi ƙaddararks sai Allah ya kawo maka ɗauki. Zaka warke bi izinillahi rabbi"
"Iyabo ki duba dangina jinina yanda suka nuna halin ko in kula da abunda ya sameni, babu wanda ya tambayeni ko ina jin wata lalura. Yanzu ko Da'u da ba sai ya zauna ya kula dani ba?"...
A'a Gwadabe kar ka ɗaura musu nauyin da ba nasu ba. Ni ya kamaci da in jinyata maka. Karma ka sake tada wannan zancan. Ga bawo kayi alwala." Shi da kanshi yayi alwala ni kuma na wanke mishi ƙafafuwanshi.
Gwadabe ka daure in kai ka kan gado kaji, sai kayi zamanka acan. Yanzu nan anjima kaɗan Laila zata tashi kwanciya."
"Ba zaki iya kaini ba Iyabo, ki je ki kira Da'u ko Nazifi ɗayansu yazo ya kaini, ko du su biyun." Bana so in mishi musu da To" Na amsa mishi, na fita da po ɗin da yayi fitsari na zubar, sai da na mayar ƙarƙashin gado sannan na je kiran Nazifi da Da'u tare da sanar dasu saƙon dake tafe dani. Abun mamaki ko da suka kinkimeshi su biyun dukkansu sai mitar yayi nauyi suka dinga yi, ƙafarshi ɗaya ma basu kama ba sai janta su kai kii. Ni ko ina durƙushe ina hawaye har suka fice ina kuka. A wajen su Yaya Haula suka shigo suka sameni idanuna sun ƴi luɓu_luɓu dasu.
"Ohh ni ƴarnan mutum ba a bakin komai yake ba, yau_ yau ɗinnan Gwadabe ya zama musaki sai an kwantar sai an tayar. Sannu Iyabo kinji sannu" Kalmar musaki data faɗa ya dafani sosai.
"Kaimu muje mu yi mishi sannu ko. Laila sai ki kwashe kayanki ki ko ɗakin su Halima da Ƙauwama sai ki koma kinga ƴan zuwa dubiya zasuita sunturi kuma dole falo za'a dinga fito dashi" Ni dai gaba nayi suka biyoni. Suka gama gaisheshi suka fita. Ni kuma ina gefenshi ina tofa mishi adda'a a ƙafar tashi, shi kuma yana kallon silin yayi wani irin sanyi"
"Iyabo kinga irin riƙon wulaƙancin da Da'u su kai mun? Kinga yatsan ƙafata ya fashe. Daga kwanciya lalura yau _yau harna soma fuskantar wulaƙanci, sai kace ba ciki ɗaya muke ba. Wannan ƙiyayyar dame tayi kama, ki duba fa yanda su Yaya Hambali suka zo suka dubani wallahi babu damuwar komai a fuskokinsu, sai cewa su kai nima karambanine yasa na shiga sana'ar da bani da ilimi a kanta. Wai sana'ar hatsari gareta." Hawayene suka gangaro daga idanunshi izuwa fuskarshi. Rarrashinshi na dinga yi, a ƙoƙarina na ganin na faranta mishi rai, wala Allah ya samu sassauci. Ruwan ɗumi na zuba a bawon na tsoma tsumma na ɗan gargasa mishi yatsan nashi da yake jini. Ya samu yayi sallah, na bashi abinci a baki da kaina, ina bashi ina sake yi mishi nasihu masu ratsa jiki, akan ya gode Allah ma da ba hatsari yayi yaji raunuka masu yawa ba, da izinin Allah muddin muka dage da adda'a koma sammunne Allah zai bamu nasara, amman zuwa gobe zamu je asibiti.
"Babu ko ficika a jikina Iyabo, kuma kinga asibiti sai da kuɗi Iyabo"
Haba Gwadabe, zan siyar da atampopina in samu ɗan kuɗin da zamu riƙe a hannunmu, mu gode ma Allah muna da abinda zamu ɗaga mu siyar ma. Ina zuwa da zafi_zafi akan daki ƙarfe. A zabure na miƙe na shiga zaro atamopin sunan ƴan biyu, kala goma na fitar na zuba a bako.
Gwadabe bari in je shagon me sai da atampopinnan ta bakin titi yarenmun nan, bazan jima ba, ga yara a falo" Ban tsaya jin abinda zaice ba na fice, sai dai kunsan mutane in suka ganka cikin matsuwa ka fitar da abu zaka siyar, sai su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login