Showing 51001 words to 54000 words out of 61296 words
tafe dani taji amman ta ƙi ya" Yaya Hamma ya dubi wannan matashin, ya dubi Daso wacce ta turɓune fuskarta kamar bata dariya.
"To jeka zata zo yanzu. Kuma ni Hamma na baka damar zuwa zance wajen Daso Manga daga yau kuma yanzu. Daso tashi kije Manga zai yi magana dake" Nasan ganin rashin wasa gami da murtukewar fuskane yasa ta bishi ba dan ranta ya so hakan ba. Tafiyarta ke da wuya Yaya Hamma ya ce.
"Bani labarin abinda yake damun zuchiyarki. Nayi miki alƙawarin magance miki matsalar duk girmanta"
A'a Yaya Hamma babu komai. Ni dai inaso gobe zan je garin Kano. Amman nayi maka alƙawarin kwana biyu rak zanyi zan dawo." Da sauri ya kalleni har tsoron da yake son ɓoyewa ya kasa ɓoyuwa.
"Kano kuma, ba dai wajen tsohon mijinki kike son zuwa ba, ko ganin yaranki ba? Kinsan yin hakan a wannan halin da kike ciku ka iya fama miki ciwon dake zuchiyarki" Da sauri na katseshi da cewa.
Ko ɗaya ba abinda zai kaini Kano ba kenan. Akwai wani shiri da nake son in yi ne a can Kanon. In abun ya tabbata kaine mutum na biyu da zan faɗa ma bayan Daso" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace.
"Au ashe Daso ta fini matsayi a wajenki? Sai ta sani kafin ma in sani ko. Nagode" Yanda ya turɓune ƴar kyakkyawar fuskarshi sai ya bani dariya ainun.
Ba haka nake nufi ba. Sabida ita ɗakunmu ɗaya da'itane. Amman kana da matsayi a wajena gaya. Ko tafiyar nan da zanyi gobe babu wanda na sanarma sai kai. Sai mun koma gida zan sanarma da Yafendo" Daɗi yaji sosai, sai kuma naga damuwa ta maye gurbin daɗin.
"Allah yasa ba ƙauyenmu bane ya isheki kike son komawa maraya ba, sai da muka shaƙu dake kike son ki gudu ki barmu da kewa." Daso ce ta dawo ta zauna jagwab a gefena tana rishin kuka.
"Ni Yaya Hamma bana son Manga. Bazan iya rayuwar aure da abokin Chubaɗo ba, gani zanyi kamar naci amanar Chubaɗo ne. Gashi kai kace ka bashi izinin zuwa zance, kuma kab garinnan waye baisan zafin kishin matar Manga ba. Ni ban shirya jefa rayuwata a cikin haɗari ba gaskiya " Dubanta yayi ranshi a bace, ko me ya tuna oho sai ya shiga aikin rarrashinta gami da yi mata nasiha. Mijintane dai ta rasashi har abada, ya zame mata dole yin sabon aure ko ba dan sha'awa ba ko dan tsira da mutunci. Ya ɗaura da cewa.
"Kuma kinsan Baba ba zuba ido zaiyi ya barki kita zama a gabanshi babu aure ba ko. Lokacin da zai matsa miki da fito da miji nake jiye miki, dan in baki fitarba al'ada zata haɗaki aure da wani ɗan uwanki ko kina son hakan, ko bakya so. Ni abinda nake jiye miki kenan. Sannan Manga kab Rugar nan ansan mutumin kirki ne, gashi da yawan shanu, kuma jarumine sosai. Ko wacce bafulatana burinta auren jarumin namiji." Zaman dandalin dai haka muka ƙareshi babu armashi, Yaya Hamma ya mayar damu gida. Muna shiga a daren na sanar ma Yafendo inaso zanje Kano in Allah ya kaimu gobe, kwana biyu zanyi. Sai da ta ɗanyi jim kamar ba zata yarda ba, kamar tana son tambayata Allah ya soni bata tambayeni ba, sai cewa tayi dani.
"Allah ya kaimu goben cikin rayayyu, sai ki shirya da wuri tafiyace mai nisan gaske" Da tunanin tafiyar na kwana a raina harma da mafarkin wai naje amman ban samu Uwani ba sai Hafizu mijinta.
Washe gari tun asussuba nayi wanka. Ina yin sallah na fito da ƴar jakata ta hannu da kuɗaɗena a ciki. Kaya ko kala ɗaya ban ɗauka ba, nayi musu sallama akan zan biya wajen Dada da Boɗdo mu yi sallama. Daso ce ta fito domin yi mun rakiya. Muna fitowa muka ci karo da Yaya Hamma a zaune a bakin wata bishiyar darbejiya yana kallon ƙofar gida yaga yaushe zamu fito. Ba Daso ba ni kaina nayi mamakin ganinshi a wajen. Dan sai da nayi turus. Tasowa yayi ya nufo inda muke.
"Yaya Hamma kaine da sassafe haka a ƙofar gida, zaman me kake yi a wajen?" In ji Daso kenan. Dariya yayi mata kawai kafin yace.
"Tunda dai Allah ya ƙaddari ganawarmu ai shikenan. Babu gaisuwa sai tuhuma ko? Da fatan kun tashi lafiya" Muka amsa a tare, sannan mu ka gaisheshi cikin girmamawa. Gidansu Yaya hamma muka soma zuwa. A ɗakin Yafendo muka zauna, a gurguje mu ka gaisa na sanar mata inaso zanje birni amman kwana biyu zanyi.
"To Allah ya dawo dake lafiya. Hamma sai ka kaita har tasha ka tabbatar motarsu ta tashi kafin ka dawo. Allah ya tsare. Hama da Boɗɗo suna garken shanu kuje ku samesu ko? Ke kuma Daso kizo in kin taso tallan Nono zamu yi magana muhimmiya dake" Kan Daso a sinne ta amsa da
"To Yafendo" A garken shanu muka yi sallama da Hama da Boɗɗo. Sai adda'a su ke yi miki, daga nan sai wajen Dada. Ni da Daso ne muka shiga, Yaya Hamma fur yaƙi shiga yace Baffa faɗane dashi bai fiye son baƙi suna shigar mishi gidanshi ba. Mu ma muna shiga ya taremu harda sanda kamar zai dokemu.
"Kai ku tsaya nan kar ku sake ko taku ɗaya a wajen" Ya faɗa da fillanci, Daso ce ta fassaramun abinda yace. Wannan kalma daya faɗa kamar ance Dada ta fito ta duba sai firit ta fito daga bukkarta. Su Cubu kuma da su Yusufu suna tsakar gidan, suna aikin dafa madara. Da sassarfa ta iso inda yake tsaye. Wallahi ɗaga sandar shi yayi kamar almara sai ya kwaɗa mata a goshinta jini ya yayi tsartuwa har a hijabina" Cikin hargagi yake yi mata magana da fillanci. Hannunta ta dafe da goshinta ta yi saurin juyawa, na fahimci umarni ya bata. Yusufu da Cubu ne suka yi kanta Cubu ta riketa zuwa ƙofar bukkarta.
"Ku je Jabu. Zan dinga zuwa dubaki. Na mancene ban sanar miki ba ya kafa dokar kar ƙafarki ta tako mishi gidanshi" Da yarbanci tayi mun Magana. Ajjiyar zuchiya na sauke ina hango irin yadda sandar ta sauka a goshinta, ba tare da wani babban daliliba, ko da dalili addini ya bada umarnin a daki mace har a zubar mata da jinine? Ko da ma suna da ƙarancin ilimin addini, rayuwarsu a kiwo da tallar Nono take ƙarewa. Ji nayi na sake jin ƙarfin guiwar hukuncin dana yanke dan cire Dada a cikin wannan uƙubar. Hawayen daya zubomun nake shirin gogewa Baffa ya ɗaga sandarshi ya sauke mun a kafaɗata, zafin ya ratsa dukkan ƙasusuwan jikina kau,. Kafin in tantance tsakanin mamaki da tsoro naji Daso tayi ihu ta jani mun rufa waje a guje. A guje muka wuce Yaya Hamma. Sai biyo mu yayi da sauri yana tambayar ba'asin abinda ya haddasa gudun. Daso ce ta bashi labarin abinda muka tarar. Ni kam hawaye kawai nake sharewa ina kallon mayafina da jinin Dadana a jiki, sanadiyyar zuwa ganinta kawai aka zubar mata da jini.
"Jabu kiyi haƙuri. Mu kanmu mun rasa yanda zamu yi mu tsamo Dada daga cikin halin da take ciki a wannan gidan. Amman abinda nake so dake shine dan Allah ki taya ta da adda'a, kuma zan baki shawarar kada ki sake zuwar mishi gidanshi, Dada zata zo har inda kike ta dubaki. Kar hakan yasa in kika tafi ki ƙi dawowa, hakan ka iya jefata a halin da yafi wanda take ciki yanzu. Zamanki tare damu zai iya kawo mata sauƙi sosai, kece babba ke zaki dinga rarrashin ƙannenki, kinga Boɗɗo kullum a cikin kuka da damuwar da Dada take ciki take." Ajjiyar zuchiya na sauke kawai nace.
Babu komai, nagode da shawara. Daso ku koma daga nan ni zan tafi"
"A'a ai kinji abinda Dadanmu tace dan haka har sai na tabbatar da fitar motarku a tasha. Daso ki koma gida ke" A wajen mu kai sallama da daso. Ni dai har muka gama wannan gwajab_gwajab ɗin fita zuwa gari hankalina baya ma tare dani. Wai duk haka Aure yake cike da ƙalubale kowa da irin nashi? Oh ya Allah ka kawo mafita a zamantakewar aure, ya Allah ka ba ma mata mafita. Har muka shiga cikin babbar tashar Adamawa babu wanda yace da wani ƙala a tsakanin ni da Yaya Hamma, dukkanmu sai tubka da warwara kawai muke yi, tare da karanta wasiƙar jaki.
"Fullo Kano ne, ko Kaduna, ko Zaria ga motar Haɗejiya?" Cewar ma'aikatan tashar da suka nufo kanmu har suna rige_ rige.
"Kano zata je, nawa ne kuɗin motar?" Cewar Yaya Hamma, tare da cusa hannu a aljihunshi.
"Nera dubu da ɗari biyu zata biya" Kuɗin ya zaro ya kirga ya basu, ni kuma ya miƙo mun dubu da ɗari biyar. Ƙin karɓa nayi, ya dubeni rai a ɓace yace.
"In baki karɓaba zaki barni cikin damuwa, da kokontan dawowarki rugar mu. Ni kuma dana tuna zaki iya ƙin dawowa, ko zaman rugarmu ya isheki take sai inji fargaba ta dirarmun. Jiya ɓarawon baccine ya ɗebeni shima cike da mafarkai akan tafiyar taki. Ungu kuɗinnan ko tsaraba kya yi musu"
Nagode sosai Yaya Hamma, in sha Allah bazaan wuce kwana biyun ba. Kuma dan Allah ka je ka dubo Dada, ko a ɓoye ne ka kai mata magani, kai mata bayani kwana biyu zanyi" Yaya Hamma bai bar tasharnan ba har sai da ya ga fitar motarmu. Sai da motarmu ta yi nisa sosai na dena hango hannun Yaya Hamma a sama yana yi mun Adabo., ban dena waige ba har sai da na dena hango shudiyar rigarshi, Ajjiyar zuchiya na sauke na lumshe idanuna ina tunano yanda Baffa ya kabɗama Dada sanda. Wannan dalilin ne yasa kullum in zanga Dada sai in ganta cikin rashin guzari da rashin walwala, kullum cike take da tunani. Ta haɗu da azzalumin miji mai kafiya, tallar Nono ya cinye mata lafiyarta da kuzarinta. A shekarunta ya kamata ace tana zaune a nutse yaranta na hidinta mata, ba wai tai ta fita tallar nono, kuma mijinta na cin zarafinta harma da fitar mata da jini. Wallahi da Baffa zai iya amincewa in fanshi tallar Nonon Dada, da tuni na famsheta na zama ƴar tallar Nono kamar yadda ya zama al'adar matan fulani musamman mazauna rugage. Ya zame mun dole in yi duk abinda ya dace dan ganin na kawar ma da Dada Ƙwallar data daɗe tana zuba a idanunta. Gaga_gaga haka mukaita cin hanya, azahar, la'asar sai dab magriba muka shiga garin Kano, a unguwa uku muka sauka, ina fitowa titi na samu Bus har ƙofar layinsu Uwani. Na ko yi sa'a tana gida, tana tsakar gida tana kwasar tuwo Hafizu kuma yana shanya kayan yara a igiya. Tana ganina ta sau marar hannunta ta miƙe a zabure.
"Iyabo kece haka afujajan?" Tana faɗin haka na fashe mata da kuka a tsakar gidan kamar ƙaramar yarinya.
"Uwani jata kuje ciki maza" Cewar Hafizu. Hannuna Uwani ta ja muka shiga ciki, wallahi na fi minti talatin ina kuka take zazzaɓi mai azabar zafi ya rufeni. Uwani da Hafizu suka rufu a kaina suna ta rarrashina da ƙyar na haɗiye kukan nawa bakina na ambaton Allah. Ganin na ɗan samu nutsuwane Hafizu ya fita ya bamu waje.
"Kawata lafiya kuwa kinga yanda ki kai baƙi kika rame kuwa? Gabaki ɗaya kin koma wata ƴar ƙauye, meke faruwa haka?" Cikin shessheƙa nace.
Labarin da tsayi Uwani, amman bari in rama sallolina sai mu tattauna tunda abinda ya kawoni wajenki kenan" Ina gama faɗar hakan na miƙe jiri na kwasheni na fito tsakar gidansu dan kama ruwa da alwala. Uwani kuma taci gaba da aikin tuwonta, ina kan yin alwala yaran Uwani suka shigo gidan da sallamarsu. Matar gidan buɗar bakinta tace
"Wannan wacce iriyar rashin tarbiyyace zaku shigoma mutane gida da gudu, kalan ku zubar mun da miyar da ko kayan ɗakin uwarku in an siyar bazai siya miyar ba?" Yaran su kai turus, ni dama nasan irin matsalolin da Uwani take fuskanta a gidannan shi yasa ban yi mamaki ba, gashi uwani ta kasance kamar zawayi wajen rashin haƙuri ai kuwa nan ta tanka.
"Maman Shamsu kenan. Baƙin cikin ki takashinki zai koma da izinin Allah. Ni Uwani nafi ƙarfinki, kuma in mijinki yafi nawa mijin kuɗi, ai ni na fiki more aure tunda mijina bai taɓa zagin iyayena ba. Kuma bai taɓa korata da watan azumin ramadana ba, dan haka ki iya bakin ki" A mugun zafafe Uwani tayi maganar cike da hargowa. Yaran na kaɗa ciki dan gudun kar su kantamo kalmomin da suka shige shekarunsu. Da Uwani da maman Shamsu sun ci uwar sabada har sai da mazajensu suka dawo daga masallaci suka raba wannan ja'iba, dan wallahi na kasa riƙe Uwani sam, har zani Maman Shamsu ta fincike mata ya rage daga ita sai gwari na tsuma ( siket ɗin ciki). Ɗayar matar gidance ta ɗaukoma Uwani zanin ta ɗaura. Baban Shamsu cikin son bin goyen matarshi ba tare da bin ba'asin abinda ya faru ba yace.
"A ɗayan biyu ya kamata ko ku ku bar gidannan, ko kuma mu tashi mu bar muku gidan. Wannan bala'in yayi yawa dan watarana wannan jarababbiyar karyar matar taka zata iya illatamun mata'"
"Karya kace mata Ƙasimu? Uwani ba karya bace tunda bata leƙen mazan mutane in sun shiga bayan gida. Uwani Iyabo ku shige ciki kar ku tanka musu" Shigewa mu ka yi mu ka barma
Hafizu faɗan. Matan gida sai ihu suke yi. Nifa harna rama sallolina ba'a dena gwabza habaice_habaice ba. Wannan ta jefa ma wannan, waccan ta rama, Uwani na tsaye a bakin ƙofa riƙe da labule sai ɓarin zance take ta faman yi. Yara kuma sai cin tuwonsu suke yi a yinwace."
Uwani dan Allah ki rabu da Maman Shamsu ki shigo mu tattauna matsaloli" labulen ta saki muka shige uwar ɗakinta duk muka yada zango a kan katifa"
Wai Uwani me matarnan take nufi dake ne haka?"
"Sharri mana, baƙin ciki take yi mini. Jiya jiya fa na kamata tana barbaɗa mun garin magani a ƙofar ɗakina, kinga ɗauki babu daɗin da mu kaita yi kuwa? Mune har gidan mai unguwa fa. Amman kinga ta sake takaloni" Ajjiyar zuchiya na sauke . Labarin duk matsaloli na ba uwani, da ƙudirina da dalilin zuwana wajenta"
"Lallai rayuwar mata cike take da ƙalubale mai tarin yawa. Wata matsalarta uwar miji irinki, wata matsalar ta ƙannen miji, wata jarabawarta maƙotane marasa ƙaunarta irina. Wasu dangin mij, wasu matan maƙota, wata ma abokin mijina, ko matar abokin mijinta sune matsalarta, banda kishiya da shegiya facala su ba'a lissafinsu ma. Na tausaya ma Dada aimun. Kuma ya kamata ku yaranta ku haɗe kai lallai ku nema mata takaddarta. Iyabo amman ramar da kika yi da sauyawarki ta ban tsoro" Hawayena na share.
Uwani ƙauyene fa sosai can inda na koma. Babu ruwan famfo, sai wata rijiya guda ɗaya jol anan ake ɗiban ruwa, ba wutar lantarki, babu sabis ɗin waya, ba titi, amman suna da makaranta, sai dai al'ummar cikin ƙauyen aikinsu kenan kiyo, matansu kuma tallar Nono, suna da ƙarancin ilimin addini, ai dole ki ganni haka. Kuma jinya nayi magashiyyan sai an ɗaga sai an ƙwantar"
Mun jima muna tattaunawa, sai da mu kai sallar isha mu ka ci abinci sannan Uwani ta zura mayafi muka nufi gidan Hajiya Salamatu.
"To naji bayaninku. Amman Uwani kin mata bayanin komai da komai dai ko?" Cewar Hajiya Salamatu tana hakimce taci gwala_gwalai kunne da wuya, da tsintsiyar hannu.
"E Hajiya na yi mata bayani. Sai dai itama bata da kuɗi kamar dai ni. Amman Hajiya in muka je can za'a cire a kuɗin aikinmu har mu gama biya. Mu ba ma daɗewa zamu yi a can ba shekara uku ya ishemu, dan da ita Iyabo shekara biyu ma tace" Hajiya tayi dariya tare da girgiza kai.
MRS BUKHARI
3064127935
Buhari Ibrahim Ladan
First bank
Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan.
Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun
Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundati
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm
NAMA YA DAHU
ROMO ƊANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
15
Kafin tace.
"Ba dai shekara biyu ba, dan a ƙalla ba a ƙasaru ba, zaku iya kaiwa shekara guda kuna biyan kuɗin jirki da duk abinda aka kashe muku. Sai dai in babban gida kuka samu suke biyanku kuɗi da kyau, amman in ba haka ba shekararnan sai kun yita. Babu rufa_rufa sai kun gama biyan kuɗin jirgi zaku samu damar yin aikin hajji da umara baki ɗaya. Amman muddin kuka zama masu hazaƙa da kazar_kazar to gidan da za'a kaiku aiki zasu soku, kuma in dawowarku najeriya tayi, su hadoku da goma sha tara na arziki." A nan na fahimci Saudiyya zata turamu, sai naji hankalina ya ƙara kwantawa. Kafin mu baro gidannan mata da tsofaffi a ƙalla mutane fin ishirin sai da suka shigo, duk akan batun tafiyar. Ni dai mun tsayar da magana akan gobe da safe in zo mu je hajj kam aimun fasfo kafin in koma garinmu, nan da wata ɗaya da kwana goma jirginmu zai ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki.
Muna tafe muna ɗan tattaunawa har bus ta saukemu a unguwar su Uwani. Muna sauka muka ci karo da mijin Uwani yana zaune a wata majalisar maza ƴan sa ido. Zumbur ya miƙe da ganinmu ya nufomu gadan_gadan.
"Ke Uwani daga ina kike?" Ya faɗa a fusace. Tsaki uwani ta ja tace.
"Aikin banza aikin wofi, ka dai ji kunya ka kuma yar da zuchiyarka kare ya cinye. Maza majiya ƙarfi masu zuchiya, ka gansu a titi suna aikin sufuri dan su rufa ma iyalinsu asiri. Banda kai Hafizu baka da aiki sai zaman majalisa, duk matar data wuce kuna ƙarema surarta kallo, ka barni da buga_buga mata a layi duk sun rainani" A faɗace take maganar tana yi tana kumfar baki. Shima zabura yayi ya ce.
"Duk macen da take fita dai ba da sanin mijinta ba mala'ikun Allah har taje ta dawo suna tsine mata. Shashasha kawai." Tsaki ta buga fuu ta wuce ta barmu a tsaye.
Hafizu ka ƙara haƙuri dan Allah. Dama har yanzu irin wannan zaman na rashin daraja kuke yi ma junanku? Ga yara sai sake girma