Showing 18001 words to 21000 words out of 61296 words

Chapter 7 - NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE

10 Sep 2025

5987

mun. Tana yi tana buga cinya, tana ɗaga murya tamkar faɗa, bil haƙƙi ita ba faɗa take yi ba maganarta ce haka, ko kuma ince mafi akasarin yarenmu suna da ƙarfin murya, da ihu a cikin magana. Ni dai bani da bakin cewa, dan nasan Gwadabe na ƙoƙari sosai, banso zuwa asibitin ba sabida gujema tashin hankali da tarzoma irin wacce ta afku lokacin haihuwar Toye, an yi ɗauki babu daɗi sosai. Dan ranar suna anci dambe an gode Allah. Burodami kokodeen ne ya katse Iyaa Debisi ta hanyar cewa.
"Yarinyar nan Iyaa Debisi ya kamata a barta haka, ko dan rabon dake tsakani, ni ina ganin dukan yayi mata yawa" Miƙewa tayi tsaye, ta tafa hannu tace.
"Ahhhh Ahhhh kokodeen Oya were ( baka da hankali)" Nan fa ta sake shiga wani babin, ta inda ta shiga ba tanan take fita ba. Shigo da yaran da ma'aikatan kiwon lafiya suka yi ne yasa ta yi shiru. Ɗakin kuwa Hausawa sai kallonmu suke yi. Iyaa Debisi take ta soma rera waƙa tana rawa na murnar zuwan jikokinta. Suma su Burodami kokodeen nan suka soma rawa suna mata tafi. Tana rera waƙar yarenmu ta musamman da akema ƴan biyu.
Gabaki ɗaya ɗakin hankalinsu yana kanmu. Murmushi kawai nayi musu, Uwani kuwa sai zolayar Iyaa Debisi take yi dama sun saba. Taiwo Iyaa Debisi ta riƙe, Burodami kokodeen kuma ya karɓi Kahinde. Sai murna suke yi, domun a ƙabilarmu babban abune haihuwar ƴan biyu, mun ɗaukesu a matsayin wata babbar baiwa da Allah ya bamu. Kuma yarenmu su kansa yaƙinin rayuwar ƴan biyunnan mai albarka ce. Ni dai a haka baccin gajiya ya kwasheni, bani na farka ba sai jefin la'asar. Ƴan uwana sun cika asibiti danƙam sai tayani murna suke yi. Ga abinci iri_iri an kakkawomun. Burodami Debisi ya zubo mun amala da miyar ewodu, da miyar wake, da jar miya dukka, ga ganda haka_haka.
"Ga abinci kici ko zaki samu ƙwarin jikin naki, gida zamu tafi" Karɓa nayi na mishi godiya. Ƴan uwa kuma aka shiga yi mun ya jiki, tare da murnar zuwan Taiwo da Kahinde duniya. ( Hassana da Usaini ) Amalata naci nayi ƙat na kora da kunun akamu me zafi, take naji na yi gyatsa mai ƙarfi, bana jin komai garau nake jina tamkar ba ni bace na haifi ƴan biyu ba. Wajajen shidan yamma aka sallamemu muka fito asibiti mota biyu. Duk tare muka ɗunguma mazanmu da matanmu zuwa gida. A tsakar gidan muka tarar da matan gidan kamar dai kullum ana zaman gulma da kace_nace.
"Ahh ƴan biyu aka samu kenan? Kai masha Allah barka da arziki Iyabo." Cewar Yaya Haula.
Yauwa sannunku" Iyakar abinda nace kenan. A ƴan uwana kuwa babu wacce ta kulasu, suma basu kula kowa ba, mu kai shigewarmu ciki. Mazan a falo suka zauna, mu kuma muka shige cikin uwar ɗakin. Anty Mulka tace.
"Abun girkin ki na ganshi a falo. Anan zan dafa miki ruwan wankan ne, ko zan iya fita ƙaddararren tsakar gidan naku?" Sai da na ja numfashi nace.
Zaki iya fita dashi ki sa ta gefen ɗakina, kafin Gwadabe ya zo ya kawo itace" Sai lokacin Bose tace.
"To wai shi gogan bai san kin haihu bane?" Kafin in yi magana Uwani tace.
"Na kirashi na sanar dashi. Yana hanyar dawowa daga legos ne, da ƙyar ma na samu wayar tashi ba sabis. Amman yace abokinshi Bara'u zai tawo daga ƙauye, duk abinda ake buƙata zai yi kafin shi ya iso, dan yace mun zasu iya kaiwa ma ɗayan dare basu shigoba, wata ƙila sai Asuba ma zasu shigo kanon." Tsaki Iyaa Debisi tayi tace.
" Isokuso asan. ( Banza marar amfani)"
Haƙiƙa naji zafi ainun, kuma maganar ta dokeni, ai ko banza Gwadabe uban ƴaƴanane." Anty Mulka ta fita bakinta a taɓe. Bose ta fita da zanin jini da muka dawo dashi daga asibiti, Uwani kuma ta ci gaba da mun gyaran ɗaki, sauran ƴan uwa kuma suka fita falo wajen su Burodami.
Zuga su Yaya Haula su ka yi, suka shigo da sallamarsu, Iyaa Debisi ce ta basu izinin shigowa. Suna shigowa ta miƙe ta koma falo"
"Iko sai Allah, Iyabo dama kunsan ƴan biyu ne a cikin naki, ko kuwa sai da kika haihu tukunna?" Cewar Gude uwar son jin ƙaƙa aka haifi mutum.
A'a dama tun cikin ma yana wata huɗu da akayi mun sikainin akace ƴan biyu ne. Kun gansu mace da namiji. Taiwo da Kahinde kenan" Yaya Haula tace.
"Au suma sunan yarbawan za'a liƙa musu, babu ko karar a saka sunan Mahaifin shi Gwadaben, ita kuma macen asa sunan Babala, sai wani Taiwo da Kahinde?" Uwani ce ta juyo tace.
"Ba tana nufin sunan yarbawa za'a saka musu ba. Taiwo da kahinden yana nufin Hassana da Usaini kamar yadda muke cewa a Yaren Hausa. Tunda ai kunsan ba ko waɗanne ƴan biyu bane ake sake musu suna ba, ko a cikin hausawa "
"To wannan ko dole a sake musu wallahi. Kun mayar da Gwadabe sai kace sususu kawai" Cewar Yaya Haula wacce da gani ta fusata. Uwani ba kanwar lasa bace na santa sarai shi yasa na katse zancan dan gudun kar su kira mun ruwa, dan ƙyas su Bose suka ji wata hayaniya zasu shigo ayi ɓatacciya, dan kowa cike yake da haushin kowa, sai kace ba Allah ɗaya muke bautama ba.
Ya'isa haka Uwani dan Allah. Yaya Haula Gwadabe na da ikon ya zaɓama jininshi duk sunan da yake da buƙata. Ni bani da ikon sashi yayi abinda baya so. Ko Toye ma shi ya zaɓi ya saka domin yai na mahaifina Allah ya jiƙan rai takwara"
"Tunda ya kasa yi ma nashi Allah ya ji ƙan ran takwaraba. Ai baki zo kin ganshi da mahaifinshi a raye ba. Dama yarbawa akuyarku ai tayi kuka wajen juya miji da jarabar bin baba lawo" Ta sake faɗa da karfi . Na riga da nasan tarzoma take son tayarmun, ayi rikici su sake kafa hujja akan jarabar yarbawa, da ƙin zaman lafiya. Haka dai suka fice a ɗakin bayan sun yi mun barka. Ni dai ban basu yaranba, dan a al'adarmu bama ba da yaro jariri ga mutane aita jagwalgwalashi. Suma sun sani tun a haihuwar Toye, kuma sun yi rantsuwar ko yara ɗari zan haifa ba wacce zata sake yinƙurin ɗaukar jaririn. Cikin ikon Allah a ƴan uwana babu wanda yaji kace_nace ɗin data faru, bayan fitarsu Uwani tace.
"Iyabo sai fa kin yi da gaske dangin Gwadabe zasu iya barinki kici gaba da rayuwa a gidannan, wannan ƙiyayyar ta yi yawa. Wallahi ko ahalul kitabi ce ke ya kamata su sarara miki haka. Duk da su kansu Iyaa Debisi sunƙi su zubar da makaman yaƙinsu. Amman ɗazu fa kinsan ina dawowa rufe miki ƙofa da kikace. Su Haula suna falonki suna kallon ɗakin. Ita kuwa baƙar kadararcan a Uwar ɗakin ki muka ci karo tana miki bincike a sib, har ta ɗakko wata atampa mai ruwan malmo, kai gaskiya kina cikin wani yanayi." Shigowar Sakina ne ya katse mana hirar.
Ah Sakina kune a tafe da yamma sakaliya haka? Maraba" Na faɗa ina dariya. Uwani tace.
"Kaga uwar gida, kuma Amarya a gidan Bara'u, Sakina lale." Cewar Uwani.
"Lale Uwani, ashe Iyabo uwar biyu an samu kai. Sannu fa mai jego. Bara'u yana falo yace a kawo mishi yarin zai musu huɗuba." Miƙewa nayi na saka mayafi, Sakina ta riƙe Taiwo ni kuma ina riƙe da Kahinde muka fito falon. Bara'u yana kujera shi kaɗai, babu kowa a falon, duk yanda akayi su Burodami kokodeen sun tafi gida ne, ko sun je su dawo. Sakina ta miƙa ma Bara'u Taiwo.
Ina wuni Bara'u. Da wannan yammar Gwadabe ya taso ku?"
"Haba dai ai Gwadabe ya wuci haka a wajena. Kuma dama muna shirin shigowa cikin garin jikin Babala yaƙi yanzu haka tana asibitin Murtala. Yaya Hambali da Sukairaju suna wajenta, amman ƙila ba gado za'a bata ba dai."
Allah sarki, ai ban sani ba. Zan shirya in je zuwa bayan magriba in dai basu dawo ba." Sai Sakina tace.
"Ke da kike fama da kan ki kuma?" Bara'u daya fita sanin dawar garin yace.
"A'a in dai akayi magriba sai ki rakata ta je ta dubo jikin ai dai ba za'ace bata nuna kulawarta ba ko ba gaskiya ba" Huɗuba yayi ma yaran da suna Hassana da usaini kamar yadda yace Gwadabe ya bashi umarni.
"To yara na yi musu huɗuba da asalin sunayen da ƴan biyu suke zuwa dashi, wato Hassana da Usaini. Taiwo da Kahinde a yarenku kenan. Sabida haka a ɓangarenmu Hassana da Usaini suke. A naku ɓangaren kuma Taiwo da Kahinde Allah ya raya su da imani" Miƙo mun yaran yayi na amshi ɗaya Sakina ta amshi ɗaya muka shiga ciki.
"Me za'a ɗaura na dare ne Iyabo magriba ta kawo kai ma?" Cewar Uwani kafin in bata amsa Iyaa Debisi ta shigo da ruwa a bawo na wankan yara ta dasa kujera.
"Fun mi ni omo ( Bani yaron) Ta furta ranta a mugun haɗe. A sanyaye na miƙa mata ina fatan kar a kuma samun matsala makamanciyar ta haihuwar Toye.
Uwani ai inaga ba sai an yi girki ba, ga Amala a kuka da faten wake, ai ya ishemu, gobe a ɗaura girkin."
Nabata amsarta. Anty Mulka ce ta leƙo tace dani in je in yi wanka ta kai mun ruwan. Wanka nayi na gargasa jikina sosai na ji daɗi. Ina fitowa Su Anty Mulka suna shirin tafiya gida Burodami kokodeen yazo zai kaisu gida. Godiya nayi musu sosai, mu kai sallama suka fita ni kuma na koma ciki. Anan naga kayan abincin da su Sakina suka kawo mana, garin tuwon masara, kuka daddawa, busassun kayan miya, albasa, shinkafar hausa, da gyaɗar miya harma da man ƙuli jarka guda, da bushasshen kifi" Godiya nayi sosai gami da yaba ƙwazon Bara'u, ya kuma yi dace da macen da bata hanashi yin aikhairin sai ma taimakonshi da ƙara ƙarfafashi da take yi."

MRS BUKHARI
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm




NAMA YA DAHU...
ROMO ƊANYE.
GAWURTATTU UKU

BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

Lamba ta shida


Shiryawa nayi cikin doguwar rigar Atampa, ɗaya daga cikin kayan da Alaja ta bani, atampar mai kyauce kuma tana da tsada da gani. Hijabi mai roba_roba na saka kalar atamfar sak. Na ɗauki Taiwo na goya, Kahinde kuma Sakina ta goya shi.
Uwani zamu je asibitin Murtala Babala tana can bata da lafiya gara in je kar in yi wani babban laifin.
"To sai kun dawo, nima ƙoƙari nake in gama gyare miki uwar ɗakin yadda ya kamata. Gobe za'a zazzo da yawa. A nan ma ni zan kwana gobe na koma gida Hafizu baya nan ya tafi Lahadin makoli mahaifinshi bashi da lafiya. Yaran kuma suna gidanmu " nace da'ita.
To Shikenan ma, sai mun dawo to. Sakina muje." Shigarmu ward ɗin mata ke da wuya na hangi su Yaya Haula dukkansu a zazzaune a tabarma da mazajen nasu. Kallona suka shiga yi da suka hangoni.
Sannunku Yaya Haula ya mai jikin?" Sai da ta taɓe bakinta tace.
"Jiki da sauƙi" Gaishe da su Sukairaju nayi tare da yi musu ya mai jikin. Yaya Harisu cikin murtukewa yace.
"Da'u ka kai su wajen Babala su gaisheta" Da'u yayi gaba muka bi bayanshi har bakin gadon Babala, tana zaune ta jingina bayanta da matashin filo. Yaya Halima kuma tana tsaye tana haɗa mata tea. Muna isowa Babala ta kawar da kanta gefe.
Sannu da jiki Babala, ya ƙarfin jikin? Na furta muryata har tana rawa.
"Da sauƙi"
Ta bani amsa ciki_ciki. Yaya Halima kuwa nunawa tayi bata ma san Allah yayi ruwan tsaron mu ba. Gaisheta nayi tare da yi mata ya mai jiki. Babu yabo babu fallasa dai ta amsa mun. Da Sakina ne dai su kai fara'a. Sunto Taiwo nayi na miƙa ma Babala ita, tasa hannu ta amsheta, Sakina ta ƙara matsa da Kahinde.
"Ba shakka gashi nan yara sun ɗebo ƙoƙon asali. Kamanninsu sak da dangin uwarsu dai kamar yadda Toye yabi sunanshi." Iyakar abinda tace kenan ta miƙo yaran. Raina ya sosu ainun ko Allah ya rayasu bata ce ba, balle ta yi musu adda'a a matsayinta na kakarsu. Yaya Halima kuwa ko kallo yaran basu isheta ba. Bayan na gama goyo ne ta kalleni sak tace.
"Na ji saƙonki na gode da har kike tunanin mahaifinki ya fi mahaifin Gwadabe daraja a wajenshi. Burinki ya cika yaranki uku babu wanda Gwadabe yayi ma takwara a danginshi. Har ni da na ɗau jimirin renon cikinshi na wata goma ya kasa saka sunana ma ƴarshi. Taiwo da Kahinde ɗin dai da kika sanar, shima shi ya jaddada a matsayin sunan yaranshi. Ko da yake dama tuni kun gama tsarin komai tun ma yaran suna ciki." Baki na buɗe inason in ba Babala haƙuri amman sai ɗaga mun hannu tayi.
"Kije kawai, bana son ganinki, bana kuma ƙaunar zamanki da Gwadabe, zuchiyata ba zata taɓa samun salama ba madamar kina amsa sunan matar Gwadabe abadan" Cikin razani da tashin hankali mai girma na shiga. Lokaci guda Gwadabe da aurenshi ya fice mun a raina kwata_kwata. Na yi alkawarin inayon arba'in zan tursasama Gwadabe sakina ko dan ya ga haske a rayuwarshi, domin na fahimci har abada Babala ba zata taɓa ƙaunata ni da abinda na haifa ba, wannan shi ake kira NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE. Ko Gwadabe bai sake ni ba, ni kuma zan fice a rayuwarshi.Wata wawuyar ajjiyar zuchiya na sauke a hankali na soma tafiya dan barin ɗakin. In sha Allah ƙarshen aurena da Gwadabe yazo, ko da kuwa soyayyarshi ita zata zam silar numfashina. Fitowa daga ɗakin ke da wuya, na jiyo Harisu yana zagina tare da ƙorafi kan sunayen yara da aka saka. Sai ji nayi na muzanta ko fita ma bazan iyaba. A tsaye Sakina ta iskeni.
"Ki ƙara haƙuri dai Iyabo damo sarkin haƙuri. Mu je kinji" Da taimakon Sakina na iya fitowa, amman har muka isa guda ban iya furta ko kalmar A ba, sai ajjiyar zuchiya kawai nake saukewa. In sa abinci a cikina wallahi na kasa sabida tsabar damuwa. Sakina da Uwani sai aukin rarrashina suke yi, amman na kasa ce musu komai. Ni tunanina ya na ga samarwa Gwadabe sauƙi dan fishin iyaye masifa ne, nayi imani fishin da Babala take kwana ta tashi dashi akan Gwadabe shi ya hana shi yin arziki. Kullum cikin faɗi tashi yake, ta hana kowa ya taimaka mishi. Yaya Hambali shago gareshi babba a kasuwa da yake siyar da dabino da gyaɗa, buhu_buhu yake siyarwa yana da yaran shago sosai. Amman Babala ta hana shi ya ɗauki Gwadabe ko da a matsayin yaron shago. Yaya Harisu shi kuma mota yake ja zuwa ƙauyuka a haka ya sai wasu motocin guda biyu ya bayar anayi mishi hayarsu. Sukairaju kifi bushasshe yake saidawa a kasuwa, shine zuwa argungi, shine zuwa maiduguri, da Yawuri saro katan katan na kifi, kuɗi yake samu sosai da sosai Ɗan fodiyo kuma Kafinta ne kuma ogan kanshi ne. Da'u shi kuma Yaya Hambali ne ya buɗe mishi shagon sai da kayan masarufi dangin shinkafar hausa, gyadar miya, masara, wake. Duk wannan matakan sun haushine da taimakon Allah da taimako da jajircewar Yaya Hambali, domin Yaya Hambali guda ne harda ɓari ga ƴan uwanshi, yana musu tsananin so.
Ina lokaci yayi da zan fita fit a cikin wannan ahalin, nima in je in yi rayuwa mai kyau. In ba haka ba bala'o'e iri_iri zasu iya saukar mana a sakamakon fishin da Babala take yi da Gwadabe. Abubbuwa nawa Gwadabe ya kama suka lalace, yayi sana'o'e a ƙalla iri huɗu karen mota shine na biyar. Amma tafiyar bata wani nisa sai abun ya lalace, ko mai gidanshi ya koreshi, ko a yi mai wani ƙazafi, ko na sata ko na ƙashin tsiya."
"Iyabo ga tea ki daure ki sha, wala Allah ruwan nono yazo miki. Kinga Taiwo da Kahinde kuka suke yi baki ma sani ba. Kar ki kuskura waccan munafukar ta falo ta fahimci kina cikin matsala, yanzu ta shigo. Surukar taki ma an sallamota tana ɗakin umman Nazifi." Hannu nasa na amshi tean hannun Uwani na sha, dan jikina har rawa yake yi tsabaragen yinwar da nake ji. Sakina ta miƙo mun Taiwo da take ta canyara ihu kamar wacce ake zare ma rai.
Ga man zaitun da audiga Sakina bani in goge kan mamana in gwada musu ko zasu jawo ruwan yazo" Miƙomun Sakina tayi, na bi kan mamana na goge da man zaitun tas na ba yaran suka soma ja. Cikin ƙudurar Allah sai ruwan nono ya soma zuwa. Nan kuka yaƙare aka shiga tsotseni. A wannan daren bana ce na yi bacci mai kyau ba. Misalin ukun dare sai ga Gwadabe, a lokacin duk su Uwani suna kan gado sun yi bacci ya shigo. Ganinsu ne yasa ya koma falo, ni kuma na ɗebo jariran na biyo bayanshi, yana zaune a kan kujera. Laila kuma tana kwance tana bacci ta yi baje_baje cinyoyinta duk a waje. Miƙa mishi yaranshi nayi yasa hannu ya amshesu yana fara'a.
"Maman biyu barka da sauka, ina fatan babu inda yake miki ciwo ko?"
Babu, sannu da dawowa" Iyakar abunda na faɗa kenan shima ciki_ciki. Idanunshi yana kan yaranshi yace.
"Ya dai akwai wani abu dake damunki ne, ko an yi wani abunne? Iyabo a yanzu ya kamata ace kin saba da komai. Ki toshe kunnuwanki dan abubbuwa da yawa zasu faru kafin ayi suna kema kuma kin sani. Yanzu haka nafi awa ɗaya da shigowa Babala naketa ba haƙuri tayi fishi wai ban mata takwaraba ita da mahaifinmu. Nace mata zan sake yin sabuwar huɗuba in hakan zai bata farin ciki. Amman taƙi fur tace mun in na sake ma yaran suna bata yafe ba, wallahi kar kiji......." Ɗan yatsana nasa a kan laɓɓana nayi mishi halama da yayi shiru, nuni nayi mishi da Laila dake kwance. Ai ba shiri ya haɗeye maganarshi. Mu ka ɗan taɓa hirarmu kaɗan, ya miƙo mun ledoji manya biyu, mu kai sallama dashi zai kwana a ɗakin zaure, ɗakin su Nazifi, Bara'u ma yana ɗakin. Da tunane_tunane na ƙarashe daren nawa, sai jefin asuba bacci mai nauyi sosai ya ɗebeni bani na farka ba sai taran safe lokacin ƴan uwana sun ƙaraso, har an yima ƴan biyu wanka sun fito ras dasu, dan Gwadabe ya kawo kayan jariri kala biyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login