Showing 42001 words to 45000 words out of 61296 words
shadda a gefe. A ƙyamace nayi bawali na fito, inda zan ɗaura alwala ta nuna mun, naga gidan kamar komai da tsari suke yinshi. Nayi alwala muka fito a tare. Har zuwa wannan lokacin Ina jiyo muryar Dada tana magana. Da ƙyar nayi sallolin da ake bina nayi jigum akan buhun da aka shimfiɗa mun nayi Sallah. Abinci wannan budurwa ta kawo mun a cikin ƙwarya an rufe ƙwaryar da faifai.
Ya sunanki ne?" Na tambayeta ina ɗan fara'a.
"Sunana Cubu"
Kin sanni?" Na sake jefo mata tambaya.
Sai ta girgiza mun kanta halamar A'a. Sai na yi ɗan murmushi nace.
Ke yarinyar Dada ce?"
Sai da tayi dariya sosai kana ta bani amsa ta hanyar ɗaga mun kanta halamar e" Kwaryar abincin na buɗe tuwone da wata miya baƙa ƙirin ba koriya ba, sai wani irin ƙamshin ganye take yi marar daɗi, amman dake ina jin ɗan karen yinwa ba shiri na nutsa hannuna a cikin tuwon. Wallahi da ƙyar na iya haɗiye tuwonnan, ko da na haɗiye dambe mu kai ta tayi, yana shirin dawowa ni kuma ina ƙoƙarin mayar dashi, dan gudun kar suce na ƙyamacesu. Inaga Cubu ta fuskanci bazan iya cin tuwon bane, sai ta miƙe ta kawo mun madarar shanu. Dana kafa kaina sai da na shanye madarar tas. Ina sauke kofin nayi gyatsa, sai ga Dada ta shigo tana sharar hawaye cikin dabara, dan ita a tunaninta ma bamu ganta ba. Zargina ya tabbata akwai wani babban abu da aketa ɓoyemun tsawon shekarunnan da ba'ason ni in sani. Ni kuma ina ganin lokaci yayi daya kamata in sani. Bakin gado ta zauna kanta a ƙasa kamar yadda ta saba tace.
"In kin gama cin abincin Cubu ta rakaki gidan Ɓoɗɗo acan zaki kwana, ƙanwatace a gidan itace uwar mijin Baɗɗo uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya babu wata matsala. In Allah ya kaimu gobe na dawo tallan nono zan biyo gidan in same ki. Cubu ƙanwarki ce ƙanwar Ɓoɗɗo, yar Yusuf. Amma. Akwai Amaduyal shine a sama da Ɓoɗɗo sai dai shi baya zama, yanzu haka suna togo, sun fita kiwon shanu tsawon shekara biyar basu dawo ba, amman ana jin labarinsu, suna yo aike gida, matarshi Sa'ada tana cikin gidannan, da yaranta biyu" Kai na gyaɗa. mamakin daya kamani shine jin Dada ta ambaci tallan nono, kenan itama tallah take yi kamar yadda na ga wasu guggun mata a Jere Banyo da ƙoren tallarsu? Iko sai Allah ai yaci ace Dada tana zaune ne tana morar haihuwa ba wai ace har yanzu aikin wahala take yi ba. Miƙewa nayi tsaye Cubu ta ɗaukarmun jakar kayana.
To sai Allah ya kaimu goben Dada"
Na yi magana a mugun sanyaye. Cubu da Yusufu ne suke gaba ina biye dasu a baya, ina kallon gari maza suna kwakkwance a tabarma, wasu kuma sunyi da'ira suna cin abinci. Yayinda samari masu jini a jika suke ta sha'aninsu kawai. Ta wani dandali muka zo wucewa nan naga kyawawan ƴan mata farare, da kyawawan Samari. Ƴan mata na waƙa samari na yi musu tafi. Wasu kuma keɓe suke a gefe guda suna musayar kalaman ƙauna. Rayuwar ƙauye akwai ban ƙawa a cikinta, bugu da ƙari akwai nishaɗi sosai. Tafiyace miƙaƙƙiyar gaske mu kayi kafin mu iso gidan Boɗɗo, duk na gama galabaita, ga gajiyar hanya da dama ban huceta ba, ga wannan tafiya me nisa da muka sake yinta. Suna kwance a tsakar gida mu kai sallama muka shiga, mazan gidan kuma kafin mu shigo sai da mukai musu sallama. Da sauri Boɗɗo ta taso ta tare mu." Ina tsaye bansan me Cubu tace da'ita ba. Kawai sai naga ta rungumeni ta fashe da kuka.
"Adda Jabu ashe zan sake ganinki a rayuwa? Cike zukatanmu suke da maraicinki" Ta faɗi hakan da kwaɓaɓɓiyar hausa. Nima hawayene suka gangaro kan kumatuna. Nan Boɗɗo ta shiga dani cikin gida tana ta nunani, ni dai Adda Jabu kawai nake jin tana ambato. Ɗakin Yafendo Kaɓoji ta kaini ƙanwar Dada surukarta kenan. Kanta ta dinga jijjigawa tana nanata sunana. Abunda na fahimta ƙanenane kaɗai sukai farin ciki da ganina. Hannuna Baɗɗo ta jawo muka shiga cikin bukkar data kasance ɗakinta, Su Yusufu na biye damu. Boɗɗo ta kalli su Cubu tace.
"Sunanta Adda Jabu. Yayar Amaduyal ce, Dada ce ta haifeta itace yarinyarta ta farko. Ina tunanin sanadintane ke sa Dada ƙunci da zubar hawayen da tun tasowarmu muka tsinci Dada a wannan halin." Runguma suka kawo mun dukkansu ukun, babu nuna ƙyama ba komai. Hawaye masu ɗumi sukaita zurubtu a kumaruna, hankalina a madadin ya kwanta sai ya sake tashi. Ni kaina na jima ina tausayama rayuwar Dada, na daɗe ina zargin bata jin daɗin rayuwa akwai wani babban lamari data ƙunsa a cikin ranta yake nuƙurƙusar rayuwarta. A wannan daren mun yi hira sosai da ƙannena na yaushe gamo, dan su Cubu sunƙi tafiya a cewarsu sai dai du mu kwana a zaune.
"Adda Jabu ki ce su tafi, Baffa zai yi faɗa sosai, ko ma yazo gidannan a darennan. Gobe Cubu zata kai nono cikin gari, Yusufu kuma zai fita da Shanu kiyo Kuma zata burga madara ta fitar da man shanu da asuba."
Jim na kuma yi jin abinda Boɗɗo take faɗe.
Cubu tunda kinsan hakane, ku yi haƙuri ku tafi gida. Ni ina nan na dawo rugarnan kenan, daku zanci gaba da rayuwata" Da kyar na lallaɓasu suka tafi, suna tafiya sai ga mijin Boɗɗo ya shigo ya miƙo balangu a baƙar leda. Boɗɗo ta gabatar mishi dani a matsayin babbar yayarsu. Cike da jin kunya ya sake gaisheni yana sosa ƙeyarshi shi a dole kunyata ce ta kamashi. Kai fulani a kwaisu da kunya da kawaici sosai. Fitar mijin Boɗɗo ke da wuya mu ka jiyo sallamar wata mata da Boɗɗo ta yo kiranta da suna Hama Ƙwarya ta ajjiye mun a gabana tace.
"Use baƙuwa"
Farar bafulatana doguwa gata da baƙin gashi. Da fara'arta muka gaisa duk da hausar kamar ta yara ƴan koyo suke yinta.
"Adda wannan matar wan su Yuguda ce, mijinta shine Babba a gidannan, yana fita aiki cikin birni.
Allah sarki, sannu Hama nagode sosai da fura" Murmushi ta kuma yi mun haƙoranta kamar ƙanƙara dan haske, a gaskiya Hama kyakkyawar macece banga wata makusa a tattare da'ita ba face ta rashin wayewa, da ƙazanta kuma dan ƙafarta duk faso fasonnan ya ɗebi wata annakiya ya adana. Ga gashi iya gashi amman kitson a furje kuma cike da yayin katifa. Boɗɗo tace.
"Hama wanna itace Babbar yarmu Adda Jabu, ba lallai bane ki san labarinta ba. Nima naci da bin diddigi yasa na san labarinta. Ta taɓa zuwa rugarnan da daɗewa lokacin muna yara ƙananu." Tare da Hama mu ka ci balangunnan mu ka taɓa hira dai haka. Duk da gajiyace ainun a jikina, ga tunane _tunane da suka haɗu suka cukurkuɗe mun rayuwata. Duk wani bugun zuchiyata bugawa yake yi da so da ƙaunar Gwadabe na. Haka tausayin mahaifiyata da son jin matsalarta suma su ka dabaibayeni. Ina fatan in zame mata sanyin idaniya, maganin zubar hawayenta.amman ta yaya tunda mijinta ma bai karɓeni a matsayin ƴa ba, tunda gashi a darennan ya kasa haƙuri ko da kwana guda ne in yi. Ko ma Iyaa Debisi ta faɗa mun yana da faɗa, bauɗaɗɗen mutum ne ainun. Tunani, da zafi, da sauro su suka hanani huce gajiya ta hanyar saka haƙarƙarina a ƙasa, katifar yayin dana kwanta akai sai sossokeni kawai take yi. Babu shiri na miƙe na fito tsakar gidan, duk yawan matan gidan suna kwance a tsakar gida bisa katifun yayi. A kan tabarma na kwanta iska na ɗan hura ni kaɗan. Da haka ɓarawon bacci yayi awon gaba dani izuwa asubar fari, kwaramniya da kukan shanu ne ya farkar dani. Ashe nonon shanu ake ta tatsa, su kuma sai kuka suke yi. Wasu daga cikin matan na gansu suna burga nono da wani itace mai kama da maburgin miyar yauƙi, wasu kuma suna ta aikin dahuwar madarar shanu, yayin da wasu suke sharar garken Shanu, wasu kuma girkin safe suke yi. Ina buɗe idanu Hama dake shara tace.
"Jabu kukan nagge ya tashe ki ko? " Tai maganar tana murmushi. Nima Murmushi nayi mata kawai, na miƙe Boɗɗo dake zaune a cikin jerin matan da suke ta burga nono ta miƙo mun buta, tai mun nuni da ban ɗaki.
Ruwa na kama na fito na ɗaura alwala na shige ciki. Na jima ina roƙon Allah yayi mun mafita, ya kuma sassauta mun soyayyar Gwadabe a ruhina, bazan roƙi ya cire mun soyayyr ba dan abadan Gwadabe bazai gaza samun gurbi a rayuwata ba. Tunano ƴaƴana yasa hawaye suka zubo mun a kumatuna, ba shiri na miƙe na fita. Ɗaya bayan ɗaya na dinga bin matan gidan muna gaisawa, mun shiga ɗakin ƙanwar Dada ma mun gaisa. Cikin garken shanu Boɗɗo ta jani wai in taya ta mu tatsi nonon Saniya ta dafa mana mu sha. A baya na bita zuwa cikin garken shanun a nan muka tarar da Hama a ciki ita da mijinta suna shafa ma wata saniya magani jikinta duk kuraje ya fito.
"Wannan itace baƙuwar tamu Boɗɗo? Ai Hama yanzu take faɗa mun cewar mun yi bakuwa kuma ma ƴar uwa" Cewar mijin Hama wani dogo siririn bafulatani sosai, ga gashi a kwance a kanshi lub, na lura kamar yafi kowa tsayi a gidan, ko dan ya fi kowa sirantane oho.
"E Yaya Hamma itace baƙuwar tamu, Ita ce sama da Amaduyal, daga ita sai shi, a birni take aure can Kano" Murmushi ya sake faɗaɗawa yace.
"Sannu da zuwa, baki tawo mana da yaran ba?" Ɗan murmusawa nayi bayan mun gaisa nace dashi.
Na baro yara a gida sabida makaranta" Baice komai ba sai ɗan murmushi da yayi, ya kaɗa shanu sama da talatin suka bi bayanshi da ƴar sandarshi da halama kiwo zashi. Ni dai ina raɓe a bayan Hama tsoron shanun nake yi, ina dai kallo Boɗɗo na tatso nonon wata farar ƙatuwar saniya mai baƙin ido, ita kuma Hama tana dai ta shafama wannan saniya magani a duk jikinta, kuɗa sai damun saniyar suke yi tana ta kaɗa kanta. Fitowarmu daga cikin garken kenan sai ga su Cubu sun shigo gidan, amman ta wata ƙofa da ban ba ta ƙofar da muka shigo jiya ba. Idanu na ƙura musu, su basu da fari can ɗinnan . Yanda duk suke kallona a kunyace su nai mun kallon so da ƙauna shi yafi komai burgeni sosai. A barandar dake ƙofar bukkar Boɗɗo muka zauna.
"Adda Jabu wadannan duk ƙannenki ne iyakarmu mu huɗu ne, shi Amaduyal shi baya nan. Iyakar yaran Dada kenan, nasan baki san iyakarmu ba, kamar yadda suma duka babu wanda ya sanki sai ni, nima saninna gani ɗaya ne." Daɗi ya lulluɓeni ganina a cikin ƴan uwana cikin Dadana, kuma sai kirana suke da Adda Jabu fuskokinsu da zuchiyoyinsu a cike da fara'a. Nawa bazai ma musaltuba. Tuwon farar masara aka kawo mana ɗumame da baƙar miya kamar kwalta, ko miyar meye wannan oho, sai madarar shanu mai zafi, tuwon sai ƙamshin man shanu yake yi. Loma ɗaya da nai karambanin sakawa a bakina da ƙyar da maƙyarƙyata na iya haɗiyewa tare da danneshi da Madara mai ɗumi. Muna zaune a wajen ina ɗan musu tambayoyi suna bani amsa, wata hausar ma da ƙyar suke fahimtar me nake nufi sabida tayi musu girma. A bakinsu naji ai kullum Dada tana zuwa cikin bini kai nono, fura, da man shanu. Tsawon tasowarsu da hakan suka san iyayen nasu, su kuma yara maza kiwon shanu suke fita yi, in suka girma har gari_gari suna iya fita kiwon shanun. Boɗɗo tace.
"Ko ni ma kullum ina fita tallar nono, mu da kuɗin wannan nonon muka dogara, bamu da wani abunyi sai kiwo. In mace ta siyar da nono, a ciki zasu ci su sha, su yi sutura, har su tara kuɗin magani in wata saniya ba lafiya a nema mata magani dashi. Ƴan mata kuma da ba aure a kansu, da kuɗin tallar nononsu ake yi musu kayan ɗaki da komai da komai, wata ma har ta tara kuɗi itama ta sai ɗan maraƙi da haka har su zama garken da yaranta zasu ci gado suma. Matan ma a wasu gidajen suna fita kiwo. Ko su Cubu suna zagayawa amman da awaki ba shanu ba." Jigum nayi ina ta kallonsu jikina a mugun mace. Dama duk uba uban tsarabar da Dada take yi mun in zata zo ganina da kuɗin tallar nono take yowa?" Sai naji zubar hawaye masu zafi, tare da saka ɗamarar sauya ma Dada wannan rayuwar tallan da izinin Allah.
Ana cikin haka sai muka jiyo sallamar Dada ita da wasu mata su su biyu, sai namiji guda ɗaya sun shigo kai tsaye kasancewar gidan duk dangin junane. Ɗakin Yafendo Kaɓoji suka nufa, mu kuma muka mara musu baya zuwa cikin bukkar.
"Zo Jabu ki zauna a kusa da Yafendonki." Wata mai kama da Dada ta faɗa. Kusa daf da ƙafafunta na zauna kaina aƙasa na gaishesu cike da ladabi. Suma cikin karramawa da haba_haba suka amsa.
"Wannan ƙannenane duka. Ga Yafendo A'i, ga yafendonki mai sunanki kin zauna a kusa da'ita. Zai Baffanku Musa gashi, sai Yafendonki Kaɓoji gata nan itace surukar Baɗɗo,. Ta nuna mun mahaifiyar mijin Boɗɗo. Kafin ta ɗaura da nuna mun su Cubu tace. " Wadannan kuma duk ƙannenki ne kece babbarsu, Amaduyal baya nan shi kuma na faɗa miki tun jiya." Murmushi kawai nayi dan na lura a damuwa Dada take sosai.
Yafendo Jabu ce tace.
"Zan ɗaukeki in tafi dake gidana, can ma akwai Daso shekarunku zasu yi ɗaya mijinta rasuwa yayi ya barta da yara tara. Zan zagaya dake dangi su ganki, zaki ɗan jima kafin ki koma ko?"
A sanyaye nace.
Na dawo nan da zama baki ɗaya ne, auren nawa ya ƙare. Kuma dan Allah a hannun Dada nake son zan zauna"
Gabaki ɗaya suka kalleni, banda Dada domin ita bata wani gane Hausa har sai da ƴan uwanta su kai mata tafintar abinda na faɗi. Da sauri ta ɗago ta kafe ni da ido cikin yaren yarbanci tace.
"Yanzu sai da wannan auren ya mutu, dangin mahaifinki sun ƙi barinki kiyi zaman auren ko? Dama tun farko da dan tani akabi da Debisin dai zaki aura domin shi yafi cancanta da sanin daraja da kimarki. Ita Iyaan taki ce ta amince miki ki dawo hannuna da zama alhalin tasan komai, zamana tare dake Jabu bazai yiwu ba. Tun jiya da kika shigo garinnan ban runtsaba har zuwa wayewar garin yau. Abinda nake so dake shine ki bi Yafendonki ki zauna a hannunta akwai Daso zaku dinga zuwa tallar nono tare, komai ma zaku ringa yi a tare. Amman ina mai baki shawarar ku koma birni inda kika fi wayo ki ci gaba da zama rayuwar Ruga cike take da ƙalubale, kumama ba iyawa zakiyi ba. Nima in kuɗaɗena suka haɗu zan je in dubo yaran naki. A hannun dangin ubansu kika baro su?"
Wasu zafafan hawayene suka gangaro kan kumatuna, tabbas akwai matsala shin mijn Dada baya ƙaunar ganina kenan, baya son ya samu ladan riƙon marainiyar Allah, ko da wani abunne wanda ni ake ta ɓoye mun ne? Duka waɗannan amsoshin na adanasu inaso duk lokacin dana samu lokaci mai kyau da Dada zata amsamun, ta bani tarihin mahaifina cikakke. Dan bansan wasu abubbuwa a game dashi ba sosai. Na dai san sunanshi, sai hotonshi babba dake kafe a falon Iyaa, sai hirarshi da watarana ke shigowa cikinn zance haka in su Iyaa na yi a tsakar gida.
Baffa Musa yace.
"Allah shi kyauta. Ni ina ganin tabi Jabu ta zaunaa a hannunta ko babu komai zasu dinga ɗebe ma juna kewa ita da Daso. Kuma komai zasu iyayi. Dan in hanuna nace ta komo bani da wata budurwar ƴa a gabana ma. Tunda tace tana son zama a zuba mata ido, in taji wuyar da bata sababa da ƙafafunta zata koma Birni aradu"
Yafendo kaɓoji tace.
"A barta a hannuna tana ganin Boɗɗo sai hankalinta ya kwanta, kuma anan akwai Hama naga tun jiya da tazo suke hirarsu tare, kuma akwai matan ƙannenta a cikin gidan ƙila tafi jin daɗi. Kema Adda Daso zuwa ganinta zai fi miki sauƙi. Zasu dinga zuwa tallar nono da Hama dan kar damuwa ta dameta."
Baffa Musa yace.
"A'a ki barta dai Jabu ta tafi da'ita can wajen nata. Ita kanta Daso tana buƙatar wacce zasu dinga shawartawa dan gudun damuwa. Ke Jabu ki je ki ɗebo kayanki sai ku tafi, Allah bashi in ita Daso mahaifiyarki ta samu daidaito da Mijinta kya dawo hannun nata, duk da nasan mutumme bauɗaɗɗe ga taurin kai da dagiya. A kan ki meye ba'ayiba a shekarun baya da suka shuɗe. Ita yar mahaifinkiToyosi ai tasan komai yaƙi an yishi"
Bani da zaɓi dole haka na kinkimi jakata na bi Yafendona zuwa gidanta, tafiya mu ka yi mai ɗa karen nisa, kamar ma ba ƙauye ɗaya suke da Dada ba, kuma fa a ƙafa su kamar ma basa son hawa Acaɓa. Gidanta kam ita kaɗaice a yadda na lura daga ita sai mijinta da yaranta.
"Jabu ga ɗakin Daso ki shiga ki ajjiye jakarki, zan tafi tallar nono yanzu, ki shirya sai in kai ki wajen Daso ku zauna kina tayata miƙa Nono. Mu nan ba'a zama daga masu kiwo sai masu fita tallar Nono " Ɗan murmushi na ƙaƙaro kawai. Bukkar data nuna mun ciki na shiga na ajjiye kayana a gefen gadon ƙasa, a kusa da inda naga jakar kayan da nake zaton na mai ɗakin ce Daso. Taya Yafendo ɗaukar ƙwaryar nono ɗaya da buhun bakonta nayi. Muna tafe muna cin karo da mata da yara kowa da ƙwaryarshi ta nono a ka za'a tafi talla. Maza da samari kuma sai wuce mu da garke_garken shanu suke yi suna shiga jeji kiwo. Rayuwar ƙauyen ta matuƙar bani sha'awa, gasu da tsabta ainun kamar ba ƴan ƙauye ba ma, ƴan ƙazaman basu da yawa. Wannan akori kurar muka kuma shiga cike da mata masu tallar Nono, sai yarata yaren Fulani suke ta faman yi, ni dai ina cikinsu ƙwalam har muka iso babban titin mota inda matafiya ke