Showing 6001 words to 9000 words out of 61296 words
da hukunci a kan Gwadabe. Ba da ban Baba Magaji ba da yanzu wani labarin akeyi. Ke dai Iyabo ki ta yin haƙuri wata rana sai labari. Ko wacce mace da irin ƙalubalen da take fuskanta a gidan aurenta, muna barma cikinmu sirrinne kawai. Murmushi kawai nayi ina hango lokacin da Gwadabe yake zuwa taɗi ƙofar gidanmu a idanuna. Tun yana zuwa ana barinshi da dai Iyaa Debisi ta ga abun da gaske ne na riga na kamu da son Gwadabe sai aka hana shi zuwa gida wajena. Ni da Gwadabe sai dai mu haɗu a wajen da nake sana'ar tuyan ƙosai da kafa da daddare a bakin titin unguwarmu. Gwauron numfashi na ja kawai mu ka ci gaba da hirarmu da Sakina. Sai da na huta na yi sallar azahar. Muna yin la'asar kuwa aka aiko yaran gidan wai in zo bakin murhu za'a ɗaura sanwar dare. Faɗan irin wuyar da nasha ɓata lokacine kawai, aikin kusan nice ƙarfin yinshi, sukaita zamewa suna barina. Ga tuwon gidan bikin ƙauye ba tuwo bane na wasa, ni na talga tuwonnan na dinga ɗiba da ƙoƙo ina zubawa a tukunya lamba talatin sai juyawa ruwan zafin yake yi. Bayan na gama talge sai na koma wajen su Zuwaira mu ka ci gaba da wanke kwanukan da aka ɓata da rana. Wanke_wanke ne bana wasa ba. Muna tsaka da wanke_wanken Su Yaya Hambali suka zo wucewa ta wajen. Dukkansu suke tafe harda Gwadabe wanda na ga idandunanshi sun kaɗa sun yi jawur. Duk da magriba ta kawo kai akwai ƙarancin haske. Kallona kawai yayi ya girgiza kai suka wuce zuwa shiyyar Babala. Haka kawai sai na tsinci kaina a cikin damuwa gami da faɗuwan gaba, take sai jikina ya mace murus. Cikin dauriya na iya tsaiwa muka kammala duk aikin daya kamata
Gwadabe:.
Tunda ya shiga ɗakin Babala, Babala ta tare shi da ruwan faɗa itace harda kukan ta ji labarin Iyabo ta shanye shi, ta mai sheshi Ɗan aikinta. Duk ta hanyar da yaso ya ɓullo mata dan ta fahimci dalilin da yasa yake mata aiki, amman Babala ta fututtuke. Su Goggo Iyatu suma suka ara suka yafa, mai makon su rarrashi ƴar uwarsu sai ma sake zugata da su kai ta yi.
"Wallahi Kyauta wannan lefinki ne. Dan wallahi da nine Tanimu ya kwaso mun ƙabila da sunan matar dazai aura. In sama da ƙasannan zata haɗe bazai aureta ba. Ki duba yanda ya shure soyayyar ƙanwarsa Laila fa Kyauta. Da ba dan na kai zuchiyata nesa ba da zumuncinmu ai ya taɓu" ( Kyauta sunan da dangi ke kiran Babala dashi kenan. Babala kuma sunan da ƴaƴa da jikoki ke kiranta kenan) Cewar Goggo Iyatu kenan. Goggo Jummalo tace.
"Ai yanzu ma bata ɓaci ba Iyatu. Har yanzu Gwadabe zai iya auren Laila. Tunda har Laila ta iya kaso aurenta domin tana son Gwadabe .Ya kamata a wannan karon ya aureta ko dan dole dan ubanshi a nuna mishi mu muka haifeshi ba shi ya haifemu ba. Wallahi a wannan karon aurenshi da Laila babu wata makawa." Da sauri Gwadabe ya ɗago jin labarin mutuwar auren Laila ba ƙaramin kiɗimashi lamarin yayi ba. Ga wata magana da Goggo Jammalo take faɗe, shi yanzu ina ya ga ta yin aure alhalin abinci ma da ƙyar yake iya kaiwa gidanshi, har yanzu bai soma sana'a a matsyin ogan kanshi ba. Ta yaya ma zai auri Laila? Wannan ma maganace da bata dace ace an ma tare shi da'itaba, duba da irin halin talaucin da yake ciki, da kuma babban dalilinshi na ƙin Lailan a bayan. Da ƙyar Gwadabe ya yakice ya bar ɗakin Babala yana yarfe zufarshi. Yana hanzarin barin shiyyar ya jiyo muryar Laila a bayanshi tana kiranshi.
"Gwadabe ji mana dan Allah " Cak ya tsaya bai juyo ba, bai da niyyar juyowar. Sai itace ta tako har inda yake, ta fuskanceshi.
"Gwadabe guduna kake yi ne?" Kallonta Gwadabe yayi, tare da girgiza kan shi.
"Tayaya zan guje ki kina gudan jinina Laila? Na ga ai mun gaisa ko, ko akwai wani abunne bayan wannan?" Ɗan murmushi Laila ta yi tare da cewa.
"Babu komai. Ka ji labarin mutuwar aurena, da musabbabin mutuwar tashi ko?"
"Ai kina jiyo duk bayanin da su Babala suke yi mun. Allah ya daidaita tsakaninku da mijinki. Laila in da gaske dan ni kika fito daga ɗakin ki, kin tabka babban kuskuren da zaki jima kina cizon yatsan ki. Sam ni Gwadabe bani da ra'ayin ƙarin aure, lafiya lau muke zaune da Iyabo, bata rage ni da komai ba, ta bani dukkan lokacinta da zuchiyarta. Haka zalika ni ma zuchiyata tana gareta. Ina mai baki haƙuri a karo na biyu." Yana dasa aya ya wuce ya barta da jin kunya.
Yana tafe yana mamakin irin ƙiyayyar da su Babala suke yi ma Iyabo, duk da dai shima irin wannan tsanar akayi mishi a gidansu Iyabo. Da dama a cikin gidansu Iyabo basa ko amsa sallamarshi. Bayan sallar la'asar kuma Babala tasa akayo mata kiran kab yaran nata, dan Haula ta tsokata mata abinda ya faru a can gida Kano da safe kafin su tawo. Shine wannan wucewa da Iyabo taga sunyi. Bayan sun gurfana a gaban Babala da Goggo Iyatu, da Goggo Jammalo, da Goggo Takura. Duk waɗannan ƙannen Babala ne, babban wansu Baba Magaji shi yana Maraɗi tare da iyalinshi. Nan Yaya Hambali ya soma yi ma Babala bayanin abinda ya faru, harda ma waɗanda suka wuce.
"Babala Iyabo ta gama mallake Gwadabe, shi yake yi mata komai da kika sani. Wallahi Babala har ruwan wanka sai Gwadabe ya kai mata, haka zaki ga ta fito tana kallon su Haula ɗaɗɗaya. Duk abunda Gwadabe ya samu akanta yake ƙarewa tas. Ai kin ganta sai ƙiba take narkawa, shi kuma yana ƙarewa kamar wanda ake lasa. Ni shi yasa nace su bar mun gidana kawai, dan ba ƙaunar buɗe idanu nake in ganta a cikin gidan ba Babala. Tunda har Gwadabe ya soma takamun burki, wataran sai duka. Kafin akai ga hakan gara su tashi kawai, ina da buƙatar wajen nasu dama zan zuba dabino a ciki. Babala irin taɓarar da Gwadabe da matarshi suke yi a cikin gida kare fa bazaici ba. Wallahi sai ki ganshi da gajeren wando yana barbaɗa mata garin Amala ita tana tuƙawa sunayi suna waƙar yarbawa. Wannan baƙin ciki da mi yayi kama" Yaya Harisu yace.
"Gaskiya ne gara ya kama mata haya a can nesa damu Babala. Ƙazantar da baka gani ba tsabta ce. Dan wannan yaron baya ko jin kunyar idanunmu, wallahi zaki ganshi a tsakar gida yana wanki tana mishi shanya, wataran har waƙar yarbawa zaki ji suna rerawa abun takaicin ya iya waƙar. Gwadabe ya rasa wacce yake so duk dangi, duk cikin ƙabilunmu na Hausa fulani kyawawa, sai wannan buskutar beyerabiyar ce ta ja hankalinshi." Haka ɗaya bayan ɗaya kowa ya goyi bayan Gwadabe ya bar ma Yaya Hambali gidanshi. Shi kuwa gogan yayi ƙuri yana jiran irin hukuncin da Babala zata yanke. Gyaran murya tayi tare da cewa.
"Na ji bayananku kab, kafin ku koma za ku ji hukuncin dana yanke. Zanyi shawara da ƴan uwana, akan batun matarshi kuwa wannan ƙabilar? Alkadarinta ya riga ya kusan karyewa. Ku tashi kuje in Allah ya kaimu gobe zaku ji hukuncin dana yanke" A sanyaye Gwadabe ya bi bayan ƴan uwanshi. Zuchiyarshi cike da ƙuna gami da taraddadin me ka je ka zo.
Iyabo:
. Sai zuwa bayan isha na samu hutu. Duk mun baje a tsakar gida muna shan iska. Ina kwance akan tabarma nayi matashin kai da hannuna. Toye yana zaune a gabana. Ƴan uwa sai hira da shewa suke ta ta yi abun gwanin ban ƙawa, ni kuwa mujiya na kasance a cikinsu, komai a tsorace nake yinshi, bana son in ɓata ma dai_dai da yaron gidan na goye rai. Ina gani ɗazu yarinyar Asiya matar Lawal tana dukan Toye, babu wanda ya kula. Gashi ba sa'arshi bace dan zata yi shekaru tara da doriya ma. Sai da ta gaji dan kanta ta barshi.
Ina kwance barci ya soma dibata Yaya Halima ta zo inda nake tai mun ƙerere a ka.
"Mandiya hamshaƙiya sai ki taso ga can kayan miya da su alayyawo zaku gyara, gobe da asuba za'a aza tukunya" Da sauri na miƙe ina faɗin wash dan wani irin ƙara ƙuguna yayi mun mai zafin gaske. Toye na kwantar ya riga ya soma bacci a zaune. Tunda muka zauna zaman aikinnan ba mu bar aikin ba sai wajajen sha biyun dare, sannan kowa ya kwanta. Da asussuba kuwa washe gari muka tashi da aikin tuwo, dan kafin takwas na safiya mun kammala tuwonnan tas mun malmalashi mun jera a fantekoki. Zuwa ƙarfe sha ɗayan rana gidan biki ya cika danƙam da jama'ar biki, sai haya_haya kawai kake ji. Daga waje ma haka ƙofar gidan take danƙam da maza ƴan ɗaurin aure. Yaron Sakina ne yazo ya kirani.
"Umman Toye wai inji ummata kizo ki yi wanka" Allah sarki ni Iyabo. Kowa a gidan sai wanka akeyi ana kwalliya, yara da manya. Amman ni babu wanda yai mun ta yin wanka. Bin bayan yaron nayi har zuwa gidansu. A falon Sakina na samu Gwadabe da Bara'u suna zaune suna cin tuwon biki. Ƙur ya ƙura mun idanu, take na ji hawaye na shirin zubo mun, har numfashina na karkatsewa. Fitowar Sakina daga uwar ɗakine ya katse kallon ƙudan da muke ma juna.
"Maman biyu tun ɗazu nake ta jiranki ki zo ki karya ku yi wanka ke da Toye, sai mu ka ji shiru kuma" Kujera na samu na zauna duk illahirin jikina babu inda baya yi mini ciwo, kuma babu inda bai yi mun tsami ba, zazzaɓi ne kau a jikin nawa ma, ga jiri da ke damuna.
Ke dai bari, aikin abincin bikine bai bani damar zuwan ba. Kinga ko karyawa ma ban yi ba. Bara'u ina kwana ya akaji da taro?" Na faɗa kaina a ƙasa.
"Lafiya lau Iyaa Toye Tsuntsun soyayya, ya jiki_ jikin?"
Alhamdulillah. Na dubi Gwadabe nace. Ekaro oromi ( ina kwana mai gida?) Ajjiyar zuchiya ya sauke kana yace.
"Kin tashi lafiya, ya jiki_jikin naki? Wato kina ta aiki bayan kinsan likita ya hanaki aiki mai wuya ko? Gobe ma kowa zai watse daga yau biki ya ƙare, tunda yau za'a kai Amarya ɗakinta ai" Boyayyar ajjiyar zuchiya na sauke, dan jina nake tamkar a ƙaya wallahi. Zame jiki Bara'u da Sakina su ka yi su ka bar mana ɗakin. Suna fita Gwadabe ya dawo kusa dani ya zauna.
"Iyabona" Ya faɗa muryarshi na rawa. Kuka na fashe mishi dashi.
Gwadabe na roƙeka da girman Allah ka sauwaƙe mun zuwa taron biki ko suna na danginka. Ba ƙaramin muzanta nake yi ba. Ka ware mana wasu lokutan domin ziyarar danginka, amman ba lokacin wani sha'ani ba." Shiru yayi yana kallona idanunshi suka kaɗa su kai jawur.
"Ki ƙara haƙuri bisa wanda kike yi da dangina Iyabo. Nasan kina takura sosai, kuma kina shan baƙaƙen maganganu marasa daɗin saurare. Amman ni ko na so barinki a Kano, kinsan ba yarda Babala zata yi ba. Kuma hakan zai ƙara haddasa wata fitinarne. Iyabo bana son kukan ki, ki share hawayenki gobe da wuri zamu bar Takai ki yi haquri kinji?" Sai na ji tausayinshi ya kuma kamani, ga ɓoyayyar damuwa ina gani shinfiɗe a fuskantar shi, duk da yana ta ƙoƙarin ganin ya ɓoye mun halin da yake ciki. Amman na san Tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi. A hankali na furta.
Gwadabe na ganka a cikin damuwa meke damunka, kar kayi yinƙurin ɓoye mun, dan bama ɓoye ma juna damuwarmu. A kai nane ko Gwadabe?" Ajjiyar zuchiya ya sauke, tare da kamo hannayena dukka biyun ya ɗan matsesu kaɗan. Idanu na lumshe ina cike da tsantsar tausayin aurenmu.
MRS BUKHARI
*DAN ALLAH KUIMUN AFUWA NA SAURARI ƘORAFE_ƘORAFENKU AKAN KU WATA BIYU YAYI MUKU YAWA. AYIMUN AFUWA MU BARSHI A WATA BIYU, NA SAKE TURO WANNAN PEJINNE DOMIN IN MUKA DANNAR ƘIRKI DASHI. NAN DA WATA BIYU ZAKU JINI DA CI GABAN LABARIN NAGODE*🙏🏻🙏🏻
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm
NAMA YA DAHU.
ROMO ƊANYE
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
Lamba ta uku
"A game da abinda ya faru a gida can Kano ne kafin mu tawo. To da Yaya Hambali, da su Yaya Harisu duk sun amince akan Yaya Hambali ya tashe mu a gidanshi mu yi nesa dashi. To Babala tace dai a barta tayi shawara da su Goggo Iyatu. To kinsan Goggo Iyatu kusan ita take sake zuga Babala akan ki. Sabida Laila ƴar wajenta da Allah bai yi mun yi aure ba kamar yanda suka tsara tun muna tsumman goyo. To kinji abinda ya ɗaga hankalina kenan, tunda nasan bani da kuɗin da zan iya kama mana ko ɗaki ɗaya, balle ciki da falo." Ƙur na zuba mishi idanu.
Gwadabe duk abinda Allah yayi a kan mu me kyau ne. Allah ba zai ba danginka ikon tozarta mu ba da ikon Allah. Kayi haƙuri jarumina duk a akaina ake yi ma hakan." Murmushi yayi gwanin tausayi yace.
"A tunaninsu matsa mun lamba da zasu ci gaba da yi, shi zai sa aurenki ya sire mun. Billa aurenki kullum sake zame mun yake yi kamar yau aka ɗaura iyabo na. Kema ki ƙara haƙuri wata rana sai labari . Sannan ina da babban albishirin da na cancanci garjejen farin goro ɗan shagamu. Allah ya nufa nima na zama matuƙin Babbar mota na tashi daga karen mota. Ma'ana an mallakamun mota." Sakina ce ta shigo hannunta riƙe da langa da kofin silver ta dure shi a gabana.
"Sakko ki ci abinci ki yi wanka mu samu mu koma gidan biki, yau biki zai ƙare Amarya zata kwana a ɗakinta" Godiya na yi ma Sakina.
"Gwadabe Bara'u yana ƙwar gida wai kaje ku tafi" Da sauri ya miƙe, mu kai sallama ya fice dan yanzu za'a ɗaura auren ƴar autar tasu. Ni ko a gurguje na karya na yi wanka zuchiyata fal murna na san a ƙalla zamu samu sassauci daga talaucin dake addabarmu. , Sakina ta yi ma Toye wanka. Leshin ankon bikin Bose da mu ka yi wata shida daya wuce na saka. Leshi ne me tsada, dan ko sanda aka fitar da leshin na cire raina da yi, amman Gwadabe sai da ya je ya ciyo bashi yai mun domin ya fitar dani kunyar dangina, leshin ya sha ɗinkin buba da zani, na saka sarƙa fashion me kyau wacce Gwadabe ya siya mun a legas da suka je. Mayafina da takalmina ma sababbine wanda matar Tamu ta aiko mun daga Habuja, da naso in bari sai na haihu in yi fitar suna dashi. Gwadabe ne ya ƙi yarda yace lallai sai dai in sa a bikin gidansu nima in fito da kyau, dan su Yaya Haula suma sun yi ɗinke_ɗinken biki kala uku_uku. Ni kuma bamu da kuɗi leshin da na sa basu san na ɗinka ba, tunda mu ka yi bikin na ɓiyeshi a ƙasan akwati abunka da tattali irin na talaka. Fitowa nayi shar dani har ƴar hoda da jan baki na murza. Toye kuma riga da wandon Atampa na saka mishi da hular ashoke irin na yarenmu. Sakina ta riƙe mishi hannu muka nufi gidan bikin. Ƙofar gidan taƙi wutuwa sabida tsabaragen dandazon maza ƴan ɗaurin Aure, sai maƙota muka faɗa akan in an sassauta ma shiga cikin gidan. Sai wajajen kusan azahar ƙofar gidan ya sarara da mutane muka samu muka shiga cikin gidan. Da Laila na soma haɗa idanu, sai naga ta shiga ƙarame kayan jikina kallo har kirjinta na hawa da sauka irin na tashin hankali. Ni mamakine ma ya kamani. Ban bi ta kanta ba kai tsaye shiyyar Babala na wuce domin in sake gaishesu. Kowa na cikin ɗakin kallona yake yi baki a sake, Yaya Haula kuwa tsabar kallona da ta shagala tana yi sai da ta zuba ruwan miya a ƙafarta mai zafi kafin ta dawo hayyacinta. Koddibuwace babba a jikinta, amman leshina ya tsole mata idanu. Yaya Halima kuwa wuyana take ta kallo kawai. A tsarge na gaggsishesu bi da bi, suka amsa a daddaƙile in da sabo na riga dana saba tuni. Na ɗan zauna jim sai ga Amarya ta shigo ɗakin ita da ƙawayenta su su biyu. Ta tsugunna ta gaisa da kowa amman kallo wannan ban isheta ba.
Sauwama Amarya an sha kyau" na ce mata ina ɗan yaƙe. In kun tanka yarinyarnan ta tanka. Abunda ya kawota ta yi ta fice da ƙawayenta. Bayan na zauna kamar na awa ɗaya haka sai na koma tsakar gida, dan naga atana alwalar sallar azahar. Ɗakin ƙanwar mahaifiyar Sakina anan nayi Sallah, mu ka ci tuwo da Sakina, na koma tsakar gida muka shiga rabon tuwo ka'in da na'in. Ban zauna ba sai da aka gama rabon abinci kab tukunna. Zuwa bayan laa'asar kuma dangin ango suka tawo da fantimotin aure, daga nan kuma zasu tafi da Amarya. Ayarin su Asiya na bi mu kai ta fita da kayan ɗakin Amarya ana sakawa a mota. Su Yaya Haula da Zuwaira harda su a ƴan kai Amarya, mutane sai da suka cika Bus guda, sai ƙaramar motar Amarya da ƴan ƙawayenta. Muna shiga cikin gida muka tsaida sanwar tuwon dare ba mu muka nitsa ba sai wajen takwas na dare, sai lokacin na samu kaina na galabaita sosai, marata ciwo take yi mun tun rana haka na kwana da ciwon marar nan. Da sassafe muka kuma tashi da aikin gyaran gida da karin kumallo. Kokko da ƙosai mu ka yi, bayan an kammala karyawa baƙi suka shiga haramar komawa garinsu, sai wanka akeyi. Sai da mu ka yi wanke_wanke muka share wajen tas kafin na samu bokiti na samu ruwan wanka mu ka yi ni da Toye. Gwadabe ne ya neme ni a tsakar gida ya same ni.
"Ki hanzarta ki shirya yanzu zamu kama hanyar Kano. Ana mun lodi a mota zamu kai kayan Legas." Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
A shirye nake ni kam tsab.
"To ki shiga ki yi sallama da matan gidan, sai ki same ni a ɗakin Babala" Yana faɗar haka ya juya da sauri. Ni kuma na shiga