Showing 33001 words to 36000 words out of 61296 words
dinga yi maka tayin wulaƙanci. Dubu goma sha biyar ta taya atampopinnan kuma manyan atampopi harda Holland, da ƙyar muka ƙarƙare a sha bakwai da ɗari biyar. A cikin daren yau daga ni har Gwadabe kusan kwana mu kai muna Sallah muna adda'a, wallahi har akai sallar asuba bama ko jin digon bacci sai jarababben ciwon kai daya jarabeni. Ana fitowa Sallah na jiyo sallamar maza a ƙofar ɗakinmu. Baban Nazifi ne yake sanar dani dattawan unguwane suka zo duba Gwadabe. Hijabi nasa kafin nace su shigo. Gaggaisawa mu ka yi dasu, tare da yi mun jajen abinda ya faru, daga bisani kuma suka shiga ciki dubo shi. Ni dai jigum nayi a wajen na rasa me ke yi mun daɗi, a wajen suka fito suka taddani, su kai mun sallama suka fita. Ruwan wanka na juyo a bokiti na shiga da sallamata. Na samu Gwadabe yayi jigum yanata aikin tunani, na sani ban isa na hanashi tunani ba, domin jiya uwar haka da lafiyarshi ras ya fita.
Gwadabe bari in ɗan goggoge maka jikinka da tawul sai ka yi asuwaki mu samu mu je asibitin ko?" Sai da ya sauke nannauyar ajjiyar zuchiya yace.
"Na yi ma Yaya Hambali magana kan batun asibiti da muke son zuwa. Bai goyi bayan hakan ba, yace ciwon yafi kama da sammu, tunda babu inda yake yi mun ciwo, sai nauyi da ƙafafuna su ka yi, kuma Oga lurwanu ma yace sammu ne"
Hakane Gwadabe, amman zuwa asibitin ai yana da amfani, in muka je suka auna basu ga komai ba shikenan sai a yi na gargajiyan
"E haka na ce mishi nimaa. Ya dai ce Da'u zai tsaya mu tafi asibitin tare." Goggoge mishi jikinshi nayi tas, na saka shi a po ya rage mararshi, yayi asuwakin zamani, kana na bashi tea da burodi, da ƙyar yaci burodi yanka ɗaya, ni ko iyaka shayin kawai na kurɓa, mu ka jiyo sallamar Uwani.
Miƙewa nayi na fita falon ina sharar hawaye, ita kanta uwanin kuka take ta faman yi. Muna cikin haka Da'u da Nazifi suka shigo, basu kula mu ba, ciki suka wuce abinsu. Ni kuma na sallami Toye ya tafi makaranta. Fitowa dashi suka yi, Da'u sai tsaki yake yi. Mu dai bayansu muka bi, ashe sun kira tasi tana tsaye a ƙofar gida. Asibitin Murtala muka wuce, ganin halin da muke ciki sai wani likita yace bari ya bamu gado ayi duk binciken daya dace a tsanake zaifi. Hakan kuwa akayi aka bamu gado a Ward ɗin maza, Da'u da Nazifi kuma jin an riƙe mu a asibiti sai suka yi tafiyarsu. Hawaye kawai nake sharewa, likita yace mu zauna daga waje.
"Yanzu tsabaragen ƙiyayya yana ciwon ma ba zasu taimaka mishi ba, a lokacin da yafi buƙatar taimakonsu ba. Tafiya fa suka yi Iyabo" Takaici da damuwa duk suka taru su kai mun yawa sosai. Muna zaune aka fito da Gwadabe a keken da ake tuƙa guragu zasu tafi ayo mishi hoto.
"Baiwar Allah ya kamata ace akwai wani namiji da zai tsaya tare da marar lafiyan ba ke mace ba, kinga da su zasu sashi a keke, kuma su tuƙashi zuwa ɗakin hoto. " Nurse ɗin daya tuƙo Gwadabe ne ke magana. Gwadabe na kalla, shima ni yake kallo ya dafe kanshi da hannun dama, idanuwanshi tamkar garwashin wuta.
To mun gode, suna hanya masu kula dashi ɗin." Na faɗa mishi haka, kafin ya miƙo mun wata takadda.
"Ki je wancan tagar ki biya kuɗin hoto, in mun fito sai ki bari in mun dawo ki bani" Karɓa nayi jikina na rawa, su kuma suka wuce.
Kuka na fashe dashi babu ƙaƙƙautawa, Taiwo da Kahinde suna ganin ina kuka suma sai suka soma kukan.
"Iyabo kije ki dawo, wannan kukan ya isa haka kinga ga yara suma sun soma. Jakata na kinkima na je na biya kuɗin hoto na dawo. A taƙaice sai da muka wuni zumbur babu wanda yazo daga dangina ko na Gwadabe, Hafizu mijin Uwani ne ya kawo mana abincin da muka ci, da naga magriba na shirin yi na dubi Gwadabe nace.
"Inaso zanje gida in dafo ruwan zafi, in tawo da tabarma."
A'a su Babala suna hanyar zuwa. Ɗazu da likita ya kiraki Yaya Hambali ya kira ni a waya" Baima gama bayanin ba sai gasu sun iso dukkansu, harda Yaya Haula tana riƙe da filas na ruwan zafi da kular abinci. Da sauri na tashi a kujera na ba Babala waje ta zauna. Abu na farko daya fito daga bakinta shine.
"Ba ga irinta ba, akan son gwanance mace kaje ka kai kan ka mahallaka. Waya sani ma ko daga danginta ne aka bugo maka wani agumun. Duk da sammu a tsakanin direbobi abune mai dogon tarihin gaske muma munsan tarihin. Gwadabe bazan yi maka baki ba, amman kaji na rantse maka da girman wanda yayi ni yayi ka buwayi gagara misali. Kana tashi zaka sallami wannan matsiyaciyar ka auri Laila, in ba haka ba sai in tsine maka ka bi duniya uban kowa ya rasa ka. Banga riba a aurenta ba sai ci baya da koma baya da rayuwarka tayi.
Ke kuma na dawo kan ki, ki zauna da shirinki, Allah na tasan kafaɗarshi ƙarshen zamanki kenan dashi, ya'isa haka, inason yarona ya dawo yanda yake. Kin shigo cikin zuriyarmu kin tarwatsa mun kan yara." Da kuka taƙarashe zancen, yaranta na bata baki kan ta dena kuka. Baban Nazifi ya ɗaura da cewa.
"Ya zame mishi dole ya rabu da'ita matsawar mune danginshi. In kuma zai sake iyaye da ƴan uwane sai mu gani. Sabida wannan baƙar kadarar matar tashi marar asali yasa na kasa tallafama Gwadabe Babala, amman a baya wanne irin so ne banyi mishi ba." Wannan yace wannan, wannan yace wancan kowa sai da ya tofa albarkacin bakinshi. Mu dai mun yi shiru kamar ruwa ya cinyemu.
"Babala kima Allah kar ki zama silar rabani da Iyabo, son gaskiya take yi mun, bazan iya samun macen da zata soni rabin nata ba. Iyakar zamana da'ita babu abunda ta taɓa yi mun na assha." Miƙewa Babala tayi tace.
"To gaka ga Iyabo. Ta maye maka gurbina dana ƴan uwanka da baka da tamkarsu. Ta zauna tayi jinyarka, ni kuma babu ni babu kai. A cikinku duk wanda ya tsaya ya kula dashi ban yafe mishi ba, ko ya cire dukiyarshi ya ba Gwadabe. Haula ɗauki abincin da kika kawo mu koma dashi.
Da gudu nasha gaban Babala ina haki nace.
Babala kiyi haƙuri ni nayi miki alƙawarin Gwadabe na warkewa a ranar zan bar gidanshi rabuwa irinta har abada. Bazan iya tafiya in barshi a wannan halin bane, ko babu komai uban Ƴaƴanane, kuma a zamanmu bai taɓa cusgunamun ba. Nima dashi da aurenshi ya fice mun a raina, wallahi ko baki ce ba ya zama dole in rabu da Gwadabe dan ba shi bane autan maza ba, kuma ba mutuwa zanyi ba. Amman fishinki masifa ne, yana buƙatarku yaya Harisu, Babala Gwadabe na buƙatar adda'arki" Duk wannan maganar cikin dimuwa nake yinta. Majinyatan dake kwance, da masu jinyarsu kab hankulansu a kanmu yake. Tsawa Babala ta daka mun.
"Gafara dallah. Ke baki da uwa dama da sai in ce ki je kisa ta mai adda'ar mana. Tunda akan ki wannan ciwon ya same shi, ke zaki yi mishi jinya dan ubanki"
Fuu suka fita suka barni. Bansan sanda na durƙusa a ƙasan ɗakin ina salati ba, Allah nake ambato a lokacin wani irin duhu ne ke mamaye mun idanuna. Uwani ce ta ɗaga ni.
"Tashi Iyabo meye haka kike kuka kamar ƙaramar yarinya, ɗakinnan kab ke suke kallo. Rabuwa da Gwadabe shi ya fiye miki." Jaye ni tayi ta zo ta zaunar dani a kujera. Gwadabe yana kwance idanunshi a buɗe suke amman yayi zurfi a cikin tunani hankalinshi baya tare damu.
"Bara in fita bakin asibiti in siyo muku ko da tuwo ne. Zan yi ma Hafizu filashin in ya kirani zan sa ya kawo ruwan zafi." Bani da niyyar bata amsa, itama bata buƙaci amsar tawa ba ta fice. Ƴan biyu suna ƙasa na shinfiɗa musu ɗankwalina suna bacci. Har Uwani taje ta dawo ni da Gwadabe babu wanda ya tanka ɗan uwanshi. Tayi yin duniya muci abinci mun ƙi yarda, damuwar da take gabanmu ta wuci a tsaya ana saka lomar tuwo a baki, ni in banda ɗaci babu abunda bakina yake yi. Mijin Uwani ma yazo yayi roƙon duniya kan mu ci abinci, ni ko magana na kasa, Gwadabe ne ma yake iya cewa a ƙoshe yake.
"Iyabo ki taso mu je gidana, in yaso Hafizu zai kwana gobe mu ma dawo"
"Ku barta tare dani, ina buƙatarta a kusa dani, damuwar zata yi mun yawa" Cewar Gwadabe, sai lokacin hawaye suka surnano da idanun Gwadabe wasu sirara. Uwani ta tattare yaran su kai mana sallama suka tafi. Da ƙyar ma'aikatan kiwon lafiya suka barni zan yi jinyar Gwadabe kasancewar ward ɗin na maza ne, akwai wata mata itama ita take ma mijinta jinya, sai muka zama mu biyu.
Shiru wajen ya ɗauka na kasa rarrashin Gwadabe shima ya kasa rarrashina. Wannan daren na ba makaranta gari ku hasaso da kawunanku.
Washe gari sassafe aka sake zuwa aka fita da Gwadabe zuwa wani hoton. Kafin a dawo dashi sai ga Yemisi da Burodami Debisi, da Lekan. Hannunsu riƙe da lodoji. Shigowarsu ke da wuya aka shigo da Gwadabe. Da Burodami Debisi aka kinkimeshi zuwa gado.
"Sannu Gwadabe ya jikin, ashe abunda ya faru kenan?" Cewar Burodami Debisi.
"Jiki sai godiyar Allah, Iyabo likita yace yana son ganinki" Tashi nayi na nufi ofishin likita.
"Duk binciken mu ya tabbatar mana komai nashi lafiya suke. Mun yi hoto har sau biyu bamu ga komai ba. Mun sallameku inaga ku nemi na gargajiya zaifi. Ina mai baku shawarar ku sai mishi keken tuƙa marasa lafiya, yafi muku sauƙi da a dinga kinkimarshi. Ga takaddar sallama, kije ki biya Allah ya ƙara sauƙi" Sai da na share hawayena kana na amshi takaddar bance mishi komai ba na fita. Kuɗin hannuna sai da suka ƙare tas ban tsira da ko ficika ba. Burodami Debisi da Lekan su suka taimakeni wajen ɗaukar Gwadabe muka samu Taxi ta kaimu har ƙofar gida. Baban Nazifi da Yaya Harisu suna tsaye a ƙofar gida su Lekan suka zo suka shige da Gwadabe, na mara musu baya. Tunda muka dawo maƙota sukaita tururuwar shigowa gaishe da Gwadabe, su Iyaa Debisi ma sun tawo kusan dukka gidan, sun kawo abinci da dubu biyar, haka mu kaita karɓar jaje daga mutanen arziki. Babala kuwa a bakin Gude nake jin wai ta koma Takai Laila ma ta je ganin gida. Atampopi na na ɗura a buhu kab harda ma ɗinkakkun bar bari ba, kala huɗu na ware kawai, na ɗauki buhunnan na fita hankali da nutsuwata basa tare dani sam. Siyan wulaƙanci sosai akaima kayan, amman biyan buƙata yafi godon buri, Gwadabe mutum da ɓari ne a wajena. Keken ɗaukar marasa ƙafa ko tsofaffi na siyo ta hannu akan nera dubu ashirin da biyar da ɗari takwas. Ina shigowa gidan kallo ya dawo gareni, ni dai babu wanda na kalla takaina kawai nake yi. Ko Gwadabe yasha ruwan mamakin ganina da wannan wul ciya sosai. Ni dai bance uffanba na tallafeshi na sashi a kan wul ciya ɗinnan. Hawaye ya soma sharewa, ni kuma ina mishi murmushi.
"Mala'ikun Allah ku shaida na sama rayuwar Iyabo albarka, kuma na ɗaga mata ƙafafuna domin ta shiga aljanna. Allah yai miki albarka ya kawo mana mafita akan jarabawar da take kanmu"
Ameen Gwadabe, ka dena kuka. In sha Allah tunda ina nan kafi ƙarfin zubar da ruwan hawaye."
Daga haka muka shiga suntirin bin masu magungunan gargajiya, mu ke nan kullum a tafe, amman babu canji kullum jiya e yau. Tafe tafe sai da mu ka kwashe tsawon wata uku muna abu ɗaya. Dangina da suke ɗan tallafamun suma suka gaji suka watsar. Babala sau biyu kaɗai tazo ta duba Gwadabe, amman ƴan Takai kam sun zazzo sosai. Sakina da Bara'u kam mayar da gidanmu su ka yi kamar aje kasuwa a dawo. Duk wata jigilar zuwa nemo maganin makarin sammun da akaima Gwadabe, tare da Bara'u da Sakina muke zuwa. Abincin da zamu ci Bara'u ke kawo mana. Ayashe da Tamu suma sun mana ƙoƙari sosai. Babbar damuwata ɗaya ce tak har yanzu babu wani sauƙi da aka samu."
MRS BUKHARI
3064127935
Buhari Ibrahim Ladan
First bank
Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan.
Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun
Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya.
Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE)
300 kacal zasu iya kuɗin karatu
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm
NAMA YA DAWU
ROMO ƊANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
10
Duk wannan ƙibar tawa da kuka ji labarinta, wallahi ta zuge sosai, na gama ramewa na fice a hayyacina sosai. Shi kanshi Gwadabe yafi tausayina fiye da kanshi. Bara'u kullum a cikin jinjina ma ƙoƙarina gami da amanaa suke yi. A kullum roƙona shine Allah ya ba Gwadabe lafiya, ya yanke mishi wannan zaman. In zaman cikin ya isheshi shi da kanshi yake tuƙa kekenshi ya fita ƙwar gida ya sha iska. Mun gama siyar da komai namu kuɗin ya ƙare a magani, ɗakina goduwar kujer da kafet kaɗai ya rage, sai tarkacen kwanuka da katifa , itama sabida Gwadabe na barta Wata rana ina zaune ina wankin kayana dana yara sai ga Uwani ta shigo, Gwadabe kuma yana ƙofar gida ya ɗan fita shan iska
"Uwar biyu wanki kike yi ne?"
Wallahi kuwa, daga ina haka na ganki afujajan?" Na tambayeta tare da kallonta. Sai da ta cire mayafinta kana tace.
"Hmm wata harkar arziki na samo Iyabo. Kin ganni daga cikin gari nake gidan Hajiya salamatu, wata matace dake kai ƴan mata da matan aure ƙashashen larabawa ko ƙasashen turawa. Amman kafinnan na samo miki maganin karya sihiri garanti, daga cikin ayayoyin Qur'ani mai girma. Bari in karanto miki, muddin kuka riƙe wannan da izinin Allah kuka yazo ƙarshe a cikin kwana na bakwai Gwadabe zai miƙe da ƙafafuwanshi." Ina jin haka na zabur na saki wanki. Na juyo na zuba mata idanu.
Dan Allah faɗi ina saurarenki Uwani" Dariya tayi tace.
"Ɗakko biro da takadda ina faɗa miki kina rubutawa, da izinin Allah waraka ta zo." Da sauri ba shiri na yago takadda, na ɗakko fensirin Toye na dawo.
"Da farko zaki samu ruwanki mai tsabta.
Sai ganyen magarya koraye bushewar inuwa guda bakwai.
Sai a karanta suratul fatiha a cikin ruwan da aka zuba magaryan, a dinga karantawa numfashin baki na komawa cikin ruwan
Sai a karanta Ayatul kursiyyu ( aya ta 255 na cikin suratul baƙara).
Sai a karanta suratul a'afaaf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122.
Sai a karanta yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan ta 82.
Suratul kafirun ƙafa ɗaya.
Falaƙi da nasi ƙafa uku_uku
Sai a karanta wannan adda'ar.
Allahumma rabban nas,azhibil ba'as ashfi wa antash shafila shifa'a illa shifa'uk shafi'un la tugadiru sakaman
Ƙafa uku za'a karanta.
Sannan za'a iya karawa da wannan adda'ar
"Bismillahi urkika min kulli shai'in yu'uziyaks wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkika
Shima ƙafa uku
In sha Allah ta'ala idan aka karanta wadannan kuma mutum ya dinga sha sau biyu a rana safe da yamma, yana kuma wanka dashi a waje mai tsabta, ko kokuma a jiƙa tawul a goge jikin marar lafiyan da ruwan maganin. Da izinin Allah cikin sati ɗaya mutum zai warke in dai sihirine a jikinshi.
( Kuma zaku iya jarabawa. Wasu malaman sun ce yana da kyau wanda yake da lafiyarshi ma yayi, domin hakan ka iya zama rigakafi kafi magani kareshi. Wallahu mista'al)
Wawuyar ajjiyar zuchiya na sauke tare da yaƙinin sauƙi ya zo ma Gwadabe. Duk da abaya masu magani sun bamu wasu mayuka tare da tofin ayoyin Allah a ciki mun yi amfani dasu da dama. Wasu kuma mu da kanmu muka zubar dasu, dan ganin shirka ta shiga cikin lamarin, amman wannan sai naji na samu nutsuwa dasu ainun.
Nagode sosai ƙawata Allah dai ya bar zumunci. Bari ki ga da zafi zafi ake dukan ƙarfe bari in wanko ganyen magaryana, ina da ruwan sama cikin robar fenti sai in yi dashi. Sai fa na gama zan samu nutsuwa." Da sauri na je na ɗebo ganyen magarya adadin na buƙatar na wanko, na kinkimo ruwa da Qur'ani izu shittin.
"Af na mance sai an daddaka ganyan magaryar ake zubawa." Cewar Uwani kenan. Da haanzari na ɗauko turmi na daka na zuba a cikin ruwan da bismillahi. Sai da muka kammala na samu nutsuwa har na sauke ajjiyar zuchiya. Daki na kai ruwan maganin na adana kana na fito."
"To bani labarin abinda ya kai ki gidan Hajiya Salamatu, uwar shige_shige Uwani"
"Wallahi Iyabo ƙasar zan bari zan tafi nemo kuɗi. Amman shekara biyu kawai zan yi in dawo" Zare idanu nayi ina dubanta da mamaki.
Ƙasar fa kika ce, to aurenki da yaranki a hannun wa zaki barsu Uwani?" Ajjiyar zuchiya ta sauke tace.."Hafizu zai lura dasu Iyabo. Wannan talauci namu yayi yawa. Duk abinda Hafizu fa ya soma babu albarka sam a ciki. Kuma shi ba jari ba. Ke yanzu haka maganar da nake yi miki ma ina gidanmu fa da yaran. An koremu a gidn haya ko ince miki an watso mana kayanmu tsakiyar layi da ranar Allah. To Hafizun ma shi ya bani shawarar ko zan nemi aikatau na ƙasashe da ake zuwa, ƙanwarshi ma yanzu haka tana Canada a gidan aiki, shima in ya samu tare zamu tafi. Ni fa Iyabo wallahi tafiya zanyi. Su Hajiya ma basu san me ake ciki ba. Babbar damuwar shine ita Hajiya Salamatu tace sai dai in ajjiye dubu Hamsin da kuma ni zan yi ma kaina fasfo. In kuma ba haka ba duk zata yi mun amman zan kai wata shida kafin in gama biyan kuɗin da duk ta kashe mun. In kuma na yi fasfo na ajjiye dubu hamshin, da zaran na tafi a cikin wata biyu zan gama biyan kuɗin girji" Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
To amman babu wani haɗari a cikin tafiyar dai ko. Kuma ina fatan bata ɓarauniyar hanya za'a tura ku ba Uwani, kuma kin