Showing 327001 words to 330000 words out of 397668 words
halin da ake ciki ma wai ya nema mani transfer, kawai takadda yake jira, nan da kwana biyu zata iso, inda ya maidoni nan Abuja, anan ne zan idasa karatun nawa, wai a cewar shi baya son yin nisa dani.
Naji daɗin hakan, lokaci yayi nima da zan roƙe shi ya koya man mota, Tunda ina da motar da na samu kyauta lokacin biki na, sai in dinga yin day kawai a kullun, ba sai na zauna Hostel ba da aure na.
Cikin wayau na sako mashi maganar Nihal, ƙoƙarin dakatar dani yake yi, ban ƙara cewa komai ba, har saida ya kammala faɗace faɗacen shi, kunsan muskili bai iya zuciya ba, sai a lokacin ne nikuma cikin siyasa da kissa irin tamu ta mata na sanar dashi yanda mukayi da Nihal ɗin, harma ayyukan da ta tayani yau mukayi.
Shiru yayi mani, kaman yayi bacci, har yanzu dai yana naniƙe dani, wani irin so na ne yake ji yana ratsa shi, yana mai ƙara gode ma Allah da mallaka ta a matsayin mata da yayi. In ba haka ba, inda wata ce yanda nasha wahalar Nihal, zan so ne ma ace rayuwar gidan tata ta lalace, sai gashi nice ma ke roƙon shi, akan cewa ya sanya baki a gyara komai.
Saida ya rungume ni yana mai sanya mani albarka, sannan yace mani, in bari yaga kamun ludayin nata, idan yaga dagaske ta cenza, insha Allahu zai san yadda Zatayi ta koma gidan nata, Amman maganar ya hana Nureen ƙarin aure ma bata taso ba, tunda shi aure lokaci ne, kuma raine dashi, dan haka koma menene ya same ta ita ce ta ja ma kanta.
Lamo nayi ina sauraren shi, inda yake sanar mani tafiyar da zaiyi goben shi da Bilal. Addu'a na dinga kwararo mashi, ina mai jaddada mashi matsayin Mom a gareshi, kwarai ya yaba a gareni, kuma ya ƙara tabbatar ma kanshi cewa koda abunda yake ta ɓoyo ya fallasa, shi yasan ba zan taɓa juya mashi baya ba.
*******
Tun tana sa ran taji an fasa ihu daga sashen namu har dai taji tsit, kenan ɓawon ayabar da ta sanya bai yi amfani ba, duk wahalar da tasha kafin taga ta samu shiga kitchen ɗin nawa ta ɗebo ɓawon ayabar har ta kai da zuba mani, ba tare da kowa ya ganta ba, a duk tunanin ta, muddin santsin nan ya kwashe ni, ƙila ma ba karaya ɗaya ba, idan ta kai goma ƙila sai nayi ta.
Saidai saɓanin yanda ta zata, sai ji tayi shiru, kuma a kan idanun ta Ya Ameen da Bilal suka dawo. Me hakan ke nufi kenan? Suna nufin sunga ɓawon ayabar ne, ko kuma ta faɗin ihun dai ne Allah bai sa taji ba? Koma dai menene zata bari zuwa safiya, domin taji abunda ya faru, Amman tana da tabbacin zuwa safiyar zata ga an cicciɓo Suhan ɗin zuwa asibitin ƙashi...
Kaman yanda ta kwana sauraren farin saƙo a gareta, haka Ya Ameen ya kwana tunanin halin da yake fuskanta, da kuma dalilin zuwan ɓawon Ayaba sashen nashi, ya tabbata Suhan aka ƙulla ma hakan, sannan yayi imanin cewa koma wanene yayi hakan yana cikin gidan, sannan yasha alwashin koma wanene gamuwar tasu ba zatayi daɗi ba.
~Oum-Deedat ce~
[1/24, 10:00 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~Page 78~*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Abin Da Ake Fada don kawar da kaidin shaidanu Masu Taurin Kai.
أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.
Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~78~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Kusan zan iya cewa kwana yau Ya Ameen yayi bisa darduma. Ina kallon shi, tun ina binshi sallar har dai nima na ɓingire a wajen, saida ya kammala ne sannan ya ɗauke ni cak zuwa saman gadon.
Ga mamaki na ma, koda ya tada ni sallar asuba tsab na ganshi. Tun daga fuskarshi da idanuna suka sauka akai, nake binshi da kallo.
Da sauri na miƙe, a daidai wannan lokacin na saba ganinshi da farar jallabiya ko mai ruwan ƙasa, saɓanin yau da yake sanye cikin wani lallausan Yadi ɗan ubansu, kalar army Green mai duhu an mashi ɗinkin osinbajo,
Ai da sauri na tashi zaune ina mai furta "Dear" a laɓɓan nawa. Shima wara kyawawan idanun shi yayi saman fuskar tawa, yana mai shafa ta da tafukan hannayen shi a hankali, lokaci guda kuma yana mai sake mani wani irin lallausan murmushi.
"Nasan kin gaji my wife, gashi kuma lokacin sallah yayi, ki daure ki tashi kiyi sai ki koma" Abunda ya furta man kenan a hankali, har yanzu hannayen nashi na bisa fuska ta.
Zuro ƙafafu na nayi daga bisa gadon, ina mai ture duvet ɗin gefe, sai kuma na miƙe, har yanzu da kallon tuhuma nake binshi. Ya kula da hakan, sai ya saki murmushi wanda ya ƙara ƙawata fuskar tashi da take fayau da ita, kaman wata ɗan daren sha huɗu.
Buɗe baki nayi da niyyar cewa wani abu, muka ji ladan ya sake ƙwala kiran sallah, da sauri ya manna man side peck, yana mai cewa dani "Dear bari inje masallaci in dawo zamuyi magana" da "To" na bishi, zuciya ta cike da alfaharn samun namiji kaman Ya Ameen, ta fuska da dama ya haɗa dukkanin wasu abubuwa da ake buƙata wajen namiji, saidai ya zuwa yanzu ɗin zuciya ta ta fara karaya da wasu al'amuran, ko bai faɗa ba nasan yana cikin wani yanayi, akwai abunda yake ɓoye man, tau kwana yayi sallah, kuma ko daya koma ya ɗan kwanta, ina jin shi kasa bacci yayi, sai motse motse da yake ta faman yi, ƙarshe ma laptop ɗinshi ya tashi ya jawo ya cigaba da danne danne.
Jiki a sanyaye nake aiwatar da komai, har kai lokacin da na kammala sallar, ina zaune kan sallayar ne ya shigo. Tun daga falo ƙamshin turaren shi yaman sallama. Miƙewa nayi ina mai naɗe sallayar.
Ta bayyana naji an rungumo ni gabaki ɗaya na, hadda hijab ɗin da ban cire ba.
"Good morning wify" Naji ya faɗa a hankali iya kunne na.
Juyowa nayi ina mai sake shigewa cikin jikin shi.
"Morning my Adorable Hubby"
Mun kai minti biyu haka tsaye, kowa da abunda yake ƙissimawa, yayinda nidai ɗan murmushi nake saukewa. Ya Ameen komai nashi daban ne.
Hannu na yaja zuwa bakin gadon ya zaunar dani. Shima zama yayi, yana mai zame baƙi siɗik ɗin takalmin shi cover shoe da suka ƙara taimakawa wajen fitar da ainahin Sirrin kyaun kwalliyar tashi, da gani dai ba sai na faɗa ba, kai kanka kasan sunci kuɗi.
"Ya gajiya?" ya furta a hankali, idanu na cikin nashi. Gaza cigaba da kallon shi nayi, sauke kaina ƙasa nayi ina mai murza yatsun hannu na.
Hannuwan ya kamo dukansu zuwa cikin nashi.
"Am sory dear na Gaza samun wadataccen lokacin da zan kasance dake, please ki ƙara haƙuri wasu ƴan abubuwa ne just a little, Amman insha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe" ya faɗa a tausashe yana mai karya kai gefe.
Gyaɗa mashi kai nayi, nasani dole akwai wani abu, saidai bana son saka kaina sosai a cikin irin hidimar mutane kaman su Ya Ameen, su sun saba, kuma na kula kaman yana da zurfn ciki, kada tun auren namu baije ko ina ba, yaga kaman ina mashi kutse ne a al'amurra.
Saidai na sani mata da dama ire-iren irin wannan hidindumun na masu kuɗi, shi ke ci masu tuwo a ƙwarya, Kaga an wadata mace da komai, amman a gaza sama mata lokacin ta dana yaranta.
Kanshi naji daidai saitin nawa, yana mai manna goshin shi bisa nawa, tsinin hancin shi yana mai gogar nawa, a hankali na lumshe idanu na, ina jin yanda zara zaran gashin idanun shi ke yawo bisa fuskar tawa, alamun dai ƙare mani kallo yake yi.
Murmushi na saki a hankali. Buɗe baki nayi da niyyar ce mashi wani abu, naji yayi caraf da leɓen nawa, ban mashi musu ko gardama ba, na kula ɗabi'a da al'adar shi ce, saboda haka na bar shi yayi yanda yaso.
Ganin kaman kayan nashi zasu yamutse ne, ya sanya ni ɗan matsawa baya, ina mai kwantar da kaina bisa faffaɗar kafaɗar tashi, numfashi nake saukewa a hankali, yayinda shima har yanzu idanun nashi suke lumshe, sai ya kwantar da kan shi bisa nawa kan.
Munkai tsawon lokaci haka, wata irin ƙaunar Ya Ameen ce ke nusa ta, ya zuwa yanzu na fara jin cewa ba zan iya kaiwa ko ina ba, ba tare da mijin nawa ba. Ban sani ba, ada cen ashe ban mashi komai ba, na daga cikin irin ƙaunar da nake mashi a yanzu.
Ko a mafarki ban taɓa kawo ma raina zan dace miji irin haka ba, mai sona, ƙauna ta, gani da tattalina ba.
Ganin mun gama hutawa daga aikin saƙonnin da muka tura ma juna ne, ya sanya ni Miƙewa a hankali, ina cemashi "Zanje kitchen Yaya, ba zaka fita haka ba, baka ci komai ba"
Baice man komai ba, saima Miƙewa da yayi shima, hannu na cikin nashi muka nufi kitchen ɗin.
"Me za'a bani Dear Mrs Ameen?" ya faɗa cikin zaulaya shima.
Murmushi nayi nima ina mai ce mashi "Oya guest mana" hannu ya ɗora daman bakin shi, alamun tunani, sai cen yace "Yes i got it" baya naja, ina mai jingina baya na da cabinet.
"Uhm faɗi muji idan Miji zai iya karantar zuciyar matarshi" nima na faɗa cikin dariya mai ɗan sauti.
"Cake and meant tea" ya faɗa yana mai karkaɗa hannu, shi ala dole hakane a cikin zuciyar tawa.
Ai bansan lokacin da na ƙyalƙyale da dariya ba. Tsaye yayi tana mai ƙare ma fuska ta kallo, dariyar tawa sai ta bashi dariya shima, kuma ta birge shi.
Akwai wani Sirrin kyau tattare da matar tashi, natsuwa da kuma sanyin halin ta, na daga cikin abunda ke ƙara jan hankalin shi zuwa ga Suhan ɗin.
Mu biyu muke ta dariya a cikin kitchen, har ta kai ga bansan lokacin da na jini a cikin ƙirjin nashi ba. Rungume ni yayi tsam yana mai furta mani kalmomi masu daɗi na so da ƙauna.
Abunda ya faɗa shi ɗin na mashi, yana ci tana man labari kala kala. Nidai kallon shi kawia nake yi, ashe haka Ya Ameen yake? Duk wannan miskilancin da take fama dashi da ina ya tafi?
Muna cikin haka ne wayar shi ta ɗauki tsuwwa.
Ya Bilal ne, saboda haka yace mashi ya shigo kawai ai bai kulle ƙofar ba, da sauri na kalle shi, ya gane abunda nake nufi, shigo man da ake yi, girgiza kai yayi alamun in kwantar da hankali na, yana mai nuna mani wata ƴar camera da take liƙe bakin ƙofar shigowar, wadda ni banma san da ita ba, duk zama na a sashen.
"Ko wanene ma ya cigaba tara shi nake yi, zan juyo kanshi ne" ya faɗa yana mai ɗan haɗe murya, sai Naji ba daɗi, ashe shima abun ya mashi zafi, ai banga ya nuna bane jiya, ashe akwai tudun da ya dafa? To Amman in hakane, me yasa tun jiyan baiyi checking ba? Domin yaga ko wanene ya shigo ya man hakan?
A hankali na sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya, ashe ina cikin kulawar Ya Ameen aduk inda yake? Lallai dace ne babba samun miji ɗin kaman Ya Ameen
Shigowar Bilal ɗince ta katse man tunanin da nake yi.
Miƙewa nayi ina mai gaishe shi, cikin sakin fuska ya amsa mani, har zaulaya ta yake yi, wai da gayya muke mashi wani abun, dan munga Ummi bata nan, to ai shima ta kusa dawowa dai, domin ma yau ne ake taron sunan.
Murna sosai har cikin raina, da anan ƙasar ne babu abunda zai hana ni leƙa ma Ummi, itama ta nuna mani so, ta jani a jiki sosai, tun kafin ma in zama yanda na zama.
"Ya sunan baby ne Ya Bilal?" na furta hakan ina mai kallon fuskar Ya Ameen ɗin da zaƙuwa.
Nuna mani Ya Ameen yayi, sai ban gane me yake nufi ba, na kalli Ya Ameen ɗin ina mai ɗan haɗe fuska.
"Ka sani shine tun jiya baka gaya man ba?" na faɗa cikin ƴar shagwaɓa, shima kallona yake da murmushi, wannan shagwaɓa tawa ko ina na koyo ta? Sipping tea ɗinshi yake yi a hankali a hankali.
"Kai a ina ka faɗa man malam? Salon kaja man wata rigimar ne?" ya faɗa yana mai maida duban shi zuwa inda Bilal yake tsiyaya tea a Mug.
"Al'ameen" ya faɗa shima ba tare da ya kalli inda muke zaune ba.
Babu wanda ya fahimta cikin mu. Shiru ne ya biyo baya, har kai lokacin da ya ɗago yana mai kallon mu cikin dariya "Yaro dai yaci sunan mijin ki, na mashi huɗuba da Al'ameen, ina fatan kuma Allah yasa yayi koyi da mai irin sunan"
Ai ba Ya Ameen ba, har ni saida wuta ta ta ɗauke na tsawon wucin gadi.
Wane irin aiki ne Ya Bilal? Ƙauna mai tsafta, ƙauna ta tsakani da Allah.
Kawai gani nayi Ya Ameen ya dire Mug ɗin tea ɗin nashi, ya miƙe gami da dosar inda Bilal ɗin take zaune. Rungume shi yayi cikin wata irin ƙauna, amintaka da soyayya.
Ni kaina Miƙewa nayi tsaye, ina mai haɗe hannu na dukansu, wani irin tsammm nake ji a jikina, bance ba za'a samu irin wannan abokantakar ba, saidai sai an bincika, sai an tona, ba duka ba.
"Ka gama man komai friend, nagode nagode Allah ya barmu tare, ya kauda dukkan wani abu na ɓacin rai daka iya shiga tsakanin mu, sannan ina sanar maka, tun daga rana mai irin ta yau, duk wasu buƙatocin takwarana na ɗauke maka su, karatun shi, da dukkan abunda zai buƙata har auren shi, indai muna da rayuwa, Allah ya raya mana shi, ya shirya shi a bisa tafarkin addini madaidaici, sai ka buɗe mashi account dan Allah zan dinga saka mashi kuɗi, duk Abunda take buƙata a ɗauka ciki ayi mashi, wannan tukuici ne, kuma ba kai nayi mawa ba, yaro na nayi mawa, saboda haka kada in sake inji kace komai friend"
Daga ni har Ya Bilal babu wanda kalaman Ya Ameen basu dakar ma zuciya ba. Sake rungume shi Bilal yayi, yana mai jaddada godiya gami da jin daɗi, yasan Ya Ameen, abunda yafi haka ma yana yi, kuma zai iya, wannan kaɗan ne daga cikin irin halayen shi kyawawa dake daɗa mashi kwarjini a idanun jama'a.
Fatan alkhairi na shiga yi masu, har yanzu sun kasa sakin juna, kuma koda suka koma suka zauna, su dukansu murmushin jin daɗi da annashuwa suke saki. Lallai wannan ƙauna daga Allah ce, ni ba zan ma iya fasalta ta ba, ko in kawo misalin ta.
Nima addu'oi na shiga zuba masu, su duka sunji daɗi, kuma sun barma ransu cewa ko gobe ba zan iya shiga tsakanin su bane, balle in kawo wata fitina daka iya raba wannan zumuncin tun na yarinta.
A take Bilal ɗin ya kira Ummin, aiko bakaji yanda take murna ba, mai son ɗanka ai kai take so, sai ga kiran ta kuwa cikin wayar Ya Ameen, bayan sun gaisa ne take sake mashi godiya, nuna mata ɓacin rai yayi, yana mai miƙo man wayar, nima godiyar tayi mani, murmushi nake tayi ina zaulayar ta da cewa mijinta na nan yana gwaurantaka, tayi maza ta dawo.
Ya Ameen ne ya duba agogon da take ɗaure bisa tsintsiyar hannun shi "friend muyi maza fa, tun cikin dare na kammala mana komai na daga abunda zamu buƙata, saboda haka ina so komai ya kammala cikin lokaci"
Shima Bilal ɗin ajiye Mug ɗin yayi yana mai miƙewa tsaye. "OK am done" ya faɗa yana juyowa inda nake tsaye nima riƙe da ƴar brief case ta Ya Ameen.
"Madam sai mun dawo ko? A gaida Hafsat fa da baby" ya faɗa shima cikin murmushi, yana mai nufar ƙofa ya fice.
Jawo ni Ya Ameen yayi da sauri na faɗa jikin shi.
Rungume ni yayi sosai. "Bilal ya sanya ni farin ciki Dear, kiyi mana addu'a please, I have no any than Bilal" ya faɗa a hankali
Gyaɗa mashi kai nayi nima cikin yarda da abunda ya faɗa ɗin.
"Na sani dear, ina maku addu'ar Allah ya sanya ma wannan tarayya taku albarka, har ƴaƴanmu"
Ya kuwa ji daɗin me na faɗa ɗin, sake rungume ni yayi tsam, yana mai raɗa mani "Nace zamuyi magana ɗazu, Amman