Showing 255001 words to 258000 words out of 397668 words
yi matuƙar sanyi, ƙunci da yake ciki zai yaye insha Allahu, ko ba komai ba zai taɓa bayyana wani abu ba cikin jama'a da sunan zai dagula hidimar bikin."
Haka yayi ma malam ɗin godiya, inda ya kawo wani abu ya bashi, saidai malam fir yaƙi amsa, yace ai aikin Allah ne yayi ba wai na kuɗi ba, kuma babu Abunda ba zai iya yi ma Muhammadu ba, saboda irin taimakon shi ga al' ummar musulmi baki ɗaya.
Haka ya dawo da ruwan a hannu yana ta ɓoyewa, ya ɗauka Al'ameen zai tsaya cin snack ɗin da lemon da suka sha, to da anan ne zai ƙoƙarin bashi ruwan ya sha ba tare da ya sani ba.
Ganin bai tsaya bane ya sanya ya ɗora su bisa fridge, yayi ma mamaki da Al'ameen ɗin ya sha Hu, duk kuwa da kasancewr su ba sanyi, kuma robar a buɗe take, wanda ga al'adr shi baya shan ruwan da wani ya buɗe. To saidai ganin hakan ne ya sanya shi gane har yanzu zuciyar abokin nashi na cike da ƙunci, koma dai minene yana fatan ace shan wannan ruwan addu'ar ya kawo mashi masalaha. Abokin NASHI Al'ameen ya cencenci koma minene daga gareshi, tinda shi ya fi kowa sani, har yanzu da BAZAR shi yake rawa. Shiyasa lokacin da soyayyar Suhan ta fara bijiro mashi, yayi ƙoƙarin yaƙar abun, saboda ba zai taɓa iya cin amanar abotakar su ba, wadda tin basu kai ga mallakar hankalin kansu ba suke yin ta.
********
Hajiya Laila wallahi ba zan iya misalta yanda nake ji ba yanzu a cikin zuciya ta, bansan dai dalilin da yasa nake matuƙar jin Nauyin yaron nan ba, kaman shi ne ya haife ni, ba nice na haife shi ba. Na rasa ta ina zan fara sanar dashi wannan al'amari, saboda ba hurumi na bane, ni kuma ba zan iya zuwa in tunkaro Hajiya Zainab ba, ko yayyen mahaifin nashi, su kuma dangi na gabaki ɗayansu shakkar shi suke ji, shine dalilin da yasa na kirawo ku nan kafin yazo, ku bani shawara" Hajiya Kubran ta faɗa, cike da wani irin yanayi da zaka kasa fassara shi, dagani dai nadama tayi mata ɗaurin huhun goro.
Hajiya Laila ce da take zaune kusa da Hajiya kubran ta nisa, sannan ta shiga cewa "Ni fa dama Allah ya gani ba da son raina akayi wannan aika aikar ba, ina ganin tinda yaron nan ya nace da sai ki bar shi, wannan aure fa daga gani bamu san Abunda Allah yayi ba akan shi, kina gani fa, Wancen aikin da Malam yayi akan su ita Umman Suhan ɗin akan su bar gidan, aikin nan yayi kyau, kuma munga sakamako, Amman da suka tashi dawowa sai suka dawo da ƙarfin su, baki bari yaron naki ya auri yarinyar ba, sai gashi mijin naki ya auri uwar, ko anan ya isa mu gane ishara ce ta Allah". Hajiya Sa'a ma da take gefe, ma'ana dai sun sanya Hajiya Kubra a tsakiya, kowacce cikin maɗaukakin gayu cikin ɗanyun laces da gwal-gwalai. Itama nisawa tayi ta amshe zancen da cewa "Nima tuni na daɗe ina wannan nazarin, kamata yayi mu ƙyale su, tinda suna son juna, Amman Hajiya Laila kece kika matsa akan lallai ayi aikin da yaron nan zaiji ya tsani yarinyar nan, kina gani jiya fa kaman yanzu yaran nan suna cikin nishaɗi, Amman wayewr gari aka ɗaura aure muka gane kan yaron nan, gashi ya ɗaga maki hankali kema duk kin ruɗe, mai kyakkyawar fahimta dole ya gane bakya cikin natsuwa.
Hajiya Kubra ce ta sake nisawa, cikin wata irin jin kunya, da zamu ce bata taɓa jin irin ta ba.
"Ni fa ban san abun nan haka yake ba, duk son zuciya ta ne yaja mani, saboda bana so Sam ace ana yayata ni a cikin ƙawaye cewa yaro na ya auri ƴar aikin mu, shine kawai dalili, Amman ko ita Maryama ina cike da kunya da nadamar duk ranar da zata dawo gidan nan, domin a rayuwa na cutar dasu, na wulaƙanta su, kuma wlh duk ina sane, saboda son zuciya ta, Amman yanzu ba wannan ba, duk ma Abunda zai faru daga baya ne. Ku bani shawarar ya zanyi da Al'ameen, kun sanshi sarai wani irin murɗaɗɗen mutum ne, shine ma dalili na na cewa yazo ya same ni nan. Kunga kuma har yanzu bai kira ba.
"Ni fa dama ina mamakin yanda kika ɗauki karan tsana kika ɗora ma matar na da yarinyar tata, naga ba sashen kike zuwa ba, Amman duk wani motsin su akan idon ki yake, nayi mamaki da bakiyi ma sauran ma'aikatan sai su..." Hajiya Sa'a ta faɗa itama
"Sa'a kema dai kin faɗa, hakanan na ji na tsane su wlh, kuma tabbas bana zuwa sashen masu aiki, saidai ina da masu kawo mani dukkanin rahoto, Talatu da Sayde, saidai Talatu ita ce kan gaba, saboda ita ce shugaba, ban sani bama dukkanin abubuwan da take zuwa tana faɗa man ɗin, ko don inji na tsane su ne? Mu bar wannan maganar ba lokacin ta bane Sa'a ku bani shawara, duk yanda za'ayi ina so yaron nan ya tara da yarinyar nan cikin daren nan, ta yanda komai zia warware cikin sauƙi, daga yanzu ba zan kuma cutar Suhan ba, saboda nasan idan nayi haka ko ma sarautar ma ba zata ƙyale ni ba. Nayi nadama da wuri Laila ku bani shawara."
" Al'ameen da take tsaye ta bayan su, duk Abunda suke faɗa ya gama ji, a hankali a hankali ya shiga takawa cikin wani irin rawar jiki, wurin yake ƙoƙarin bari, ko don kada ya faɗi a wajen.
Baisan lokacin da ya kai kanshi bakin mota ba. Jikin shi kyarma kawai yake yi, tuni fuskar tashi ta rine da kwanciyar jini, haka idanun shi, baisan halin da yake ciki ba, a haka ya shiga jan motar cikin tuƙin ganganci. Har yanzu zuciyar shi ta kasa gasgata Abunda yaji, to da wani ne yazo ya faɗa mashi wannan maganar, Allah ne kaɗai zai iya raba su dashi a ranar nan.
Haka ya shiga cikin gidan yana mai haɗa hanya, kaman wanda tasha giya kwalba goma.
Da sauri Bilal ya miƙe yana mai taro shi suka zube kan kujera.
"Friend gaya mani me ya faru kuma? Kaje gidan ne? Me ya faru ko in kira Mom ɗin?"
Bai iya cewa ƙala ba, sai wasu irin hawaye masu ɗumi dake shatata a idanun nashi.
Dakatar da Bilal yayi da hannu, da ya zaro waya yana mai ƙoƙarin kiran Mom.
*"Dont call her"*
Ya faɗa a tsawace, wani irin miyau na feshi daga bakin shi, mai kumfa kumfa.
Ruɗewa Bilal & in yayi, zai iya cewa bai taɓa ganin abokin nashi cikin wannan halin ba.
To me yake faruwa ne?
"To ka faɗ aman Friend lafiya? Ka tada mani hankali fa, idan ba zaka faɗa ba, i'll call her defenetly"
Shima ya faɗa cikin fushi, kukan da yaga Al'ameen ɗin nayi ya ɗaga mashi hankali.
Tun hawaye na zuba, har ya fara sakin sauti, yana mai dafe da kanshi da yake ji kaman zai tsage mashi biyu.
Da dukkanin hannuwan shi yayi amfani wajen kamo Al'ameen ɗin da ya kuma sake miƙewa ya nufi zuwa bedroom ɗin.
Fizgewa yayi, yana mai wucewa yana haɗa hanya.
Baiyi fushi ba, a zafafe shima ya miƙe ya bishi
"Please Friend kada ka ɓata mana wannan ranar, ka sanar dani me ke faruwa don Allah, tin kafin nima ka sanya ni kukan, ba tare da sanin me ke faruwa ba"
Ya faɗa yana mai zaunawa shima Ƙasan carpet, kaman yanda yaga Al'ameen ɗin yayi.
A hankali ya fara rage sautin kukan nashi.
"Bilal dukkan abunda ke faruwa dani Mom ce sila, Mom tana da masani ya, Mom ce dalilin tsanar Suhan da nayi, Mom ce da ƙawayen ta, Dalilin barin Su Suhan gidan namu Wancen karon, Mom ta azabar da su Suhan da Umma, a lokacin zaman su gidan namu, duk ba tare da ni ko Dad mun sani ba, Bilal ka faɗa man wace irin uwa ce Allah ya bani? Wane irin hali Mom ta jefa kanta na bin bokaye da sunan malamai? Me Mom zata tsinta a yin hakan da tayi? Me Mom ta nema ta rasa a rayuwar ta? Me su Suhan da Umman ta suka tsare ma Mom? Sai gashi yau da bakin ta duk tana faɗar waɗannan abubuwan. Da wanne ido zan kalli Suhan da Umman ta duk ranar da suka ji hakan? Shin bata tunanin su samu saɓani da ƙawayen nata su fita waje su tona mata asiri.? Bilal ka faɗa mani ya zanyi? Bilal ba abunda na nema na rasa wanda Allah bai mallaka mani ba, Amman ya jarabce ni da samun Uwa mai halin Mom. Bilal ina nadamar tsanar da na nuna ma Suhan a yau. Duk da ba wai ina jin son ta ya dawo mani bane ɗari bisa ɗari. Dole in danne zuciya ta, Bilal ka bani shawar wai ya zanyi ne?"
Ya faɗa yana mai sake sakin wnai kukan.
Shi kanshi Bilal idanun nashi sun kaɗa sunyi jawur. Dole dama zuciyar shi na raya mashi cewa harda sa hannun Mom a duk Abunda take faruwa, ya sakankance da lamarin Mom tin wata rana da ya same ta tana waya akan irin hakan, saidai bai fahimci komai ba, haka ya juya ya fita, ba tare da ya bata damar ganin shi ba, balle ta kawo ma ranta cewa ko yaji Abunda take faɗa a wayar. To ya zasuyi, uwa uwa ce, dole su jure, dole su danne, saidai suna gudun ranar jin kunya, kuma sun sani dole ne tana nan zuwa.
Miƙewa Bilal yayi ya nufi fridge yana mai ɗauko gorar ruwa ya sake dawowa, inda Al'ameen ɗin yake zaune.
Miƙa mashi yayi, bai wata wata ba ya sanya hannu ya amsa, yana mai ɓalle murfin ya sake kafa kai.
Cikin matuƙar rausayawa yake kallon abokin nashi, ikon Allah kenan, yanzu dai gashi babu Abunda Allah bai mallaka ma Al'ameen ɗin ba kaman yanda yace kuɗi, gidaje, motoci, kmafanoni, ilimi, kyau, asali, nasaba, farin jini da sarauta, Amman shi kuma ta nan tashi jarabawar take, kowa dole ne Allah ya jarabce shi, wallahi kabar ganin mutum a cikin sutura, wani mai kuɗin ma da zai buɗe maka cikin shi, to tabbas sai ka fahimci ashe kai ne Allah yake so, kai ne Allah ke ma sutura, ashe shi kura ce lulluɓe da fatar akuya, Abunda da yawa mu Talakawa bama kawo ma ranmu kenan, muna ɗuaka idan Allah ya bamu kuɗi shikenan ba wata Jarabawa da zata iya biyowa baya.
Gefe ya koma ya zauna yana mai kallon abokin nashi da ya haɗa kai da guiwa yana mai sakin ajiyar zuciya a hankali a hankali.
Suna haka ne kiran Mom ya sake shigowa wayar tashi.
Kai hannu yayi da niyyar latse kiran, Bilal yayi saurin ɗauke wayar ya amsa.
"Mom Al'ameen yana wanka ne, kuma mun fara shiri, please kiyi haƙuri ko zuwa gobe ne sai kuyi maganar, saboda ya faɗa mani cewa kina neman sa, bama so ne mu makara" ya faɗa mata haka, yana mai katse kiran ba tare ma daya jira cewr ta ba, yasan hakan da suka yi mata bai kyautu ba, saidai basa da zaɓi ne baya ga hakan, dole duk wani abu da zai haɗa Al'ameen da Mom ɗin a yanzu su kauce mashi, ko don halin da Aminun nashi ke ciki. Kai gidan ma baya fatan ace ya taka yau, so yake ace har sai kowa ya watse, domin baya so zuciya ta kwashi abokin nashi ya aikata ba daidai ba cikin mutane yanda zuciyar na tashi take haka.
Yana katse wayar, Al'ameen ya miƙa mashi hannu alamun ya bashi, ba musu ya miƙa mashi. Kashe ta yayi gabaki ɗaya, inda ya wurga ta cen bisa gado, domin ko alamu ma baya fata da burin sauraren Mom ɗin tashi a yau.
Ita kuwa ta ɓangaren ta mamaki take yi, duka yaushe yace mata yana wanka, kuma har ya sake komawa wani? Wai me ke faruwa ne? "Hidima ce tayi mashi yawa Hajiya kibi a hankali"
Cewr Hajiya Sa'a.
Ajiyar zuciya ta sauke, dole akwai buƙatar ta kira alhaji, domin ta faɗ ama shi buƙatar masarautr, shi sai ya kira shi da kanshi yayi mashi bayani, tinda dai shi yake namiji, ba kaman ita ba da take mace.
Ko da ta kira Alhajin yana cikin mutane, sai dai ya bata uzirin zai kira ta daga baya.
Dole jiki ba kwari ta miƙe tana mai komawa ciki, inda ta sanya aka ƙra haɗa wasu kayan ciye ciyen zuwa wajensu Mama Fulani. Tare da guest Pass ɗinsu, kaman yanda Bilal ya kawo mata.
Ai tuni gida ta ƙara harmutsewa ƴan zuwa dinner. Inda har motocin kwasar Mutane sun fara yin oarking a harabr gidan, domin basa fatan ace anyi African time saboda an gaji kowa ya kwanta da wuri ya huta.
********
Ni kau tin magariba aka sanya nayi wanka, sai bin ko'ina na ɗakin da kallo nake yi a sace, hatta da ruwan wankan da aka sanya nayi wankan dasu daban suke, wani irin ƙamshin daɗi ne yake fita daga cikin su. Sannan aka sake turara ni, har da na tsugunne. Domin Mama Fulani ta aiko da mai gyaran jikin, kuma ta faɗa mata cewa yau ne ango zai shiga ɗaki, ba kowa ya sani ba, Shiyasa take ta sake haɗe ni da wasu irin sirruka, tana yi tana sakin dariyar da ita ce kaɗai ta san ma'anr ta.
Hatta da gashin kaina ba'a bar shi ba. Gashi kuwa indai ba na kaina ba, duk jiki na babu inda yake. Haka aka dinga bani wasu irin turaruka ina murje ma jikin, har da na matsawa, duk da ba wai shiga yake ba, haka ake sanya ni ina shafawa gefe gefe. Kai har dai na gaji, dan dai bana da yadda zanyi ne, tunani nake tinda ba yau ne ango zai shigo ɗaki ba, menene na yi mani wannan fi'ilin.
Nan fa ko ina ya ɗau ƙamshi, har falo kana iya jiyo ƙamshin. Dama sashen bama da yawa ciki. Su Afnan ne da Jidda sai Asiya, Hafsat, khadeeja Raihana da Huda, sauran duk sun koma sashen su. Sai haɗimai guda biyu da suke zaune falo suna jiran ace suyi wani abu.
Ƙamshin jikin nawa duk da yana da yawa sosai, amman hakan baisa yake hawan kai ba. Tana gama gyara ni, sai ta miƙa mani wani turare, tace in tabbata yau da gobe idan zan kwanta na shafa a jiki na. Wannan wani sirri ne da sai nayi mata godiya.
Haka ta fice, inda mai kwalliyr da Afnan ta ɗauko tazo ta fara aikin ta.
Cikin ƙanƙanen lokaci kamanni na suka cenza, na koma kaman wadda aka ɓanɓaro daga inji. Tuni na ɗau sheƙi da walwali. Wata irin doguwar wedding gown ce mai kakar Royal blue akan kawo mani har ƙasa tana jan ƙasa, sai wani irin head da mai kwalliyr ta tsaya ta zubda zallar fasaha ta wajen ɗaura mani shi, shi kuma fari ne tar, har yana ɗaukar idanu. Sai wasu irin flowers da zan riƙe a hannu na, da ƴar post ɗin takalman mai kalar fara tar da duwatsun bula sai walwali take.
Hatta da sarƙar wuya na abun kallo ce. Tuni suka ɗau sowa da tafi. Inda su kuma suka shirya cikin riga da skirt na english wears kalar baƙin skirt da ruwan miyon goro ta riga, sai hula da suka kakkafa pecing cap itama baƙa, inda kowacce ta saki gashi ta hudar bayan hular. Sunyi kyau sosai suma kaman zasu bar ƙasar.
Muna cikin wannan shirin ne, inda har yanzu an ƙi bari na hakanan in huta, sai ƙalailaicewa ake yi. Saƙon anguna ya iske mu akan cewa ƴan matan amarya su fito, Amman banda amarya, ango ne da kanshi zai zo ya tafi da ita. A barta ita da wata Ƙawar ta guda.
Nan aka fara muhawarar da wa za'a barta.
Hafsat dai ita aka zaɓa akan ta zauna jiran yayan nasu.
Inda kowacce Ƙawar amarya da abokin ango guda cikin motar shi.
Nan fa duk motar da ka buɗe ka shiga, ita ce ta abokin angon da zaku zauna wuri guda gashi har a gama dinner ɗin.
Hafsat wadda bata sanya irin kayan sauran ƙawayen ba, wata doguwar riga ce jikin ta, kalar Orange da baƙin head, sai rigar taba cikin damar zama daram. Ita dama ai tana mamakin ace wai wani naƙuda take yi, gashi har zata je pherty ɗin hankali kwance, inda Sadeq ya shaida mata tare da Al'ameen zasu zo da Bilal.
Cikin sa'a Jidda na buɗe motar da taji zuciyar ta ta aminta da Yusuf (Dady) ɗinta na ciki. Tana shiga ta sakar mashi murmushi, inda ya kashe mata ido guda shima yana mai faɗin, "Ai ni wata budurwa nake jira ta faɗo nan my jiddo, kinga ƙawa ce sai yayi daɗi ko?"
Ɗan haɗe fuska tayi, itama cikin wata irin shagwaɓa tace "ai nice budurwar ko kuwa baby?"
Jinjina mata kai ya shiga yi, cikin wata irin ƙauna da sauƙi, to dama su ɗin har yanzu amare ne, hakan ya sanya na bar su, ina mai nufar motar da naga Afnan ta buɗe ta shiga.
Cikin sa'a ya ɗago kanshi, domin ganin wacece ta shigo.
Hasken fatar tata, na ɗaya daga cikin Abunda ya shaida mashi ita.
Ko ba'a faɗa ba, tabbas wannan jinin su Al'ameen ce, watau gayen da ya ƙwace mashi Suhan. Sai yaji ba daɗi sosai, yanzu ba komai ne da ya shafi Al'ameen take so ya ganshi kusa dashi ba, dan dai baya da yadda zaiyi ne, har yanzu kishin Suhan ɗin na sukar mashi zuciya. Saidai gaida shin da tayi ne cikin fara'a ya sanya ya ɗan kalle ta kaɗan yana mai amsawa, sai kuma ya sanya hannu yana kunna ƙira'a a motar, inda motar ta ɗauki shiru banda tashin ƙira'a, yana jiran a basu umurnn fara