Showing 291001 words to 294000 words out of 397668 words
mani, sai kuma yanzu gashi kana neman ja mani wani, ka sani cewa yaron nan shine kawai wanda nasan zai tsaya mnai wajen kwato mani haƙƙi na, Alhaji don Allah kace ya dawo, ni ko na kira shi ma bata shiga"
Itama ta faɗa cikin wani irin yanayi, kaman dai ta saduda, Amman har yanzu idan ka kalli kwayar idanun ta, zaka iya hango tashin hankali tsantsa a cikin su, Hajiya Kubra kenan, damusa mai kwanciyar ɗaukar rai.
Sai da ya gama kallon ta da nazari ta, sannan ya nisa, sai da sharaɗi guda ɗaya, muddin kika cika shi, to tabbas zaki samu Al'ameen da matarshi sun dawo gidan nan."
Ba tare da wani dogon nazari ba tace" Na yarda Alhaji" ɗan murmushi yayi, "Tun ma baki ji sharaɗin ba?" itama gyaɗ a mashi kai ta sake yi cikin amincewa
Muskutawa yayi, cikin jin girman Abunda zai faɗa mata, domin yasan a wannan yanayi da ake ciki, bai zama lallai ta iya yarda ba, masalan ma na zafin Umman Suhan da ya lura da ta fara ji" Sharaɗin shine zamu je Adamawa tare dake, watau ina nufin Mahaifar Su Umman Suuhana, idan har kin yarda kin amince kin bini, to fa lallai zamu dawo mu tadda su Al'ameen da matar tashi a cikin gidan, kuma tabbas ba zan hana shi shiga cikin lamurran karɓo maki dukiyar ki ba, kuma sanin kanki ne cewa tabbas idan lamarin ya koma hannun shi, to fa sai inda ƙarfin shi ya ƙare... "
Cikin wata irin tsabar kaɗuwa ta ɗago a matuƙar firgice tana kallon shi, cikin rawar murya da rawar baki tace" To Alhaji na yarda na amince, indai har wannan zai sanya ka kyale Al'ameen ya kwato mani haƙƙi na, ba damuwa zamu iya zuwa, ko yaushe kake so"
Shima murmushi yayi, da mamakin jin furucn nata, lallai Hajiya Ku ra bata haɗa kuɗi da kowa da komai ba, ita su ne mutumcin ta, kuma bata yadda a ƙasa ba, mahaifinta ma tin a wancen lokacin haka yake, saboda kaf duk garin na Katsina babu wanda bai san da zaman Alhaji Ibrahim kwangila ba.
Miƙewa yayi shima cikin jinjina kai yana faɗin "Sai ki fara shiri, idan Allah ya kaimu zamu yi sakon tafiya ne"
Da kallo ta raka shi, gabaki ɗaya Alhaji Mustaphan nata ya rikiɗe ya koma kaman ba shi ba, sai da yaje gab da fita ne, tayi ta mazan sake cewa "To Alhaji wai ya maganar Nihal ne? Naga har yanzu yaron nan bai zo ba fa, bai kuma aiko ba, ya kamata asan halin da ake ciki fa, na gaji da zaman nata a haka wallahi, gashi har an fara yada mani magana akan hakan"
A hankali ya juyo yana mai ƙare mata kallo, sai kuma ya girgiza kai,yana mai juyawa ya sanya kai yana mai ficewa tare da ce mata "Ba yanzu ba....."
~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹
🌺🌺🌺🌺🌺
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
Yin Kabbara Da Tasbihi Yayin Da Ake Cikin Tafiya
Allahu akbar. اَللهُ أَكْبَرْ
Subhanallah. سُبْحَانَ اللهِ
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_
*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_
*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._
*Page ~71~*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°
Tafiya yake a hankali, zuciyar shi gabaki ɗayanta a cunkushe take, fuskar nan tashi sam babu walwala, duk kuwa da ƙoƙarin da nayi wajen ganin ya saki ran shi kafin ya fita ɗin, dama tinda yaga wayar dady ɗin nashi saida gaban shi ya faɗi, har kawo lokacin da ya ɗaga yake sanar mashi cewa ya same shi guest house ɗinshi dake bayan gari.
Yasan maganar, kuma yasan kan zancen, wannan ce ta sanya har yanzu ba zai iya tantance a matsayin da yake kai ba, ya sani sarai Mom ba zata lamunta hakan ba, Amman da ba abunda zai tsaida shi a ƙasar, balle dukkan Abunda zai faru ya faru yana nan, har ya juye zuwa kanshi, to saidai baya jin zai iya barin amaryar tashi da har yanzu basu rufa sati guda ba ma cur a tare, wanda zai iya cewa har yanzu bai san daɗin angonci ba saidai ƙalilan, yana matuƙar ganin ƙoƙarin Suhan, duk da ta fahimci Abunda ke faruwa, Amman Sam bata bayyana mashi fushin ta ba, in banda ɗan tashin hankali ƙalilan da yake iya hangowa a kwayar idanun nata, duk kuwa da ƙoƙarin ɓoye mashi da take yi.
Da haka ya isa ga guest house ɗin, inda mai gadi ya buɗe mashi gate ɗin, a wajen parking ya tadda motar Dad, alamun da ke nuna mashi Dad ɗin nashi na jiran shi kuwa.
Kallon agogon rolers da yake hannun shi yayi, lokaci guda yana mai ayyanawa a ran shi dare yayi, dole yayi maza ya kammala abunda yake ya koma ga Suhan ɗin da ya baro ta cikin tsoron rashin sabo, masalan a ɗakin hotel ita kaɗai, girgiza kai ya shiga yi a hankali, irin ƙaddarar tashi kenan.
Da salon tafiyar shi cikin ɗan hanzari ya tattaka zuwa cikin babban falon da ya ƙunshi kujeru da dama, mai ɗauke da manyan ɗakuna da suka taimaka wajen ƙara ma ginin guest house ɗin girma.
A ƙaramin falon dake cen ciki ya tadda Dad ɗin nashi, zaune yake cikin kamala da dattako kaman ko da yaushe, jarida ce ta daily trust a hannun shi yana dubawa, gefe guda kuma Mug ne mai ɗauke da cufee da ƴar ƙaramar buta mai kyau fara tas da ita.
Gefen Dad ɗin ya samu ƙasa ya zuƙunna yana mai tankwa she ƙafa, gaida Dad ɗin nashi ya shiga yi, daga yanayin da Dad ɗin ke kallon shi, ya karanci tsantsrr damuwa dake yawo cikin zuciyar tashi.
Cikin sakin fuska ya amsa, ko ba komai yana buƙatar ya kawo wani yanki na sassauci a cikin zuciyar Son ɗin nashi, tausayi yake bashi matuƙa ainun, saboda hakan ne ma ya yanke hukuncin Abunda yake ganin shine zai kawo masalaha ga al'amarin.
Gyara zama yayi, yana mai nuna ma Al'ameen kujerar da take kusa da tashi, alamun ya dawo bisa ya zauna, ba musu ya miƙe ya koma bisa sofar.
Da hannu yayi mashi alamun da ya zuba Cofee ɗin shima, jim yayi kaman ba zai zuba ba, sai kuma ya miƙa hannu yana mai tsiyaya kaɗan.
Har yanzu Dad nazarn shi yake yi. Gyaran murya yayi, yana mai kallon Yaron nashi cikin wani irin yanayi ya fara magana.
"Al'ameen dalilin da ya sanya nayi kiran ka anan shine, sanin kanka ne cewa ya zuwa yanzu Abunda ke faruwa a cikin gidan namu ya fara zaga kunnen mutane, saboda haka ne bana so hankalin ƴan jarida ya dawo kanmu, ka ganta nan? (Ya nuna mashi jaridar dake hannun shi) jarida ce ta gobe wadda zata fita, ka duba title ɗin dake sama me Kaga an rubuta?"
Ya faɗa yana mai miƙa mashi jaridar.
*WATA DAMBARWA NA NEMAN KUNNO KAI A GIDAN AMBASSADOR ALMUSTAPHA YUSUF DAMBULAN, SAKAMAKON DAMFARAR MATARSHI MAI SUNA DR. HAJIYA KUBRA DA WANI MUTUMI MAI SUNA ALHAJI YARO DA YA KASANCE MIJI GA AMINIYAR TA HAJIYA LAILA MAMUDA, DAMFARA KUMA DA ZAMU IYA CEWA TA MILIYOYIN KUDAƊE, WANDA HAKAN NA IYA KAWO RUƊANI DA FARUWAR WANI MUHIMMIN AL'AMARI*
A matuƙar ruɗe Ya Ameen ya ɗaga yana kallon Dad ɗin nashi. Duniya kenan kana bacci ana maka munshari. Watau wannan maganar har ta iya fita waje kenan? To wanene ya fidda ta? Ko dai Hajiya Sa'a ce?
Bai iya cewa komai ba, sai bin takardar yake da kallo, kaman tsohon makahon da idanun shi suka buɗe a lokaci guda.
"Kada ka tashi hankalin ka, Abunda nake jiye ma Mom ɗinka kenan tun tuni, wannan al'amari kuma na iya kawo mana naƙasu da koma baya ta fannin kasuwancin mu, masalan ma kai da yanzu idanun kowa suke kan ka, saboda ɗaukaka da Allah yayi maka. Wannan ne dalilin da ya sanya na nemeka nan domin in sanar dakai Abunda nake so kayi, domin idan muka daka ta mahaifiyar ka, ba za'a taɓa samun masalaha ba"
Jinjina kai yake yi cikin tashin hankali, me mom ɗinshi take so ta zama ne? Wai shin yin kuɗi ko Arziƙi kansu farau ne? Bai taɓa danasanin arziƙin da yake dashi ba sai yau, bai taɓa danasanin haihuwar shi gidan da suka rufa suka tada kai da Arziƙi ba sai yau, yana ji ace dama gidan da kullum rana ta Allah sai an fita an nemo za'a kawo masu suci, suyi makaranta ta gwamnati, su kwana a saman katifa ko tabarma, aka haifeshi yana jin da hakan da sai yafi zama mashi mafi alkhairi da kwanciyar hankali.
Maganar Dad ɗinne ta katse mashi tunanin da yake yi, "Idan Allah ya kaimu gobe ka ɗauko Matarka ku dawo gida, ni da Mahaifiyarka da Alhaji Yaya zamuje cen garin su Umman ita matar taka, mai martaba sarki na neman ganin mu, saidai ina so kafin mu dawo duk yanda zakayi ka nemo dukkan info akan Alhaji Yaro, da dukkanin harƙallolin da Mom ɗinka keyi ba tare da mun sani ba, wannan kuma zai faru ne tare da taimakon Barrister Kabeer, saboda haka dole ne ka ɗaura ɗamba, ka ƙarfafa zuciyar ka, ni na sani zaka iya cin karo da abubuwa da zasu iya dagula maka lissafi, saboda kasan Halin Hajiya sarai, ba jin magana take yi ba a lokutta da dama, dole ka aro jarumta ka sanya ma ranka, dole ka ƙarfafa ma kanka guiwa, insha Allahu zamu kawo ƙarshen wannan al'amari cikin sauƙi, nima kuma idan na dawo da izinin Allah zan taimaka maka ɗin. Don haka yanzu ka tashi kaje wajen Matarka, zuwa da safe kuma ku koma gida, saidai kafin safen ya kamata kayi nazari ta yanda zaka ɓullo ma wannan al'amari cikin sauƙi ba tare da kaja hankalin ƴan jarida ba, ko gidajen redio"
Sai da ya nisa sosai, sannan yayi ma Dad ɗin nashi sallama, da kallo ya bishi, yana mai kallon Mug ɗin Cofee ɗin da ya ajiye ƙasa, wanda bai ma san ya sauke shi ba, ko sau ɗaya kuma bai kai shi bakin shi ba. Har ya fice daga cikin falon, sannan ya sauke numfashi yana mai cewa "Hakanan zaka ci gaba da haƙuri da mahaifiyar ka, abubuwa da dama da take aikatawa bata yar a ƙasa bane"
*******
Har bacci ya fara fizga ta lokacin da naji shigowar shi, saida ya kulle ko ina sannan ya nufo ɗakin, lokacin har na sauko daga bisa gadon, jiki na sanye da pajamas masu taushi tare da salƙi, kaina sanye da hula mai taushin gashin mage, na cusa dukkanin gashi na da yake tsefe ciki, sai nayi kyau, koni lokacin da nayi wankan na gama shiryarwar kasa dena kallon kaina a madubi nayi, duk da fuska ta babu komai saman ta in ka ɗauke face cream da glow dake sama.
Bakin ƙofa muka ci karo dashi, yana ƙoƙarin shigowa ni kuma ina ƙoƙarin fita, saman ƙirjinshi na faɗa ban sani ba, saidai Naji ya sanya dukkan hannuwan shi ya zagayo bayana dasu, ya rungume ni tsaf a cikin faffaɗan ƙirjin shi.
Luf nayi, ina mai amsar saƙon zuciyar tashi.
Saidai yanayin yanda Naji tana bugawa da sauri da sauri ne ya sanya ji ɗagowa cikin hanzari ina mai kallon fuskar tashi.
Idanun nashi a kulle suke ruf, sai zara zaran gashin idanun shi da nake iya hangowa, haɗe da girar shi mai kyawon yanayi.
"Yayana kana lafiya kuwa?" Abunda na iya cewa kenan, har yanzu ina cikin jikin shi sosai.
A hankali ya buɗe idanun nashi yana mai ɗora su saman fuska ta, sai kuma ya shiga zame hular kaina a hankali zuwa rabin kan nawa, yana mai ɗora bakin shi bisa fore head ɗina ya shiga sakar mani wani irin Kiss.
Nidai har yanzu tsaye nake, hannun shi guda tallafe da ƙugi na, a haka na shiga jan shi, zuwa bakin gado. Safar shi na shiga saɓule mashi, tun da ya riga ya cire takalman already. Bai hana ni ba, sai kallo na da yake yi, wata irin ƙaunar shi na ratsa ni, a yanda nake ji a yanzu, ba zan taɓa iya rayuwa ba tare dashi ba.
Toilet na wuce nan haɗa mashi ruwa, yau kam saidai ni na taimaka mashi wajen wankan, ina lura dashi yanda jikin shi yake sanyaye, kuma yana yawan tafiya tunani. Hakan ce ta sanya koda muka kwanta saidai ya rungume ni yana mai sakin ajiyar zuciya akai akai. Inda ni kuma Naji daɗin jikin nashi, tuni bacci ya kwashe ni, yayin da shi kuma ya zurfafa a cikin tunani, dole ne yace ma Bilal ya dawo, ba zai iya shi kaɗai ba, matsalar Mom zata iya tarwatsa mashi kwanya tuni. Yana buƙatar mataimaki, kuma baya so damuwar shi ta shafi Suhan ɗin, Shiyasa dole ne duk yanda zaiyi ya kauce mata wajen faɗa wa cikin damuwar itama zaiyi.
Da safe bayan mun gama komai na Al'ada ne yake ce mani in shirya kaya zamu koma gida, kaman yanda bai man wani cikakken bayani ba, nima hakan ban tambaye shi ba na shiga haɗa kayan, hakan da nayi ya matuƙar burge shi, kuma hakan na nuna mashi ba zan taɓa bijire ma umurnn shi ba, sannan ni ɗin ba mai shiga al'amarin da aka juna ba'a so da in shiga ɗin ba.
Ya santa da sanyin hali, hakan ne ya sanya dole ne duk yanda zaiyi wajen ganin ya bata kariya daga dukkan wani abu zaiyi, baya jin zai iya lamuntar damuwa da halin da yake ciki ya shafi matar tashi. Bai same ta da sauƙi ba, haka kuma dukkan wani al'amari da ya shafe shi baya jin shi da sauƙi.
Har muka isa gidan motar tsit, ba mai cewa komai, sai naga yau ya koma man kaman Ya Ameen ɗin da na sani da cen baya, muskili mara walwala da fara'a. Nasan damuwar shi, kuma ina ganin ƙoƙarin shi matuƙa, hakan ce ta sanya nima sai ban nuna mashi nasan yawan damuwar da yake ciki ba, gudun kada yace ina shiga sha'anin shi shi da Mom ɗin tashi.
Yayi mamakin da akace mashi su Dad ɗin sun wuce, Nihal ce ke sanar dashi hakan, lokacin da muka shiga cikin gidan, bata tanka mani ba, haka nima ban tanka mata ba, nasha alwashin matuƙar gyara mata zama cikin ruwan sanyi, shi bai ma ko kula da rashin gaida ni ɗin ba, ya sanya kai riƙe da hannu na muka fice daga sashen.
Da kallo ta bimu tana mai taɓe baki cikin ƙaunar zuciya, cikin ranta take rayawa an gama da yayan nata, saidai duk yanda zata yi ta ƙarƙashin ƙasa itama sai tabi domin cusguna ma zaman nawa da yayan nata a cikin gidan, muddin tana cikin gidan (Nace ai sai kiyi ta zama, ki kalli Abunda zai kashe ki da rayuwar ki)
Koda muka shiga sashen namu bai zauna ba, na kula yana cikin sauri ne, sai ban tsaida shi ba, na raka shi har ƙofa ina mai yi mashi a dawo lafiya, saida ya bani peck a goshi sannan ya fice.
A sanyaye na koma cikin gidan, wannan wace irin rayuwa ce? Dama haka Rayuwar masu kuɗin take? Ashe hakanan talaka ke sha'awr Rayuwar masu kuɗi, ashe matsaltsalun su sunfi na talakawa yawa, takalma ne zai kwana Baida ko sisi yayi bacci hadda munshari, Amman mai kuɗin da yake da biliyoyi ya kasa bacci, kaman yanda Ya Ameen yayi a daren yau ɗin.
Kitchen na wuce bayan na gama gyara ko ina, dole in sama mashi Abunda zai ci, wanda zai iya sanyaya mashi rai kafin ya dawo, duk da nasan maganin masalar tashi saidai Allah.
*******
Kai tsaye office ɗin Br. Kb ya wuce, shi kanshi Br ɗin yayi mamakin jin cewa wai Ya Ameen ɗin ne da kanshi yazo wajen nashi, ba ɓata lokaci ya sanya aka shiga dashi har cen ciki.
Miƙewa yayi da niyyar kawo mashi abun sha ya dakatar dashi.
Bayan sun gaisa ne ya buƙaci da ya kawo mashi files na dukkanin ƙaddarorin Mom ɗin tashi, da dukkanin wata takarda dake ɗauke da shaidar zuba hannun jari ta, da kuma sauran duk wani abu daya shefi Mom ɗin tashi. Yayi mamakin ganin himilin tarin takaddu sosai a gaban shi. Haka ya dinga bun su ɗaya bayan ɗaya yana dubawa.
Ba zan iya fasalta halin da ya shiga ba, da yana da hali kaf, gabaki ɗaya dukiyar Mom sai ya amshe ta daga hannun ta, ko za'a samu zaman lafiya, da zata iya zaman aure, kaman yanda ko wacce mace keyi, Dad ba abunda ya rage ta dashi, saidai har ta kai ga tana yin wasu huɗɗoɗi da kuɗaɗennnata da bata iya sanya wani daga cikin su saidai shi Brst ɗin, shima dan ya dama dole ne, gudun irin hakan.
Zuciyar shi sai Fat-Fat take kaman zata tsago ƙirjin shi ta fito. Ba Arziƙi ya nemi Layin Bilal. Daga yanda yaji maganar aminin nashi ya san ba lafiya, Shiyasa tun kafin ma ya faɗ a mashi dalilin kiran ya shiga sanar mashi cewa gashi nan a airport zai taso. Kashe wayar yayi ba tare da ya ce komai ba, ya rufe folders ɗin, yana mai maidawa bisa table ɗin barrister ɗin da ya koma shima ya zauna yayi relax yana ta Kallon al'ameen da sai ka rantse da Allah bai taɓa dariya ba, idanun shi sun kaɗa sunyi jawur dasu.
A hankali ya ɗago yana kallon barrister ɗin, inda a hankali ya buɗe baki, muryar shi na cracking ya shiga cewa "Ina so in gana da Baba Alhaji"
"OK yallaɓai zamu iya zuwa yanzu"
Abunda Barrister ya faɗa kenan yana mai Miƙewa ya shiga tattara folders ɗin ya zuba cikin wata