Showing 33001 words to 36000 words out of 46143 words
tayima Tv ƙuri da ido dukda ba kallon Tvn take ba ,gabanta yazo ya tsaya juyin duniya su tashi su tafi ta ce bazata je ba ,a haka momy ta fito ta tarara dasu suna faman tirka²
A jere suka haɗa baki wajen kiran sunanta "momy" cikin ɗaga murya tace "what?"
Buɗe baki nadiya tayi zatayi magana kawai sai kuka ,waigowa tayi ta harari Adams "Me kayi mata kuma?" Dariya ya guntse "Mom wallahi ban mata komai ba wai daga nace mata Inaso zan nemi auran kausar tana bani tausayi innatuna ta soya mata fuska ba wani ɗan gayu da zai aureta saidai ƙauye kuma ,to shine fa take ta masifa" hararansa tayi ta buga masa tsawa kamar gaske "Kamun shiru nace " daganan ta cigaba da rarrashin Nadiya d ƙyar ta haƙura ta miƙa mata lafcecen mayafin da ya miƙa ma mom ɗin ta bata ta saka
Hararanshi tayi sannan ta turo ma momy baki "Mom so yike yina kashemun kasuwa shi yinada wanda zai aura Ni kuma kar insamu saurayi mai kyau kowa ya ɗauka Ni matan aurene "
Shiru mom tayi lamarin nadiya akwai buga kai ita ko sai yaushe zata yarda tayi aurene ba rabuwa oho
Adams katse tunanin momy yayi saboda ya lura kanta ya kulle
"Indai kin daina saka ƙananan mayafai nima zan fasa auren kausar kuma bazan sake kula kowata maceba ,muyi ta tafiya a dukkanmu masu aurene kin yarda?" Harara ta banka masa ta yafa mayafin a kafaɗa "muje kaine zakayi kwantai gwarani ɗanyar jini ce"
Murmushi yayi kawai yabi bayanta saboda ta fice fuuu taci gaba , ɗaga murya mom tayi "Allah ya tsare ka kula mun da ita "
"Yes mom"
Ɗaure fuska tayi suka fara tafiya waƙarsa ya saka a motar amma haka ta hayyyaƙo masa a kashe bata son damu ,ba musu ya murɗa ya kashe ,aka cigaba da zaman en kurame
Haka sukaje sukayi signing ta fito ta zauna a motar tana jiransa ya fito
[7/6, 19:25] 😘😘😘: 35
Tana nan zaune a motar tana jiransa ya fito ,ta hango wasu gungun en shaye² a zaune ƙarƙashin bishiya ,suna ta hiransu da ƙarfin gaske ,yanda suke maganar da ƙarfi yasa ya jawo hankalinta
Cikin wani buɗaɗɗen magana ,dakaji kasan wannan tsaf zai iya limama mutum wuƙa a ciki ya mace
"Ance na mari soja !! to a wajenma saida na sake marin wani ,nasha zaisa mun alburushi sai akace a cusashi mota kawai"
Duddulo ido tayi ta manne hancinta a jikin glasses ɗin motar tana kallonsu a mugun furgice
Hargitsewa sukayi da hayaniya , da gardama kamar irin suna ƙaryata shi bazai iya marin soja ba yaci lafiya,wage baki yayi ya zaro wuƙa a maransa ta wando ya karta a ƙasan kwalta gab da inda motarsu Nadiya ke parke da sauri ta ƙanƙame ido. Ta haɗe jikinta waje guda ,cikin gadara ɗan daban yace
Nifa yanzun nan zan sama wajen nan fetur in ƙyatta ashana ,Ni ne zaku ƙaryata?"
jikin Nadiya a take ya soma rawa ɓaɓal ɓaɓal ,sam bataji shigowa motarsa ba sai ƙarar kullo ƙofar ,wani ƙara ta kwantsama ta aza ko ɗan daban ne ya shigo motarsu zuƙan fetur .
Tana ganin shine ta saki wani ajiyar numfashi zufa na tsatsafo mata
kallonta yayi ta wutsiyar ido kawai sai ya kwashe da dariya
Da ta rasa me zatayi kawai sai ta fara masa kuka
"Wai ke kuka baya maki wuya?"
"Fufu mu bar wajen nan" ta faɗa tana nuna masa en daban nan a tsorace tana daɗa waige² .
Sai sannan ya lura da wainda ta gani "to ina ruwanki dasu ? Kina mota ai You Are safe"
"Daka shigo fa na aza ƴan daban ne suka biyo ta baya zasu damƙo mun wuya !"
Yanda ta duddulo da idon ne tana magana kamar wata wawuya ko irin yaran nan under age
Tsir ya kasheta da ido sosai ta bashi sha'awa baisan sanda bakinsa ya haɗe kalmominba,sai cewa yayi "I love You baby girl"
Zaro Ido tayi saidai ta kasa magana sai ta nuna masa ƙirjinta irin alamun "Ni?" Kautar da kai yayi saboda yaji kunyar yanda yake yarfa kansa
Tada motar yayi zai bar wajen ,horn yayi masu amma sukaƙi tashi kawai sai ya figi motar zai ciki dasu ,wani tarwatsewa sukayi kana sukabi motarsa da gudu suna jifanshi ,sannan ne suka ankare da number mota
Babura suka hau sukabi bayan shi dasu gariyo da adda ɗirma masu zagi sukeyi suna binshi da gudu ,wai shegu masu tara kuɗi da gumin talaka ,Nadiya kuka ta fashe dashi "Fofo kai suke bi mun shiga uku ,shikenan sunana...gawa😭"
Jawota yayi ya saka a ƙirjinsa yina shafa mata baya a hankali ya lura ta firgita sosai ƙila tabbas bata taɓa ganin en daban bane dukda shima yasan yayi risking life ɗinsa Amma dole ya natsu kar ya kasa tuƙin gata tana pressurizing ɗin sa a gefe
Bata wayarsa yayi yina gaya mata sunayen da zata kira masa tana kwance a cinyarsa hannunta na taɓa screen ɗin da kyar take kiran wanda yasata shikuma direct layinda yike da inda zai shiga yike faɗawa shuwagaban en sandan da sojoji ,sukuma kafin ai haka sun tado da bataliyarsu sai kace yaƙi ya tashi suna gudu sam basa tsayama go slow kaucewa ake kawai ana basu waje .
Daidai inda suka ritsa motarsa en daban suna wasan baburan akan kwaltar kamar titin iyayensu suna ƙuza ƙarfen mashinɗin akan titi yina kuka ƙurrrrrrrrrr! Suna zagaye motarsu ,ja yayi ya faka motar yina murmushi ita kuwa nadiya kukan ma ya ɗauke saidai ta ƙanƙameshi tsan kamar zata koma cikinsa
Sa gariyo sukayi suna kaiwa bullet proof ɗin motarshi sara kararaff kaffff!
Shidai gabaɗaya yayi saranda baisan haka en zauna gari banza sukeba sai yau,to wai ma me nayi masu?
Wata sashe na zuciyarsa yace ɗan ƙaramar izzar da ka masu cikin samfarin izzarka ,ka tarwatsasu don suji tsoronka ne shine ya jawo maka .
Bai auneba yaji sun fasa glasses ɗin baya yayi da sauri gabaɗaya galsses ɗin ya zube ,da sauri tayi ƙasan ƙafarsa ta kwanta tana ihu ,ranshine ya ɓaci sosai kawai sai ya ɓallo motar ya fita ,ƙwalla mai kira tayi "Foufouuuuuu! " Kullota yayi ya tsaya a jikin ƙofar
"Ku ƙananun daƙiƙaine ,jiku en kuci kucinku da ya kamata kna school amma kunzo kuna tada ta'addanci saboda rashin ilmi ko? To zan tuɓe muyi dambe in maku duka ,na cire wani muƙaminada ko ni wanene"
Tsageran cikine ya dubi wani yaro mai wani irin kwasashen aski an salle ƙeya an masa Da-da a tsakiyar gashin kansa
"Dugujaaa!?" Ya kira sunan me Askin Da_dan ,aikuwa da jan ido ya ɗago
Zaro wata er ficikar wuƙa yayi a ƙugunsa ,ya nuna ma Wanda aka kira da duguja ɗin
"Duguja me sunan wannan?" Huro hanci yayi ya kumburo baki sannan yace "Tsitakaaa"
"Amsa tsikatar nan ka shigarmasa ka rungumesa ka soka in ka soka sai ka murzo sai ka zare ka basu waje su zubo " (yina nufin ya soka ma Adams wuƙar a ciki sannan ya murza sai yaba hanjin cikinsa waje su zubo ƙasa) aikuwa fincika yayi yai kukan kura ya tunkari gaban adam
Nadiya sauri tayi ta shige gaban Adams,ta karesa da hannunsa tana kuka tana er tsalle ta kasa tsayawa a waje ɗaya
Cikin zafin nama yake ƙoƙarin cireta yina mata masifa "Wayace ki fito ehem?"
Dugujan kallon Nadiya yayi da jajayen idonsa da suka sha kwalli "ke ban waje ko In ɓarar dakai "
"To majanunin banza,Allah ya isah tsakaninmu da uwarka da ta haifan mana gurɓata gari irinku😭"tana magana tana kuka kundai san ɗan daba dason uwarshi aikuwa wani kukan kura yayi ya kifeta da mari da saida tawani irin wantsale ta fadi timmm a ƙasa
Adam a husace ya miƙa hannu zai shaƙoshi regardless of wuƙar da ya gani mai bakin zarto ,durum wani soja ya sakar mata Alburushi a gadon baya sai ga jini ya wanke fuskar Adams
Nadiya ihu ta fashe dashi ta taso ta ƙanƙame Adams ta ɗauka shi aka fasa ma fuska "wayyo Allah na wannan wani irin lukutar masifa ne ! "Rungumeta yayi sosai a jikinsa,lokacin sojojin da suka fara zuwa sun bi matasan da gudu da kafafuwansu saidai sojoji da suka saba training ɗin gudu a daji bare kan titi,taku ƙalilan suka caccafkesu
Su kuma wata mota aka sakasu aka wuce dasu gida saida suka kusa isa gida saiga en sandan sunzo ran Adams sosai ya ɓaci "sai ku koma office ku cigaba da sulhun aure da sata da ƙwace ,da na bi taku da yanzu an kasheni da Amaryata" sake lafewa nadiya tayi a jikinsa tana jin kamar tana rabuwa dashi za'a sake kawo masu farmaki
Suna shiga gida momy tazo yina fitowa a motar nadiya na ƙanƙame a jikinsa ,ta haɗa su ta rungume ,duk en gidan sun fito ,shidai baice komai ba ya wuce ɗakinsa ,nadiya na jikinsa ita bata ganin gabanta ma ,ta tsorata ƙarshe
"A falo ya zauna yina mamakin yanda ɓata gari sukayi yawa ,kuma me zaiyi ya kawowa Al'ummar hausawa agaji ?! Din rashin abunyi ke damun yaran nan sun zama en bangan siyasa a basu kuɗi susha wiwi suyi ta ƙone² In sun mutu iyayensu ne kaɗai sukayi asara ɗan siyasa nacan besan fuskokinsu ba
Shigowar momy yasa nadiya miƙewa ajikin Adams a kunyace ta mike zata fita
"No dawo ki zauna you Are depressed ,karki fita ... Sweetheart ka gani ko? Kullim ina ce maka ka daina fita ba securities sai kaƙi ji da yanzu kasa na rasaku duka " As she's talking while she's about to cry
"Mom ya wuce ,but zan ma dady magana ,community needs politics affairance wajen gyaran Al'ummarsa,nima ina plan a raina "
[7/7, 18:19] 😘😘😘: 36
"Mom ya wuce ,but zan ma dady magana ,community needs political appearance wajen gyaran Al'ummarsa,nima ina da wani plan a raina" fita tayi tana sake masa Allah shi kyauta ,nadiya ma ta miƙe sum sum ta fice
Kwanci tashi asaran kwana ,shaƙuwane sosai ya shiga tsakanin nadiya da Adams ,hira kam kamar abokai son junansu suke basa iya ɓoyewa ,A gefe guda kuma adams kullum jarabarsa yina akan nadiya saidai ko ya shirya mata plan saita zille don itama ta soma gane nufinsa a kanta ,Adams yanzu shi yake girkinsa da kansa don momy tace tunda yinada mata bazata ringa masa girki ba ,shikuma girman kai bazai ce Nadiya ta masa girki ba dukda idan nadiya ta soma hallakasu da ƙamshin girki kowa sai ya sani amma bata gigin masa tayi bare yace mata ƙazama,Akwai wani lokacin da yina sake koya mata yanda ake karatu ta laptop ɗin ta ,ɗaukan excuse tayi ta wuce ,kicin tayo ma kanta Dambun indomie da ƙwai ,tayi apple and coconut juice ta dawo ta zauna ƙamshi yina tashi tanaci a hankali tana kallon screen ɗin ,Sosai yaji indomie ɗin ta bashi sha'awa "Ke wa ya girka maki wannan"
"Kaina" ta faɗi tana cigaba da cin abinci ta a hankali
"Dama kin iya dafa indomie?"
Ji tayi yaudai Bara ta feɗe masa biri har wutsiya "Foufou wait ,Ina ranar da kaje Lagos ka kira mom kace kuna hanya tayi maka dambun couscous ? Har ka dawo kaga mai kayan lambu da hanta kace baka taɓa cin kuskus me daɗinsa ba?" Jinjina kai yayi cikin jin dadin hiranta "To nice nan ,nayi ba wanda ya saka mun hannu"
Tsai da ransa yayi yina tunanin maganar don gaskiya Abincin yayi santinsa sosai kuma a lokacin batace masa komai ba "Anya ?? Anya kece a lokacin fa bakice kece ba"
"Nasan bakason girkina amma ai shiyasa momy tace bazata sake maka girki ba,saboda ka raina Ni"
"Gaskiya har yanzu ban yarda ba ,in kinaso in yarda je kiyi mun wani simple abu da zanji daɗinsa"
"Foufou barshi karka yarda ,Ni dai tunda ina jin daɗin girkina kuma ina enjoying ai shikenan "
"Habawa keko don ma kin samu zan ɗan ci "
"Ni ƙazamace and banida value shiyasa ka ke kirana da ke ,Kum inajin haushi saidai nasan bankai matsayin da zaka kirani da wani suna ba se ke"
"Wani suna kike so in kiraki dashi to? "
"Nadiyata mana "
"To shikenan je kiyi mun girkin "
"To fada inji"
"Hmmm wannan shi ake kira da titsiye ,kijezan faɗa"
"Tp shikenan nima bari in Gama cin abincina kar yayi sanyi "
Daga wannan ranar ne ya fara yarda nadiya suna shiga kicin tare dayaga wata zubin kamar tama fisa iya wasu abun sannan ne ya soma bari tana masa girki
Sai kuma me ? Sai ya tsiri sai ta kwanta wajen 10 na dare yace suzo ya koya mata karatu yayita faman en shashafe mata hannu ,ita wawiyar bata kawosa a komai ,saida ya fara koya mata Sex education ,ba kunya ya fara koya mata abu filla² girma taji karatun yayi mata shikuwa ba kunya yike faɗa mata organs ɗin sex na maza da na mata da alamomin shaawan maza da na mata,itadai sunkuyar dakai take ƙwaƙwarar motsi ta kasa yi "ok question " jinjina kai tayi still kanta a ƙasa "define concept sexuality" muryarta harɗewa yayi cikin daburcewa tace "Shine mutum yasan kansa ,da feelings ɗin sa da kuma desire to Sex activities" murmushi yayi "Da kyau karkasuwan sexuality" haɗe gira tayi "Hu'um na sani mana kawai mu wuce "
"Saifa kin fada "
"Akwai Homo sexuality ,shine jinsi ɗaya ya nema jinsi ɗaya ,in mace da macene ana kiranshi lesbianiam maɗigo kenan ,in kuma namiji da namiji ne ana kiranshi gay luɗu kenan.......sai kuma akwai hetro sexuality shine mace da na..miji amma haramun ne musulunci ya hana" murmushi yayi
"Amma banda miji da mata in an ɗaura aure ya halatta miji ya taɓa hannun matarsa yayi sexual intercourse da ita ,kuma ma lada zata samu indai an ɗaura aure ..." Zaro ido tayi "Har damu da aka ɗaura aure baka sakeni ba ? Gaskiya ina?"
"Sosai amma shiyasa Ni ban matsa maki tunda bakison Auren kuma kinsan munyi right ɗin mata akwai rashin tursasawa a wajen kwanciyar aure ko auren dole...now mubar hira mu koma karatu " hamma tayi "Foufou barci nakeji "
"Taf bako isaba sai mun gama "
"Don Allah wallahi wannan karatun iskancine fa "
"Ai Shine likitancin Ni zauna"
Shiru tayi ya cigaba da koya mata alamomin balaga
Kinga tashen balaga yina farawa daga shekara goma zuwa 19 ,akwai early 10 zuwa shekaru 14 akwai kuma late adolescent shikuma 15 zuwa shekaru 19 a wannan lokacin ne mata suke fara Nonuwa ,shine farkon Alama,gashi zai fito masu a private area na jikinsu ,man jikinsu zai ƙaru shine in suna ƙazanta sai pimples ya fito masu ,a wannan lokacin suke fara sanin su mata ne bai dace suna wasa da maza ba da sauransu a lokacin ne akeso iyaye su kula da tarbiyyan yara sosai saboda suna farajin taɓi da tasowar sha'awa matsananci kuma suna so suji an yi sex dasu ko sau ɗayane saboda suji yanda matan aure keji,don haka ake son uwa tayi takatsantsan taji damuwar yarinyarta ta koya mata wankan sabulu dana Tsarki wanda akeyi idan an gama Al'ada ko miji ya kwanta da mace,Alamomin da kuma zaka gane yaronka ya balaga ,zakaga ya zama energetic komin yawan aiki baya gajiya ,komin tafiya me nisa zaiyi ,Zakaga yina saka kaya a hangitse ,zakaga bayacin abinci masu nauyi yafi Gane snacks da junks food irinsu awara ,wainar fulawa ,ɗan sululu da sauransu ,zasunayin wasu irin magana wanda sa'oinsu kaɗai suke fahimta ,Alokaci. Sunason a yarda da ra'ayinsu in sun kawo sunason ayi shawara dasu ,sunason a nuna ana sonsu ,sunada kafiya da dagiya ,a lokacin ke uwa ba duka sai nasiha da janta a jiki ta gane ke ɗin ƙawarta ne ,kisan sirrinta ki bata shawara neatly ,tasan Al'auranta ta daina kwanciya cikin maza koda en uwanta ne ,sunan birjik ..." tuno baki tayi "Uhm Ni wannan ba amfana na zasuyi ba kawai mu canja topic innaje ɗaki zanbi a hankali in karanta"
"Amma watarana zaki zama uwar kuma har yanzu kina cikin sahun wainda na lissafo don haka Nine zan kula dake in zama abokinki in baki shawara in koyar dake ko?" Turo baki tayi "Kawai mu barshi haka "
Adams ya zama babbar malamin nadiya duk abunda aka Turo na karatu shi yake koya mata ,fannin addini ma yina ɓata lokacin sa wajen ganin ya ilmantar da ita ya kuma bata tarbiyya ,ya saka mata littafi kuma suna karatun ƙur'ani ,sosai halayyar Adams ya fara zama na nadiya saboda shine malaminta shi yake ɗaurata akan komai ta natsu sosai ,sam ta daina zancen ya saketa saboda a cikin nasiha ya gama faɗa mata azaban da yike ga macen da take neman saki a wajen mijinta ,sannan a kullum yina mata nasiha akan bijirewa miji a wajen shimfiɗa ,takanji ta wata guilty tanajin inama watarana Adams ya nemeta itakuma zata bashi mamaki ta hanyar da bazatayi masa musu ko wani abu ba ,koma ba komai ai tana sonsa shiɗin ne dai baya sonta yafison kausar ........Na ce tunanin Nadiya kenan
Yau Adams yina kwance a ɗakinsa ciwonsa ne ya tashi masa sosai ,Nadiya ganin ya gota lokacin koya mata karatu bai kirata ba yasa ta ɗaura mayafin gown ɗin jikinta ta kwasa laptop ɗin ta ,ishmawi da Alƙur'ani A falo ta tarda momy,ta tsallaketa bayan tayi mata saida safe da nufin ta tafi karatu ,inta gama zata kwanta a ɗakinta
Da siririn sallamarta ta shiga ɗakin ,dulum ɗakin ba haske sai wani dummy guda ɗaya jal ta dumly light ɗin ta jangoshi kwance cikin bargo
[7/7, 18:19] 😘😘😘: 37
Foufou nazo karatu ko har kayi barci?"
Cikin gwaruwan haƙora yake magana "kije kawai baby girl yau ba karatu"
Tsoro taji da sauri ta ajiye littafan akan table taje gefen gadon ta inda kansa yike ta tsaya "Foufou meke damunka ?"
Cikin ƙudundune jiki irin na me rawan sanyi yace "Baby girl kije bazaki iya mun komai ba" hawayene ya sirnano mata a fuska lokacin ta saƙa hannunta a gefen wuyarsa taji zafi sosai
"Foufou zan iya wani abu I'm a nurse to be,ina zuwa zazzaɓi ne ke damunka inajin "
Haurawa gadon tayi ta yaye bargonsa ta fara cire masa botiran rigarsa tayi exposing ƙirjinsa mai ɗauke da mayalwatan gashi da ƙyar tana nishi tace "Iyaaaah washhh" ta cicciɓesa daƙyar wai tanaso ta zaunar