Showing 21001 words to 24000 words out of 46143 words

Chapter 8 - Gidan Dadi Book 2 End Complete

01 Sep 2025

8641

raɓata ya wuce ,kurma ihu tayi ta falla da gudu ɗakinta ta ɗakko waya tana kiran Antyn ta Nusaiba "Anty dama kince shine wallahi shine gayican ya kaɗasu ,bansan me yace masu ba sun fita da gudu ko kallona basu yi ba"
"Yanzu me kikeyi ,kin fada wa momy?"
Saida ta sharɓe hawaye kana tace "A'ah "
"yawwa karki faɗa mata inada dubara...."
[7/1, 10:42] 😘😘😘: 27
Al'amarin Nadiya da Adams sai Allah ,A da a ɓoye yike Koran mata samari amma yanzu da ya gane ta ganesa ,a sarari yikeyi ,ko suna cikin zancene da saurayi zaizo ya ritsasu ya bubbuɗewa yaron mutane ido ,wai ba auranta yazoyiba yaga lutin jikine Yayi admiring haka zai ɗaurawa yaron mutane sharrin da bazai iya karyatawa ba,sai ya kuma fake da hakan ya koreshi yace kar ya sake zuwa ,ko yasa a ɗaureshi


Ranar ƙarshe da yayi mata hakane ta ritsashi a bakin ƙofa yina shirin fita "Malam meye haɗin ka da Ni da zaka ringa koramun Mutanena ,Ni ina saka maka ido akan enmatan ka ne ,wannan baƙincikine kaga yarinya akwai farinjini ga kyau "
Tsaki yaja ya mata wani irin ƙasƙantaccen kallo na irin har ke nan ɗin nan ,ganin still tana tsaye riƙe da ƙofa yasa ya doka mata tsawa ,wanda ya sata sakin ƙofa da sauri ta fashe da kuka shi kuma ya wuce ɗakinsa yina murmushin ƙeta.


*****
Tun ana i sati uku bikin Nusaiba ta tattara kayanta ta gudu abujan itadai momy tace zasu zo ranar ɗaurin aure ,Adams kam baisan da gaske yina son Nadiya ba saida akayi sati baijin motsinta ,rannan dai ƙasa daurewa yayi ya kalli mom "momy Ina yarinyar can ?"( Dama shi baya kiran sunanta saidai yarinya )
Harara ta watsa masa ta cigaba da hidimarta Kobi ta kamsa batayi ba "Mom kun ɗauko yarinyar mutane Atleast ya kamata Ku rinka sannin inda take zuwa da irin yaran da take hulda dasu kullum ita kenan tara gayu suna ƙetaro securityn da duk suka kewaye gidan nan suna shigo mana duk saboda ita haba don Allah ,to yanzu wai tana ina tsawon kwanaki uhum?"
"Ubana kuma ? Zo ka shaƙeni kaji ,ai bansan yanda ake tarbiyya ba tunda har na haifeka na kasa maka tarbiyyan sai kazo ka koya mun"
"Ni dai mom banceba Amma ai dai macece ya kamata ki kula da ita "
"Adam banyi ba ɗin ,idan kazone ka tasani da iyayi tashi ka bani waje"
"Miƙewa yayi ya wuce ɗakinsa ,ransa a ɓace,to Ina tashige ne?" Laptop ɗinsa ya jawo da ya kwana biyu bai duba sashen Nadiyar ba , ya fara kallon a natse har yazo ƙarshe inda take haɗa akwatunanta dasu handbag ,tsaki yaja ok ? Makaranta ta koma da zama kenan ? Zai kashe laptop din yaga ta saka waya a kunne "Anty on my way to airport azo a ɗaukeni banso inzo Abuja ,ina jiranku ,just gwarumpa"
Shiru yayi cikin damuwa "kardai tsanani na ne ya kori yarinyar nan?"


Bayan sati ɗaya ,lokacin an shiga satin bikin Nusaiba ,nadiya kuma satinta biyu a Abuja ,Ansha gyaran Amare duk abunda taga ƙawayen Nusaiba sun mata na Sudan itama sai an mata don haka in ka gansu sai ka rantse da Allah dukkansu amaren ne tare za ayi masu aure ,lallen nan ya bala'in masu kyau ,programmes sun cigaba da tafiya on progress samari kuwa Nadiya sai zuba masu wulaƙanci take ta samu wani sudaniest ta liƙe masa sunata shan love ,Ranar ɗaurin Aure Saboda mutanen dady na nesa ƙarfe biyu aka saka ɗaurin auren don haka ,ƙarfe 10am jirgin Momy da Adams ya sauka ,dukda baiyi niyyar zuwa ba ,sai don momy ta matsa masa ,musamman saboda mai girma gomna nada ganawa da manyan Commissioners nasa ,tace bai kamata basuyiwa Nadiya kara ba haka ,aikuwa suna shigowa varendar da ita suka fara arba ,jikin nan sai zuba glowing yike ta na sanye da wata gown mai kyawun gaske onion colour ,tsaye take jikin wata vibe car ,sai anacen saurayinta ,dasuketa shan hiransu ,amma sai isuwa take masa "Yuzarsif takalmina yayi ƙura zai ɓata mun gayuna " ,da sauri ya sunkuya ya kamo ƙafarta bai duba mutanen da suka cika compound ɗin ba ya fara goge farin half cover ɗin ta da yaji adon stones sak itace amaryan ,ɗan miƙa masa hannu tayi tana dariya wai ya bari ,su kuma su umma sai ɗaukarsu hoto sukeyi ana dariya ,Adams takaicine ya hanashi fitowa daga motar a ransa yace "wato yarinyar nan nine Bata ƙauna ,takan mistakenly nace mata bitch ta kama yawo da hijabi amma jiba ta miƙa ma gardi ƙafa yina goge mata takalmi idonsa nakan farin ƙafar ta da yasha jan lalle su kuma en zuga me kantu sai hoto suke masu? " Ɓalle ƙofar yayi ya fito basuyi aune ba sukaga ya finciki ƙafarta ya wurgar ,ya ɗagoshi ya tsinke sa da mari Wanda saida ya kifa ,yayi tambul a ƙasa


Ɗagowa tayi a tsorace duk zatonta ma ko wani daga cikin en zafin kawunan nanta ne ta ɗago zatayi masifa ta ganshi riƙe da kwankwaso bayansa guards ɗin sa ne tsaitsaye da bindigogi,gaba daya haraban tsit kamar ba motsin halitta kowa ya ƙosa yaga yanda dramar zai tsaya saboda kowa dai yasan Nadiya masifaffiya ce ,to zata yarda ta ƙyaleshi ya kunyata ta cikin taro? Wasu kuma mamakin ganin Adams suke a gidan bikin matsashin multi billoniya da ake ji dashi a ƙasar nan ,koda ba abun mamaki ba ne in anyi la'akari da yanda baban su nadiya ke hulɗa da manyan en siyasa ,shiyasa da yawan en mata suka sai kaya suka saki ɗinkuna saboda sunsan they will shine their eyes ,su darzo zuƙeƙen Attajiri
"Wani zalunci kenan wannan? Ka sanshine ,to bari kaji a kan Dr. Yuzarsif zan iya ɓatawa da kowa ,bar wani isa da tozon wuya nan ba gidanku bane gidan mune ,kuma a ɗan samu da sallamar mana wainnan mutanen masu baƙaƙen kaya da jajayen ido ,su tsaya a daga gate don kai ba shafaffe da mai ,ba ne" banza da ita yayi yina daɗa ƙare mata kallo ƙafarta ɗaya sai karkaɗawa yikeyi


"Kace masu su fita mana ko ku fita duka ,mun gode zuwa ɗaurin auren" shiru ya sake mata ganin bazai tankata ba ,ga masoyinta zube a ƙasa kunya ya hanashi ɗagowa yasa ta miƙa hannu zata ɗagosa "Kaji tashi masoyina" tsawa ya daka mata "karki taɓashi " tsar ta saka idonsa cikin nasa cike da rashin kunya tace "in an taɓa "
"Zaki bar gidan bikin nan kuma kin gama shi yanzu nan " shewa ta saki "Allah sarki wallahi kuwa kaci ƙarya ka kwana da yunwa nan ba gidanku bane da zaka ringa koranmun masoya "t takai hannunta ta janyo hannun Yuzarsif kaji "Zo muje masoyina ,kace kana sona nace maka bana yi ,ka fitine Ni wai ana soyayya dolene ? Ni kalar larabawa nike so ,kaji mu yuzarsif kayi haƙuri nan gani abarmu dole .....Nadiya dai gata anan Gagadako Toron Giwa ,cinyar sa maganin mai haɗama,saiƙo ɗauke ganin kaya,nan gani kuma a Barni ya zama dole....ta ƙare tana banka masa harara ,bayan ta jujjuya ta ƙara juyawa


Kallon securitynsa yayi kawai suka damƙo wuyar Yusuf suka jefa cikin Hilux ɗin su suka tada mota da gudu zasu bar gidan ,watsewa tayi akan gwuiwarta ta fashe da ihun kiran "Momyyyyy zaisa su sabauta mun miji"
Zaro ido yayi ya nunata "Ai ashe kinada miji ,yanzu fa kikace Ni anacene ,na kafe ina sonki kina mun wulakanci,ok I'll show you how to defict love by power..."
"Na daɗe da sanin kai mugune but let me tell you this our home"


Banza yayi mata ransa na Azalzalarsa yina tunanin irin bugun da zai sa a yiwa Yuzarsif
Nusaiba ce tazo da sauri,saboda kiran ta da Ummu tayi a waya ,duk en matan sun watse sun barsu su kadai "Nadiya bakida kunya ,meye haka ya Adams ɗin kike musayan yawu dashi " wucewa yayi fuuuu ya barta a tsaye yina nadamar me yasa yazo bikin ma At the first place?gashi kamarsa ana masa wulaƙanci a cikin taro ? What a shameful thing?"


****
Janyo nadiya akayi daƙyar cikin guda tana kurma ihu ,a sannan ne iyayen suka san meke faruwa her Excellency cikin fushi ta ɗauki waya take kiran Adams ,kan nadiya akan cinyarta ,tana rarrashinta ,saboda yanda take kuka itafa kawai yasa a sakin masu ɗan mutane ba a ƙasar nan yike ba ,saidai duk kiran da take masa line busy ,Adams kam ,hotel ya wuce yaje ya kwanta kawai damuwa na nuƙurƙusansa Ya bar guide ɗin sa ya duba masa zuwan Dadyn nadiya ,ƙarfe 1.0pm gabaɗaya unguwar ya ɗin ke da Bil'adama ba wajen packa mota saboda yawan motocin da suka fita layin an kashe hanya kwata kwata ,cikin tururuwan jama'ar Adams ya shigo ,dady dake zaune tsakiyan masu ɗaurin aure ana jiran ƙarasowar iyayen Hisham , ga manyan mutane a kekkewaye ba yaro ko guda ɗaya kowa ka gani babane ,Adams dama ya samu yaje har gaban dady sannan ya roƙeshi zasuyi magana na minti biyu
Girman Adams da yake gani shi yasashi ɗan gusawa kaɗan daga cikin taron wanda tuni en jarida suka fara flashing camerorinsu a kansu ana watsawa a gidajen TV kowa na gani ,Nadiya da take kwance a cinyar Her Excellency kamar mara lafiya ,an barsu a ɗakin su kaɗai ,sai zuba mata shagwaɓa take ,hasko babanta da Adams taga anyi a wajen ɗaurin auren ,zaro ido tayi "Mom me yike cema dady kuma?" Murmushi tayi mata "yina masa Allah ya sanya Albarka mana "
Ji tayi ranta bai natsu ba a hankali ta fara Karaye kerayen wayan dady saidai bai ɗauka ba


A ɓangaren su da kwa jan Adams mota yayi suka fara magana a tsanake ,suna fitowa Dad ya koma wajen masu ɗaura aure aikuwa nan en jarida wanda suka daɗe suna neman daman da zasuyi magana da Adams basu samu ba suka yayyaɓesa da mike rasa wanda zai amsawa tambayar a cikinsu yayi ,kawai sai ya daga masu hannu "kuyi haƙuri yau rana na ne ,zan angonce don haka ina ma duk baƙin da suka halarta bikina ,godiya Plz ku ƙyaleni haka..." Ya kufce ya faɗa mota shida Guards ɗin sa suka kukkutsa suka fice a cikin taron.


Ba nadiya kaɗai ba harta momy ta firgita da maganar Adams ,inda en jarida suka ɗauka da sharhinsu akan auren Adams


"Momy wa zai aura ɗin?"
Kafin momy ta iya lalubo amsar da zata bar kawai sai ga kiran Yuzarsif "Nady ya sa an sake Ni kuma ya bani haƙuri kema kiyi masa haƙuri plz"
[7/2, 10:22] 😘😘😘: 28
Tsaki taja ,shashasha na mata mai ƙashin gwuiwa wanda bazai iya fighting ma kansa ba,wai yasa an sake ni ya bani haƙuri(ta kwaikwayi maganarsa cikin gatsali,sannan ta ɗaura da daka masa tsawa kamar uwarsa) Ni dallah katse waya,kar ka cika mun kunne da trash,mtseww"


***
Mom miƙewa tayi tana kiran wayar Adams still line busy ,wannan ya tabbatar mata da yayi Black mailing numbobinta ne,da sauri ta hau kiran private number ɗin mai girma gomna,da ta katse ta sake kira ,mai girma gomna dake tsaye a gaban taron yina bada Speech jin kiranta ba ƙauƙautawa yasa yai curtailing maganar ,ya ɗauki excuse da sauri ya fita ya ɗauki wayar "Excellency kana Ina?"
"Calm down plz,meke damunki ?"
Kawai sai tayi kamar zata fashe masa da kuka "Yallaɓai Yaron nan zai kunyata Ni a cikin taro zaisa in kasa fita cikin jama'a ,zaisa ana nunani ana zagina ,Plz do something!" Magana take da sauri da sauri kamar ranta zai fita a jikinta ,ya daɗe rabon da yaga bribe matarsa a cikin wannan critics ɗin ,don haka shima ji yayi hankalinsa ya ɗan tashi ,amma kansa duhu ya shiga baisan wa ya ɗugunzumo masa mataba ,don tunaninsa bai basa Adams ba don shi ɗin baida rashin jin magana


"Wai me akayi maki,kuma wanene shi? Beside kina inane,Wai Ina excos ɗin da kuka je dasu meye amfanin su?"
"Excellency Adams ,fadansu da nadiya har a cikin taro ,i try to convince Nadiya but very unfortunate ya bi babanta wajen daura aure ,and if I guess well ,He is seeking his hands on marriage to her "
Sosai abun ya baiwa Gomna mamaki ,baisan me zai ɗaura wannan auren akai ba ,auren manufa ko auren dole?,amma saboda ya kwantar mata da hankali sai cewa yayi "Then? Dama ba kun damesa ya kawo mata ba ,shine yau ya fidda ɗan sa kunya zai baku suprise da yarinyar ki,dama i perceived love rltnship with..." Katsesa tayi da sauri "This is an arrogancy oh houuu?"


"No plz I'm a man and a politician too . so, nasan Tunanin Adams bazaiyi abinda zai ɓata mun suna a gomnatina ba ,calm your nerves ,Get some rest bari inbi abun a natse...."


Jifa da wayar Momy tayi saboda ƙaran da nadiya ta tsage dashi "what am I hearing do I have hearing hallucinations....momy ya kasheni wayyo Allah na ,this very time da zan fara cin enmatanci na da tsinke ya cuceni mom kicemun ƙaryane ,ba aure na da Adams bane akeyi kawai Anty da ya Hisham ne" rungume nadiya momy tayi tsantsan tana mata Addu'a a kunne ,wanda hakan yasa ta shiru sai wani irin hawaye dake gangaro mata a kunci masu tsananin azaban fita ,yunƙurin magana Nadiya takeyi Amma momy na danne mata baki "kiyi haƙuri Nadiya I'm his mother komai zai zama normal kinji " nuna mata Tv Take a na nuno hotunan su dabam dabam ,nashi saye da suit sai ƙwara ɗaya jal da fararen babbar riga ,ita kuma ga nata nan birjik cikin gayun da ta dingayi a events ɗin Anty Nusaiba ,ana jaddada shelar ɗaurin auren matashin multi billoniya ɗin ,kuma yaron Gomnan da ita Nadiya ......wasu hawaye suke sharara a idonta "Mom me zakiyi bayan an ɗaura auren ? Me zakiyi da gaskene wallahi da gaskene ,Adams ka cuceni kai kanka kasan ban taɓa jin sillin sonka a raina ba sai tsantsan tsana,mugu Azzalumi ,maƙetaci ,Allah zai saka mun" matse mata baki momy tayi da sauri
"Nadiya stop mijinki ne in kika zageshi zai kashi yanzu kaifin bakinki yafi tasiri akansa fiye dani uwarsa". Fincike jikinta tayi da sauri a jikinta ,sannan ta bita da kallon tuhuma
"Oh mom kar kice mun dake aka hada baki a cuceni " janyo hannunta tayi zata rungumeta ,da sauri ta ƙwace kanta "No! Just confess dama nasan kina sonsa da yawa Ni kuma baki damu da farin cikina ba ko?"


"Haba Nadiya you knw I love you more and more!"
"Ok faɗa mun ,ki nuna mun kina sona ki kirashi kisa ya sake Ni yanzunan don yayi kaɗan yasa akirani da ƙaramar bazawara gwara kowa yasan an warware auren yanzu yanzun nan"


"Shikenan idan anyi hakan zaki daina tuhumata?" Ɗan murmushi ta saki haɗe da wani hawaye ,sannan ta gyaɗa mata kai


Wayarta ta ɗauka ta cigaba da kwatanta dialing Kiran Adams ,cikin hukuncin Allah ya ɗauka "She need her divorce,inason ganinka a gidan in nothing less than 20 minutes ko ina kake ka zo " tana gama magana ta kashe wayarta cikin ƙunar rai ,haƙiƙa taso matuƙa ta zama inlaw ɗin nadiya amma yarinyar tana ƙin Adams ƙiayyyar da ƙila in an barsu tare zata iya kashesa




En uwane da dangi suka ringa knocking kowa nason zuwa yaga idon matsiwaciyar amarya ,basu son fitinar da akeyi a ciki ba ,mom ce ta leƙa a hargitse tana basu haƙuri


25minutes After


Cikin tashin Hankali Adams motocinsa suka shiga turo kai cikin compound ɗin ,ya canja kaya zuwa Riga long sleeves da cinos ɗin wando baƙi sai half cover ɗin baƙar takalmi ,gashi kansa sai sheƙi yike kai da gani kaga matashin arnen mai kuɗi ,sawa yayi ai masa iso zai shigo gidan ,ai kuwa tuni mata suka ɗauki guɗa "Wai kaga marasu kunyan Angoye ,anzo rarrashin amarya mu ko ganin idon amaryan ma bamuyi ba tunda aka ɗaura auren " Nusaiba da taci kuka ta ƙoshi ne ta fito tana masa kallon da yina gani yasan na tsana ne
"Ka jira bari in fito maka da ita"
Murmushin ƙeta yayi na iyaka saman leɓɓansa sannan ya koma back seat ɗin motar sa dake tsakiyar na gurds ɗin sa




Nusaiba na shigowa Nadiya ta miƙe ,zatayi tsiya momy ta ɗaga mata hannu sannan tayi mata magana a kunne "kar ki mata tsiya kawai,kije wajen sa kina zuwa ki haɗe rai ya baki takardan sakinki ki fito kalas!" Jinjina mata kai tayi taje wajen sink ta wanko fuskarta da yayi dameji ,ta ferfesa turare ta fito Anty Nusaiba da sauran ƙawayenta suka rufa mata baya ,har wajen motar da yike,yina hangota tun daga nesa amma ƙirjinsa lugude yike masa yanda Idanuwarta sukayi lu lu saboda kuka abun daɗi yayi masa ,sai yaga ta ƙara kyau a idonsa , bazai so wasan ya ƙare a hakan ba ,zaiso yaiyi ta ganin launin kukanta a gidansa ,amma ya zaiyi mamansa tace ya sake ta? Kai haba ina! Babu biyayya wajen saɓa ma mahallici momy saidai kiyi haƙuri ban auri Yarinyar nan don in saketa ba ,sai don manufar in koya mata hankali ta gane akwai tazara riɓi dubu a tsakanin mu ,kuma tasan Ni ba sa'anta bane" amsar da ya baiwa kansa kenan kafin guides suka buɗe mata ƙofan bayan da yike zaune ,ta shiga ta zauna Anty Nusaiba tana kiciniyar buɗe front seat wajen me zaman banzan driver .
Da sauri ya leƙo da kansa ta ƙofar da Nadiya take zaune har jikinshi na gogan nata "Anty Plz zamu ɗan sasanta kanmu in mun gama will let you be" jinjina kai tayi ta juya da su Ummu duk ba wanda ya kalleshi suka koma cikin gida


Harara ta kwasa mata da jajayen Idanuwarta "god forbid kasan babu sasanci a tafiyar ,gwara ma ka sahalewa kanka don kasan Ni ɗin ruwan manyan mutanene ba Sa'arka ba" dariya yayi ya taune leɓen sama sannan yasa halshensa yayi liking leɓensa na kasa ,cikin cusa haushi yace "Haka ne fa ,to waye manyan mutanen ina bani ba,wow programmes of event ɗin aron da kikayi sun maki kyau gaskiya ke ɗin kalar camera ce" fusata tayi
"Wannan ba damuwarka bane ai dama nasan events din bikina na musamman ne ,mijina kuma yinacan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login