Showing 15001 words to 18000 words out of 46143 words
uncle ɗin" dafe kai nadiya tayi saboda ba wani uncle da tayi wa Chuchu "sunanshiiiii uncleeee....." Taɗan ja fasali , fincikar motar da sukaji anyi da ƙarfi yasa su sakin ƙara momy wayar da takeyi ya faɗa gefen ta ,bakinta na rawa tace "Yadai me ya faru wannan wani irin tuƙin kasadani kake yi Sweetheart?" Ji yayi kamar ta watsa masa wuta a zuciya da ta kirasa da wani Sweetheart ,atleast fyn babe ya kamata ta kirasa da wannan sunan ba mamansa ba.
Shan kunu yayi ya cigaba da driving idonsa sun firfuto sunyi ja jijiyoyin kansa sunyi raɗa² kallo ɗaya mom ta masa saida ta firgita da ƙarfi ta ƙwalla kiran wait!!! Kashe mota ka sauka gefen hanya "yina hura hanci yina kumbura baki ya sauka,kamar wani kumurcin maciji haka yike feso Numfashi
"Bakada lafiya ne ? "
Waigawa yayi ya kallesu sai wadansu suke kamar ba abinda ke faruwa "mom ke kika matsamun in kawo ku airport bayan kinsan inada wajen zuwa amma sai ku maisheni driver?"
A ɗan daburce tace "au subhanallh Shine kake wannan abun,haba har naji tsoro wallahi ,Nadiya koma gidan gaba ,yayanku baison a kirasa driver ,shiru tayi ita bazata iya cema mom bazatayi ba itakuma bazata je ɗin ba ,kafin tayi wani responding yace "Taf Nine wannan zata shigar mun gaban car ,sannan tai spoiling mun ciki a banza ?"
Tattare gira mom tayi "meye haka kaga classy babe en matan Abuja tunda ta shigo ƙamshinta ya gama gauraye motan,Kai ina bacin ta sanmu ka isa ta shiga gaban motanka,kalleta fa kalar madara ,kalan sawa gaban babbar mota ,ko yarinya maza koma gaba kinji Nadiya ta ,Allah ya nuna mun zuƙeƙen mijinki wallahi sai yashad dogayen sharuɗɗa kafin in yarda in basa baby na"
Banza yayi mata yanda take kwaɗa Nadiya da yanda yarinyar take wani jijjin kanta ji yayi kamar ya kwalfeta da mari yaga ƙaryan iyayi
a hankali nadiya ta mike "Yes mom" ta fada a taƙaice ta koma gidan gaba ,ta kulle a lalace bai rufu ba,shi yaƙi magana ,sai daɗa hawa yike kamar fulawa yasha yist itakuma sai shafa sabuwar waya ta take tanayin kamar tana chating a face book tana wani ƙasaitaccen murmushi
Zaman shirun ne ya ishi mom tace "mu tafi mana"
"Ce mata ta rufe mun ƙofa da kyau"
"Haba Sweetheart bansanka da ƙorafi ba na za auto ce motan,ka rufe mana "rufewa yayi ya fincika motar " ta so faɗowa jikinsa,ko taji ta damu ta cigaba da chatting din ƙarya a Facebook ,tana ɗan smilling ,sai can ta ɗan tare bakinta da tafin hannu taɗanyi wani slight dariya "oh hahahah" in ya waigo sai ta sha kunu ,suna zuwa bakin ƙofar ɗakin mom saida Nadiya ta taɓa ƙofa zata buɗe yaja wata anniyar kwana wanda inda ba babbar mota bane dole ta kife ,a furgice Nadiya ta ƙwalla ƙaran kiran momyyyyy!
A ransa yace "Banza me ƙwacen uwa tunda kika shigo rayuwarmu an daina kula dani" yina zancen zucin ne amma idonsa hararanta yikeyi don haka motar na gama tsayuwa ta fice wayarta manne a kunne ta kama wayar ƙarya (Fake call)
Momy a hankali ta fiddo Chuchu itama tabi bayan nadiya da gudu tana kiran ta jirata ,mom a hankali ta fita shikuma yaja motar da sauri ya bar gate ɗin cikin part din mom ya shiga second gate ɗin ajiye motoci ,da nufin ya canja mota yayi ficewarsa ,Black car ɗinsa ya shiga saidai ya kasa tada motar saboda yanda kansa ya sara masa hakan ya sashi kifa kansa a sitiyarin kawai yinajin ransa na suya ya rasa meke ɓata masa rai ,Mom a falo ta bar nadiya da Chuchu suna shigo da kayanta da ma'aikatan suke shigowa dasu ,ɗakinta ta shiga ,ranta na ɗan rawa ,tsoron irin fitan da taga Adams yayi take tana zancen zuci take kiransa a waya "Nikam na rasa wani irin tsana Adams ke yiwa nadiya ,Yarinya tayi kyau kamar me? Ni Ason samuna wallahi sai na bashi nadiya bazanso in bashi baren da zata auresa don kudinsa ba ,ga na gida mai son Baby amra mun san halinta ta san namu,amma na lura zazzafar tsanar da yayiwa yarinyar nan ba na wasa bane..." Saida ta kira sau uku sannan ya ɗauka
"Kana ina?"
"Ina car "
"Are you ok?"
"Yes" ya bata amsa a taƙaice
"Ok safe drive sweetheart "
Jinjina kai yayi kawai ya ajiye wayar ita kuma ta kashe a hankali tana masa en ƙananun addu'a
*Gidan Daɗi ,Littafin kuɗine ,regular 300₦ vip 500₦ special 1000₦ katin mtn a tura ma wannan Number 09065990265 ko a biya ta nan bank din 7782217014 , Mohammed hassana ,fcmb*
Oum Aphnan✍️
[6/28, 11:14] 😘😘😘: 23
Saturday
Ƙarfe shida na yamma gida ya kacame da ƙamshin girki ga na turaren dakuna dabam dabam ,yes Nadiya tasan momy nada tsafta amma kuma ,yau abun is odd ,har abubuwan da ba'a taɓa saida aka goge ,Wando falazo ta saka da er riga mai kyau pink colour sai ta tufke gashinta da yasha oiling ta matse da Pink band ta zura silipas ɗin ta na ɗaki ta fito ba kowa a falon sai burners dake fidda ƙamshin turarruka ,labulaye na ɗan wulwuli saboda iskan dasuke kaɗasu a hankali ,bin door exist tayi ya kaita wajen Quarters ɗin baya inda take jiyo hayaniya ma'aikatan gidan ,aikuwa sai talo² sukeyi wasu na dicing su carrot abundai azimun ,zuwa tayi gaban rabi mai aiki
"Rabi baƙi zamuyi a gidan ne?"
Washe baki tayi "haba ƙaramar Hajiya baki da labari? Ai surukuwar Her Excellency ce ta dawo Nigeria bayan tsawon jinyar da tayi na Wata takwas a Cairo yanzu shine tayi lafiya za'a ɗaukota ,inajin su Hajiya ma sunje ɗaukota" ɗan jim nadiya tayi "Ok tabbas banga kowa a gidan ba ,shine kuka ƙuƙe anata girki kamar zakuyi baƙi tururu? "
"Kai hajiyar nan Hmm Wai halan bakida labarinta ? "
"Ni ban taɓa sanin su Adams sunada kaka ba ma"
"Aiko ga part ɗin ta can wannan na rufen na kusa da na Adams ,ai ji da ita Adams yikeyi in tana nan bame ganinsa yina ɗakinta "caɓe baki tayi "kice shi yasa ku wannan wahalar?" Shiru tayi bata amsata ba ,saboda tana tsoron kar munafukan cikinsu su kaita gaba
Wucewa kicin tayi ta sama wani cinyar ɗawisu an soyeshi da fulawa ta saka a ƙaton tray ,ta zuba coslow a wani ƙaramar roba ,ta tsiyayo ' ketcup ta jera ,ta haɗa green tea ta fito abunta a center table ta ajiye ta ƙara gudun Ac ta kamo channel ɗin larabawa tana bin waƙoƙin da suke sakawa a hankali cikin nishaɗi saboda duk yawanci ta iya ,Dirkan motarsu taji a hankali ta leƙa ta window harda er ɗagenta tsohuwa ce har ta duƙa tana ɗan dogara sandan girmanta a hankali shikuwa ya rungumota ,a hankali suka shigo da ita Hajiya momy rirriƙe da kayanta Chuchu na en tsalle tsallen ta
Saida suka shigo gabaɗaya sannan nadiya ta ɗauki sauran naman da ya rage a jikin ƙashinta zuge a baki ,ta miƙe da sauri
"Oyoyo hajjaju makkatun ,to ya sahan jiki meye na riƙe sanda bayan ance kin warke " ta warce sandan hannun hajiyar ta riƙe hannunta "Oya ga wakan larabawa nan irin naku ɗan rausaya muna mu gani eye...eyehn ba" sakin baki Adams yayi yina kallon ikon Allah itakuwa Hajiya tsohuwa ƙanƙame hannun Nadiya tayi ta ɗan murmusa "Ayya er nan ba ƙafa"
"Ba ƙafa shine aka dawo dake? Aikuwa baki warkeba yanzun nan zamu koma cairo kai inajin sauya Maki Asibiti ma za'ayi " Hajiya tsohuwa da ta tsani zaman asibitin wanda silar hakan ta nemi sallamar dole ,saurin girgiza kai tayi ,kunsan dai sha'anin tsoffi in angirma halin yaranta ke dawowa ,kumbura baki tayi cikin shagwaɓa "Uhm uhm zan tattaka amma a Barni in zauna cikin gata na" zame hannunta tayi a hankali ,ta nuna mata kujeran da tsakaninsu dashi bai wuce taku goma ba ,tasan zata kai bata wahala ba "oya jeki can kafin in irga goma ko yanzu mu koma cairo kinsan Ni fa likita ce" a hankali Hajiya ta tattaka kafin ta ƙarasa tai saurin miƙa hannu ta riƙe kujeran ta zauna da sauri tace "Washhhhh" aikuwa tayi tsalle sai tafi Raf Raf Raf duk ɗakin dariya aka saki Adams kuwa gefen ƙofa ya tsaya ba abinda yike kallo sai manyan Ass ɗin Nadiya da take jujjuyasu ga Nonuwa tsam a ƙirji tubarkalla,amma a haka batajin nauyin jikinta take daka tsalle
Mai girma gomna da ba wanda yasan da shigowarsa saida ya magantu "Ahhhh Hajiya mama anyi lafiya ,dole bazamu koma cairo ba saidai muje Umrah muyiwa Allah godiya " bata rai tayi "Kai Allah na tsani hawan jirgi ,ka barni in huta" janyo hannuna tayi "Zonan ƙawata me kyau" a hankali naje gabanta na zauna ƙasan carfet ina ɗan matsa mata yatsun ƙafarta a hankali amma fuskarta na kan fuskarta ,shafa mata kuncin tayi a hankali sannan ta kalli momy da ta samu kujera ta zauna sai kallon su takeyi "Wai ina kuka samo wannan zuƙeƙiyar Fillon ,Kar ku faɗa mun Adamu aure yayi baku faɗa mun ba? " Dariya aka fashe dashi duka ,kowa yina kallon réaction ɗin Adams ɗin daidai da gomna da bai faye zaman gida ba yasan da er tsamin da ke tsakanin Adams da Nadiya ,aikuwa kafin kowa yayi magana yayi saurin carkewa "Allah shi kyauta wannan ƙazamar a matsayin matata"
Cikin tsiya tace "kai gafaracan wallahi wannan yarinyar tafika komai ga kyau ga kirki " nadiya kwantawa tayi a ƙafar Hajiya mama mai lafiya ta kalli fuskar Adams kawai ta fakaici idon kowa ta masa gwalo ,habawa wani husata yayi yazo da gudu zai kai mata mangari ,a zuciye Hajiya tace "Akul ɗin ka ko yanzu kaji saukan yatsuna guda biyar a kuncinka,kaga mun lalataccen yaro ƙatuwar budurwa kamar wannan zaka duka ,jiba tunda nazo sai matsamun en yatsu takeyi ,ta koya mun tafiya yanzu nayi taka tara ,abun banzayen likitocin can suka kasa ,wannan likitan mai ilimi tafi en can sanin makaman aiki wallahi ...." Bushewa da dariya akayi Itakuwa ta ɗaure fuska saboda iyakan gaskiyarta ta faɗi ,shima kishine ya murtukesa ,cikin ɓacin rai yayi magana "Amma kina kallo gwalo tayi mun ko ,ita bakiyi mata magana ba sai Ni "
"Gwalon gidanku? Gwalo na ƙari ne? Nuna mun gwalon a jikinka...ke er fillo wai kin masa gwalo "?
Ta tallafo fuskata tana tambayata ,Girgiza mata innocent face ɗina nayi "Uhm uhm hajjaju ,kawai dai jinin mu bai haɗu dashi bane "na sake fakaitan ido na kantara masa fuska alamar "weeeyyy an gwaleka ɗin nan ".
"To ahir ɗinka kar inji kar in gani ,yo ko wannan baƙin halin ya hanaka samun masoyiyan da zata aureka ,Ni jurga ban waje"
"Gaskiya ana cutana da yawa a gidan nan dad ,tunda nadiya tazo gidan nan momy ta soma mun faɗa ,Chuchu ta rage sona ,yanzuma gashi ta ƙwace mun fada a wajen uwata ,saura kai kaɗai ka ragemun dady"
Cikin ba'a His Excellency yace "Nima nabi bayan Hajiya mama ,kaga bakada kowa kenan,ko er daddy ?" Ya juya akalar tambayarsa yina kallona
Mamaki nayi ashe gomna yinada barkwanci ,a hankali na ɗaga masa kai ina dariya ,duk na takura na kasa tashi saboda kayan jikina bansan da gomna za'a shigoba ,ga Hajiya mama ta shaƙuro mun wuya katamau sai shafa mun gashi take duk na jigata.
"Fatsima ,wai halan er ɗan uwankine na Sudan naga kyawun yayi yawa ga sunan nata ma na larabawa ,mai wuyar faɗi wai...nidai zance er fillo"
Momy da tun ɗazu take shan dariya tana kallon mu duk nayi zufa tace "Hajiya er kawatace ,a Abuja suke amma tana karatun likitancin ta ne anan shine take zaune damu ,Hajiya sakar mata wuya tana shan wuya "
Dasauri ta zare hannunta a wuyana ,tana shafan wuyan da lallausan hannunta da ya gama dagwargqajewa saboda zama cikin AC "wayyo sannu Fulani yahaƙuri kinji,wato mutan Abuja ne,Allah sarki har na tuna da Alhajina marigayi sanda mukayi zaman habujan nan ya gatanta ni lokacin shine jakadan shugaban ƙasa zamanin mulkin farar hula wani Shugaban ƙasa ne kuwa???" Ta tafi tunani .tsaki Adams yayi
"Yanzu zata fara damunmu da surutun begen mutumin da tuntuni ƙasusuwansa sun daɗe da fari a kabari ,Ni inje inci abincina nagama haɗa betta na an tada hankalin mutane sai anje taryoki "
Ɗaga murya tayi kamar za tayi magana da wanda yake nesan duniya ,da baki ta nuna dady da momy "Ga wainda kayiwa tsaki nan a zaune ba niba ,ɗan tselanƙwa kawai kwanan nan zamu koreka a gidan nan indai baka nemo mata ba " wuce ta yayi inda sabo ya ci ya saba da gorin hajiya mama ga shi in yayi mata magana ta zage iyayensa a gaban idonsu
Kayan abinci aka shiga furfutowa dashi ,shikuma mai girma gomna ya tsallake ya tafi sashensa saboda in yina nan masu aiki basa shigowa ,A fujajan ya fito Yina hura hanci kamar zai hauka
"Momy wayacin min naman da na soye shi " riƙe cikina nayi saboda dariyar da yazo mun yanda ya faɗi kalmar "Soye shi " ɗin nan daga gani shi kansa ya yaba yasan zai daɗi
"Ina zan sani Sweetheart,muda muka fita tare? kaje ka nema a hankali,zai gudu a kicin ɗin ne ?kai matsalar ka baka duba abune sai kazo ka tada hankali"
Yi yayi kamar zai fasa ihu "Mom ko mayyar nan ne tacimun wallahi in itace inji dalilin da bata biyani ba"
Kallona tayi "Nadiya ke kika ci?"
"Mom nidai bansaniba ko nashi naci ,na shiga kicin ina jin yunwa naga Abinci da yawa sai naga ansoya wani nama mai fulawa shine nacinye...." Kafun ta gama magana ya ɗaura hannu aka "shikenan momy ta kasheni "
"Dalla gafaracan baga namomi kala ² nan ba kaci wani mana" cikin fushi yace "ke tsohuwan nan kin dameni fa ,wayace maki inacin abincin ƙazaman can ,Ni a biyani abuna" saka hannu tayi cikin ɗan roban wanke hannu ta wanke hannunta ta saka a cikin plate ɗin swallow ,ta gutsura tuwon a hankali dayasha miyar ganye dasu stock fish da ganda,saida ta haɗiye sannan ta gyara murya "Ka zama bishiya ƙarukon tsayuwa tunda bazaka haƙuraba ,lamarine dai ba duka ba zunguri ,Ke ernan sa hannu muci abincin en aiki ,ƙila mu kamu da zawo duk mu mace nafika ƙaryan gwalangwalaso " murmushi nayi na wanke hannuna yanda naga tayi na saka hannu nima dukda banson tuwo a rayuwata amma lumshe ido nayi na haɗiye daƙyar kamar zan kuka "Hajiya tuwo akwai daɗi wallahi " sauri tayi ta ja naman gandan a bakinta ta fara taunawa tana mun magana "Habawa bazaki san na kwankwaɗi azaba ba sai na faɗa maki tunda naje ƙasar nan farau farau irin namu ban ga idonsa ba saidai wasu abinci da ina jin ƙamshinsa nike fara kuka,shiyasa ina zuwa tashan jirgi nayi waya nace a mun tuwo da kunun tamba " girgiza kai nayi kamar munafuka "Ayya Yi haƙuri Hajjaju ,inga dalilin da zaki koma ƙasar nan bayan gani babbar likita a gida" dafa kafaɗana tayi ,cikeda gamsuwa "Ahaaa Ashe dai kin gane ,wallahi duk kinfi banzayen likitocin nan sanin makaman aiki su saidai suzo duk safe da yamma sukewaye ka suna juya harshe mismismismis "
Dariya momy ta fashe dashi nikuwa na ɗaure fuska irin fuskar tausayawa ɗin nan
"Allah Hajiya wayyo kice sun daɗe suna saki cikin fargaba"
Zare hannunta a cikin roban tuwon tayi tana siɗe yatsu yanda zataji daɗin bada labari ,nima da tun loman farko ban kuma maida hannu ba da sauri na zare ina kallonta tana magana ina gyaɗa kai kamar da gaske ina gamsuwa da maganarta
"Wani fargaba In kinji fargaba ɗaya ne,wato ranar da aka kaini waje gari da safe ina farkawa daga barci sai na gansu farrrrrr da fararen kaya gashinsu a kwance har gadon baya,maza fa? Kuma sunyi takwas macen cikinsu kuma gashinta me ruwan ƙwai har mazaunai ,kinga da na daddage na runtuma salati ,na fashe da ihu wayyo Allah uwata! Sai suma suka danna a guje suka bar ɗakin wai na basu tsoro ,nikuma ina nan kwance na ɗauka Mala'ikun zare rai ne.
Ke wannan gari kar ala maimaita" dariya na fashe dashi har ina burgima a ƙasa ,Adams dayaga mun maisheshi drawing ba mai bi ta kansa tsaki yaja ya bar wajen ,sai kiran magriba muka watse
Bayan Hajiya ta ce ma momy ai ita taga ƙawa mai tayata hira ,in dawo bayan isha
Momy cikin gundura ta haɗe rai "Hajiya er makaranta ne zatayi karatu ki ƙyaleta haba !"
Waigawa tayi ta kalleni "wai haka ƙawa? "
Gyada mata kai nayi alaman abunda momy ta fada hakan ne
"Kinga er nema kinbi bayan uwaki ko? Shikenan Allah yayi Albarka "
"Kema gwara ki huta muje in tayaki ki kintsa ki wanka ki huta ki barcin gajiya" haka dai momy ta lallaɓata suka tafi sashensu Nikuma na tafi ɗakina
Bayan Isha'i momy ta kirani a waya ina ɗauka tace "Na kirane in fada maki dadynku yace mu shirya naxt week end zamu tafi Umrah Ni dake da Hajiya da Amra ,saboda murnan kinci jarabawanki ,kuma ya baki kyautar motan zuwa makaranta" ihu na saka na fito da gudu dagani sai bomshort da half vest Wai in je ɗakin momy tunda mu kaɗai ne a saman ,wato saman ɗakina yina kallon nata bangaren ,ta corridor ɗin matakalar benen da ɗaya zai kaika ɗakina ɗaya kuma zai kaika ɗakin momy nabi wai in tsallaka nata sashen waiyo abun elaaa ,kawai naji rigijif nayi karo da jikin mutum ,cikin dumly light blue ɗin dake wajen na ganshi tsaye da jallabiya da carbi alamu dai daga masallaci yike zaije suyi sallama saida safe da mamansa ,ƙashin ƙuguna ne ya bugu da belcony ɗin ,shikuma shayin gahwa ɗin dake hannunsa a take ya ambule a ƙasa ,yuuuuu nayi na sulale ƙasa saboda santsin tiles da ya haɗe da ruwan gahwan da tazube a wajen
Wani furgitaccen ƙara na dafe wajen natafi suuuu na fara gungure daga steps ɗin benen ina mulmulawa a matakalan benayen
Zaro ido yayi da gudu ya saki mug din da carbin yabi bayana shima nan santsi ta kwashesa ya tafi wurrrrrrrrr ......✍️
*Gidan daɗi,Littafin kuɗi ne ,regular 300₦ vip 500₦ special 1k katinmtn ta wannan Number 09065990265 ko ta nan bank