Showing 9001 words to 12000 words out of 46143 words
motar
"Hey Handsome"
Kallo ɗaya ya mata ya kunna motar Ba tareda ya cemata komai ba ,jin still tama tsaye yasa ya miƙa kyakyawar hannunsa daya lulluɓe da kwantarcen gashi zai kullo ƙofar motar da ta kakare da jikinta
"Hello ??!" Ta sake Kiran attention ɗin sa ba tareda ta jirga a ƙofarba
A hankali ya ɗaga fararen idonsa ya watsa a cikin fitsararrun Idanuwarta ,ji tayi kamar an mata flashing ɗin haske da sauri ta cire idonta a hankali ta saci kallon ƙawayenta da suke tsaitsaye suna jiran ganin ƙwaƙwam, cikin dakiya ta gyara murya "Mr. Adams seems like you couldn't recognize me? Kamar baka wayeni ba yanda ka nuna mun a zahiri "
"Yes and leave" (Eh kuma ki tafi)
Wasge baki tayi kamar ya fada mata abun da zai sata dariya ta waiga ta kalli ƙawayenta "Oh really? Laifina ne I'm kausar a very person that you call...." Gabaɗaya fuskarsa ne ya yamutse saboda yanda ya gaji da jin ƙamshin turarenta shi sai yanzune ma ya gane wacce ita gaskiya filter shegen abune wato da ya ganta a zahiri ba a hoto ba duk sai yaji ya bawa kansa kunya
"Are You dull? I said leavvvvvveee" ya danna mata wani tsawa da saida ta cirga da sauri tsawansa na mata amsa kuwwa a kunne ,a take ƙawayenta suka maimaita "Dull? Oh wow!" Cikin izgilanci suka juya suna ƙunshe dariya
Itakuma kafin tayi wani motsi har ƙofar ta rufe kanta da kanta
Saida ya huta na mintoci yina saisaita kansa ,Duk Ƙarfin gudun A.Cn dake motar bai hana ma Aorta ɗinsa zama stiff ba ,jinin jikinsa ya fara gangara beyond normal a take yaji zufa na tsatsafo masa numfashinsa na sama da ƙasa yina laluben numfashin tamkar Asthmaticus .
Ya daɗe yina ƙoƙarin saita temper ɗin sa kafin yabar wajen yina kallon agogon motar ƙarfe 11am ,sannan ya lura da tarin kiran da akayi masa wanda duk na mutanen da zai meeting dasune Sai ƙarshe yaga text message na yawo akan screen ɗin wayarsa
"We held up the meeting,to make you comfortable Sir!"
Tsaki yaja ya daki sitiyarin motarsa
"Oh shitt!"
"Jibi yanda yaran nan suka ɓata mun budget,Inji dalilin da bazan ɓatawa yarinyar nan raiba"
[6/25, 11:51] 😘😘😘: 18
Nadiya tana fitowa daga Exams ta kira waya "Mom na gama exams ko a turo driver yazo ya ɗaukeni yau ko a turo mun da kuɗin jirgi in dawo gida yau ,don na gaji da gida tareda wancan fitinannen halittan"
A sanyaye tace ki bari sai zuwa gobe mana kar Excellency taji ba daɗi "Mom No! Gskiya nayi kewar gida in Ni bakiyi kewata ba nayi kewar abincin Anty Nusaiba "
"Au saboda Abincin Nusaiba zaki dawo? To aikuwa ki zamanki saboda ta ma fara aiki a hospital abunta kinga babu ke ba cin girki"
"Haba momy..Haba" Nusaiba da ke zaune tana yin care plan ɗin patient ɗin ta ,gyara takardun tayi ta fuskanci momyn dake kishingiɗe akan 3seater "Momy ki barta ta dawo mana ai tayi ƙoƙari wlh "
Lumshe ido tayi tace "Antynki ta roƙar maki zan turo maki yanzu " ihu tayi ta daka tsalle "Godiya nike babbar yaya"
"Ni karki fasa mun kunne sai na jiki"
"Okooo "
"Shikenan ko?" Kumburo baki tayi ,tai ƙwalƙwal kamar zatayi kuka "Momyyy"
Menene kuma?"
"Momy kin daina sona "
"Ohyeah sorry ,na manta ne safe trip I love you"
"I Love you More durling" ta kashe wayar cikin tsantsan fara'a ,waigawar da zatayi sukayi two eyes da Abul-hassan "Idonki kenan ko Nadiya ? Inta kira naki ɗaga mun wayata ko?"
"Shikenan ba kira a wayaba gani ka ganni me zaka bani"
"Me kikeso"
"Muje ka yankan mun ticket zan tafi Abj yau" shiru yayi yina kallon tattausan laɓɓanta dasuke matuƙar jan hankalin sa a koda yaushe ,hure masa ido da iskan bakinta tayi sannan ta kira sunansa ,firgigit yayi kamar wanda ya tashi a barci "Me kake kallone haka"
"Kyau" ya bata amsa a taƙaice "kyau kuma ? A wajen wa? A wajenki ,nadiya bazan ɓoye maki ba tun ranar da muka haɗu dake sonki ya tafi da imanin tunanina,shagwabarki ya tsayu ƙyam a cikin zuciyata ,lukutin jikinki inna tuna sai inji na zama susutacce , kullum ji nake kamar in lumshe Ido In ganki a cikin jikina ni kuma zan bashi ma'adani na musamman ,ke bazan tsaya a hakan ba sai na ƙara da sunantan kyawawan laɓɓanki jajaye kamar kunnen fure ...." Ƙyar ta masa da ido bata ko ƙyaftawa , tun da Nadiya take gabaɗaya rayuwarta wasane ,bata taɓa tunanin tsayawa tai tunani mai kyau ba sai yau ,a ranta ƙissimawa take kenan wannan mutumin kwartone ,nima so yike mu lalace dashi irin yanda su kausar keyi ...god forbid
"Ya naji kinyi shiru"
Ajiyar numfashi tayi "Naji larabcin naka ne ya girmi ƙwaƙwalwa ta dadai so samu ne ai mun dalla dalla zanfi ganewa "
"Haba ban gane ba ke fa babbar kaice duk yarinyar da za'a kawo ta University ta kuma iya zama a Hostel ai tasan komai so yanzu abinda nikeso dake ki ɗaga tafiya abujan nan yau ,sai in kama mana hotel mu kwana mu jiyarda juna daɗinmu kinga a gida zasu ɗauka kina Hostel ne ,ƴan Hostel ƙawayenki kuma zasu ɗauka kina gida ne" galala tayi kamar wawiya ta ɗaura hannuwanta akan cikinta ta riƙe su
"Hakan kake so ayi? To Shikenan zanje in jira ka a Hostel " godiya ya mata suka rabu har ya ƙule tana kallonsa tana tafiya har tana buga tuntuɓe kamar zata faɗi
Soma tuhumar kanta tayi da rashin kamun kai har yaba namiji damar tuntuɓarta da aikata zina
A Hostel zama tayi tai shiru akan gado ,tanata tunani ta dafa noodles Amma ta kasa ci ,Ummu sosai ta gane akwai abunda ke damunta
"Nadiya lafiya kike?"
Tsaki taja batace mata komai ba ta haye gado tabar abincin anan wajen ta kama barci kasantuwar tana fashin sallah saida takai magrib saidai shan ruwa yasata ta miƙe,sam cikinta ya cushe amma tabbas bazata koma Abuja ba sai tayi clearing doubt ɗin Abul-hassan akanta Amma how?
Bayan magrib
Duk ƴan ɗakin sun furfita saura Nadiya da take kwance a gado tana waya da su Anty Nusaiba ,sai kuwa Ummu dake kan praying mat tana en Addu'oin ta
Wata kiran ne ya ringa shigo mata waya ,ba'a duba tana waya ,tsaki taja ta hau bala'i "wai wani mahaukacin ne kamar bayajin mutane suna waya zai ringa damunmu da kira ?" Tana kashe wayar Abul-hassan ya sake kira ,ɗauka tayi ta kanga a kunne tayi shiru ba tareda tayi masa magana ba
"Babe nakirane in tambayeki a'ina zan kama mana hotel ɗin? "
"A'inda shugaban ƙasar ku in yazo nan yike sauka kuma a Vip nakeso ,irin ɗakin da manyan mutane kamar Ni zasu wataya ina maƙotaka da gomnoni da shuwagabannin ƙasa "
"Bakida matsala aike daƙwalwace konawa namiji ya kashe a kanki bai asara ba,A'ina zamu haɗu ko Ni zan zo in ɗauke ki?"
"Ni ,kai kana ina?"
"Ina wuraren new low cost"
"Ok ai akwai joint ɗin chicken a wajen ko? "
"Sosai ma"
"Yawwa mu haɗu a wajen zanzo a nappep sai ka siyamun abinci inci tukun don wallahi yunwa nikeji bazanjira sai munje hotel ba "
"Shikenan I'm be waiting "
Kashe wayar tayi ta kalli Ummu "ummulkulthum in roƙeki alfarma"
"Menene?"
"Inaso ki rakani chicken joint anan new low cost ,wani saurayina ne Abul-hassan yakeson wai in kwana a wajensa a hotel so ,zan shiga ciki muyi siyayya sai ki tsaya da me keke nikuma kina ganin na fito ki sa me keke ya tada keken mu gudo da kazan kinji "
"Kina ganin ba matsala a'ah nadiya na rabaki da mazan zamanin nan"
Ke ba matsala inshaalh ,ai Nurse anaesthesia ne so munsan identity nasa
Tashi sukayi suka saka dogayen jilbab ɗin su har ƙasa suka feffesa turare suka fice daga su sai 1k a hannunsu suka tsaida me keke sukayi hayanshi.
Yina zuwa joint ya zauna a motarsa yina jiran isowarsu har aka kira sallar isha ,kafin ya shiga Masallacin wajen,isu Nady suna isa Ummu ta juya ta ɗayan titin itakuma ta tsaya a park ɗin tana laluben inda zata hangosa,a hankali ta ɗauki waya ta kirasa,nan yike shaida mata yashiga mosque Amma yanzu zai fito ,Hmm kawai tace ta koma wajen Ummu a keke ,ummu dake shafa wayarta ta rage kaɗaici ganin ta shigo keken yasa tace "Ke halan ƙarya ya maki" girgiza mata kai tayi "yina sallah ne" ,can kuwa sai gashi ya kirata aiko ta hangosa a ɗayan tsallaken titin ,tafiyarta ne gabaɗaya taji ya sauya har ta ƙarasa wajensa ,yina ganinta ya washe mata baki ya miƙo mata hannu wai ya riƙe ta su shiga ,noƙe hannunta tayi kana ta hau masifa "club zamu shiga ne da sai ka riƙe mun hannu? Akan titi fa muke" haƙuri ya bata cikin lallami,suna shiga ya zauna yace taje tayi order ,aikuwa ta wuce da sauri
"Hello,me kuke dashi?"
Nan suka bata list din abubuwan da suke dashi
"A bani fried rice with chicken, chips with chicken,a bani Energy drink guda biyu....waigawa tayi ta kalli inda yike zaune ,nayi ordern da kaine?"
"No zanci tuwo a hotel din"
"Shikenan a haɗo da Ice cream babban roba"
Haɗo komai da na buƙata akayi sannan ,aka bashi bill ɗin ,ya miƙa Atm card a cire
Kafin a kawo mana ne ya kalleni "wancan keken kuwa ba tareda yarinyar ciki kuke ba? na ga ,ɗazu kin fito a keken kuma har yanzu basu tafi fiba"
Caɓe baki tayi ta bashi amsa a taƙaice da "Nop"
Miƙewa yayi ya ɗauki wayarsa kamar zaiyi kira ya fita yazo gaban keken yinason yayi magana da Ummu amma tasha kunu ,dole ya koma ya zauna aka kawo order da receipt ɗin payment ɗin ledoji uku ,miƙewa yayi cikeda taƙama a dole bazai ɗauki leda ba ,nikuwa na amshe ,na tunkari ƙofa tim tim tim da kaya a hannuna na ɗaure fuska kamar hadari
Ko kallon hanyar motarsa banyi ba na tsallaka titi .
Ummu na ganin nadiya ta fito da kaya niƙi ² hannu tace me keke tada keke tana shigowa mu tafi ?"
"Ko me yasa malam kayi mana kar wancan mutumin ya tsallako shima" me keke kunna keken yayi ,aikuwa ina tsallakowa shima ya biyoni ina shiga back seat ya zauna a gaban driver ,ya riƙe ƙarfen
"Nadiya ya dai ,kizo mu tafi "
Miƙawa Ummu ledojin nayi ,sannan na kalli direban keke "Malam muje "
"Kar ka fara ka tafi nariga da na ɗauki hoton plate number Dinka kana tafiya zan kamaka "
Me keke ja yayi ya tsaya a ɗan tsorace
Haɗe baki Ummu da nadiya sukayi wajen ce ma me keke "Malam mu tafi mukace ko shi ya daukeka?"
"Amma kika ce baki santa ba" banza tayi masa kamar batasan da ita yike magana ba ,ta ɗaure fuska kamar bata taɓa sanin inda ake dariya ba
"Ok kai mai keke muje ka kaini dasu inda nike so" ma'ana zai tafi da dukkanmu hotel ɗin ne ko ya yi ke nufi oho
Nadiya nuna ma me keke kwanan roundAbout tayi da zai iya kaika har hotel ɗin da yike magana "ok bi ta nan ne" ummu ta ciro wayarta "yawwa mai keke kaimu barikin sojojin dake can gaba ,zaka sani ne ...." Nadiya cikin shouting tace "Yawwa Kiramun lafazi ummu kira lafazi a wayanki ,kice masa gamunan kawo masa aiki" aikuwa muka fara harhaɗa numbobi kamar zamu kira waya
Dakawa mai keke tsawa yayi "malam tsaya nace" dasaueri muka haɗa baki "malam karka tsaya muje"
"Ka tsaya zan fa kamaka" nadiya kallonsa tayi "to ai gashi a gefenka kamashi mana dallah me keke muje" me keke ya cigaba da tafiyarsa
Ganin an kusa isa barikin sojoji yasashi cewa "Me keke nace ka tsaya in sauka ko? Wallahi in na fita naji ciwo saina ɗaureka " ba wanda ya kuma tankasa ,kawai sai ji kake ƙuuuuu ya kama ƙarfen keken ya dirka a tsakiyar kwalta me keke yajashi ƙuuuuu takalminasa haka yike ƙuzan kwalta kafin ya saki ƙarfen sai gashi rimmm ya kimu a tsakiyar kwalta ,daga ² me keken yayi zai faka a gefen hanya ganin mutane sun taso kawo ɗauki ,still ce masa mukayi "Me keke yi tafiyarka " aikuwa me keke yaci taya mukuwa muka fashe da dariya ,kwaikwayar maganarsa na kamayi "moo keke zan kwamaka zan kwamaka fhahh ka tsaya in sauka in ka bari ma sauka naji ciwo zaka sani......rimmmm mugunka a ƙasa " sai ƙyalƙyal ƙyal duk muka fashe da dariya har me keken "waik nidai Yau naga comedyn da ya sani dariya sosai"
Zaro roban ice cream ɗinmu mukayi muka kama sha ,sannan mukace ya kaimu hanyar makaranta ,wani mai motane yazo da gudu ya ma direban kekenmu thumb up "Mun gode da ka riɓar da shege Allah ya saka da Alkhairi" fashewa da dariya muka sake yi
Wato su mutane sun ɗauka Abul hassan yina cikin ma'aikatane masu saka mofty ba kayan aiki ba ,suna tsayawa a gefen titi suna kama masu abun hawa unknowingly, suna kaisu office ana cajansu kuɗi shine da ya shige gaban keken me keken ya wurgoshi ƙasa ,basu san Gaye ne me ji da kyau da kuɗi ba,Infact a nurse him self.
Dariya muka daɗa fashewa dashi kafin me keken yace wai me ya farune baku sanshi bane?"
"Saurayi nane ,shine fa wai me keke don yaga kamar kaina yina rawa zai ce zai kama mun hotel mu kwana ,muje muyi iskanci ,shine nace muje mu ci abinci in ya siya na huce haushin takaicin da ya dasa mun ,yanzu kaga sai yaje gida in yinada mata ta gasa masa kwankwaso kafin yayi tsami "
Dariya ya fashe dashi ammafa kun yi maganinsa wallahi kun bashi tsoro gayen ya furgita "mtseww I know now" Nadiya ta Dan ɓata rai ,ta kalli Ummu "ke had it been muka kai wajen sojojin bai faɗo ba ya gudu ya zamuyi da ƙaryan mu ta ƙare fa kenan ko?"
"Kai sojoji na tausayin mata zuwa zanyi in shaida masu wannan yina nemanmu da iskanci ga abun da ya faru shine muka ce a kawo mu nan ,kiga Ni yanda za'a ci ubansa "
Dariya me keken yayi "shima yasan Gwale ²n sojoji me shiyasa ya gummace ya faɗo a tsakiyar titi da a kaishi barrack"
Muna zuwa bakin gate din makaranta muka tsaya muka miƙa ma me keken 1k ,malam bamu da canji ya za ayi?"
"Nima ko Banda canji duk tafiyar nan da zaman jiranku da nayi ai na ci dubun ko? Kuma da a sama yanzun nan kuka ciyo dubanni ?" Fita nayi na shiga shagon provision na rokesu suka raba mun biyu 500_500# ,na miƙa masa ɗari biyar ɗin
"Malam kayi haƙuri da wannan wallahi ko ficika bamu maganinsa in muka baka duka " karɓa yayi ya wuce muka masa godiya muma muka nufi Hostel
Oum Aphnan✍️
09065990265
[6/25, 12:53] 😘😘😘: 19
A ɗaki muka ajiye muka fara fiddo energy drink zamu sha ,saboda yanda maƙoshinmu ya bushe ,kafin na kalli ummulkulthum "Ummu I felt so guilty about this event wallahi,inajin kamar laifi nane da kaina ke rawa shiyasa har maza suka fara testing interest ɗin su akan ko muje muyi iskanci" yanda Ummu taga naci serious yasa ta ƙara firing ɗina Bata sani ba ko sanadiyyar hakan yasa in ɗauki wasu ɗabi'un masu kyau in implementing a halayya na
"Haka ne wallahi in ba don ya lura kamar ke ɗin banza bace Ni ya kalleni da taɗin iskancin mana?"
Zaro ido nayi "ko? Ummu to ya zanyi? Gaskiya raina ya ɓaci ,zata sake magana kenan Zayd saurayin Ummulkulthum ya kirata a waya ,tasha mamaki da taga numbersa na nan Nigeria saboda yina cairo acan yike karatu "Hello sweet"
"Hey Huort gani a parking lot ɗin gaban Hostel ɗinku"
Miƙewa tsaye tayi ta ƙwalla ƙara kamar wacce ta ƙone ,da sauri Nadiya ta miƙe "ke lafiyanki kuwa?" Kobi ta kaina batayi ba ,ta zarce da tambayarsa "Sweet are you serious?"
Dariya yayi yina shafa ƙasumbarsa da ya tara "fito ki ganin ma idonki zaki hudan tympanic membrane ki kuma tsorata roomies ɗinki"
"Oh murna ne sweet ,ganinan zuwa"
Kallona tayi ,shirya ki rakani wajen sweet ,Ni da na zabga tagumi ina kallonta ina jin haushin kaina yanda kowa ke nan nan da saurayinsa amma Ni Ko nayi saurayin sai mun tsiyace "kina jina Nady" ajiyar numfashi nayi "wa'as sweet ? Ba saurayinki bane ? Gaskiya bazani ba"
"Taf harma kin isa wallahi kullum ina basa labarinki a waya ko In muna cht yanzu yazo ƙasar nan kice bazaki zo ki gaisa ba ,wallahi bazata saɓu ba ,murmushi nayi na maida jilbab ɗina itakam saida ta zaro rantsatsen abaya sabo ,ta saka da takalminta mai kyau tayi rolling veil baƙi mai girma ya rufe mata kewayen fuskarta zuwa kafaɗa duka kamar ta saka hijabi ,ta manna wrist watch na Rolex ,sannan ta feshe turare har ta cikin jeans din cikin jallabiyarta kallonta na dinga yi saida na ga ta lalubo powder zata saka kana na katseta
"Haba Kulthum dare ne fa ,kin saka bakar Abaya ki kai masa sauro mota ,ga wani makeup tamkar ba nan da wajen Hostel zakiba ,gaskiya abun yayi yawa" gwatsaleta tayi da cewa
"A'a wallahi ke dabam sauran matan da sukeson su ƙulla alaƙa da samarinsu yanda sukeyi suma dabam ,Ni auran Ya Zayd zanyi Dole in ringa masa gayu ta yanda zan makantar da idonsa daga ganin kowata kalar mace ,in kashe hancinsa da sirrin kamshina ta yanda ba wani turare da zai masa tasiri a zuciya ,in masa Daɗaɗan kalamai masu kwantar da hankali ta yanda bazan bari kalmomin wata mace suyi tasiri a kunnensa ba,sauran cikon biyu zuwa ukun kuma sai naje ɗakinsa
Cikin zaƙuwan son ji nace "Su kuma meye sauran cikon "
Shafa lips balm a baki tayi tana ɗan haɗe laɓɓanta akan mirror "to tunda kin matsa kiji ,zan kasance mai tsafta ke irin tsaftar nan da ake kira ƙalƙal ,tsinke bazan taɓa bari ya samu muhalli a gidana ba bare idonsa ya gane masa aibuna ,girki kuwa nasan wannan ƙwararriyace Ni a fannin amma tabbas sai na shiga catering school Wanda zasu koya mun samfarin abinciccika na larabawa dana turawa ,tunda kinga shiɗin a cikinsu yake ,sai na karshe.....kawai sai ta fashe da dariya ta saka takalminta
Miƙewa nayi "Fada mana