Showing 24001 words to 27000 words out of 46143 words

Chapter 9 - Gidan Dadi Book 2 End Complete

01 Sep 2025

8642

wani duniya yina begen matarsa ,malaminsu ban takardan sallamata Inyi gaba"


Kauda fuska yayi yinajin wani kishi na shaƙosa ,amma ya kanne kawai ya basar ,ya cigaba da danna wayarsa kamar baisan da wata halitta ba a zaune
Sun kwashe kusan 10minutse kafin haƙurin nadiya ya fara ƙarewa
"Malam Inada abubuwa masu muhimmanci da nikeso Inyi kana ɓata mun lokaci " waigowa yayi yina kallonta ta ƙarƙashin ido kamar mejin barci ,saida ya hargitsa gashin kansa kafin ya aje numfashi a hankali "Me ma kikace kina so?"
Zuciya ne taji ya kawo mata wuya amma ta kanne saboda momy tace ta lallaɓashi
"Divorce"
"No faɗa mun da Hausa"
"Ok yau bakajin turanci ko? Takardan saki nikeso" murmushi yayi silently sannan ya kai hannunsa saman kafaɗarta dasauri ta goce sannan ta tattare giran sama da ƙasa "wai meye haka? Fyaɗe zakayi mun" Ta fada da hargagi "Ayya driver na baya jin Yaren da kikeyi ,and motar is sealed and tinted ba Wanda zai jiyo noisy behavior of yours so mind your self plz Kar ki triggering ɗina into negative action yanzu yanzun nan"


Tsaki taja cikeda tsiwa amma ƙasan zuciyarta gabanta ne yike faɗuwa


"Mai kikace ma kina so?"
Banza tayi masa
"Driver kaini hotel ɗin da na sauka" aikuwa take driver ya fara ma motarsa key ,sauran ma ganin an tada motar Adams suma suka tashi motarsu


Ƙara ta saki "Noooooo ka saukeni mana" banza yayi mata ya koma ya lumshe ido yina sauraran kukanta kamar ihu ,kiciniyar ɓalle ƙofar takeyi ammma gim gim kaman dutse saboda securityn ƙofar ,waigawa tayi taga har sun fita titi sun fara gudu ,jinjigasa ta fara yi


"Wallahi gwara ka sa a buɗe Ni in ba haka ba duk inda mukaje saina kunyata ka nasa maka ihun ɓarawo zance satoni kayi "
Cike da gadara yace "Zaki iya ,kinada rashin mutunci shiyasa naba en jarida damar yayata hotunan mu da auren mu yanzu ba labarin da yake raining a ƙasar nan irin labarin auren matashi mai zamani da Troublesome wife ɗin sa (ya ƙare yina tallafo mata haɓarta ,idonsu ya shiga cikin na juna ) Kije kiyi ƙaryataki kawai za ayi "


Kufce fuskarta tayi akan hannunsa ta buga kanta a wajen glass ɗin motar kamar mahaukaciya ta fashe da ihu


Sa tafin hannunsa da ya gauraye da ƙamshin gyaran jikinta da tasha yayi a kan hancinsa sannan yaja numfashi mai kyau yinajin wani sanyi a ransa
"Wai auren ƙiyayya ma haka yike da daɗi ? Ka taɓa mace kaji ƙamshinta duk sanda kaso ina ga auren soyayya,wow!" Shiru tayi duk da kukan da tayi tana kallon sa kafin taja wani mugun tsaki ,da sauri kuwa ya rungumota ya manna ma saman leɓenta da ta cunosa saboda tsaki sumba ,fincike bakinta da jikinta tayi a jikinsa


Gyara zaman sa yayi yina ɗan ƙanƙame jikinsa kamar wanda yike cikin shauƙi sannan ya ƙara cewa "But wow! "
Da ta rasa me zatayi kawai sai ta shiga tsiyayar da hawayen asara.


Paradise Hotel suka shiga har upper floor motocinsa suka haura dasu zuwa cikin filin ajiyar motocin ɗakunan saman ,kallonta yayi sannan ya kalli wajen ɗakunan da suke a jere


"Ma'am cry cry mun kawo"
[7/2, 23:56] 😘😘😘: 29
Banza tayi masa da ya lura tabbas bazata magantu ba kawai sai yayi ficewarsa ta side ɗinsa ,guide dake tsaye ,riƙe da ƙofar ɓangaren ta taƙi fitowa sai jijjiga jiki take saboda masifa ,kewayawa yayi batai auneba taji ya na neman ɗagata ,rirriƙe kujeran tayi tana ihu ,sukuma guides ɗin sai riƙe dariya suke
"Kasan Allah ko na saki jiki na baka iya ɗagani ,ko wancan karon Albarkacin rashin lafiya ne" banza yayi mata ua daddage ya finciketa cak sai gata a saman hannunsa ƙafafuwan ta na walainiya a sama ,gaban ƙofar ɗakin ya tsaya ya buɗe da kansa ya shiga akan kujera ya direta
Zabura tayi zata danna da gudu tana numfarfashi kamar itace ta ɗauki kanta shi kuwa kamar bai ɗauki wani abuba haka yikeji ,ƙyaleta yayi taje tana jijjiga ƙofar amma a datse ganin hakan ta sulale ta zauna a wajen sai hawaye
Tsaki yaja "A lallai hawayenki zasu ƙare a banza tun baa zo wajen kukan ba " wuce ta yayi yaje ya yi wanka ya fito dagashi sai towel ɗaure a kwankwaso yina goge fuskarsa da ƙarami ,gurin mirror ya tsaya yina kallon kansa ,yina kuma hangota still tana kife a wajen har ta fara gyangyaɗi saboda ita kanta rikicin ta gaji dashi ,ƙyar yayi mata da ido yina mamakin ikon Allah baizo Abuja da nufin aureba amma jishi da matarsa ,lallai aure da mutuwa lokacine inji malam bahaushe .
Fesa tulare yayi a hankali ya ajiye kwalbar akan mirror ƙamshin turaren ya farkar da ita karaf tayi kwalli dashi tsaye dagashi sai towel ,wani zimmmm taji a ranta saidai kafin ta cire idonsa a kanta cikin mugun kunya har yayi zaraf ya faɗa ta da ƙyar da hantara "ke dalla can baƙauyiya meye kuma abun kallo a jikina ?"
Cire idonta tayi da sauri ta kalli gefe ,nadiya baki bayi mutuwa da sauri ta rama "me zan kalla jiki duk a bubbuɗe kamar ɗan dambe" jinjina damtsen hannunsa yayi
"Lallai yarinyar nan ke er sa idone ,ina nan gayenka sai yabon halittana ake? Karki damu sai kinyi aiki tuƙuri kafin wannan Hot gayen ya zama mallakin ki"
Tsaki taja
"Abin amai wai zuciya taƙi tashi ,Ni in ka gama shakaran rashin kirkin naka kazo ka bani takardan sakin ka kuma sa a maidani gidan Biki Munada lunching by 3pm" taɓe baki yayi "au ke kina tunanin wai Inyi asaran sadakina saboda kuɗi yayi mun yawa?"
Ya faɗa yina saka boxy da singlet
A yanda take idonta a rufe tace "da wani ya aikeka asaran ?"
"Ok ke bakin rashin kunyarka bazai mutu ba ko? To in kin shirya karɓan takardanki kyamun magana ya juya zai haura kan bed ,wangale Ido tayi sai kuma tai sauri ta rufe ganin yanda yike "To malam karka iskantani mana ,bakada kayane? Ka sa kayanka mana"
Kwanciyar ruf da ciki yayi ya karkashe wayoyinsa ya jawo laptop ɗin sa ya fara video call ɗin sa da wata Balarabiyar kuwait data liƙe masa ,hiransa yikeyi kamar ma ya manta da halittarta a wajen sai dariyarsa yikeyi ya lulluɓe rabin jikinsa da bargo amma time to time yina kallonta ta wutsiyar ido yaga wani reaction zatayi ,Nadiya dukda batason Adams yanda ya barta tana mulmule a ƙasa shi kuma hankalinsa kwance yike hiransa da wata ya ƙona mata rai ,wannan dalilin yasa ta miƙe ta masa waras da Idanuwarta a kansa "Malam sallame Ni mana ,anafa jirana " ji tayi muryarta yayi rauni ƙiris ya rage ta fashe da ihu


"Ke nifa karki matsamun ,biyan sadakina ki gaba "
"Nawa ne kudinka in biyaka Ni ka sallame ni"
Kashe laptop ɗin yayi ya gyara zama "Sadakinki sadakarki aka bani bako sisin kobo ta ,saidai na ba da tsohin miliyon guda ,maroƙa na basu kyautan motoci guda Ashirin nayi kyautar kujerun hajji Bansan adadi ba yanzu gaskiya amma kya iya tuntuɓen PA ɗina sai yayi maki bayani ,sannan gashi en jaridu sun fitar min da tsadaddun hotuna na kowa ya gani suma a kasuwa suke sai kin biyani"
Rau rau tayi da ido kamar zata saka ihu "Gaskiya banda ko 1million a Account ɗina ,to wa ma zai bani? ,Kawai dai in zaka Barni in tafi ka barni kaga za ayi ta kirana wayar na barota a mota"
"Su wa zasu kiraki? Ba wanda zai kiraki bayan ansan kina tare da mijinki ,don haka munanan tare dake mugani zuwa nan da kwana goma ...kinzo da kaya kuwa? Oh ba matsala za'a sayo mako lefe ma" zaro masa ido tayi ,da sauri ya dafe baki "Ai mijin aro ne fa ,yanzu dai zaɓi naki,inma ki biyani sadaki na in rubuta maki saki ko kuma ki hauro gadon nan ki mun tausa ,in buɗe maki ƙofa a maidake gida ,ko kuma mu kwana goma a nan wanne kika zaɓa ?"
Hawaye ta fara sharararwa na nadama "banson duk zaɓinka kawai ka barni inje wajen masoyina ,nasan zuwa yanzu duk ya damu ,Ni banda wayar da za muyi hira bare yaji sanyi kamar yanda kai gashi kuma chating da taka budurwan" A take annurin Fuskarsa ya gushe jin ta ambaci sunan saurayinta ,da sauri ya shige bargo ya rufe ido yina son saisaita kansa ,Ya Ilahi wai menene haka ne?


Zama tayi ita a kan stool sai tufka take da warwara a haka har aka kira sallar la'asar ya shiga yayi Alwalarsa yazo zai wuce ta ta kuwa zabura zata fita ,sai ya fasa fita yayi sallarsa a ɗaki ,ya koma ya kwanta "kina iya yin Sallah ko da kafura nike zaune?" Banza tayi dashi ,don haka shima ya ja bargo ya kama barcinsa ,bai farka ba sai 6.15pm lokacin nadiya ta gama galabaita da yunwa duk ruwa da lemun da ya ajiye kusan hudu ta shanye ,wanka ya sake shigayi ya barta a zaune ya ɗauro Alwala ,yina fitowa taga yina ɗiga da ruwa mamakine ya isheta ganin zuwansu yayi wanka na biyu ,cikin tsiwa tace "Yau ga dangin kwaɗi" shareta yayi ya tinkari ƙofa zaije sallar magriba dasauri tabi bayansa ya kama handle zai buɗe itama takai hannu
Jikinsa ne ya kama rawa "Karki taɓa Ni ,nayi Alwala" cak ta tsaida hannunta cikin mamaki ,to ita ɗin najasa ne da har yike buɗe murya haka duk saboda hannunta zai gogi jikinsa ?
Tana kallo ya fice kafin takai sawayenta wajen har ƙofar ya kulle ,bai dawo ba sai bayan Isha'i lokacin ta dangana tasan tabbas bazai kaita gidaba dole taje Toilet itama tayi wanka saboda kar ya rainata ,ta ɗauro Alwala ta shimfida praying mat ta fara jero Sallah amma yunwa tasa a zaune ta ƙarasa ,tana rakaar ƙarshe ya shigo bayansa ma'aikatan hotel ɗin ne sun kawo masu abinci wanda duk swallow ne sai chocolate tea rabi rabin kofi ,ji tayi kamar ta tsinke sallar ta fita da gudu kafin ya sallami mutunin ,kafin ta gama yanke hukuncin ya kullo ƙofar ya dawo ya zauna yina kallonta ta idar da sallah ta zauna akan darduman ta rafka tagumi ga kayan jikinta sun jiƙe saboda Batada kayan sauyawa ,ji tayi duniyar tayi mata ƙunci


Fridge ya buɗe ya kwaso snacks da dambun nama yaci sosai ya koma ya zauna yina chatting a system yina sipping drinks
Kenan shi abincin hotel dinma baya ci saboda ƙyanƙyani


Ƙasa daurewa tayi ,saboda ta fara rawan sanyi "Don Allah ka bani kayan da zan sauya kayan jikina sun jiƙe"
"Alwala ne kika jiƙa kaya kamar yarinya to Banda kayan mata ko kinga nan yayi maki kama da boutique" rausayar da murya tayi cikin neman agaji
"Wayyo wanka nayi wallahi sanyi na damuna zanyi ciwo "
Miƙewa yayi ya fiddo wata Jallabiyarsa ya miƙa mata ,tsayawa tayi tana juyawa a ranta ,taya zata fara saka kayan maza ? Zube mata kayan yayi akan gado "Idan kin gama ga abinci can ina fara barci by 9 bana farkawa sai 2.30am don haka sauri minti 23 in barci ki gaggawar gama abinda zakiyi kafin nan"


Ɗaukar kayan tayi ta wuce toilet ta saka ta fito ,tana buɗo ƙofa ya hango soson sa ba inda ya ajiye ba zato ido yayi "Ke da wani soso kikayi wanka?"
"Na ciki " ta bashi amsa kai tsaye jikinta na rawa saboda yunwa taje ta shiga buɗe kwanukan turus tayi ganin tuwon samo miyan ugu ,sai chocolate tea ,hawayene ya gangaro mata
Adams dake tsaye a kanta riƙe ƙugu yayi "miƙa kije da kanki ki jefa soson a bin,ya tashi aiki,sannan daga yau karki sake taɓa mun abu in baki tambaya ba"


A sanyaye ta girgiza kai ta ɗaga kai ta ƙwalƙwale tea ɗin rabin kofi da ta gani a cikin tray ɗin ba tareda ta tamka masa ba
"Ba dake nike magana ba?"
"Ka bari in gama cin abincin horon da kasa a kawo mun ai" banza yayi mata shima ,a galabaice
ta miƙe saboda yunwa ,gashi batacin tuwon akwai ƙulalliyar gaba tsakaninta da tuwo ,kallonta yayi ya ƙunshe dariya yinajin ya rama naman shi da ta cinye masa ranar da hajajju ta dawo daga cairo ,Kamar yanda ya umurce ta haka take ta jefa soson a waste bin,ta koma .
,zama tayi akan kujera tana jero hamma hawayen jin barci na zubo mata a ido ,kallon resting chair me kamada courtch yayi "Oya je can ki kwanta lokacin barcina yayi "
Cikin Muryar tausayawa tace bazani gidanba ?" Ɗif wutan ɗakin ya mutu gabaɗaya ,miƙewa tayi da lalube kamar tsohuwa taje ta haye kan banƙararriyar sofan mara daɗi irin na turawa ,haka ta kwanta ,tana ta tunanin mafita ,ko ta yaya zata kwana ɗaki ɗaya da namiji fitila a kashe ? Wani hali iyayenta suke ciki ne?" Da wainan tunanukan har barci ɓarawo ya kwasheta


Cikin barci garin juyi ta danƙaro ƙasa sai ji kake tum !! Ta faɗo ta kuwa yanka ihu ita ta ma manta a ina ta kwana,duk zatonta akan gadonta take "wayyo Anty Nusaiba ki kunna fitila wai ina kike?"


Gyaran murya yayi sannan ya kunna dummy lamp ɗin gefen gadon mutum ta hango kwance akan gado ko motsi baiyiba saboda rashin imani bare aje ga tunanin wai ko zai taso ya ɗagata
Daƙyar ta miƙe ta koma ta zauna akan sofa ɗin saboda barcin ma ya gudu sai zullumi take da tunanin wai yaushene zata bar wannan wajen ?


Wannan shi ake ce ma tsalle ɗaya ake a faɗa rijiya amma sai akayi yunkuri dubu baka fitaba ,da ace bata biyoshi ba ai bazai ɗaukota ta ƙarfi ya kawo ta nan ba to rashin kunyarta ya ja mata


A gida fa ko suna en wanne???
[7/3, 19:51] 😘😘😘: 30
Adams saboda rainin wayo Dadyn nadiya ya kira wai sun wuce da nadiya ,saboda tanada exams Next week ta daɗe a Abj
Murmushi yayi irin tasu na manya a tunaninsa ko zumuɗin amarya ne baisan nasa salon zalincin bane .
Gida ba wanda ya bi takan ba Nadiya sai bayan an gama lunching sannan ne aka ankare ba Nadiya, suna magana ,momyn ta tace ai sun wuce da angonta ance en ganin ɗakin amarya zasu biyo uwar ango ,itadai her Excellency kunyatan duniya ta gama yinsa amma jin shiru nadiya bata dawo ba sai hankalinta ya ɗan kwanta amma kuma a cikin ranta sai ɗas ɗas! Yikeyi ,batasan wani kalan fitinan da sukeyi ba ,mutanen da ƙalau ma sunyi fitina bare kuma ga dalili?
Ita yanzu babbar damuwarta wani gida za'a kai dangin amaryan ? Govement house ko gidan Adams da ya ƙera yaƙi komawa ? Anya zata yarda ace gidan nadiya dabam da ita ,batasan halin da suke ciki ba koda zasu kashe kansu?


Adams kam ashe tunda ya wanki kan baban nadiya ya tabbatar an ɗaura aure kawai ,ya sa PA ɗin sa a canja deco ɗin komai na gidansa part biyu sama da ƙasa a sauya masu tsari ,suna tahowa nan da sati guda


Don haka shi a tsarinsa sai bayan sati guda ne sannan zai kai amaryan .
***
Washekari hankalin en Biki ya karkata kai amarya Nusaiba gidanta ,itakam sai rizgar kuka take in tayi tayi tai dialing number Nadiya Amma saidai yayi ringing ya tsinke bata ɗauka ,haka aka kaita aka mata nasiha aka watse
Momy a nutse ta tattauna da mai girma gomna bayan ta samu sunyi waya da Adams anan yace mata ai suna lafiya ,kawai a wuce da en uwan Nadiyan gidan Gomnan suga gida ,shi ba yanzu zata tare ba sai ta gama makaranta ,hakan ne yasa taji sanyi a ranta "To yanzu kuna ina da Nadiyar?"
"Muna hotel ɗin da na sauka ,banson en uwanta su gane auren dole akayi mata kar a zagi iyayenta da kwaɗayi bayan Ni na ja masu amma idan kun koma ,ku faɗa mun zamu biyo jirgi mu taho "
"Ok Ban Nadiyar in Bata haƙuri "
Kallon sashenta yayi yaga ta rafka tagumi cikin zuzzurfan tunani ita ko sanin yina waya batayi ba saboda yanda yike shake murya kamar mace "Mom barci take ,in ta farka zan kira ki"
Godiya tayi ta masa tana shi masa Albarka a tunaninta ya riƙe nadiya lillahi War rasulihi


Yina kashe wayar ya koma ya kwanta ya cigaba da shafa laptop ɗin sa yina meeting ɗin sa da en kwangilarsa


Cikin hawaye tazo ta zube a gwuiwoyinta "ka maidani Gidan mu don Allah " banza yayi mata ,still Bata dandara ba ta dawo ɓarin fuskarsa nan taga mutane Zazzau ne sun kewaye table shi kaɗai suke kallo ta tvn bangon ɗakin meeting ɗin


Wani mugun kallo ya dallara mata ,amma ko kallonsa batayi ba ta ɗaga masu hannu "Good morning All" washe baki sukayi suna gaisheta
Latsa laptop ɗin yayi ya kashe ya hayayyaƙo mata kamar zai daketa "Kina haukane zaki ringa shiga sha'anin aikina ,mutunci na!" Murguɗa masa baki tayi "Nima dai na rama ,kaji in da daɗi" sai kuma ta ragwagwaɓe fuska zata koma fuskar tausayin ta kamar yanda ta soma "Don Allah ka maida Ni gida Ni ba er iska bane " sakin baki yayi yina kallonta ,kafin ya wani huro hanci "Kin mun shiru ko sai na ɓarar dake matsa bani waje"


Harara ta banka masa "Kar Allah yasa ka maidani gidan don ma kaga ina damuwa ne ko ? To ganinan ka jiƙani ka shani" taune leɓen ƙasa yayi ,sannan ya hura iskan bakinsa "kar ki sake in jiƙaki in Sha don jinya zakiyi sannan ki gode Allah ke ba kalar matan da nikeso in aura bane ,da yanzu na yi fata² dake na gwada maki mazantakana ,saina sa Kin daina rashin kunya ma duk wani namiji a duniya ,because of my manhood ,but be careful" shiru tayi jin ya fara wasu magana na dabam




3days Later
Momy kam sun dawo gida Da tsirarun en uwan Nadiyan,sun so ace sunga gidan amarya amma momy tace zasu zo ganin ɗaki da amaryan na musamman ,da tunane² suka tafi saboda sudai an baro Abuja ba amarya anzo nan ba Amarya kodai an cinikin kan ɗiyarsu ne basu sani ba ,ji gida Aljannar duniya bayan kasantuwarsu gidan mulki kuɗi sun zauna a wajen mamallakan gidan nan tabbas

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login