Showing 12001 words to 15000 words out of 46143 words
menene?"
"Kawai tashi muje kunya nikeji"
"Kai haba ke kin isa ki samun rai kiƙi ƙarasa faɗa mun?"
"Tom maida wuƙar ,zan zama gwana a fanni sarrafashi a bed ,zan zama karuwa amma a ɗakin mijina zan zama isashiyar mace bazan taɓa bashi damar kallon wata da sunan ya ƙara aureba saboda gazawata ba,saidai don in yayi ra'ayi saboda kwadayin kyautata sunnah na ma'aiki tunda kinsan su maza an yi su don mace hudu ne to daya basa taɓa basu dukkan gamsuwa sai mace mai tsananin dace zata sami mijin da zaice ke kadai a gidansa kamar futilar Vespa " kwashewa da dariya mukayi sannan muka tafa ,daidai munkai wajen tarin motocin da bamusan wannene nasa ba,waya ta ciro zata kirasa sai kuma taga an buɗe ƙofar motar ,zaro jikinsa yayi ya fito ya bubbuɗe ƙofofin motarta koma wajen driver ya zauna still motar a kunne take ya kunna fitilun motar haske all over ga ƙamshin turare da na Ac na tashi ko ta ina
Shiga gaba tayi ,Ni kuma na lafe a baya
Ƙurrr ta masa da ido kawai saita fashe da dariya tana tafa hannu ,bubbuɗe hannunsa yayi yina kallon ƙirjinsa kyakyawar namijine mai tsawo da musculo_body ,choco skin gareshi amma kai da gani kasan Naira ya zauna ,lashe leɓen kasan bakinsa da yike jajur kamar mele tsabagen hutu da zama a cikin AC yayi ,kana ya lumshe idonsa ya buɗe
"Any fuck up?" Tafa hannu tayi ta riƙe haɓa🤔
"Ewwweeh see my babe😘 kaga yanda ka ƙara kyau kuwa? You look handsome ,beautiful ,champ and chop away kai ka haɗu gabaɗaya ,woni woni matar mijinta,gaskiya nayi Sa'a amma abu ɗaya zai kwafsa mana wannan tumbin da kayi ya nuna baka exercise daɗinka kawai kake ji ,Da munyi aure zamu fara zuwa gyming" dariya ya fashe dashi "kai wannan washi haka gashi kin kasa bari mu gaisa da ƙawarki ,rufe fuskarta tayi da tafukan hannunta "I'm sorry sweet kasan ai zumuɗin ganinka ne" ta waiga ta kalleni danike zaune a kujeran baya ina ɗan game da wayata ,sannan ta nuna masa Ni da yatsa "This is my very ..." Kafin ta ƙarasa ya cafe da cewa "Nadiya Our friend "dariya suka fashe dashi gabaɗaya wanda ya sani ɗagowa nima na tayasu ,ɗan ɗaga mun gira yayi "Hope na cinka dai?" Nodding kaina nayi alamar tabbatarwa sannan nace "Good evening our respective guest"
"Thank you durling nice meeting you babes"
Hira suka zarce dashi na yaushe gamo nidai bana saka masu baki ,sai lokaci lokaci suke tsomoni sosai na farajin a raina nima in kwaikwayi ummu ko zan samu Hot guy dazai soni irin zayd
Kiran wayata ya katse mun tunanina ,zaro ido nayi ,dasauri na kalli wajen Kulthum "Ummu Abul Hassan ne fa ke kira" tsaki taja "Yoo ɗauka mana tsoronsa kike ne?
Oum Aphnan✍️
09065990265
[6/27, 07:02] 😘😘😘: 20
Ɗauka nayi bance komai ba na kanga a kunnena "Nadiya?" Still bance komaiba saboda inajin kunyar inyi tsiya a gaban saurayin ƙawata bayan ada banjin shayin koma wanene ,wai meke faruwa ,me ke shirin faruwa dani ne? Tambayar da nike wa kaina kenan ,katsaham na sake jin ya kira sunana wannan karon da ɗan ƙarfi "Nadiyaa!" Da sauri na ƙanƙame wayar a kunnena saboda yanda naji yina neman suɓucewa a hannuna ,cikin dakiya nace "ina jinka"
"You go pay the task you made na rantse da Allah " "kana hauka wallahi kai bakaji kunyar abunda ka aikata ba ,saboda bakada kunya har kanada liver din kirana ,see wait,kamun maganar banza nikuma na fashe haushin takaicina da kaza da Ice cream so ka goge numberna nima zan goge naka"
"Haka kikace ko? Zakiyi bayani a bayan kanta ,duk inda kike sai en sanda sun zo sun ƙwamuso mun ke an ladafta ki " yina kai aya ya kashe wayansa ,shiru nayi ina kallon wayar ,cikin nuna kulawa Ummu tace. "wai me yike cewa" Buɗe baki nayi da nufin Inyi magana aikuwa kamar suna jira saiga hawaye shaushau suna mun Ambaliya a fuska "Nasa calm down now wai menene?"
A hanakali na maida mata abunda yace ,zayd da besan kan maganar ba da sauri ya cafe ,wai me ya faru,a hanakali duk kulthum ta labarta masa komai
Sosai ya nuna alhininsa "kinaji ko kiyi shiru ban numbersa samun numbersa a wayata ,ke kuma Ummu koma bayan ki rarrasheta bari in kirasa muji yanda za'a shawo kan matsalar"
Yina kiransa kuwa hopely ya dauka a mutunce suka gaisa amma sama² Abulhassan ke magana saboda pain ɗin da yikeji ,sannan ya shaida masa shiɗin yayan Nadiya ne ,ai yina ambatar sunan nadiya tamkar ya watsa masa garwashin wuta ,ya hau masifa wai yinada yaya babban lawya ne yace ya shigar da ƙara kotu kawai tunda yinada hujjoji masu ƙarfi ,ga sabuwar farar shaddarsa nan ya yage saboda janshi da sukayi a kwalta kar azo kan damfaransa ya kaisu siyáyya da sukayi ga mugun rauni da sukaji masa ,sosai sunyi attempting kashesa ne tunda ya faɗo a tsakiyar titi da da ƙaran kwana da tifa ta markaɗe masa kai .
Yanda yike jaraba yina haƙiƙancewa ne ya tunzura zayd
"Dakata kasan menene Inaso yanzu ka faɗa mana inda kake ayi duk abunda za'ayi tunda naga Alamar kai ɗin ba ɗan mutunci bane ,kuma maganar kotu Inaso kasa da sunana a cikin wanda zaka kai ƙaran sunana zayd Abubakar ,kuma wannan numberna ne tabbas kai saving ɗin sa ,ina jiran sammaci a kotu kuma wallahi in baka kai ƙara kotu ba Ni sai na kaika bisa yunkurin keta ma ƙannena haddi dakaso yi ka fitar dasu da daddare ,kaso yin Fada dasu akan titi ,kuma ka sani tayi recordimg cewan dakayi zaka kaita hotel kuyi iskanci ,so ina jiran sammaci kafin Ni in kaika"
"A'ah ni ban iya rigima ba tunda mamana ta haifeni banda Abokin fada ,yanzu haka ma gani a hospital an min ɗinkin ciwukan da suka jijjimin ,so Banda lafiyaryin tashin hankali,kuma Ni bance zan iskanci da itaba daga nace zan kama masu hotel"
"Uwarka zaka masu a hotel ɗin matayenka ne?" Dafe kai yayi kamar zai fashe da ihu ,haka ya kumbura kumatu yina magana a shagwargwaɓe "Malam wallahi tallahi ita ɗaya nace ,naji kana jam'u kuma nima sun zalinceni"
yanda yayi magana kamar zaiyi kuka shiyasa zayd sassautowa
"Kana da mata ?"
"Eh "
"Shikenan bari in gaya maka wallahi bakasan sharrin mace ba ,Ni mace ta ja mun bala'i da kake maganar zaka kaisu ƙara kotu Ni mace nayi soyayya da ita taje tayo ciki ta rantse ta raya Ni na mata a sanadiyar haka har gidan yari saida nayi bare kai sunada hujja?"
Ɓarkewa da salati yayi "Innalillahi wainnailaihir rajiun,to nidai don Allah kayi haƙuri Ni ba me niman fitina bane me yayi zafi,cewa fa sukayi me keken ya tafi dani malam ko kaine ya zakaji ? Wai a tafi dani Hmm,Amma dai kawai don Allah suyi hakuri "
"Aah ba wani hakuri saifa ka kawo sammaci nan"
"Haba malam saikace kai ba namiji dan uwana ba ,kana maganar kotu ina halin jinya duk na yi raga² nace na janye maganar Allah ya isa"
Kulthum Alama ta masa da ya kashe wayar ,yina kashewa suka fashe da dariya ,aikuwa sai gashi ya sake kira "malam amma kaga na kyale ta ko? To ka zama shaida tana sake kirana a waya zan kiraka in fada maka" anan Nadiya ta kada baki tace "Ni dama na taɓa kiranka a wayane ? Can da yawanka womanizer kawai"
Saida aka gama settling case din kafin Ummu ta kalli zayd "sweet kace har gidan yari kayi saboda mace Ruda masa ciki kaso yi ko da gaske " ɗan haɗe gira yayi "Wallahi da gaske ,it was just a year we met dake muka fara soyayya " mamaki abin ya ƙara ba nadiya da Ummu wai wannan fresh handsome din ne ya taba gidan yari
"Sweet bamu labari"
"Kinaji nayi wata budurwa sunanta Kausar!"
Take anan gaban Kulthum ya fadi kardai Kulthum nasu
"Yarinyar nan bataji sosan gaske ,tanada samari da yawan gaske wanda tsautsayi yasa ina cikinsu ,shikenan kwatsam sai nahi labarin zatayi aure wai zata auri wani airforce amma bikin bazai ɗauki lokaci ba ,Da fari auren ya sosan rai daga baya na cire abin a raina,hu'um bayan anyi Biki baifi da wata biyu da rabi ba sai akace mijin ya saketa kuma ya kaita ƙara kotu ,ashe miji tunda akayi aure aka barta a kano bai zo gidan amarya ba yinacan Lagos sai kawai yaji labarin kausar ta haihu ,just imaging aure bai kai wata uku ba,nan ya bude 2utan sai ta fiddo da mijin ɗa bayan ya danna mata red card ,nan ta fara bankaɗo samarin da ta rainawa wayo ,wanda suka taɓa iskanci tare shinefa ta lissafo har dani ciki,aka kawo mana sammaci kotu ba kunya tace a cikinmu akwai me ɗan ,masu mata wanda sunada aure su hankalinsu yafi tashi don duk matansu sun masu bore sun koma gidan iyayensu haka aka cusamu gidan kaso kafin a gama bincike ,saida mukayi kwanaki bayan an masu gwajin DNA test an gano waye baban dan sannan mu kuma aka sake mu ,na kwafi yarinyar nan in mata duka amma ban kuma ganinta ba har na tafi cairo ,shiyasa Nike bala'in jin tsoron hulɗa da yarinya maraji kar ta roro damuwarta ya shafe Ni"
Shiru sukayi kafin nadiya ta kalli Kulthum "Ummu ko dai Kausar ɗin mu ne?"
"Kar ki tabbatar mun da saƙar zuciyata " tsoma masu baki yayi "kunada wata ƙasa kausar ne wacce bataji ita ma? Mu ɗan ga pic dinta "
Hade baki sukeyi wajen rejecting "Muuuu? Allah shi kyauta haɗuwar makaranta rabuwar Hostel ,bame hotonta anan" Nadiya t cigaba da masifa nan bakinta ya bude tar ta manta ma baƙon basu saba ba
"Kash ! Amma naso in clearing doubt dina " ummu da ta fara jin kishi ,shiga whatsapp group dinsu na aji tayi tana scrolling saiga hoton ta ajikin dp dinta ,tana hasko masa tun yina booting ya daki sitiyarin motarsa "wallahi itace,kai wannan yarinyar beyong your expectations gwara kuyi nesa da ita bata da Alkhairi astagfirullah bansani ba ko ta shirya "
Shiru Kulthum tayi yina kokarin amsar wayarta cikin zafin kishi ta kashe wutan screen ɗin ta aje wayar akan cinyarta "forget about Kausar,muyi hiranmu idan kuma ita din kazo gani then I will find my way sai ka kirata ku zanta "
Dariya ya fashe dashi don tura kishi ke walagigi da ita "ma'am a maida wuƙar Ni me zan da kausar? Yanzu fa nike cemaki na nemeta in zaneta " burne face tayihaka suka cigaba da hiran ,da dai ya gaji da rarrashi ya lallaɓa ya bata tsarabar da ya taho mata dashi sukayi sallama .
****
Washenkari Nadiya ta tafi Abuja
[6/28, 08:51] 😘😘😘: 22
Nadiya kam ta goge an zama fancy babe ,ita ba a waje ba hatta a gida shan ma kowa ƙamshi take sai ayi ta magana ,itakam sai anyi mugun sace zata jefa one word ,tun yanayin dolen da ta sakawa ranta yina wahalar da ita har ta soma sabawa ,En gidan kam suna kwasan abun mamaki wai over sabi kenan.
Anyi anyi ta koma school HUTU ya kare tace Allah ya kasheta Bata komawa sai result ya fito saboda ,tasan koranta ma za'ayi to gwara tayi zamanta in ba'a koretan ba ta koma in ankoreta ta miƙe ƙafa a gida
Yammacin ranar kuwa sai ga saƙon Ummu ta wxp hotunan result ne Nadiya taci clean pass ba Carry over ,Amma an kori mutane 8 ciki harda mariya budurwan Examination officer da suke iskanci a office tana kawo ma ƙawayenta Amsa
Tsoro abun ya baiwa nadiya gani take kamar ƙaryane bazata taɓa iya passing ba don ita kanta ta firgita da karatun ,but how? Ta daisan ba'ayin follow up bare tace anbi mata takardanta ta sama ne .
Ɗaukan waya tayi ta kira Ummu ,ringing ɗaya Ummu ta ɗauka wajen da take akwai hayaniyar ɗalibai masu gardama nayi masu kuka nayi
Cikin makyarkyatan murya take tambayar ta "Ummu da gaske wai na ci jarabawa?"
Er ƙwallar daɗi Kulthum ta goge "wallahi munci Nady ,ga mutane nan kowa ya duba yaga ya ɗebo carry over sai ya duba naki in akaga clean pass sai ace wai ai dama daga gidan Govenor kike an bi maki ta sama ne " lailayo ashar ɗin da bata shirya ba tayi ta maka masa "Yaci ubansa govnor sunsa na zagi babba ,kin manta kwanan dare da nike a zaune ?"
"Wallahi kowa ya saka ran dole sai an koreki " "Wallahi koni na sakawa raina sai ga su mariya yarinyar da nan danan ta gama ta kai " ɗan matsawa nesa da ɗaliban Ummu tayi "Bari muyi gulma dake Aminiya" matse murya Nadiya tayi kamar tana kallon ummun "Ina jinki"
"Ashe duk jarabawan nan da mukeyi linked ne?"
Zaro ido tayi "ke ban gane ba "
"Wallahi kuwa ina faɗa maki ,wai ashe examination officer dai saurayin Mariya ne ko ince dadironta ,shikenan wai kullum idan zamuyi paper in malamai suka kawo masa question and answer ,as in ya rubuta tambayoyin yayi judging da amsoshin malaman ,sai ya kira Mariya d yamma ,abun haushin ba tambayar yike bata ba ,a'ah amsar yike Bata,sai ya bata sabon booklet ,ta tsallake pages biyu sai ta kwashe duk amsoshin da numbobin tambayan, sai ya amsa booklet ɗin ya aje in munzo jarabawa ana raba Mana plain booklet sai shi ya bata wannan da ta rubuta amsa a ciki ,sai tayi rubbish dinta a first 2 pages sai ta soke shikenan taje tayi submitting ,to ranar da Asirinta zai tonu ,shine na course din mr Joshua me Applied physics dinmu Ashe yayi setting question ɗin da yasan bazamu iya amsawa bane yaga tayi calculating neat exactly irin nasa ,shine ya tubure an ƙwafar masa amsa ,bincike yayi bincike shine aka gano ,yanzu maganar da nike maki da ita da ƙawayenta duk an koresu gasu can daga mai suma sai me suma ,shima EO ɗin an saukeshi a eo an canja masa department an rage masa matsayi......kai mudai mun gode Allah "
"Hmm Addu'ar iyaye shi kadai yike tafe damu a makarantar nan,kinga illar iskanci ko? Allah shi kyauta "
"Yaushe zaki dawo?"
"Goben nan zan biyo Flight ,amma zan sauka a gidan momy sai jibi zan shigo school"
"Shikenan sai kin zo"
"Thanks ,nice finding you as friend of mine " ta na kashe wayar ta durko a gado tana ihun murna "Wayyo daɗi ku firfuto naci jarabawa ....ina Ya Hisham Anty Nusaiba kiramun shi a waya ki faɗa masa naci jarabawa yamun Alƙawarin iPhone x tunaninsa faɗi zan ,to maza² a bani wayata gobe zan koma school...kuma momy dady ,Anty Nusaiba kowa inga prix ɗin sa"
Iyayen da duk suka fito jin ihunta washe baki sukayi "How sure you are that you passed that top " miƙa masu wayarta tayi "Duba da idonku ba ƙarya na maku ba"
Nusaiba rungumeta tayi ,ta raɗa mata wani magana a kunne ai tsalle tayi akwai sukayi ɗaki da gudu ,mayafi Nusaiba ta ɗauka ,kafin nadiya ta mata wani kallo "Ni ? In fita ban wanka ba ,bayan Ihun da na dinga yi zufa ya tsatso ai sai in je ana jin tsamina ,jira yanzu zan fito wow yau zanje nice outing"
Sai dare suka dawo ,masu gadi suka tayasu shigo da kaya ,da sabuwar wayarta ,ba abinda Nusaiba ta siyo mata sai zallan takalma ,irin masu kamar huffi ɗin nan da hijabai dogayen kusan kala goma ,turaruka designers da shades masu kyau ,a daren suka haɗe akwatin big girls washe kari 10am Nadiya suka taso 2hrs sun iso tana sakkowa jikinta doguwar jilbab har ƙasa da takalminta half cover ta goya jakan baya tana tura wani ,hango motocin govement house tayi nan ta murmusa tasan anzo ɗaukanta ne ,har ta ƙaraso bata ga an buɗe motar Ba,hakan yasa ta duba red car ɗin da ya fita odd a ciki ta ƙwanƙwasa ,Bawai mom da Adams basu san tahowar Nadiya wajen bane A'ah sun sani saidai yanda tayi haske baki ɗau da red jambaki ,gashi dai hijabin har yina sharan ƙasa amma jakar bayan da ta saka yasa ya janye ,tayi azaban kyau su kansu ta tafi dasu basu taɓa kawowa nadiya bace .Knock din da tayi ,da gaisawarta da takeyi da exco ɗin su muryarta da sukaji ya tabbatar masu da Nadiya ce ,zullo baby amra tayi ta kalli Adams dake wajen driver itakuma tana wajen me zaman banza "Fofo its Anty Nadiya oooo she look good" ta fara kici kici zata ɓallo ƙofar ,tsawa ya daka mata daidai murfin motar ya buɗe ta baya nadiya ta shiga ,duk en gidan ta gani a motar momy ita kadai a baya ,faɗawa jikin momy tayi ,tai maza ta cire shade ɗin fuskarta "Momy I miss youuuuu" ta ja maganarta Adams wani muguwar tsaki yaja "Gulmar banza! zaki zauna mu rufe ƙofa mu tafi ko kuwa inada wajen zuwa" fuskewa tayi ta zauna tayi balance ta tsurawa mirror ido bata ko motsa ba ,momy na shafa mata kunci "Wow my dota me momy ta baki kika zama kalan en turkey " murmushi tayi me stayel ta miƙa hannu ta gaba "My chuchu baki ganni bane waya taɓa mana ke?" Sai sannan hawayen da ta rike suka zubo cikin yanga tace "ohyeah ohyeah don't cry plzzzz" ta kare maganar cikin rarrashinta
Tsaki ya daɗa ja kamar jikan tsaka ya juya masu ƙeya "Bayan ... Bayan fofo ne takan nace kinyi kyau shine shine..." Kafin ta ƙarasa magana ya daka mata tsawa karku sakoni a shirmenku ,caɓe baki nadiya tayi ba tareda tace komai ba ta ɗan miƙe ta dawo da ita baya ta raba tsakaninsu da mom daketa amsa waya "Ni kaina nasan mai kyau ce ko an faɗi ko ba'a daɗi ba my love kiyi shiru kinji , nayi maku sabon uncle da zai ringa fita damu outing yina siya muna Ice cream ,chocolate da teddy bear" ehuuu Amra ta saki "Anty zai soni kamar ke da Uncle fofo "
"Yina sonki sosai da ya ga hotonki a wayana ,yace oh my love I love you...unwahhhh yama hotonki feck a jikin screen ɗina " haɗe hannuwarta tayi a ƙirji "Awwnnnn ,nima ina sonaka uncle...." Sai kuma tayi shiru ,with stamina face tace "Anty meye sunan