Showing 27001 words to 30000 words out of 42870 words

Chapter 10 - HALLITAR ALLAH CE COMPLETE

11 Jul 2025

2211

a ƙasa, saboda ƙarfin bankar da Mamanta ta mata.

"Wai Mama lafiyarki? Tun daga maƙota nake jiyo ihunki." Zaliha ta faɗa ta na ƙoƙarin miƙewa tsaye.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Abdul kuwa, da ya tabbatar Kande ba zata taimake shi ba, hasalima ta tafi ta bar shi, kawai sai ya miƙe ya juya yana kuka, ya nausa cikin jejin dake mararraba da karkarar.

A haka ya ci gaba da tafiya kamar yanda ya yi a baya, ba abinci ba ruwa ba wani mataimaki.

Ga shi Damana ta kawo kai, tunda har an fara ruwa haka Abdul ya ci gaba, duk iska da ruwan da ake a kansa suke ƙarewa saboda rashin mafaka, wani lokacin idan ana sheƙa ruwan sama sai ya samu guri ya takure tare da haɗa kai da gwuiwa ya na kukan maraici.

Idan an gama ruwan ya miƙe ya ci gaba da tafiya, wasu lokutan talalaɓiya ta ja shi ya faɗi ƙasa, duk jikinsa ya kukkuje.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
A can Sokoto Kuwa, Hajiya Hasina ce zane a ƙasa duk ta daburce, ta kasa furta ko da harafin A ne.

Alhajin ya sauko daga kan gadon ya zo gabanta ya tsaya yana cewa "Hajjiya mi zaki yi da takardun gonata?"

"Am dama...dama, na ce dama." Sai kuma ta yi shiru tare da duƙar da kanta ƙasa.

"Dama me?" Ya jefo mata tambaya.

Gabanta ya yanke ya faɗi, can kuma ta tuna cewa ai ta magance shi, don haka ta ɗago kai cike da gadara da yaƙinin aikinta ya yi ta ce "Dama ina so ne in duba in akwai yiwuwar a saishe ta sai a sesuwa."

Shiru ya yi tsabar mamaki, baki a sake yake kallonta.

Ita kuwa ganin bai ce komai ba ta sakankance a ranta maganin ya ci, don haka, ta miƙe haɗe da juyawa cike da tsiwa ta na rausaya ta wuce ɗakinta cikin nishaɗi......

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Lamarinsu Alhaji Bilya kuwa, abin ya ta'azzara don kuwa tuni sun baza yaransu a ƙauyukkan garin da kewaye, kusan sati Uku kenan amma har yanzu shiru kamar an shuka dusa.

Wannan lamarin ya fusata yayyen alhajin sosai, don haka suka sauke fushinsu a kan dukiyarsa.

Ganin abinda suke aikatawa ya yi yawa ya saka Mizbahu ya same su watarana da dare, suna tsaka da shawararsu ya shigo masu, yana cewa "Yan uwana ina mai muku wasiyya da ku ji tsoron Allah mahaliccinku, ku sani makirci, tuggu ko hassada ba za su kai ku ko'ina ba, face su jefa ku a tafkin nadama da danasani mara amfani, haƙiƙa duk wanda ya hau motar kwaɗayi ba inda za ta sauke shi sai tashar wulaƙanci."

A fusace yaya Sunusi ya wanke shi da mari, kamar ya samu ƙaramin yaro.

Bilya kuwa ya miƙe yana faɗar "Da kyau! Ka burge ni Sunusi, na lura yaron ga yanzu ganin ya kai dai-dai yake damu, saboda ya yi aure kamar yadda munka yi, haka yahi mu kuɗɗi yaka ji shiyasa ya ga damar hwaɗa muna magana."

Mizbahu dai murmushi kawai ya yi ya juya ya na faɗar "Ita gaskiya guda ta daga ƙin ta kuma sai ɓata, haka kuma ɗan hakkin da ka raina, shike tsokale maka ido, Allah ya shirye ku."
Yana gama faɗa ya sa kai ya wuce zuwa gidansa, saboda ba a taɓa ci masa zarafi irin na yau ba, haƙiƙa da ba yayansa ba ne, ko wanene ya mare shi a yau sai ya gani.

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

9Rabiul awwal/26 October.
1442hjr/2020.









________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*


PAGE 35-36

Alhaji Munir kuwa tsabar mamaki ko zama ya kasa yi, a gun da ta bar shi tsaye a nan yake har zuwa wani lokaci mai tsawo.

Ranar dai bai kuma tamka mata a kan maganar ba, jira yake ya ga iya gudun ruwanta, yana so ya tabbatar da zarginsa, shin ta haukace ne ko kuwa raini ne ya cika mata ciki?

Isar ta ɗakinta ke da wuya, ta zauna kan gado tana mai da numfashi, haƙiƙa daga farko ta tsorata ainun, shiyasa har yanzu ƙirjinta ya ke harbawa kaɗan-kaɗan.

Bayan ta gama sai ta nutsuwarta ta kira Kulu a karo na biyu, ta labarta mata abun da ya faru.

Buɗar bakin Kulu sai cewa ta yi "Ai bokan nau aikinai kamar yankan yuƙa na, dama tun da yacce miki haka, indai ke yi aiki da maganin yadda ya kamata ina tabbatar miki da cewa sai ke yi duk yadda kika so da Alhaji, ke ko cewa kiyyi ya kwanta ki taka shi da ƙahwa, wallahi sai ya kwanta."

"Ke habah! Da gaske mutuniyata?." Hasina ta faɗa

"Kina wasa da boka Bakuza, ni na san aikinai kuma ina jin daɗin aikinai sosai, ke dai Allah ya kashe ya baki."

Dukkansu suka bushe da dariyar keta sai ƙyaƙyatawa suke, haka dai suka ci gaba da hirarsu kafin daga bisani suka sauka a layi, da alƙawarin cewa gobe tun safe Kulu zata zo.

Haka kuwa a ka yi, washegari Tun ƙarfe takwas na safe, Napep ta sauke Kulu a ƙofar gidan.

Mai gadi ya sha mamakin ganin ta tun da sassafe haka, amma sanin cewa ƙawar hajiya ce yasa bai yi yunƙurin hana ta shiga gidan ba, buɗe mata ƙofar ya yi, kai tsaye ta shige zuwa ciki.

Tun a harabar gidan ta kira Hasina a waya ta shaida mata.

Hasinar da kanta ta zo ta shigar da ita ciki.

A falo suka zauna, Hajiya ta ƙwalawa Ladi kira "Ladi! Ladi!! Ke Ladi!!!"

Kafin ta gama rufe bakinta sai ga Ladi ta shigo da sauri tana faɗar "Gani Hajjiya."

"Yawwa Ladi kawo ma Abbukiyata abincin kari ke ji." Hasina ta faɗa.

Cikin girmamawa ta miƙe ta juya zuwa ɗakin girkin don cika umarnin uwar gida.

Ba jimawa ta dawo da tiren abinci ta dire a gaban baƙuwar, ta juya tana mamakin wannan ziyarar haka.

Bayan Kulu ta ci ta yi nak, Hasina ta ce "To ina ga yanzu ke yi ƙwarinda zaki iya kallon dramar da kyau, bari in kira shi."

Miƙewa ta yi zuwa ciki, jimawa kaɗan sai ga su sun fito a tare tana gaba yana biye.

Dinning Area ya nufa kai tsaye, don ko bai ma san da zaman wata baƙuwa a gun ba, ko da Hasina ta shiga ciki bata gaya masa ba,cewa kawai ta yi ya fito su karya.

Sai bayan ya zauna ya fara cin abincin sannan ya lura da wanzuwar Kulu a kan kujerar da yake fuskanta.

"Alhaji ina kwana." Kulu ta faɗa tana sunne kai saboda kwarjinin da ya mata.

"Lahiya lau." Ya amsa, sannan ya maida kallonsa ga Hasina da alamar mamaki a fuskarsa.

"Abukkiyata ta Kulu ai kasanta." Hasina ta faɗa.

Shi dai bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da cin abincinsa har zuwa lokacin da ya kammala.

Miƙewa ya yi da zimmar shiga ɗaki, dama tuni Hasina ta gama cin abincin ta dawo kan kujera kusa da ƙawarta ta zauna.

"Alhaji taho nan ka zauna." Ta faɗa cikin bada umurni.

Juyowa ya yi ya kalle ta, sosai ya ke mamakin sauyawar hajiyar daga jiya zuwa yau, amma bai musa mata ba ya je ya zauna kusa da ita, a tunaninsa ko akwai abinda take son gaya masa ne.

Murmushi ta jefe shi da shi tana kallon Kulu ta wutsiyar ido.

"Gani Hajjiya mi halam?" Ya tambaya.

"babu komi kiranka ɗai niyyi."

"Ko da yake danna min ƙahwahuna, yau na tashi suna min ciwo." Cike da izza take maganar, wai ita a dole ta asirce shi.

Wani shegen kallo ya watsa mata, wanda ya saka ta shiga ruɗani gami da al'ajabi.

Amma duk da haka bata karaya ba, ta kalle shi a ɗage ta ce "Ka danna min ƙahwahuna nicce, mi kat tsaya kallo?"

Kulu dai na daga gefe tana kallon show sai ƙunshe dariya take, ba abinda take jira sai ta ga yanda alhaji sai durƙusa yana matsar ƙafa.

Shi ko Alhajin ɗaga mata hannu yayi cikin tsawa ya ce "Ya ishe ki haka Hasina! Wai mi ka damunki ne? tsakanin jiya da yau na kasa gane miki, sai hauka kikai iri-iri, in ke samu taɓin ƙwaƙwalwa na ki hwaɗamin in kai ki asibiti ya hi ki tsaya kina karanta min shirme."

Har ya juya zai tafi kuma ya ci birki yana cewa "Kuma daga yau sai yau, kakki ƙara yimin maganar banza irin wagga ko da gani sai ke, balle gaban wata ƙazamar mata, sannan ki tabbatar ke maisammin takardar gona ta kahin dare, in ba haka ba....."
Bai samu damar ƙarasawa ba tsabar taƙaici da ya turniƙe shi kawai sai ya wuce fuu! Zuwa cikin ɗaki.

Dukkansu suka saki baki sototo! Kamar garkar wawa, suka bi shi da kallo.

Kulu ta ci haushin kiranta Ƙazama da ya yi, don ko kalmar nan ta caki zuciyarta sosai.

Hasina ta sha kunya, ji ta yi tamkar ƙasa ta tsage ta shige ciki, wai ita zai ciwa zarafi a gaban macen dake ƙasa da ita? Ko da yaushe Kulu na girmamata da jin shakkarta amma yau Alhaji Munir ya zubar mata da mutunci da darajar ta, tabbas ba zata taɓa barin shi ya ci bulus ba, dole ta ɗauki mummunan mataki a kansa.

Hasina ta manta cewa shi ta so ta wulaƙanta sai reshe ya juye da mujiya.

Kulu ce ta katse mata tunanin da take ta hanyar faɗar "Hmm! Tofah! Meka hwaruwa nan wurin ga? Ko dai ke yi kure wurin anhwani da maganin?"

Dogon numfashi ta ja ta sauke sannan ta ce "Tabbas akwai matsala, ni dai na san na bi komi bisa tsari, amma yanzu ki tahi gida zan binciki inda matsalat take."

Kulu ta ɗauki jakarta ta fice daga gidan tana yiwa Hasina dariya a ranta ta ce "Yau fa rana ta ɓaci ga mata, su Hasina an shiga hannun kwalawa, ai na so ace ya zabga mata mari wallahi da na ci dariya, amma bakomai randa rana ta kuma ɓaci inda rabo na gani."

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Ina labarin yaro Abdul?

Yaro Abdul dai ya nausa a cikin jeji sai tafiya yake, tun yana ƙirgen kwanaki idan ya ga dare ya yi gari ya waye ya ce ɗaya, gobe ya ce biyu, har a ka kai lokacin da lissafi ya ƙwace masa.

Zuwa lokacin shanyayyiyar ƙafarsa ta ɗage sosai, da ba don Albarkacin sandunan da yake tare da su ba, tabbas da ba zai iya matsawa ko daga nan zuwa can ba.

Tun yana damuwa tare da licin ciwukan dake jikinsa har ya daina damuwa dasu, ya yanke ƙauna, hawayensa ko tuni sun ƙafe, ya kuma fitar da rai ga samun mataimaka.

Ba abinda yake sai roƙon Allah a zuci da sarari domin ya kawo masa ɗauki.

Allah ma ji roƙon bawa.

A wata rana daga cikin ranaku a ka kwana a na tsala ruwan sama kama da bakin ƙwarya, Abdul bai samu mafaka ba, don haka a kansa ruwan suka ƙare.

Da safe ruwan ya tsaya cak kamar ba a yi ba, can zuwa rana tsaka rana ta ƙwalle sosai, tamkar ba jiyan nan aka tsala ruwa ba, ikon Allah kenan.

A daren ranar Abdul ya kwana da wani irin zazzaɓi mai zafi, don haka ya kasa tashi ya ci gaba da tafiya yana nan kwance a'inda ya kwana, zuwa can da ya ji rana ta yi zafi sosai ya yunƙura daƙyar ya kwashi sandunansa ya ci gaba da gangarawa cikin jejin jikinsa sai kyarma yake.

Tun daga nesa yake jiyo busa mai daɗin gaske ta na kawowa kunnensa ziyara.

Cike da tsananin murna ya ci gaba da bin sautin busar ya na jin nishaɗi.

Ba komai ne ya saka shi farinciki ba, sai don tunanin cewa zai samu mataimaki, ko ba komai dai ya san zai samu abinda zai sakawa bakinsa idan mutumin dake tafe mai jinƙai ne.

Can bayan wasu daƙiƙu ya iso gun wata bishiya mai girma da inuwa sassanya, a ƙasan bishiyar ya hango mabushin zaune, sai dai bayan mutumin kawai yake iya gani, domin daga bayansa Abdul ɗin ya ɓullo.

Nan ya ci gaba da nufar mutumin da zimmar ya kewaya ta gabansa su haɗu.


Shi ko wannan mutumin jin motsi a bayansa ya saka shi miƙewa cikin hanzari tare da saita bindonsa da wani mulmullen dutsi mai ɗan girma, ya juyo a fusace ya na jiran ƙarasowar mai kawo harin.......


Hmmmm! Tofah! Shin mutuminan wanene shi? Me yake a jeji? Zai harbi Abdul kuwa?

Ba wannan ba, anyah zai taimaki yaro Abdul idan ya yi arba da halittarsa?🤔🤔🤔



Don jin ya zata kaya sai ku biyo NI a pages na gaba.


More comment more typing.....

Follow me on Wattpad @Ruky_I_Lawal.



Vote share and comment.





RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹


Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal.





RUKY I LAWAL🌹🌹🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

15Rabiul awwal/1 November.
1442hjr/2020.



Wannan page SADAUKARWA ne ga masoya wannan book ɗin, iya wuya ana jone🥰🥰




________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*



PAGE 37-38

Ganin haka yasa antar Abdul kaɗawa, a take ya tsaya cak a gun, tare da runtse idonsa da ƙarfi, domin a tunaninsa ba abinda zai hana mutumin nan ya same shi a dai irin wannan saitin da ya yi.

Shi kuwa mutumin har yanzu bai sauke bindonsa ba, sannan bai yi yunƙurin matsowa kusa ba, domin halittar yaron ta saka shi al'ajabi, sai dai bai ji ko ɗigon tsoro ba, kasancewarsa maharfi da ya saba yawo a dazuka, ba irin abinda baya cin karo da shi a yayin da ya shiga jeji, don haka ganin wannan ma bai saka shi tsorata ba.

Jin shiru ya saka Abdul ya buɗe idonsa, ganin mutumin bai yi ko gezau ba, ya saka shi fara takawa don zuwa gun shi.

"Dakata yaro!."

Maharbin ya faɗa cikin ɗaga murya.

Tsayawa ya yi cak a inda yake, kamar yanda aka umurce shi.

"Mutum ko aljan?"
Ya jefo masa tambaya.

"Mutum na." Ya bada amsa.

"Yaro meke tafe da kai?"

Cikin raunanniyar murya ya ce "Taimako nika biɗa, ka temake ni, ba ni da lahiya kuma ina jin kishirwa da yunwa."

Da ganin yanayinsa ka san yana jin jiki.

Sai a lokacin Maharbin ya mayar da bindonsa, sannan ya matso kusa da Abdul ɗin.

Hannunsa ya saka a jakar bayansa ya fito da shantalin ruwansa ya miƙa wa yaron ya sha, sa'annan ya ja shi zuwa gindin bishiyar da yake zaune, ya ɗauko ragowar gasasshiyar tsuntsuwar da ya ci ɗazu ya miƙa masa.

Da sauri ya ƙarba ya cinye, duk da naman ba yawa kuma bai masa maganin yunwa ba, amma ya toshe masa wata kafa, don kuwa ya ji damar yunwar da ta addabe shi.

Bayan ya yiwa yaron duk taimakon da ya kamata sai ya miƙe ya cigaba da zagayawa a jejin ko ya samu wani naman da zai kai gida.

Abdul ya bi bayan shi, har ya fara nisa a tafiyarsa ya ji motsin mutum a bayansa, juyowar da zai yi haka sai ya ga wannan yaron ne da ya taimaka 'yan mintinan da suka wuce.

"Yaro lafiya dai?" Ya tambaya cike da mamaki.

"Babu komi, dama cewa niyyi zan bika mutahi." Abdul ya faɗa cikin rawar murya.

"Ni fa ba na gane wannan Hausar taka, wai ina zaka bi ni?" Ya kuma tambayarsa.

"Ni ko ma ina na mu tahi ɗai." Ya faɗa.

Zuwa lokacin Maharbin ya fara ƙuluwa, ga haushin rashin samun abun farauta tun safe da ya fito, ga shi baya gane Hausar yaron, saboda haka ya ce "Kai yaro saurare ni da kyau, na riga na maka taimakon da zan iya, ko kai aljani ne ya kamata ka bar ni haka."

Ya na gama faɗa ya yi gaba abinsa, Abdul ya fashe da kuka ya kuma binsa a baya tamkar jela.

Da Maharbin nan ya ga abun ba na ƙare ba ne, sai ya tsaya ya yiwa Abdul gargaɗi da babbar murya tare da tsoratar da shi, a kan idan ya yarda ya biyo shi sai ya yanka shi ya kai namansa gida a madadin naman tsuntsaye.

Bisa ga tilas Abdul ya haƙura, ya yasu a gun ya na kuka, Maharbin kuma ya ci gaba da nausawa jeji ran shi wasai, yana neman abun farauta.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

A can gidan Alhaji Munir kuwa, hankalin Hajiya Hasina ya kai ƙoluluwar tashi da ta fahimci cewa maganinta bai ci ba, sai zarya take a falon ta na ƙoƙarin tuna inda ta yi kuskure a cikin aikin.

Ta yi iya yinta amma ta kasa gano inda matsalar take, haka ta ci gaba da zarya, ranta sai tuƙuƙi yake mata, ko ta halin ƙaƙa tana so ta nunawa Alhaji Munir cewa ruwa fa ba sa'an kwando ba ne.

Ta na cikin wannan halin Alhajin ya fito da shirin zuwa kasuwa, ya zo zai gifta ta gabanta ya wuce ta kira sunansa.
"Alhaji!"
Ko kallonta bai yi ba ya ci gaba da tafiya.

Har ya je ƙofa ya tsinto muryarta tana faɗar "A dawo lafiya mai gida."

Wani uban tsaki ya ja ya fita, cike da ƙunar zuciya.

Haƙiƙa yana daf da kamuwa da ciwon zuciya, ga damuwar ɓatan tilon ɗansa, ga wannan matar da take so ta ƙara mishi damuwa a kan wadda yake ciki.

Haka ya bar gidan da kuntaccen kai.

Tafe yake a mota shi kaɗai ya na tunanin rayuwa, damuwa ce cunkushe a ƙasan ransa, har ya zama na cewa tuƙin kawai yake amma hankalinsa baya kan titin.

Ikon Allah ne kaɗai ya kai shi Marna police station, ya je don ganawa da officern da ke riƙe da case ɗin ɓatan Abdul.

Bayan sun gaisa officern yake tambayarsa, "Alhaji hay-yanzu dai shiru a ɓangarenku babu labarin komi? Ba wani wanda kaka zargi da aikata wanga laihin?"

Shiru ya yi kamar mai nazarin wani abu, can ya ɗago kai ya ce "A'a officer ba na zargin kowa, yanzu dai abinda nika so gare ku, don Allah ku ƙara tsaurara bincike wallahi ina cikin damuwa, ku yi ƙoƙari ku gano min maƙiyina da ya raba ni da tilon ɗana, ya sani cikin zullumi da tunanin halin da rayuwar ɗana za ta kasance a lokacin da ya nisanta da gida."

Shiru ya yi na ɗan lokaci, yayin da ɗan sandan ke faɗar "Insha'allah! Alhaji zamu ƙara ƙoƙari akan wanda mu kai, da yardar Allah sai mun kama mai wannan laifin mun tabbatar da an yanke mai hukuncin da yaddace da shi."

Nisawa Alhajin ya yi sannan ya ce "Ina ji a jikina cewa Abdul ya na cikin matsala, ko barcin kirki ba na iya yi, ina yawan mafarki da shi ya zo yana kiran 'Abbu ka temake ni, ina cikin matsananciyar matsala' shiyassa ka ga hankali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login