Showing 30001 words to 33000 words out of 42870 words

Chapter 11 - HALLITAR ALLAH CE COMPLETE

11 Jul 2025

2210

yana kasa kwanciya Officer."

"Dole hankalinka ya tashi Alhaji, ɓacewar ɗan mutum ba wasa ba na, yanzu dai ka koma insha'allah za mu zo nan gida domin akwai wadda muka zargi a cikin ahalin gidan." Cewar ɗan sandan.

Zaro ido Alhaji ya yi ya ce "Wa kuke zargi?"


"Matarka Hajiya Hasina." Ya ba shi amsa.

Ya so ya musa, amma shi kansa yanzu ya fara zargin ta don haka bai ce komai ba ya yiwa officern sallama ya ƙara gaba.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Hasina kuwa bayan fitar Alhaji ta kuma faɗawa dogon nazari, can ta yanke hukuncin cewa za ta ƙara amfani da maganin wankan, domin a nan kokontonta yake, don kuwa ba ko shakka a gabanta ya ci abincin da ta sakawa maganin, wankan ne dai bai yi da kyau ba.

Da yamma bayan dawowar Alhaji gida Hasina ta same shi a ɗaki ta durƙusa a gabansa.
"Don Allah Alhaji ka yi hanƙuri ka yafe min, na tuba ban ƙarawa, kuma ma na mai samma takardun gonakka ka yi hanƙuri mijina."

Banza ya mata kamar ta na yi da bangon ɗakin.

Ganin hakan yasa ta fashe da kukan makirci ta na ƙara roƙarsa.

"Don girman Allah Alhaji ka yi hanƙuri na tuba, ni kaina ban san mi ya hau kaina ba nit aikata abubuwan da niyyi, ka yahe min."

Kuka take kashirɓan kamar gaske, a zahiri za ka rantse ta yi nadama, amma a cikin ranta ba haka ba ne, zuciyarta cike da son ganin ta mallake shi.

Sai a lokacin ya ɗago zuciyarsa cike da tausayinta, ya lallashe ta ka na ya yafe mata, tare da tabbatar mata da cewa komai ya wuce a gunsa.

Take a gun suka shirya suka dawo kamar da.

Ganin ta samu wannan nasarar ya saka ta shiga shirya yanda za ta yaudare shi ya yi wankan ruwan maganin.

Kashegari kamar waccan ranar, ta kuma zuba magani a ruwan wankansa, sa'annan ta tsaya a ƙofar banɗakin ta yanda za ta iya jiyo duk motsinsa.

Bai kawo komai a ransa ba ya shiga wankan, sai dai kamar waccen ranar, ƙaiƙayi ya ta so masa, da kamar zai ɗibi wasu ruwan ya wanke sai kuma ya tuna ya na sauri ne, da yake ba sosai yake jin ƙaiƙayin ba, kawai sai ya ɗora towel ɗinsa ya fito.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Wasa-wasa sai da Maharbin nan ya share sama da sa'o'i biyar amma ko tsuntsu ɗaya bai haɗu da shi ba, har ya sare ya cire rai ga samun wani naman.

Gwuiwoyi a sanyaye ya juya don komawa gida, sai dai ya na cike da zullumi da tunanin yanda zai tunkari iyalinsa hannu rabbana.

Har ya ci rabin tafiya, kamar daga sama ya ji an ce "Ka manta da yaron da ka wulaƙanta ɗazun nan, da dai ka koma gare shi wataƙil da ka dace."

Nan fa ya hau waige-waige ya na neman mai maganar, amma bai ga kowa ba.

Sai a lokacin ya tuna da wancan yaron da suka haɗu, har ga Allah shi ya ma manta da rayuwar yaron shaf, sai yanzu da aka tuna masa....








RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

21 Rabiul awwal/7 November, 2020.
1442hjr/2020.

DEDICATED TO: ANTY HAUWA (MAMAN USWAN)








________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*


PAGE 39-40

Cikin hanzari ya juya ya nufi inda suka haɗu da yaron ɗazu.

Sai da ya iso bakin bishiyar da suka zauna ɗazu, nan fa ya hau dube-dube ko'ina ya na neman yaron, amma bai gan shi ba sam, nan fa hankalinsa ya dugunzuma, ya bazama a cikin jejin yana neman yaron, sai da ya shafe tsawon lokaci ya na nemansa, amma ba amo ba labari.

Zuwa lokacin gajiya ta gama riskar dukkan gaɓɓan jikinsa, gun bishiyar ya dawo ya zauna don ya huta, sa'annan ya nufi gida.

¥¥¥™™™

Yaro Abdul kuwa, tun lokacin da ya fahimci cewa Maharbin nan ba zai taimaka masa ba, kawai sai ya miƙe daga inda ya yasu, ya ci gaba da tafiya yana sharar ƙwalla, zuwa lokacin zazzaɓin dake jikinsa ya tsananta, amma saboda kafiya da ƙarfin hali irin na shi ya ci gaba da tafiya, cikinsa tamkar ba na shi ba saboda yunwa....

Komai rashin imanin mutum idan ya haɗu da Abdul a cikin wannan yanayin, tilas ya tausaya masa, saboda yanda ya ƙwarjame ya yi duhu sosai, dauɗa ta gama samun muhalli a jikinsa, tufafinsa kuwa har sun canza launi saboda datti.

Da yake lokacin da zai baro gidan Kande tufafin da ya baro gida dasu ne ajikinsa, tun barinsa gida sau ɗaya aka wanke su, lokacin da Basiru zai yi wanki ya haɗa dasu, nan ma ba don sun fita ba, tunda yaron bawai ya iya wankin ba ne sosai...

Wandon jins kalar blue black ne a jikinsa da riga light blue, amma wandon har ya fara dafewa saboda datti, rigar kuma ta fara zama brown.

Yau kusan kwana goma kenan rabonsa da gidan Kande.

Haka ya ci gaba da gangarawa, yana cikin tafiya kawai sai ya yi tuntuɓe da wata baƙar leda.

Cikin rawar jiki ya durƙusa tare da ajiye sandarsa, ya zauna.

Janyo ledar ya yi ya buɗe ta, sai ga lafiyayyar shinkafa da wake a ciki, dama ledar kusan a cike take.

Cikin tsananin murna mara misaltuwa Abdul ya ɗaga hannu sama ya ce, "Allah na gode ma."

Nan da nan ya fara afa shinkafar nan, tamkar mayunwacin zakin da ya jima bai yi kalaci ba.

Duk da cewa baya da lafiya sai da ya cinye shinkafar tas sa'annan ya miƙe don neman ruwa.

Abun mamaki, sai ya ji rabin ciwon ya tafi, har wani irin ƙarfi ya ji ya zo masa.

A bayyane ya ce "Kai! Dama ashe yunwa ta nika ji, ita at rabin ciyon." Hahaha, ya bushe da dariya shi kaɗai cike da nishaɗi ya matsa gaba.

Can zuwa rabin sa'a yana tafiya, idonsa ya sauka kan wata kwalba cike da ruwa, murmushi ya bayyana a fuskarsa, ya je ya ɗauko ta, ya buɗe ya kwankwaɗa sai da ya sha fiye da rabi sannan ya wanke hannunsa ya tafi da sauran.

Abinda Abdul bai sani ba shine, duk abin nan da ke faruwa aljani Barkuza ya na tare da shi, kuma shine asalin aljanin da ke tare da shi ya na gadinsa tun yana gida, shine ya ƙwace alewar hannun Abdul ya yar, lokacin da yaya Sunusi ya kawo masa alewa mai guba.

Haka a lokacin da su Gumush suka sace Abdul ya ɗan ɗaga zuwa wani guri, da ya dawo ya tarar ba yaron shi ne ya ba zama nemansa, har ya taddo inda yake.

Tun lokacin ya na tare da shi, har zamansa a gidan Kande, ya bar yaron ne ya ɗanɗana wahalar rayuwa, domin ya san zafi da ɗacin rashin iyaye da kuma wahalar nema saboda rayuwarsa ta gaba ta inganta.

Shi ne ya ajiyewa Abdul wannan shinkafar da ruwa da siyo a kasuwar wani ƙauye dake kusa da su, ya ajiye masa a fakaice yanda ba zai tsorata ba.

Shi kuwa Aljani Mazkud shi ne ya shiga jikin Abdul a kwanaki uku na farkon zamansa a jeji, haka zalika shi ne wanda ya je gidan Kande ya tsorata ta, shine kuma wanda ya bi Maharbi a baya ya tuna masa da yaro Abdul.

¥¥¥¥¥¥™™™™™™

A Sokoto kuwa, labari ya sha bam-bam da na baya, domin ko a cikin satin nan biyu abubuwa da dama sun faru marasa daɗi, domin kuwa Hasina ta yi nasarar mallake Alhaji Munir, yanzu fa sai abinda take so yake yi, bayan kwana uku da zuwansa station 'yan sandan suka zo gida domin sake gudanar da bincike, buɗar bakin Alhaji sai cewa ya yi "Ku tahi ɗai ofisa ni ba ni da wani ɗa da ya ɓace don kuwa ban ma taɓa haihuwa ba, ga matata nan ku tanbaye ta."

Ƙwalalo ido waje suka yi su duka, suka cika da tsananin mamaki, to miya ke damunsa? Shekaranjiyan nan fa ya je da buƙatar a tsananta bincike a kan ɗansa yanzu kuma ya ce baya da wani ɗa.

Ofisan ya shanye mamakinsa ya ce "Alhaji ko dai ka sha'afa ne? Nina hwa Asp Bello Yahaya, wanda case ɗin ɓacewar ɗanka Abdul yake hannuna."

Alhaji Munir ya kalle shi a ɗage cikin wata irin murya ya ce "Na ce maka ni ban taɓa haihuwa ba... Hajjiya ko na taɓa haihuwa?" Ya ƙarashe zancen ya na kallon Hasina.

Cike da izza da isa ta ce "Har sai ka tambaya Munir? Ni ce dai matarka kuma ban haihu ba."

Maida dubanta ta yi ga tawagar 'yan sandan ta ce "Ofisa kuna iya tahiya mu ba mu da wani yaro da yat ɓace."

Har ogansu zai buɗi baki ya yi magana, Hasina ta ɗaga mishi hannu cikin tsawa ta ce "Kuna hita ko sena jissat muku kwandon rashin mutunci?"

Kallon inda Alhaji ke tsaye suka yi, ya na nan a gun baya da niyyar motsawa bare ya yi yunƙurin dakatar da ita, tsaye kawai yake kamar wani soko.

Ganin hakan ya saka ta ce a ranta "Bari na nuna muku ƙarfin ikona."

Kallon Alhaji ta yi cikin isa da bada umurni ta ce "Munir shiga cikin gida."

Ba musu ya juya zuwa ciki, tamkar yaron da uwarsa ta masa umurni.

Nan take idon ogansu ya fara tara ƙwallar tausayi, "Tabbas ta na ƙasa tana dabo." Ya faɗa a ransa tare da juyawa bai ce komai ba ya yi gaba, sauran tawagarsa suka bi sa a baya, yayinda Hasina ta raka su da harara...















RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*

👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

*AND NOW*
*HALITTAR ALLAH CE*

PAGE 41-42

Abdul kuwa ya cigaba da nausawa cikin jeji ba tare da gajiyawa ba, duk da cewa ita kanta sandar hannunsa ta ɗanɗana kuɗarta, don zuwa wannan ranar har rufin sandar na ƙasa ya guntule, duk ta moƙaɗe a wasu gurare, tsabar faɗi tashin da yake a cikin duwarwatsu.

Ƙafarsa kuwa, tun yana damuwa da zogin da take masa, har ya zo ya daina damuwa, tuni ma ƙafar ta ɗage sama, saboda rashin kulawa.

A haka ya cigaba har bayan shuɗewar wasu kwanaki.
Watarana yana cikin tafiya ya hango alamar wani gari a gabansa.

Farinciki ne ya cika zuciyar Abdul, sai sauri yake zubawa cike da zumuɗin ganin ya isa garin.

Tafiya kawai yake bai yi aune ba sai ji ya yi ya yi tuntuɓe da wani murgujejen dutse, kansa ya bugu da dutsen, wata uwar hantsilawa ya yi, har sai da ya tsallake dutsen, ba shiri ya baje a ƙasa magashiyan, jini kuwa sai tsartuwa yake daga goshinsa.

Daga nan bai kuma sanin inda kansa yake ba.

**************

Wata tsaleliyar mota ce ke tafe, sai sharara gudu take tana nufo gun, da dukkan alama matuƙin motar yana sauri ne.

Saura kaɗan ya taka yaron,ba shiri ya taka burki yana sakin ajiyar zuciya da alama ya firgita.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!" Shi ne kaɗai abinda mutumin ke maimaitawa.

Buɗe motar ya yi tare da fitowa ya yo kan yaron.

Hannu ya saka ya birkito shi da nufin ya taimaka masa.

Ba shiri ya janye hannunsa, don yin arba, da mummunar halittar yaron, ja da baya kaɗan ya yi, haƙiƙa ya kaɗu matuƙa da ganin wannan yaron.

A ransa ya ce "Ko dai aljani ne?" Ras! Ƙirjinsa ya buga, tsayawa ya yi jim, kafin ya maida dubansa ga yaron, ganin goshin yaron nata zubar da jini ya saka ya kai hannu ya ɗauki yaron bakinsa na furta duk addu'ar da ta zo mashi.

Ya yanke a ransa zai tafi da wannan yaron zuwa cikin gari don kai shi asibiti, ko da kuwa aljani ne, yasan Allah zai kare shi daga sharrinsa, don shi ya yi ne saboda Allah.

Motarsa ya nufa ya saka yaron a gidan baya, ba tare da ya lura da ƙafar yaron ba, bare har ya fahimci cewa gurgu ne ya nemo masa sandunansa.


Zagayawa ya yi ya shiga mazaunin direba, sannan ya ja motar da gudu ya ci gaba da tafiya cikin sauri, dama can a hanzarce yake, yanzu kuma ga yaron nan da yake ƙoƙarin ceto ransa.

A haka yata zuba gudu a hanya, har Allah yasa ya isa cikin garin Kano, kai tsaye asibiti ya nufa da yaron, dama can kafin ya ƙarasa asibitin ya kira wani abokinsa likita sanar mashi buƙatarsa, don haka bai sha wata wahala ba, yana zuwa aka karɓi yaron.

******™™™™™™™™™

Su kuwa su yaya Bilya yanzu duniya ta masu daɗi, sai cin karensu suke ba babbaka.

Mizbahu da a kullum yake cikin takaicin wannan hali na 'yan uwansa, da kuma mamakin abinda ya sami Munir ya susuce haka, ya zubawa su yaya Bilya ido suna ɓarnatar masa da dukiya haka.

Da dai ya ga abun bana ƙare ba ne, ya shirya watarana bayan Magriba ya tarar da Alhaji Munir a gida, tunda yanzu gidan iyayensu da yake zuwa kullum ma ya daina, sai can ba a rasa ba zaka gan shi.

A harabar gidan ya tarar da Munir ɗin kan kujerar roba, ya yi shiru ya zuba tagumi kamar mai son tuna wani abu.

"Assalamu alaikum." Ya faɗa.

Munir bai ko ɗago ba, da alama bai ma ji sallamar ba.

"Assalamu alaikum." Mizbahu ya kuma faɗa, a lokacin da ya ƙarasa daf da Munir ɗin.

Nan ma bai ɗago ba, sai da ya dafa kafaɗarsa, sannan ya yi firgigit, kamar wanda ya dawo daga duniyar mummunan mafarki.

"Tunanin mina kaka yi haka Munir?" Mizbahu ya faɗa.
Murmushi ya yi ya ce: "Sannu da zuwa yaya ashe har ka ƙaraso."

Girgiza kai ya yi alamun tausayawa ƙanin nasa, sannan ya ɗauko ɗayar kujerar dake nesa kaɗan dasu, ya ajiye kusa da Munir ya zauna.

Kallon Ƙanin nasa ya yi ya ce; "Alhaji, nasan kana sane da irin ɓarnat da su yaya Bilya sukai da dukiyakka, shin mi yassa har yanzu baka ɗauki mataki ba?."

"To ni kam yaya mi zan musu? Ai 'yan uwana na, miye a ciki don sun ci dukiyata, tunda ba nida Magaji, ko na mutu suna dai at magadan." Cewar Munir.

Da mamaki Mizbahu ke kallonsa, "Ba kada Magaji hwa nij-ji ka ce." Ya faɗa.

Ɗaga mashi kai ya yi alamar tabbatarwa.

Nan fa mamakinsa ya ƙaru, tabbas ɗan uwansa na cikin wani hali, ko dai ɓatar ɗansa ce ta zautar dashi har haka?.

Shanye mamakinsa ya yi ya ce "In har baka da ɗa, shi kuma Abdul ɗin hwa, wa at Babanai?"

Da kallon mamaki Munir ya bi yayan nasa, sannan ya ce "Wa at Abdul kuma yaya? Ni hwa ban taɓa haihuwa ba ko ka mance?."

Zuwa yanzu mamakin Mizbahu ya rikiɗe zuwa tsoron lamarin ƙanin nasa, tabbas akwai lauje a cikin naɗi, don kuwa ruwa baya tsami banza, amma ko miye ya yi alƙawarin bankaɗo shi, don kuwa shi ba waɗanda yake zargi sama da su yaya Sunusi, don haka bai ko tsaya sun ƙarasa maganar data kawo shi gidan ba, sanin hakan bai da amfani a yanzu, yasa ya miƙe tare da yiwa Ƙanin nasa sallama ya tafi.

*®®®©©©©©©©*


Bayan an shigar da Abdul ɗakin majinyata Mahmud ya wuce office ɗin likita Yasir abokinsa don tattauna matsalar.

Dr Yasir na zaune kan kujerarsa Mahmud ya shigo, su ka kuma gaisawa, sannan ya zauna kan kujerar dake fuskantar ta Yasir.

"Likita bokan Turai, ya aikin kuma?" Cewar Mahmud.

"Aiki gashi nan muna fama, Mutanen Kd yaushe a gari? Da alama ba don matsala ta kawo ka ba, ba zansan ka shigo garin bahar ka tafi."

Dariya Mahmud ya yi ya ce "Ba haka bane, tafiyar ce ta gaggawa, nima wani Meeting ɗin gaggawa ne ya kawo ni nan garin, ƙarfe biyu za'a fara, ina son magriba ta riske ni a garin Kaduna, don kuwa a can ma ina da wata fita ta musamman bayan isha'i, kasan bana son saɓa alƙawari."

Yasir ya yi ɗan murmushi da cewa "Hakane."

"Amma wannan yaron fa, a'ina ka samo shi?"

Fuskarsa ta canza zuwa yanayin damuwa ya ce "Wallahi akan hanyata ta zuwa nan na tarar da shi kwance a tsakiyar wani titi mara hayaniya, saura kaɗan na taka shi, Allah ne ya kiyaye, da na ga yana neman agajin gaggawa yasa na kawo shi nan."
"Da fatar dai ba wata babbar matsala."

Yasir ya ce "Ba wata babbar matsala bace, ya samu babban rauni a goshinsa, muna kan bincike dai ko zamu gano wata matsalar dabam."

"Ohk, Ni bari na shiga gari na shirya don zuwa Meeting ɗin, kaga yanzu har ƙarfe ɗaya ta yi." Mahmud ya faɗa tare da miƙewa, ya miƙa wa Yasir hannu suka kuma yin musabiha, sannan ya juya.

Har ya kai ƙofa, kamar wanda ya tuna wani abu ya waigo ya ce "Don Allah Abokina ka samarwa yaron nurses da zasu kula dashi ko da zai farka kafin na dawo."
"Insha'allah, baka da matsala akan wannan." Yasir ya faɗa.
Shiko ya juya ya fice daga office ɗin.

A cikin ɗakin majinyatan Abdul ne kwance kan gadon Asibiti, annaɗe mishi kai da bandage bayan an ɗinke gun.

A hankali ya buɗe idonsa dake kallon sama, sai ya ganshi kwance a guri mai rufi, nan fa ya fara tunani "To yanzu kuma me ya same ni?, Ina ne nan?"
Da sauri ya tashi zaune yana kuka.

Sister aysher ta yo kansa tana lallashinsa, har aka samu ya ɗan yi shiru.

®®®®®®®®

Shi kuwa Mahmud bashi ya dawo ba, sai wuraren ƙarfe biyar na yamma.

Koda ya dawo ya tarar Abdul ya tashi, don haka ya matsa kusa da yaron yana masa sannu.

"Sannu yaro, ya jikin?"
Nan fa Abdul ya shiga rarraba ido, sai a lokacin ya ji kansa ya masa nauyi, ko da ya shafa sai ya ji bandeji, nan fa ya saka sabon kuka...

Daƙyar da siɗin goshi Mahmud ya samu ya ciwo kan Abdul ya daina kukan.

Anan yake tambayarsa "Yaro ya sunanka?"
Ya ce "Sunana Abdul."
"Ina ne garinku, sannan ina iyayenka? Ya kuma tambayarsa.

Nan fa ya yi shiru kamar mai son tuna wani abu, can kuma ya ce "Bansani ba, Ni dai nasan cikin daji nika rayuwata ni ɗai, tunda Mama Kande takkore ni daga gidanta."

Zaro ido Mahmud ya yi, jin yaron ya ce a jeji yake rayuwarsa shi kaɗai, har ya buɗi baki zai ce wani abu, Yasir ya turo ƙofa ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.

"Wa'alaikumus salam." Sister aysher ta faɗa.

Shi kuma Abdul a dai-dai lokacin fitsari yake ji sosai, nan ya shiga dube-dube ko ya ga sandunansa amma wayam, nan ya shiga damuwa, sai ƙara raba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login