Showing 9001 words to 12000 words out of 42870 words
tare da ficewa daga gidan baki ɗaya.
Tun daga ranar Alhaji Munir ya dakatar da duk wasu harkokinsa ya zauna a gida domin bawa Abdul kyakkyawar kulawa.
A lokacin ne kuma ya tara 'yan uwansa ya kuma ɗora su a kan kasuwancinsa domin su cike guraben da ya bari, cikin Sa'a ya bawa Mizbahu kula da gun siyar da motocinsa, su kuwa sauran ya bar su a kasuwa.
Alhaji Munir bai san cewa ya bawa kura fiɗa ba ne.
Hakan ya baƙanta masu rai ba kaɗan ba, duk da cewa Mizbahu jininsu ne uwa ɗaya uba ɗaya, amma ba haka suka so ba, sun so ace ɗaya daga cikinsu ne ke kula da wurin ta yadda zasu yi barnarsu da kyau, amma a yanzu suna da tabbacin Mizbahu ba zai basu damar da za su yi handama ba.
A haka Alhaji Munir ya ci gaba da kula da tilon ɗansa, shi ke masa wanka, wanki, ba shi madara da duk wata ɗawainiya da ya kamata uwa ta yi, yayin da 'yan aiki ke hidimar gyara gidan tare da dafawa Alhajin abinci.
A takaice dai sai da ya shafe tsayin shekaru biyar ba ya fita ko'ina kuma baya aikin komai sai na kula da yaronsa, zuwa lokacin bakin jama'a ya yi yawa a kansa, sai takura masa ake da zancen aure, musamman Hajiya inna ta sako shi gaba da maganar aure, acewarta bai kamata ya zauna haka ba mata ba, ko don wannan yaron ya kamata ya yi aure a samu mai kula da shi.
Daƙyar da siɗin goshi ta ciyo kan Munir ya yarda zai yi aure, amma ba don soyayya ba, sai don wannan yaron nasa da yake buƙatar tasowa acikin kulawar mace, don kuwa yasan ba zai taɓa maye gurbin uwa ba, sai dai ya yi iya abinda zai iya.
Tuna hakan da ya yi ya saka ya bawa Hajiya inna dama ta nemo masa bazawara mai hankali da imani ya aura.
A cikin shekarar ne ta haɗa shi da Hasina 'yar ƙawarta, domin a'iya abinda ya bayyana a gare ta yarinyar tana da kirki matuƙa, ga haƙuri, ladabi da biyayya da tausayi, shiyasa ta zaɓa masa ita a matsayin wacce zata riƙe masa amanar ɗansa, bata sani ba ashe kura ce lulluɓe da fatar akuya....
More comment more typing..
Idan na ji shiru kuma zaku ji shiru🤷🏻♀️
Follow me on wattpad @ummu inteesar
RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹
*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
*DEDICATED TO: HAUWA'U S ZARIA (ANTY HAUWA)
SHUGABA TA GARI MUNA ALFAHARI DA KE.
*JINJINA:*Jinjina ta ban girma ga yaya Yusuf gumel, haƙiƙa ba Ni da wani abun faɗa face godiya a gareka da addu'a, Allah ya baku zaman lafiya da kai da amaryrka tare da zuri'a ta gari.
Godiya marar adadi.
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 13-14
Ba a wani ɓata lokaci ba aka ɗaura masu aure, kasancewar dukkaninsu ba yara ba ne, bayan sati biyu da ɗaurin auren amarya Hasina ta tare a ɗakinta.
Washe garin ranar tariya, Alhaji Munir ya zaunar da Hasina ya na mata nasiha da riƙon amana, ya kalle ta sosai ya ce "Da farko dai ina miki Barka da shigowa wanga gida mai albarka, da fatan Allah ya ba mu zaman lahiya mai ɗorewa, bayan haka, ke riga ke san komi akaina, ke san ina da yaro Abdul ke san kuma na gaya miki ba shi da lafiya, amanata ne shi ɗin, yanzu kuma zan damƙa wannan amana tawa a gare ki, a matsayinki na uwa, da fatar za ki tarbiyyantar da shi, ki kuma riƙe shi amana tare da nuna mai soyayya tamkar ɗan cikinki."
Hasina da kanta yake sunkuye, sai lokacin ta ɗago da murmushi a fuskarta ta ce "Insha'allah Alhaji na maka alƙawarin zan riƙe shi amana ai shi ɗa na kowa ne, da ƴaƴa da dukiya ba asan mai morarsu ba."
Dan tsagaitawa ta yi a lokacin da Alhaji Munir ke saka mata albarka, can ta ce "Alhaji wai ina yaron nawa ne? Bangan shi ba tun jiya."
Miƙewa ya yi ya je boys quaters da kansa ya karɓo Abdul da ya bari hannun Ladi kwana biyu, ya shigo falon yana janye da hannunsa.
Miƙewa ta yi cikin hanzari ta nufo su tana cewa "oyoyo! ga ɗana."
Ita a zatonta ko yaron bashi da lafiya ne kawai, kamar yanda mahaifinsa ya gaya mata.
Sai dai me ta na matsawa kusa aka yi rashin Sa'a idonta suka sauka akan mummunar halittar fuskarsa.
Yam! Ta ji tsikar jikinta ta tashi, rintse idonta ta yi da ƙarfi a ranta ta na faɗar "Subhanallah! Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!"
Can kuma kamar wacce aka mintsina ta yi saurin buɗe idonta, ta na wanyancewa da faɗar "Bari in buɗe idona in ga kyakkyawan yarona, kasan in za'a wa mutum suprise dole ya ruhe idonai."
Nan da nan Alhaji ya sake fuska saɓanin ɗazu da ya tamke ta saboda ganin Hasina ta rufe ido, ya ce "To ai ga shi nan yanzu, amana ne shi a hannunki, ina sonai matuƙa, dan haka ina ƙara roƙonki da ki riƙe min shi amana don Allah, ke ga sai ki jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, ga lada ga la'ada."
Matsawa ya yi kusa da Abdul da tun shigowarsu ɗakin ya yiwa Hasina ƙuri da idonsa ɗaya, ya sunkuya ya ce "Abdul yaron kirki, ga mamakka, nasan baka santa ba koh?"
Yaron ya ɗaga kansa saba alamar eh.
Baban ya ce masa "To ita at mamakka ka ji, ka yi mata biyayya, ita za ta rinƙa maka wanka da wanki da duk abinda ni ka maka da."
Ita kuwa da ta ga Alhaji ya tsinke yana hira da ɗansa kawai sai ta sulale zuwa ɗakinta, sai haƙi take kamar wacce ta shiga gasar tsere.
Ita kam a tsayin rayuwarta bata taɓa cin karo da mummunar halitta irin wannan ba, wai kuma a haka Alhaji Munir ke yaudarar kansa da cewa za ta kular masa da wannan dodon? Inah! Ai sam ba za ta saɓu ba, bindiga a ruwa.
Ita fa ta zo nan gidan ne don ta huta ba don ta yi bauta ba, amma idan yasan wata ai bai san wata ba, za ta ɓullo masa ta bayan gida ne.
Da wannan tunanin ya shigo ya same ta a ɗakin.
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
A haka rayuwar ta ci gaba da gangarawa, Alhaji Munir ya ɗauki yarda gaba ɗaya ya bawa matarsa Hasina, don haka yanzu ya koma a bakin kasuwancinsa ba tare da fargabar komai ba, wai shi a dole ya samu mata mai amana, don ganin irin tarairayar da take yiwa Abdul a gabansa, ya manta cewa ba a yabon ɗan kuturu sai ya shekara goma da yatsa.
'Yan uwansa ba su ji daɗin wannan komawar tasa kasuwa ba, domin ya dawo ya maye gurbinsa da suka cike.
Sun masa ɓarna mai yawa a dukiya, sun saci ta sata sun ci ta ci, ba tare da yasan me suke aikatawa ba, sai bayan komawarsa ya tarar da wannan ɓarnar, ganin shagunan sun rame sosai, ya saka ya tara su don yin bincike.
Ganin ya titsiye su sai suka yi masa karyar cewa ɓarayi ne suka shiga shagunan da dare suka yi sata, a lokacin sun so su gaya masa, amma gudun kada su tashi hankalinsa a yi haihuwar guzuma ɗa kwance uwa kwance, ya saka suka tsuke bakinsu, kuma wai sun yi iya ƙoƙarin su ganin komai ya dawo dai-dai amma hakan ya ci tura.
Ba dan ya yarda da waɗannan tatsuniyoyin na su ba ya sallame su suka tafi, a ransa yake cewa "Da ba don ku 'yan uwansa ba ne, da ba abinda zai hanani yin ƙararku, amma idan na yi hakan kamar na daɓawa cikina wuƙa ne."
A bangaren da ya bar yaya Mizbahu kuwa, ya ji daɗi sosai yanda ya tarar da komai na tafiya yanda ya kamata, ga kuma uwar riba mai yawa da aka samu, don haka ya kasa janye yaya Mizbahu a gun.
Wannan abun ya baƙantawa sauran 'yan uwansa rai ba kaɗan ba, don haka suka fara tunanin ko zasu haɗa da mizbahun ne a cikin list ɗin maƙiyansu.
©¥¥¥¥¥¥¥
Bayan shekara shida Abubuwa da yawa sun faru tsakanin farin ciki da saɓaninsa, acikin abubuwan da suka faru kuwa har da shiga bokaye da 'yan tsibbu da 'yan uwan nasa suka yi domin su ga bayansa.
Akwai wata rana ma da suka saka ma Abdul magani a abinci ya ci, ya sha ciwo sosai kamar zai mutu, amma da yake yana da sauran shan ruwa a gaba sai ya rayu, tun wannan lokacin ne kuma bai kuma lafiya, don kuwa baya cikakken wata bai yi ciwon da zai danganta shi da asibiti ba, maganin ya masa illa sosai a jiki.
A cikin wannan jinyar ce aka samu akasi, watarana da aka masa allura sai ƙafarsa ɗaya ta shanye, anyi maganin an har an gaji amma ƙafar bata miƙe ba.
Wannan ita ce mummunar ƙaddara ta biyu da ta afku a rayuwar yaron, hankalin mahaifinsa ya kai kololuwar tashi, da ya ga an shafe shekaru biyu a haka sai ya siyawa yaron keken guragu don sauƙaƙa masa.
¥¥¥¥¥¥¥¥
Hasina kuwa ta ci gaba da yiwa Alhajin zagon ƙasa ba tare da saninsa ba, ita fatanta bai wuce ta mallaki dukiyarsa gaba ɗaya ba, don haka ta shiga sahun maƙiyansa na ɓoye masu san hallaka shi shi da yaronsa.
Ta ko'ina farautar rayuwar ɗan talikin yaron nan ake, amma da yake Allah shi ke bawa bayinsa na gari kariya, sai gashi har yau sun kasa samun nasarar hallaka shi.
*Dawowa da ga labari.*
Ranar wata Laraba da misalin ƙarfe 10:05 na safe Abdul ne zaune kan kekensa a ƙofar ajinsu, wasu 'yan yara sa'aninsa ne suka zo wucewa, cikin rashin Sa'a keken ta taɗe ɗaya daga cikinsu ya faɗi bakinsa ya fashe, sauran suka nufe shi don su tada shi.
Abdul ya kalli wanda ya faɗin ya ce "Don Allah ka yi hanƙuri ba da gangan na ba."
Ɗai daga cikin yaran ya ce "Babu wani nan baƙin mugu, mummunan banza, da gangan kat aje kekenka bisa hanya tun da ka na son ka maida kowa gurmu irinka."
Sadik abokin Abdul ya yi saurin matsowa ya ce "Kai Shamsu, mi at haka? Halam ku baku da tausai, ai dai ba shi yat maida kai nai haka ba, kuma baku wuce zama haka nan ba, kuma tunda ka ce da gangan na, to an ture, ka yi abinda zaka yi."
Daga jin haka Shamsu ya matso kusa dama rigimammen yaro ne, nan fa faɗa ya kacame dambe suke sosai.
Su na cikin haka sai ga wani malami ya zo wucewa, tsayawa ya yi, ya raba su tare da neman ba'asi.
Abdul sai kuka yake ganin ana rigima saboda shi.
Sadik ya kwashe komai ya gayawa malamin, nan take malamin ya bawa Shamsu rashin gaskiya kuma ya masa bulala biyar, kasancewar a makarantar ba a raga maka idan a ka kama ka da laifin takurawa ko ciwa nakasasshe zarafi, acewar malaman makarantar, makarantar ta nakasasshi ce, masu lafiyan sakaya su kawai aka yi ba don komai ba, sai don kada nakasasshin su ga an ware su ko an nuna bambanci tsakaninsu da masu lafiya...
Wannan abun da ya faru yau a makaranta ya saka Abdul ya ƙara jin tsanar karatun, ga shi yaro ne mai hazaƙa har yafi masu lafiyar saurin fahimta.
A ransa ya ce "Yau kam, dole in faɗawa Abbuna ya cire ni makarantar na gaji, tunda kowa baya sona gwanda na zauna gida."
Da aka tashi daga makaranta Baba direba ya zo ya ɗauki Abdul zuwa gida kamar kullum.
Da da dare bayan Alhaji Munir ya dawo, suna cin abincin dare shi da iyalinsa, Abdul ya kalle shi ya ce "Abbu ni don Allah ka cire ni dam-makarantar nan ban son karatun na gaji." Ya faɗa ya na shirin yin kuka.
Baban ya dube shi cikin kulawa ya ce "Haba ɗana! Mi anka maka kaka son barin makaranta bayan Kana da ƙoƙarinka?"
Murya na rawa yaron ya ce "Ni dai na gaji tun da kowa bai sona an tsane ni, gara in baz-zuwa cikin mutane, ɗazun ga Shamsu yacce min mummuna baƙin gurmu."
Ya faɗa ya na fashewa da kuka.
Cikin tsananin tausayi Baban nasa ya kalle shi ya ce ".......
Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal
More comment more typing....
RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
*DEDICATED TO: All members of HALLITTAR ALLAH CE FANS GROUP
Ngd da adduoinku a gare ni, Allah ya bar zumunci, much love🥰🥰
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 15-16
Cikin tsananin tausayi Baban nasa ya kalle shi ya ce "Ka ƙara hanƙuri yarona, kakka damu da maganar Shamsu, insha'allahu za ka ji dama ƙahwakka zata miƙe, yanzu dai ka cigaba da zuwa makaranta, ka ga saura kaɗan ku ƙare primary, kuna ƙarewa shikenan sai ka bar zuwa ka ji."
Da wannan zantuka ya samu ya yiwa Abdul wayo, har ya yarda zai cigaba da zuwa makaranta.
Bayan kamar sati ɗaya da yin haka Abdul ya kwanta rashin lafiya wacce ta sada shi da asibiti, wani irin zazzafan ciwo ciki ne ke damunsa, a haka ya share sati Uku a asibiti ya na jinya, inda Hajiya Hasina ke kula da shi a asibiti bayan Alhajin ya ɗaga zuwa kasuwa ko wani guri cikin asibitin.
A zahiri idan ka ga yanda Hasina take yi, za ka rantse da Allah ta na kula da shi tamkar ɗan cikinta, sai dai wannan fuska ce da take ara tana nunawa mutane, idan ya rage ɗakin daga ita sai shi, to fa a nan za ta fitar da fuskarta ta ainahi, ta dinga zubawa yaron ranƙwashi a kai kenan, ita ko tausaya masa ma bata yi, saboda zuciyar kafirai ke gare ta.
Bayan ya warke a ka sallame su zuwa gida.
Washegarin ranar da misalin sha biyu na rana, Abdul ne kan kekensa ya na ta yawo a harabar makeken gidansu shi kaɗai, sai wasarsa yake abinsa, domin tuni ya saba da kaɗaici.
Hasina ce ta zo za ta wuce zuwa ɗakinta, cikin rashin Sa'a Abdul ya taka mata ƙafa da kekensa ba tare da sani ba.
Wata shegiyar ƙara ta saki tare da juyowa a kufule, ta saka hannu biyu ta hantsilar da keken cike da rashin imani.
Jikake Gwaraf! Abdul ya faɗi ƙasa, hancinsa ya ƙumu da ƙasa take hancin ya fara feshin jini.
Yaron ya zabga ihu a wahalce don jin wata irin azaba da ya yi.
Takowa ta yi cike da mugunta ta zo inda yake kwance a kife kan gefen kuncinsa na dama, ta so ta kama kunnensa ta mirɗe, sai dai bangaren hagun dake sama ba shi da kunne nan ma a shafe ne, ganin haka ya saka ta birkito da shi zuwa bangaren dake da halittar kunnen, ta kama kunnen ta mirɗe sosai ta na faɗar "Wato kai dan ubanka ni za ka take ma ƙahwa? Ka ga shegen yaro, dama irinku na aka cema gurmu kahi mai ƙahwa iya shege, ɗan nema mai shafaffar huska, in kak-ƙara takina sai na cire maka sauran kunne gudan da yarrage ma, in ga ta iskanci."
Shi dai bawan Allah Abdul bai ce komai ba, zafin ya haɗe masa biyu ga zafin gumuwar da ya yi gana mirɗe masa kunne da ta yi, wanda har zuwa yanzu bata saki kunnen ba.
Jin shiru yasa ta ci gaba da cewa "Shina ina magana kak-ƙyale ni? wato ga mahaukacciya koh? To wallahi bari ka jiya duk ranar da kat kuskura kat hwaɗama babanka ko wani ina maka mugunta, wallahi sai na kashe ka...."
Ta na cikin wannan sababin da jiyo sallama a ƙofar shigowa tsakar gidan, a hanzarce ta saki kunnensa tare da tallabo shi ta na faɗar "Sannu! Sannu ɗan ga, ba ka dai ji ciwo ba koh?"
Dai-dai lokacin ne kuma Salamatu ta iso tsakar gidan, kai tsaye gun su ta nufa ta na faɗar "Subhanallah! Mi ka hwaruwa nan?"
Ido cike taf da ƙwalla Hasina ta ɗora Abdul kan kekensa ta na faɗar "Allah sarki bawan Allah!, sannu ka ji!." Ta faɗa, sannan ta juyo ga Salamatu ta ce "Wallahi hwaɗuwa yay-yi shina hancinai yat hwashe."
Ta na maganar ta na ƙoƙarin shanye ƙwallarta, idan ka ga yanda take yi ba za ka taɓa tunanin cewa ita ta kayar da shi ba.
"Allah sarki! Sannu Abdul, Allah tsare gaba." Salamatu ta faɗa.
Tura keken Hajiya Hasina ta yi Salamatu na miye da ita har suka shige falon, inda ta bar Salamatun a falo ta je don kai Abdul ɗakinsa.
Bayan ta shigar da shi ɗakin sai da ta falle shi da kyakkyawan mari a ɓangaren da yake a shafen, daman bata da gurin da take duka a jikinsa sama da nan, acewarta ya fi daɗin mari nan da yake a shafe sumul kamar siminti.
Sai da ta gama zazzare masa ido tare da ƙara tsorata shi a kan idan ya faɗa kashinsa ya bushe, sannan ta fito daga ɗakin ta na shimfiɗa yanayin damuwa a fuskarta.
Anan inda ta bar Salamatun a nan ta same ta, zama ta yi don su gaisa.
"Sannu Hajiya, ya gida, ya ƙoƙarin kula muna da wanga yaron." Salamatu ta faɗa.
"Alhamdulillah! Ƙoƙari kam, anan nan ana yi, ya anka iya? Ai rayuwa ce." Ta mayar mata da amsa.
Salamatu ta dube ta ta ce "Hajiya haƙiƙa yaron nan Abdul yana matuƙar ba Ni tausayi, idan na tuna tun haihuwarsa har zuwa yanzu bai san daɗin lafiya ba, gashi ya rasa mahaihiyarshi tun yana jariri, daga baya kuma lalurar gurmunta ta same shi, har kuka nake masa idan na tuna wallahi."
Hasina ta marai-raice fuska kamar da gaske ta ce "To ya anka iya, dama bawa bai isa ya guje ma ƙaddara tai ba, shi kuma haka tashi ƙaddarar take, ana ta neman magani amma ciwo sai gaba ya kai."
"Kuna zuwa asibiti ko Hajjiya?" Ta tambaya.
Ta ce "Haba Yaya Salamatu! sanin kanki na yadda Alhaji ka son Abdul bai zuba mai ido haka kurum, bayan yana da kuɗɗin da zai biɗar mai magani, ke gamu kullum yawon asibiti, ɗa kamat ɗan roƙo? Yanzu dai wani sati ma zamu komawa asibiti can Kano, don a mai aikin ƙafar a gani ko Allah na