Showing 6001 words to 9000 words out of 42870 words
mutuwarsa suka ji, Munir da Mizbahu da ƙannensu mata sun sha kukan wannan rashin da suka yi, yayin da su kuwa su yaya Bilya ko a kwalar rigarsu, a ransu ma cewa suke tafi nono fari, ai gwanda ya mutu tunda dama ba sonsu yake ba ya fi son Munir, shiyasa ya ɗauke shi ya kai shi inda zai yi arziƙi.
Bayan an yi bakwan mutuwar Alhaji Abbas, iyayensu mata suka tattaro su tare da ƙara jadadda masu wasiyar mahaifinsu da ya bari.
Amma su kam su Sani, inda suka ji maganar anan suka bar ta, ba ɗaya da ta shiga kunnensu, sai ma wutar hassadar da ta ruru a ransu, sai dai sun danne hakan a can ƙasan ransu.
Bayan kamar wata uku da mutuwar uban, suka takura akan a raba gado a bawa kowa nasa, ba don iyayensu mata sun so ba, haka aka kira malamai suka raba musu gadon saboda sun takura.
Da aka zo rabon gadon Munir ya kawo shawarar me zai hana a bar wannan gidan da iyayensu suke ciki don su ci gaba da zama, ko ba komai bai kamata don Babansu ya mutu a siyar da gidan ba, amma fafur su Sani su ka ƙi suka ce sai dai a siyar.
Ganin hakan ya saka Munir ya siyawa iyayensa gida a unguwar Miyatti Allah domin su koma can da zama, bayan siyar da wannan, haka kuwa aka yi.
Bayan rasuwar mahaifiyarsu da kamar shekara ɗaya Mamansa ta rasu ita ma, ya shiga damuwa da alhinin mutuwarta ba kaɗan ba, shikenan fa shi yanzu ba shi da kowa sai matarsa Zulaiha, ya yi kuka har ya gaji, da ya ga ba mafita dole ya ɗauki na annabawa wato haƙuri.
Bangaren matarsa kuwa har yanzu bata sake zani ba, domin har zuwa lokacin bata samu haihuwa ba, don haka suka duƙufa da addu'a ba dare ba rana, ya kuma rarrabawa malamai abin sadaka domin su taya su da addu'a har saukar Alqur'ani aka yi.
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
Allah maji roƙon bawansa.
Bayan shekara ɗaya da mutuwar Mamansa ciki ya bayyana a jikin Zulaiha, farin cikinsu ya kasa ɓoyuwa.
Bayan wata tara Zulaiha ta haifi ɗanta namiji, ya kama shekara goma cif kenan kafin su samu haihuwar.
Wannan haihuwar ta zo masu da yanayi biyu, farin ciki da kuma damuwa, domin yaron ya zo duniya a cikin wata irin siffa mai ban al'ajabi da sanya imani da tsoron Allah a cikin zuciyar duk wanda ya gansa.
Yaron ya kasance baƙi ne a kalar fata, rabin fuskarsa a shafe yake sumul ba alamar yankan halitta a gun, komai nasa rabi ne, kunne ɗaya, ido ɗaya, rabin hanci da rabin baki.
Duk da wannan irin siffar da yaron ya zo da ita, hakan bai saka Alhaji Munir ko Hajiya Zulaiha sun ƙyamaci ɗan su ba suna matuƙar sonsa, kuma sun yi godiya da wannan kyautar da Allah ya masu..........
Follow me on wattpad @ummu inteesar
ÜMMÜ INTEESAR CE🌹🌹🌹🌹🌹
*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 9-10
A lokacin da 'yan uwansa suka ji labarin haihuwar tuni sun yi nisa a shirin su na kashe shi da suke, domin a gobe ne ma suke so a kaddamar da shirin, sai ga labarin haihuwar ya zo masu.
Sun yi matuƙar baƙin ciki da haihuwar, amma ba yanda suka iya bisa ga dole suka dakatar da shirinsu, sanin cewa zasu yi 'aikin banza yiwa kare wanka' domin ko da ya mutu basu da gado saboda wannan ɗan da aka haifa masa shi zai gaje komai, kenan ya zama dole su yi sabon shiri domin ba'a fafe gora ranar tafiya.
A ranar ba a kwana ba sai da yayyen Alhaji Munir suka shirya su dukansu da dare suka je ganin jinjirin da aka haifa masa.
Haƙiƙanin gaskiya ba sun tafi ne don taya shi murna ba, sai don su ga wanda ya ɓata masu shiri domin su san irin matakin da zasu ɗauka a kansa.
Bayan shigarsu gidan a babban falo suka yi masauki suka zauna, suka yi zuru-zuru sai rarraba ido suke, kallo ɗaya zaka masu ka gano cewa suna cikin tashin hankali, Mizbahu ne kaɗai ya ke cikin farin ciki.
Bayan Alhaji Munir ya zo sun gaisa ne, suka nemi da a fito masu da Jariri su gani, saboda har zuwa lokacin ba wanda Hajiya Zulaiha ta bari ya ga ɗan, domin tsoron gulmar mutane.
Shiga ɗakin Zulaiha ya yi ya tarad da ita rungume da ɗan nata tana sharar ƙwalla, abu biyu ne ya haɗe mata ga zafin ciwon da take fama da shi tun bayan haihuwar, ga kuma damuwar wannan halittar ta ɗan nata.
Ƙarasawa ya yi, ya zauna bakin gado ya na faɗar "Zulaiha me ka damunki?"
Share hawayenta ta yi tace "Bakomai Alhaji."
Gyara zamansa ya yi ya dube ta cike da tausayawa da alhini, domin yasan yanda take ji, don kuwa shi ma yana jin irin wannan yanayin, amma ba yanda zasu yi, kyautar Allah ce, haka ya ga dama ya basu wannan kyautar cikin iyawarsa da hikimarsa, domin ya zame musu wa'azi su da sauran al'umma.
Daƙyar ya buɗi bakinsa yace "Ki yi haƙuri Zulaiha, ki jure mu samu mu cinye ƙaddararmu, ki tuna shekara goma muka share ba haihuwa, yau kuma Allah ya dube mu da idon rahama ya mana wannan babbar kyautar bai kamata mu butulce masa ba."
Nisawa ya yi sannan ya ci gaba da cewa "Allah maɗaukakin sarki yace Inna khalaqnal insana min nuɗufatin amshajin nabtalihi, faja'alnahu sami'an basiraà." Ma'ana
"Lallai mu muka halicci ɗan adam, daga ɗigon maniyyi garwayayye, muna jarabta shi, muka sanya shi mai ji, kuma mai gani."
A cikin wata ayar kuwa cewa ya yi
"Inna hadainahus-sabila imma shakiran, wa imma kafuraà."
Ma'ana
"Lallai mu muka shiryar da shi (Ɗan Adam) hanya guda biyu, ko dai ya zama mai godewa Allah, ko kuma ya zamo mai butulcewa Ubangiji."
"Duba da wadannan ayoyin guda biyu, ya kamata mu ɗauki haƙuri mu rungumi kaddara domin kada mu kasance cikin masu butulcewa ni'imar Allah."
Ya na gama faɗa ya saka hannu ya ɗauki yaron dake kwance a gabanta, cikin sanyi jiki ya nufi hanyar fita yana faɗar "Su yaya Bilya ne suka zo ganinsa."
Bai jira amsarta ba ya fice abinsa.
Tafiya yake kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki har ya ƙaraso gabansu, ya miƙawa yaya Bilya yaron yana cewa "Ga yaron."
Karɓarsa ya yi ba tare da ya lura ba, sai bayan ya saka yaron a cinyarsa ya kai dubansa a kan fuskar yaron, a razane ya kauda kai gefe yana faɗar "Subhanallah! Miye wannan Munir? Ina ka samo wannan dodon?"
Wannan zancen da ya yi ne ya karkato da hankalin sauran, suka kalli fuskar yaron da kyau, nan take suka razana jikinsu ya dinga kyarma, domin ko a mafarki ba su taɓa ganin mummunar halitta irin wannan ba."
Cikin dakiya Mizbahu ya matso kusa ya saka hannu ya ɗauke yaron daga kan cinyar yaya Bilya yana faɗar "Kai masha'allah! Allah abun godiya, Allah mun gode maka da wannan kyautar da ka mana."
Sauran suka tada kai suka kalli Alhaji Munir sai suka ga kamar bai ji daɗi ba, ganin hakan ya saka Sani ya yi saurin cewa "Masha'allah! Allah ya raya mana, mu zamu tafi."
Kamar masu jira, yana rufe bakinsa duk suka miƙe suna faɗar "Allah ya raya." suka yi gaba, Mizbahu ne kaɗai ya ɗan tsaya, har zuwa lokacin da Alhaji Munir ya harhaɗo kalmomi daƙyar ya ce "Yaya sun tafi fa, kada su barka a nan, mun gode sosai."
Da gama faɗa ya karɓi ɗansa tare da juyawa ya shige ciki rai a jagule, domin wannan ƙyamar da 'yan uwansa suka nunawa ɗansa bai ji daɗinta ba ko kaɗan, ko ba komai wannan yaron jininsu ne bai cancanci haka daga gare su ba.
Bayan kwana uku dangin Zulaiha suka zo daga Jalingo, su da suka zo taya murna sai abin ya rikiɗe zuwa taya juna alhini, sun matuƙar razana da ganin halittar wannan yaron.
'Yan Barka kuwa duk wanda ya zo ba a bari ya ga yaron, sai 'yan uwan Hajiya su kawo uzurin cewa ana yiwa yaron wanka ne, wani zubin su ce yana gun Babansa ne, domin sun lura da biyu mutane ke zuwa barkar ma'ana dai gulma ce kawai ke kawo su.
Ranar suna yaro ya ci sunan Abdulrazzaƙ(Bawan mai azurtawa) wanda mahaifinsa ya raɗa masa, ba don komai ya raɗa masa wannan sunan ba, sai don tuna shekarun da suka shafe kafin samunsa.
Je ka ga yanda gidan Alhaji Munir ya cika a ranar suna, 'yan shan miya da magulmata duk sun zo, a cewarsu dole ai a fitar da yaron ran suna kowa ya gani, amma sai suka ga saɓanin haka, domin sun ta bulala ido amma ba su ga jinjirin ba, da alama a ranar ma ɓoye yaron a ka yi.
Wuni cur, aka yi ana shagalin ciye-ciye da shaye-shaye, duk da ba shagalin suna ne irin wanda aka saba gani ba.
®®®®®®®
Bayan watse taron suna dangin Zulaiha suka koma gida, dama sun ƙagu a yi sunan su tafi, saboda tsakani da Allah basa iya jure kallon wannan halittar kowa ƙyamar zuwa kusa da shi yake.
Zulaiha ta yi kuka mai yawa har hawayenta suka ƙafe, ganin yanda 'yan uwan nata ke ta zumuɗi da murnar tafiya gida, ta gane nufinsu sarai, nan take ta tuno da Margayiyar mahaifiyarta da kuma mahaifinta, ta san da suna raye, ba za'a mata irin wannan cin kashin ba ko don albarkar idonsu.
Ga baki ɗayansu suka watse, ba wacce ta tsaya har zuwa lokacin da za'a fita jego.
Bayan komawarsu Jalingo da kamar kwana uku sai ciwon Hajiya Zulaiha ya motsa, ta dinga fisge-fisge kumfa na fita a bakinta, cikin kiɗima 'yan aikinta suka kira Alhaji suka shaida masa.
Ko cikakken minti talatin ba a yi ba, sai gashi ya shigo a kiɗime hankali tashe ya kinkime ta zuwa asibitin koyarwa ta Usmanu danfodiyo dake jihar Sokoto.
Bayan yin gwaje-gwaje aka tabbatar masa ta kamu da cutar convortion ne, galibi masu ɗanyar haihuwa sukan haɗu da shi, mafi yawa daga cikin matan da lalura ta sama mutuwa suke, sai mai nisan kwana ce zata rayu, wasu ma haukacewa suke.
Gado aka bata a asibitin, sai da ta shafe kwanaki masu yawa tana jinya ƙarƙashin kulawar likitoci da 'yan aikinta, sai shi kansa mijin nata.
Bayan doguwar jinya aka dawo da ita gida, ta cigaba da kula da ɗanta cikin nuna soyayya da kulawa, domin ta sa hannu biyu ta rungumi ƙaddararta.
A ranar da ta cika kwana arba'in da haihuwar Abdul, bayan fitar Alhaji Munir daga gida zuwa wurin aikinsa, tana kwance a ɗaki ita kaɗai sai yaronta da yake manne da ita ko-da-yaushe, kawai sai ciwon nata ya motsa ba tare da sanin kowa ba, ta dinga fisge-fisge gumfa na fita a bakinta, ta kwashi kusan awa a haka, kafin shigowar Ladi ɗakin, domin ta tambaye ta kalar abincin da za'a dafa.
Ganin yanayin da hajiyar ke ciki ya saka ta ratsa ihu, ta nufi boys quaters da sauri, ta lalubo wayarta har hannunta na kyarma, ta kira Alhaji ta sanar masa.
A gigice ya ƙara so ya sure ta sai Asibiti, ko tsayawa ɗaukar Abdul bai yi ba, sai Ladi ce ta yi ƙarfin halin ɗauke yaron zuwa sashen su domin ta kula da shi kafin dawowar iyayensa, domin kuwa tana matuƙar son Hajiya Zulaiha saboda yawan alkhairan da take mata.
Da isarsu asibitin, kai tsaye Emergency ya nufa da ita, cikin hanzari a ka karɓe ta zuwa ciki don bata agajin gaggawa, bayan likitoci sun yi iya ƙoƙarin su aka samu ta dawo hayyacinta, sai dai a matuƙar galabai ce ta ke, anan ta roƙi nurses ɗin dake kula da ita da su kira mata mijinta don su yi bankwana.
Bayan ya shiga ɗakin ya nufi gaban gadonta, cikin murya mai sarƙewa haɗe da kakari ta ke cewa "Alhaji ina so ka sani, ni tawa ta riga ta zo ƙarshe, mutuwa zan yi, ga yarona Abdul nan na baka amanar shi, nasan duk duniya ba wanda zai so shi kuma ya iya ba shi kulawa sama da kai, na roƙe ka da ka kula da shi, sannan ka sama masa uwa ta gari mai jinƙai da imani wacce zata kalli tawayarsa ta tausaya masa, ko bayan raina ka da ka bari Abdul ya wulaƙanta wannan ita ce wasiyata, na so na rayu da yarona don bashi cikakkiyar kulawa amma ina! Kaddara ta riga fata, ina sonka Munir."
Ta na gama faɗa numfashinta ya sarƙe shaiɗarta ta yi sama, cikin sarkaƙƙiyar murya da karyayyen harshe ta karanto kalmar shahada, sannan numfashinta ya yi fit ya fita.
A gigice Alhaji Munir ya miƙe ya je kusa da gawar matarsa, ya na jijjiga ta faɗar yake "Ki buɗe idonki Zulaihat ba zaki mutu yanzu ba, mun yi alƙawarin zamu rayu tare kuma mu mutu tare, ki tashi mu raini ɗanmu a tare, mu zame masa gata, mu ba shi kulawa irin ta kowanne ɗa mai gata domin shima ai *HALITTAR ALLAH CE*"
Ganin ko motsa wa bata yi ba, ya saka ya fice daga ɗakin a kiɗime domin kirawo likita......
Follow me on wattpad @ummu inteesar
*RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 11-12
A tare suka koma ɗakin da likita, bayan likitan ya dudduba ya tabbatar da ta cika, kawai sai ya ja mayafin dake rufe da jikinta ya rufe mata fuska ya juya zai fita, a diririce Alhaji Munir ke kallonsa bakinsa sai rawa yake amma ya kasa furta ko kalma ɗaya.
"Ka yi haƙuri Alhaji, Hajiya kuma an cimma sa'i." Ya na gama faɗa ya fice cike da tausayawa ga Alhajin.
Alhaji Munir ya yi kuka mai yawa irin wanda bai taɓa yi ba ko a lokacin rasuwar mahaifansa, wannan mutuwa ta girgiza shi matuƙa, ga baki ɗaya ya fita daga hayyacinsa.
Bayan ya tabbatar da mutuwar abar ƙaunarsa, sai ya koma gida domin duba yaronsu da ya bari a ɗakin lokacin da ya fice da ita zuwa asibiti, ganin ba yaron ya kuma shiga táshin hankali, baki na rawa ya kira ma'aikatan cikin gidan yana tambayar su ina yaronsa da ya bari a ɗaki?
Ladi ce ta matso gaba ta na faɗin "Ranka ya dade ni nit ɗauke shi dan na ga babu kowa a sashen, ya jikin Hajiya?."
Wannan tambayar da ta masa ce ta famo masa da ciwo da zogin dake ransa har bai san lokacin da hawaye suka kece masa ba a gaban 'yan aikin nasa, cikin hanzari ya juya ya shiga ciki.
Hakan ya tsora ta su sosai, aransu suke cewa duk yanda aka yi jikin hajiyar ne ya yi tsanani, cikin mutuwar jiki Ladi ta juya ta je ta ɗauko masa yaronsa tare da yin sallama a ƙofar ɗakinsa.
Yana fitowa ta miƙa masa yaron ta juya.
Rungume yaron ya yi sosai yana kuka, haƙiƙa an masu mutuwa mai tsayawa a rai, yana matuƙar tausayawa yaronsa don haka ya ƙuduri anniyar tsayawa kai da fata akan al'amuran da suka shafi rayuwar yaronsa ma'ana ya ɗora ɗamarar rainon yaronsa da kansa, domin ya sani cewa a yanda ake ƙyamatar halittar nan tasa ba kowa ba ne zai iya kula da shi.
Sai bayan an yiwa gawar sutura an kawo ta gida ne 'yan aikin suka fahimci dalilin kukan Alhaji, suma sun sha kuka kam, kuma ba su ga laifin Alhaji ba da ya ke kuka don kuwa ya yi babban rashi, ga kuma ɗan talikin yaron nan da ta bari.
A lokacin da labarin mutuwarta ya riski su yaya Bilya sun yi farin ciki sosai, yanzu mutum biyu ya rage masu su kauda don handame dukiyar Munir, matansu ne kaɗai suka yi baƙin cikin mutuwar, domin su ba su san komai da mazajen nasu ke ƙullawa ba.
A lokacin da labarin mutuwar Zulaiha ya riski mutanen Jalingo sun yi baƙin ciki sosai, musamman ƙanin mahaifinta da dangin mahaifiyarta, anan aka fara shirin tafiya Sokoto don yiwa mijinta da danginsa gaisuwa, sai dai me? Duka mata zame jikinsu suka yi, sai uzuri suke kawo wa, ba don komai ba sai don suna tsoron su je a haɗo su da wannan mummunar halittar, sun sani kuma ba su isa su ce ba za su karɓa ba saboda jinin Zulaiha ne.
Maza ne kawai suka haɗu suka yo mota ɗaya suka zo, bayan sun yiwa Alhaji Munir gaisuwa suka juya tare da masa fatar Allah Ya ba shi ikon riƙe wannan yaron.
Bayan kamar kwana arba'in da mutuwar Hajiya Zulaiha, su yaya Bilya suka zo gidan don ganin ko lafiya domin a ranar ake saka ran ya koma bakin aikinsa, sai dai da alama ba shi da niyyar komawa aikin bare a yi zancen kasuwanci.
Anan yake gaya masu "Ni fa babu wani aiki da zan komawa, tuni na gama shirya takardar aje aikina turawa ɗai ya rage, ba ma aikina ba ɗai, na dakatar da hita kasuwancina da duk wata harƙalla da ni kai domin in kula da rayuwar yarona wanda ya kasance abin tausayi ga duk wani mai imani."
Jikinsu ya yi sanyi da jin wannan zancen, Sunusi ya kada baki ya ce "Yanzu kenan haka zaka bari kasuwancinka ya rushe saboda wannan yaron ko ya ya? Ni dai ga nau gani kawai ka biɗammai Nanies masu kula da shi, sai ka ci gaba da harkokinka don in kaz-zauna haka kawai zaka canye abinda kat-tara ne ba tare da kowa ya mora ba."
Murmushin yaƙe ya yi ya ce "Yaya ba zaku gane ba ne, ba kowa ne zai iya kular min da Abdul tsaka ni da Allah ba, don haka niz-zaɓi na yi aikinga da kaina, yanzu dai kuna iya tahiya zan biɗe ku daga baya akan maganar kasuwancina da ku ka kula da shi, kowa ya ci gaba da kula da ɓangarenai kahin insan abin yi."
Daga haka ya miƙe ya yi ciki, ya bar su nan zaune suna nazari, wato Munir dai ya zame masu alaƙaƙai ƙadangaren bakin tulu.
Da suka ga zama ba ya yi, domin kuwa zugunne bata ƙare ba wai an sai da akuya an sayi kura, sai suka miƙe