Showing 15001 words to 18000 words out of 42870 words
cewa an cika aiki.
A lokacin Hasina tana barci ko farkawa bata yi ba, ba wani zancen sallar asuba a gare ta, cikin magagin barci ta jiyo ƙarar wayarta, miƙa hannu ta yi ta ɗauka ba tare da ta buɗe idonta ba.
Jin albishirin da Kulu ta mata ya saka ta buɗe idonta da ƙarfi tare da hantsilowa daga gadon cikin tsananin murna, baki na ɓari ta ce "Kai! Amma na ji daɗin wanga labari ƙwarai, Kulu ki jira kirana dan ko kina da kaso mai tsoka ke da yaranki, bari in tahi in gama da matsalar mutanen gidan ga."
Da gama faɗa ta kashe wayarta, ta miƙe cike da tsananin murna ta nufi ɗakin Abdul, shigar ta ke da wuya ta fito kai tsaye tsakar gidansu ta je ta tsaya tare da ware murya ta ƙwalla ƙara cikin wani firgitaccen yanayi, idan ka ganta ka rantse da Allah cewa da gaske ta na cikin tashin hankali.
Ihunta ne ya tayar da 'yan aikin gidan daga barci mai nauyin da suke.
Mai gadi da Baba direba ne suka fara shigowa tsakar gidan a gigice suna faɗar "Lahiya dai hajjiya meh-hwaru?"
Ko kafin su rufe bakinsu sai ga ma'aikatan kitchen sun iso sashen su ma a firgice suna faɗar "Hajjiya meh-hwaru?."
Nan take idonta ya fara zubar da ƙwallar makirci, kuka take sosai, daƙyar da siɗin goshi aka samu ta dakatar da kukan, bayan kowa ya gama firgita ta ce "Abdul na yat ɓace, ban ganai ba, Abdul ya tsere daga gidan ga."
Cikin matuƙar tashin hankali kowa ya zaro ido waje, dukkansu suka runtuma zuwa ɗakin Abdul ba tare da sun jira umurnin Hajiyar ba.
Bayan sun dudduba ko'ina da ko'ina na cikin ɗakin sun tabbatar ba ya nan, suka fito tare da bazuwa kowanne lungu da saƙo na gidan suna nemansa, matan suka ba zama zuwa cikin sauran ɗakunan dake sashen.
Abu kamar wasa sai da suka shafe awanni suna nemansa, har boys quaters suka dudduba amma ko mai kama da shi ba su gani ba.
Hankalinsu ya kai ƙoluluwar tashi, ba ma kamar Hasina wacce ta kasa zaune ta kasa tsaye tsabar kiɗimewa.
A sanyaye suka watse domin sun gaji da jiran gawon shanu, sun cire tsammanin za su gan shi a gidan, sai dai ko wannensu da abinda yake saƙawa a ransa, kamar ba su yarda da maganar Hasina ba ta cewa wai Abdul guduwa ya yi ba, musanman Baba mai gadi da ya digawa hajiyar ayar tambaya, ya na tantama a ransa cewar wai yaron guduwa ya yi, to wanne dalili ne zai sa Abdul ya gudu daga cikin wannan daular bayan Mahaifinsa na matuƙar sonsa? Gaskiya da lauje a cikin naɗi, amma ba komai akwai ranar ƙindillanci ta na zuwa, ranar da za ta girbi abinda ta shuka, domin ya tabbatar in tana da hannu a cikin wannan lamarin watarana asirinta zai tonu, don kuwa 'yan magana sun ce rana dubu ta ɓarawo ɗaya ta mai kaya.
Da wannan tunanin Baba Direba ya koma bakin aikinsa cike da alhini.
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
Har zuwa ɓullowar rana bawan Allah Abdul ya na nan kwance inda suka yada shi bai farka daga sumammen barcinsa ba, sai zuwa lokacin da rana ta ƙwalle ta yi zafi sosai, zafin ranar da kuma zafin gasassun duwatsun dake gefe da gefensa ya saka Abdul ya fara buɗe idonsa a hankali tare da yin juyi don jin baƙon yanayi a tare da shi.
Gama buɗe idonsa ke da wuya ya ci gaba da waige-waige zuciyarsa cike da tsoro, tun kafin ya gama tantance inda yake zuciyarsa ta cika da ruɗani da tashin hankali.
Bayan ya tabbatar da a jeji ya ke kuma bai ga wani mahaluƙi a kusa ba, bar ta mutane ko tsuntsu bai gani ba, kawai sai ya taƙarƙare ya buɗe rabin bakinsa ya tsunduma ihu tun ƙarfinsa.....
More comment more typing......
Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal
RUKY I LAWAL CE
*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
16 Safar/4 October.
1442hjr/2020.
DEDICATED TO: Jinin jikina🤭🙈
Allah ya ƙara maka lafiya mai amfani, ya azurtaka arziƙi na halal.
Readers asaka mun Jinin jiki a addu'a🙈🤭🏃🏻♀️
Special gift to: Fatima Sunusi Rabi'u(Ummu Affan)
Ƙawar amana..
Allah ya ƙara haɗe kanmu ya saka ki santalo mana 'yan biyu sau biyu, mu je Kaduna shagalin suna...🤭😹
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 21-22
Ihu yake kamar ba gobe, sai dai wannan ihun da yake yi shi ake kira da ihu bayan hari, don kuwa ya na tsakiyar jeji ne ihunka banza, ba wani mahaluƙi a kusa bare ya ji har ya kawo masa ɗauki.
Ganin wannan ihun ba zai fitar da shi ba, ya saka ya yunƙura cike da ƙarfin hali ya tashi zaune, ya fara waige-waige wai koya ga sandunansa.
Ai kuwa Allah ya masa gyaɗar dogo, don kuwa ya hango su nesa da shi kaɗan, hannu ya miƙa don janyo ɗayar sandarsa da ta ɗan masa nisa, kawai sai hannunsa ya sauka a kan wani gasasshen dutsen dake kusa da shi, ba shiri ya tsandara ihu tare da janye hannun nasa.
Cikin matuƙar ƙarfin hali ya samu ya ɗauko ta tare da miƙewa ya fara dogara sandunan, domin ya ƙara gaba ko ya samu wanda zai taimake shi, don zuwa lokacin yunwa ta fara addabarsa ga kishir ruwa da yake ji sosai.
A haka ya ci gaba da tafiya, ya na tuntuɓe da duwatsu da itace dake gun, sai faɗuwa yake ya na tashi, wasu sassan jikinsa duk sun kukkuje, amma da yake yana da jarumta sai ka ga ya miƙe ya ci gaba da tafiya.
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
A can gida kuwa, hankalin mazauna gidan Alhaji Munir ya kasa kwanciya gaba ɗaya, ga shi Hajiya ta hana kowa ya sanar da Alhaji ko wani dake waje ɓatar Abdul, a cewar ta bata so a ɗaga masa hankali alhali ya na gun kasuwancinsa, hakan ya saka kowa ya ja bakinsa ya tsuke suka zubawa sarautar Allah ido.
Can zuwa sha biyu na rana Hajiya Hasina ta fito da shirin fita unguwa, sai dai ba ta yi wata kwalliya ba, duk da cewa mayafi ta saka, amma kallo ɗaya zaka mata ka gane bata cikin walwala.
Da fitowar ta kai tsaye gun motarta ta nufa, Direbanta ne ya zo da sauri don karɓar makulli, domin a zatonsa shi zai fitar da ita, ga mamakinsa sai ya ji ta ce "A'ah! Hamisu komawakka ka huta, yau da kaina zan hita, dan yawo zan yi da yawa a garin."
Da mamaki ya kalle ta ya ce "Amma hajiyya baki cikin yanayi mai daɗi, kuma kahin Alhaji ya tahi sai da yammin umurnin cewa in tabbatar duk inda za ki na na kai ki, kat in bari ki hita da kanki."
Ɗago kanta ta yi da alama zancensa ya ɓata mata rai, cikin alamun fushi ta ce "Yau kuma sai nicce ma ban buƙatat tuƙinka, ka banni in ji da damuwata, so ni kai in kai rahoton ɓacewar ɗana wurin 'yan sanda da kahwahen yaɗa labarai kahin Alhaji ya dawo."
Har ya buɗi baki zai kuma cewa wani abu, ta ɗaga masa hannu ta na cewa "Ban son jin komi dagga gareka, in kakƙara yi min gardama wallahi a bakin aikinka."
Ta na gama faɗa ta shige motar tare da mata key ta juyo hancin motar da ƙarfi, har ta na yunƙurin bige Hamisu direba, da ba don ya janye da sauri ba, da ɓarna ta auku.
Jiki a sanyaye Hamisu ya isa teburin da Baba direba ke zaune yana kallon duk abinda ke faruwa a gun, ya zauna kawai bai ce komai ba.
Haka ma Baba Direba bai ce komai ba, amma yana ji aransa cewa Uwar ɗakinsu tana da sa hannu a ɓatan yaron nan, yanzu ma wata munaƙisar za ta je ƙullowa wata ƙila, duk kuwa da an ce zato zunubi ko ya kasance gaskiya.
¥¥¥¥¥¥¥
Hajiya Hasina na barin gidan ta miƙi hanya sosai, maimakon ta nufi station ko gidan rediyo sai ta durfafi cikin gari, gidan ƙawarta Kulu mai adashen sharri, da yake awa biyu baya kenan da suka yi waya da ita, ta shaida mata cewa sha biyu na rana su Gumush za su zo karɓar kuɗin aikinsu, don kuwa sun dawo daga aikin da ta saka su.
Mintuna ashirin ne suka kai ta cikin ƙofar Atiku, da yake a unguwar gidan Kulun yake, sai da ta shiga da motarta har cikin lungunsu, sannan ta faka nesa kaɗan da gidan.
Ta fito cike da nishaɗi hannunta riƙe da ƙatuwar jakarta, ta ƙarasa gidan a ƙafa.
"Assalamu alaikum!"
Ta yi sallama a ƙofar gidan, ba tare da ta jira an amsa ba ta faɗa ciki kai tsaye ta na faɗar "Ina kike mai adashen sheri?"
Da murna Kulu ta fito daga ɗakin tana cewa "Gani nan Hajjiyata! Aiki ga mai ƙare ka, mu shiga ciki."
Murmushi ne kwance a fuskar hajiyar ta nufin ɗakin tana yiwa Kulu mita.
"Gaskiya Kulu ki canza wanga baƙin gida, haba! Dan Allah duk kuɗɗin da kika samu a ce kina zaune cikin wagga baƙar shiya? Wai don bala'i ko mota bata shigowa lungun ga sai dai a aje ta garkat wani? habah!"
Mitarta take har suka isa cikin ɗakin Kulu bata ce komai ba sai dariya da ta yi.
Maimakon ta tamka Hasina a waccan maganar sai cewa ta yi "Hajjiya ga sunan ga ki."
Ta nuna su Gumush da suka bararraje akan ya galgalallun kujerin falon.
Daƙyar Hasina ta iya zama a kan kujerar, sai da Kulu ta ɗauko mata filo ta ɗora sannan ta zauna a kai, ta na kallon su Gumush da murmushi a fuskarta.
Gumush ne ya ce "An gaida Hajjiya mai yawo da kuɗɗi, nerori basu wuya ga hannunki ga mu mun taho an ce kina biɗar mu."
"Ƙwarai da gaske, kun yi min aikin da nijji daɗi nai sosai, tun shiga ta gidan Alhaji ba a taɓa ranar da niyyi hwarinciki ƙwarai ba irin na yau, don ko kun kawas min da dodon da nit tsani gani a duniya, yanzu ku hwaɗamin nawa at ladar aikinku?"
Wata uwar Shewa Gumush da yaransa uku suka buga, sannan ogan na su ya ce "Ai Hajjiya ki ɗai kwatanta, mun san zaki yi muna adalci."
Murmushi kawai Hasina ta yi, ta buɗe jakarta ta ciro bandir ɗin 'yan dubu guda huɗu ta ajiye masu a gabansu.
Ihu suka hau yi suna godiya, Gumush ya yi saurin kwashe kuɗin ya miƙe ya na faɗar "Ku taso mu tahi, sai mu shaggun madatsa, yau duk sai mun addabi kowane ƙaramin ɗan iska da at madatsa."
Su na gama faɗa suka yi gaba har sauran sun fice, Gumush ya dawo daga baya ya ce "Hajjiya mun gode, ko gobe an ka samu wani aiki irin wanga ko ma wanda yat hishi karki ji komi ki kira mu, zamu miki shi sussettifully." Ya faɗa wai shi a dole ya ji turanci.
Da gama faɗa ya juya ya bar ɗakin.
Kulu kuwa har jikinta ke ɓari ta ga an ajiye mata nata kuɗin, gajin haƙuri ta yi, ta ce "Hajjiya nihwa? Ina nawwa?"
Dariya Hasina ta yi ta ce "Matsalata dake kenan Abbukiyata gajin haƙuri, to ga na ki."
Ta faɗa a lokacin da ta zura hannu jaka ta ɗauko dubu ɗari biyu ta bata.
A raine ta kalli kuɗin ta ce "Haba dai Hasinata! Waɗanga ai ke san sun min kaɗan, ko su sun hini samu hwa?"
"To ai sun hiki shan wahalar aikin." Ta mayar mata da zance.
Ita kuwa ta ce "A'ah hwa Hajjiya! Ni ke san hat inda nissamo su? Sai da hwa nittahi har tsakiyar madatsa, nit lalubo tataccin 'yan daba sannan ni sasu aikinki."
Gyaɗa Kai Hasina ta yi da murmushi a labbanta ta ce "Ina motata sun kawo miki?"
Maƙullan ta miƙo mata ba tare da ta yi magana ba.
"Riƙe su can hannunki, ki ɗauki motar ki ƙara na baki ita halak malak, sai dai in aikina ya tashi zaki bashe ta amin."
Ihun murna Kulu ta saka, sai da ta gama murnarta da godiya, sannan ta ce "Ni kam Hajjiya Alhaji Munir hwa? Ya san shegen ɗan nan ya ɓace?"
Wata Shewa Hasina ta yi ta ce "Ina hwa yassani? Ai na hana kowa ya hwaɗa mai, kuma nima ban hwaɗa mai ba, don ban son ya taho ya ɓata min ranar hwarincikina, ke san yau dole in yi kwanan hwarin ciki."
Ta ƙarashe zancen cike da fara'a.
Kulu ta ce "Kai! Gaskiya sai yanzu nika ganin ba mu kyauta ba, don yadda Alhaji ka son ɗan nan ya na iya haukacewa dan rashi nai."
Miƙewa Hasina ta yi ta na jan wani uban tsaki tare da faɗar "Ke shi at matsalakki wallahi, to ni ke ga tahiyata, in kina jin tausai nai ki tai ki dawo da shi."
Ta na gama faɗa ta yi fuu! Ta wuce, Kulu na lallashinta bata ko saurare ta ba, ta faɗa motarta ta wuce station ta kai report don kare kanta daga zargi, daga nan ta je gidan rediyon vision fm sokoto da garkuwa FM da sauran kafafen yaɗa labarai ta kai rahoto, sannan ta wuce gida.
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
Bawan Allah Abdul kuwa, a haka ya wanzu ya na tafiya a cikin jeji har shuɗewar wasu sa'o'i ba tare da ya haɗu da kowa ba.
Zuwa lokacin yunwa ta gama cinsa ya rasa abinda zai ci, don haka ya shiga zince-zince a ƙasa, duk wani abun da ya gani a ƙasa mai kama da abinci ɗauka yake ya kai baki, haka ma daƙyar ya samu wasu ruwan kududdufi ya ɗiba ya sha.
Tafe yake a hanya tun ya na kuka har hawayensa suka ƙafe, ya rasa wanene ya masa wannan ɗanyen aikin, duk da cewa shi ƙaramin yaro ne amma ba wanda ya fara zargi a ransa inba Mamansa ba, ya na ji a ransa da saka hannunta a jefar da shi da aka yi.
In ba ita ba, waya isa ya shiga ɗakinsa har kan gadonsa ya dauƙo shi ya fito da shi daga gidansu?
Haka ya ci gaba har dare ya riske shi, ya yasu a nan cikin tsakuwoyi ya kwanta ya na tunani kala-kala.
A ransa yake cewa "Allah sarki ni! Yau ina haɗaɗɗen gadona? Ga ni kwance babu ko shimfiɗa."
Abbunsa ne ya faɗo masa a rai, a take ya shiga tuno ran da suka rabu na ƙarshe a daren ranar da zai yi tafiya zuwa kwatano, ya zaunar da shi su na hira, a cikin hirarsu yake cewa "Abdul ɗina gobe tun da sahe zan yin tahiya, ka kula da kanka, ga mamakka nan na san zata kula da kai sosai, ka mata biyayya, ka maida hankali ga karatu, in zan dawowa ina kawo maka kayan daɗi, sannan bayan na dawo muna komawa asibiti a duba ma ƙahwakka ka ji? Yanzu dai mi kaka son in kawo ma?."
Gyaɗa Kai ya yi ya ce "Abu dai mai daɗi da kyau."
Abdul na zuwa nan a zancen zucinsa ya share hawayen da ya gangaro masa, ya rufe idonsa, nan take barcin wahala ya yi gaba da shi...
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
Bayan kwana biyu da ɓatar Abdul Alhaji Munir ya dawo gida cike da farin ciki da sa ran zai ɗora idonsa a kan tilon ɗansa, don ko ya jibgo masa tsaraba mai yawa, sai dai me? Ya dawo gida ya tarar da mummunan labari wanda ya tarwatsa tunaninsa da farincikinsa gaba ɗaya.
Ya shiga tsananin tashin hankali da damuwa da ruɗewar ƙwaƙwalwa, a ranar bai samu runtsawa ba, zuciyarsa cike da zargi.
Washegari ya tara dukkan mazauna gidansa ya shiga tuhumar su a kan ya a ka yi ɗansa ya ɓata?, sannan me suka yi bayan ɓatarsa? me yasa ba'a gaya masa ba?"
Baba Direba ne ya yi karaf ya ce "Tun shekaranjiya da yat ɓace munka so hwaɗa maka, amma Hajjiya ta hana mu sanar maka ta ce za ta biɗo shi kahin ka dawo."
Juyawa ya yi zuwa ga Hasina ya na tambayar ta cike da tuhuma.?
"Missa kin ka min haka Hajjiya?"
Nan take idonta suka kawo ruwa, ta yi rau-rau da ido, cike da damuwa ta ce "Da ma ni ban son a ɗaga maka hankali, shiyasa nicce kat a hwaɗa ma, amma ai na kai rahoto a...."
Bata samu damar ƙarasawa ba saboda saukar wani gigitaccen mari da ta ji a kuncinta, cike da mamaki ta ɗago idonta da take gani disishi ta sauke su a fuskar Alhaji, da yake tsaye cikin ficewar hayyaci.
Mamaki ne ya rufe ta, yayinda Alhajin ke tsaye cikin ficewar hayyaci, shi kan shi bai san ya aka yi ya mare ta ba....
Sai dai bai damu da hakan ba ya hau ta da masifa a gaban 'yan aikinta, faɗar ya ke "Ke san abinda kinka aikata min kuwa? Ina hankalinki da wayonki sun ka tahi? Ta a'a tilon ɗana kuma amanata ka ɓacewa baki hwaɗamin ba? Ya ma anka yi har kuka bari masu garkuwa da mutane suka shigo har cikin gida sun ka ɗauke min gudan jinina?"
Ganin Alhaji ya rufe ido ya na ta surfawa matarsa masifa, cikin wani irin yanayi da ba su taɓa ganinsa a ciki ba, ya saka duka ma'aikatan suka sulale daga wajen kafin ya juyo kansu, don ko da ɗai basu taɓa gani ko jin ya yiwa matarsa ko da tsawa ba sai ga shi yau har da mari, dole abin ya bawa mutum tsoro.
¥¥¥¥¥¥¥¥
Lokacin da labarin ɓatar Abdul ya riski 'yan'uwan Alhaji da Mamansu kuwa, Mizbahu da Hajiya Inna sun shiga damuwa matuƙa yayin da su yaya Bilya,Sani da Sunusi suka ji tamkar su zuba ruwa a ƙasa su sha, labarin ya musu daɗi sosai don ko abin nema ne ya samu matar falke ta haifi jaki.
Sai dai sun ɓoye wannan murna a ƙasan ransu, don ko duk ƙwanƙwantonka baka isa ka gano wannan ɓoyayyiyar murnar tasu ba, inka gan su zaka rantse da Allah sun fi Alhaji Munir ɗin shiga damuwa.
Har gida suka je masa jaje, sannan su kansu mutane kan zo har gidajensu don masu jajen ɓatan yaron ɗan'uwansu........
More comment
More typing.........
Follow me on wattpad @ Ruky_i_lawal.
RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹
*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*
*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
*DEDICATED TO: YAYA MUKTAR MUSA ƘARAMI (ABU HISHAM)*
MILIYOYIN GODIYA ZUWA GAREKA, RABBI YA BAR ZUMUNCI, ALLAH YA RAYA MANA YARANMU;
HISHAM MUKTAR MUSA ƘARAMI
AISHA MUKTAR MUSA ƘARAMI (MIMIE).
ALLAH YA