Showing 24001 words to 27000 words out of 42870 words
wa kala-kala ba wacce bata masa.
Basiru ko idan ya ga Abdul na kuka sai ya zauna ya taya shi, yana matuƙar son Abdul, shi kaɗai ne ke nawa Abdul farinciki a gidan sai Zaliha babbar yar Kande (mai shekaru 16) da take tsananin tausayin yaron tun bayan da ta dawo gidan ta same shi.
Kande ta sha ƙudurin ta kori Abdul daga gidan, sai dai tana tsoron kada mai gidan ya shammace ta ya juyo da wuri, shiyasa ta ɗaga ƙafa zuwa wani lokacin.
Yau ma kamar kullum, tun da asuba Kande ta tashi, ta nufi tulunta da ya yi sanyi raɗau, ta tsiyayo ruwa cike da babban kofin silver ta nufo ɗakin da yaran ke kwana.
Haska fitila ta yi, ta tashi yaranta "Badaru! Basiru! ku tashi zuwa Sallah, ko ɗan kun ga Babanku baya nan ne? Wai ba zaku tashi ba?"
Haka ta yi ta faɗa ta na daddaɓarsu har zuwa lokacin da suka tashi suna mitsittsika ido, kowannensu ya fita waje don yin Alwala ba tare da sun tamkata ba.
Da ta tabbatar sun fita ta juya zuwa inda Abdul ke kwance, cike da ƙeta ta kwarara masa ruwan sanyi nan a jiki.
Firgigit ya farka da ƙarfi ya zabura kamar zai miƙe sai kuma ya dawo zaune ba shiri, don jin yanda ƙafarsa ke raɗaɗi.
A take ya hau rarraba idonsa yana ƙyafƙyaftawa, don neman wanda ya masa wannan aikin.
A gabansa ya ganta tsaye ta na ƙyalƙyala dariya, can kuma ta tsuƙe fuska kamar bata taɓa dariya ba ta ce "Kai kuma ɗan iska nakasasshe me kake jira, duk sauran yara sun tashi zuwa Sallah amma kai kana kwance?"
Hannu ya kai ya janyo sandunansa, sai sake ajiyar zuciya yake, don kwata-kwata jikinsa baya son sanyi sosai, ga shi an yi ruwa a daren jiya don ko damana ta fara.
Miƙewa ya yi ya nufi ƙofar fita, dai-dai lokacin Basiru ya shigo ɗakin don canza kayan jikinsa.
Haska fitila ya yi ya ga Abdul a jiƙe, ga kuma Mamarsu riƙe da kofin ruwa.
Ya fashe da kuka tare da rungume Abdul yana cewa "Ka yi haƙuri Abdul, muje ka canza kaya."
"Ba wasu kayan da zai sauya a haka zai je masallaci, ko Kanada wasu kaya a gidan nan ne?" Ta ƙarashe zancen da tambayar Abdul.
Gyaɗa kai alamar a'a.
Ta ce "To ɓace mun da gani Dodon banza."
Basiru ya ja hannunsa zuwa gun bakon kayansa, ya ciro wasu yana faɗar "Yi maza ka saka mu je, ka ji an kira sallah."
Har hannunsa na ɓari gun karɓa domin tuni ya fara makyarkyata.
"Kai Basiru! dan ubanka baka ji me nace ba?"
Kande ta faɗa cikin ƙaraji.
"Habah Inna! Don Allah ki bar shi ya canza baki ga yana jin sanyi ba?"
Harara ta wurgawa ɗan nata ta ce "Ya mutu mana, ina ruwanka?"
Matsawa ta yi ta ƙwace kayan a hannun Abdul tare da zuba mishi ranƙwashi a kai.
Ai ko Basiru ya fashe da kuka, cikin kukan yake cewa "Wallahi Mama ko ki ba shi kayan nan ya saka, ko Baba na dawowa gidan nan in gaya mai duk abinda kikewa Abdul."
Ganin ta yi shiru kuma bata bayar ba ya ce "Kin dai san halin Baba da masifa, har dukanki zai iya yi a kan haka."
Jikinta ne ya yi laƙwas da jin zancen yaron, ba shiri ta watsawa Abdul kayan ta fice daga ɗakin tana zancen zuci.
Ɗaukowa Basiru ya yi, ya miƙawa Abdul ya saka suka fice zuwa masallaci don ko tuni Badaru ɗan baƙin hali ya bar gidan.
¥¥¥¥¥¥¥
Da hantsi Badaru da Basiru suka je gona don taya manoma aikin gyaran gona, kamar kullum.
Abdul shi kaɗai zaune a tsakar gidan abun duniya duk ya dame shi, ga yunwa ta fara kama shi, amma ya san ko giyar wake ya sha ba zai cewa Mama Kande ta sammasa abinci ba.
Hannu biyu ya saka ƙarƙashin haɓarsa ya zuba tagumi sai tunani ya ke, haƙiƙa gidan ya kasance masa tamkar inuwar bagaruwa ga sanyi ga ƙaya.
"Assalamu alaikum." Ya jiyo sallama a ƙofar gidan.
Amsawa ya yi daƙyar.
Zaliha ce ta shigo gidan hannunta rungume da ƙwarya, da alama ta dawo daga niƙa ne.
Ganin yanayin shi ya saka ta ajiye ƙwaryar ta nufe shi, a gabansa ta durƙusa, ta ɗora hannunta a kafaɗarsa "Abdul meke damunka?"
"Yunwa nika ji yaya Zaliha." Ya faɗa idonsa na kawo ƙwalla.
Girgiza kai ta yi cikin tausayawa ta ce "Share hawayenka bari na kawo maka abinci."
Da hanzari ta je madafa ta sako masa ɗumamen tuwon masara da miyar kuka ta zo ta miƙa masa tana faɗar "Ga shi daina kukan, ai nan gidanku ne ba zamu...."
Bata ƙarasa ba don jiyo Muryar Kande daga nesa tana faɗar "Sannu mai gida!"
Zaliha bata ce komai ba sai miƙewa tsaye da ta yi, don ta na shakkar Maman tasu.
"Uban wa ya ce ki bawa wannan dodon Abincina?"
"Yi haƙuri Mama, na ga yana jin yunwa ne, kuma shi amana ne a gurinmu idan muka...."
"Rufe mun baki ja'ira!" Kande ta daka mata tsawa.
Ta ci gaba da cewa "Lallai wuyanki ya isa yanka Zaliha! ni kike gayawa wai shi amana ne a gurinmu? To sai dai a gunki amma ba ni ba, kuma ki sani abincinki kika ba shi, don Wallahi ba za ki ɗibi wani ba."
Tana gama faɗa ta juya ta koma cikin ɗakin rai a ɓace; dama ta na tsaye ne a ƙofar ɗakin....
More comment more typing.......
Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal
Vote, share & comment.
RUKY I LAWAL🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*
*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
3Rabi'ul awwal/20 October.
1442hjr/2020.
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 31-32
Zaliha kasa motsi ta yi tsabar mamaki, "wai meyasa Mama bata son yaron nan ne? Ko ta manta cewa shi ma iyaye ne suka haife shi? Har yanzu fa bata san ko ɗan waye ba amma take wulaƙanta shi, mai yiwuwa ma ɗan wani hamshaƙin mai kuɗi ne."
"Yaya Zaliha!" Abdul ya katse mata zancen zucin da take.
Juyowa ta yi tana faɗar "Na'am ƙanina Abdul, ya aka yi ne?"
"Ga abincin ni na ƙoshi ki canye sauran." Ya faɗa.
Murmushi sosai ta yi, a ranta ta ce "Ka ga yaro mai hankali, Allah ne kaɗai ya san irin baiwar da ya yiwa wannan bawa nasa."
A zahiri kuwa cewa ta yi "A'a ƙanina ka ƙara ci dai, karka damu da ni, a ƙoshe nake."
Ta faɗa mishi haka ne don ta kwantar masa da hankali ya ci abincin sosai, amma zahirin gaskiya tana jin yunwa sosai, sai dai ta sani zata fi shi samun abinci cikin sauƙi duk sanda ta buƙata.
Bai musa ba ya saka abincin a gaba ya cinye, da yake dama bai ƙoshi ba, sanin halin Mama ne ya sashi faɗar haka.
Sai da ya cinye shi tas, sannan Zaliha ta ɗebo masa ruwa ya sha.
Ɗakin Mama ta je ta ƙara bata haƙuri sannan ta gaya mata zata je gidan su ƙawarta Rabiba.
Da Zaliha ta san me fitar ta zata janyo, tabbas da ta gwammace ta kwana da yunwa a kan ta fitan.
Fitar ta ke da wuya Kande ta fito ƙofar ɗakinta ta tsaya ta na ƙare wa Abdul kallo, ta ma rasa me zata masa ta fashe ƙurjinsa da take da, kwatsam sai dabara ta faɗo mata.
"Tabbas wannan kyakkyawar dama ce a gare ni tunda gidan ba kowa." Ta faɗa a ɗan bayyane.
Bata tsaya wani dogon nazari ba, ta hau waige-waige da ta tabbatarwa kanta ba kowa kawai sai ta nufi Abdul gadan-gadan.
Finciko hannunsa ta yi da ƙarfi tana faɗar "Hatsabibin yaro kawai, maza ka ɗauki wannan ƙarafan naka yanzun nan za ka bar gidan nan."
Abdul na kuka wiwi yana rokonta ta bari Basiru ya dawo su yi sallama, amma da yake an ce wanda ya yi nisa baya jin kira, sai bata sauraresa ba.
Haka ta tasa ƙeyarsa gaba tabi ta ƙofar baya suka fice daga gidan tana ingizar ƙeyarsa.
Ganin baya sauri ya saka ta duƙa ta goya shi don ko bata son ɗaya daga cikin yaranta ya dawo gida ya samu bata nan, gudun kada su zarge ta.
Tafiya take tana zabga sauri, duk wanda suka haɗu a hanya ya tambaye ta lafiya a'ina ta samu yaro, ina za su? Sai ta ce abokin Basiru ne gurgu ne ya kawo masa ziyara shi ne zata mai dashi ƙauyensu.
Sai da ta yi nisa da ƙauyensu sosai, don har ta fara fita karkarar(da yake ƙauyen nasu ƙaramin ƙauye ne sosai) sannan ta ajiye shi, tare da masa gargaɗi sosai.
Kunnensa ta kama ta murɗe ta ce "Ka na jina ai ko?"
Gyaɗa kai ya yi alamar Eh.
"Ko da wasa kada ka sake na ga nakasasshin ƙafafun nan naka a gidana, idan ka sake ka dawo aradu sai na ƙona ka da wuta, na tsani ganin wannan mummunar halittar taka."
Shi dai Abdul banda kuka ba abinda yake, abubuwa sun taru sun caɓe masa.
Duk wannan masifar da ta masa bata ishe ta ba, tsabar mugunta ta saka hannu biyu ta tura shi ya faɗi baya da ƙarfi a kan wani dutse mai tsini, har sai da bayansa ya fitar da jini.
Wata mahaukaciyar dariya Kande ta bushe da ita ta juya cike da annashuwa ta fara tafiya.
"Don Allah Mama ki temake ni kamat yadda Allah ya temake ki! dan Allah ki koma da ni gidanki na miki alƙawarin ba ni sake cin abincin gidanki zan tahi in yi bara a maƙwafta, ni dai ki banni in zauna tare da abokina Basiru, Wallahi in yaddawo bannan zai shiga damuwa."
Duk wannan uwar magiyar da yake zubawa bai saka Kande ta ji tausayinsa ba, sai ma haushinsa da ya ƙaru a ranta, a haka ta wuce abinta ta bar sa nan yashe yana faman magiya.
¥¥¥¥¥¥¥
A can Sokoto kuwa, sai yamma liƙis Alhaji Munir ya dawo gidansa.
Ya dawo a gajiye sosai, don haka bai ko zauna falo ba kamar yanda ya al'adanta, kawai sai ya wuce uwar ɗakansa ya watsa ruwa sannan ya kwanta.
Hasina ta na ɗakinta don haka ba ta san ma ya dawo ba, sai wuraren ƙarfe shidda na yamma ta fito daga ɗakin.
Kai tsaye ta nufi ɗakin Alhajin sanin har yanzu bai dawo ba da ta gan shi a falo ko kuma a ɗakinta.
Ta na shiga bata zame ko'ina ba sai gurin walldrop ɗinsa, sannu a hankali ta buɗe ta ba tare da fargabar komai ba ta janyo akwatin sirrinsa (inda yake ɓoye duk wasu takardu ko wani abu nasa mai muhimmanci) ta ajiye shi a ƙasa sannan ta fara kiciniyar buɗewa.
Alhajin dake lafe a kan gado ya rufa da blanket tsabar gajiya, tun shigowarta ɗakin yake binta da kallo, da fari har zai mata magana sai ya ga ta nufi walldrop, wata zuciyar ta ce masa "Bari ka ga me zata yi?"
Don haka ya ƙara lafewa tare da daina motsi, ikon Allah sai kallo kawai sai ya ga ta ɗauko akwatin sirrinsa, nan fa ya cika da mamaki matuƙa, shi dai a iya saninsa ba wanda ya san da wannan ajiyar tasa, bai taɓa tunanin hankalin Hasina zai kai kan wannan akwatin ba.
"Tafɗijam! Dole na canza gurin ɓoyo."
Ya faɗa a ransa.
Ita ko Madam Hasina shagalin gabanta take bata ma san da wanzuwar mutum a ɗakin ba.
Daƙyar ta samu ta buɗe akwatin, wani shu'umin murmushi ta yi ta ce "Alhamdulillah!"
Nan fa ta shiga fitar da takardun kadarorinsa ɗaya bayan ɗaya tana dubawa har ta je kan takardar wata makekiyar Gona da ya mallaka a ƙauyen Tangaza.
Faɗaɗa murmushinta ta yi ta ware takardar gefe sannan ta tattare saura ta mayar kamar yanda suke ta rufe akwatin tare da maida shi muhallinsa kamar dai ba wanda ya taɓa gun.
Shi dai Alhaji sai kallon ikon Allah ya ke, zuciyarsa na masa saƙe-saƙe a kan matar tasa, hakan na nufin sata take masa kenan? Ita ce mai satar masa kuɗaɗe idan ya ajiye dama?"
Bai taɓa tsammanin haka daga gare ta ba.
Kallonta kawai yake har ta duƙa ta ɗauki takardar ta saka a bayanta, ta nufi hanyar fita tana faɗar "Yanzu komai ya yi dai-dai...."
"Hasina!" Ta jiyo muryarsa daga bayanta kamar saukar Aradu.
A kiɗime ta juyo don tabbatar da abinda kunnuwanta suka jiyo mata.
Ƙafafunta ne suka kasa ɗaukar ta tsabar kiɗimewa, ganin shi zaune kan gado a bayanta ba ƙaramin razana ta ya yi ba,hakan ya saka ta zauna daɓas a gun.
Ƙoƙari take ta tuna lokacin da ya shigo ɗakin, sai dai a iya hangenta da tunaninta bata tuna lokacin da ta ga shigowarsa ba, hasalima ƙofar a rufe take tun shigowarta har yanzu.
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
Tashin hankali!
A can ƙauye bayan komawar Kande gida bata tarar da kowa ba, hakan ba ƙaramin daɗi ya mata, don haka ta shige cikin ɗakinta tana faɗar "Kai har na ji sakayau wallahi! Yau dai na rabu da wannan dodon."
Muryar Abdul ɗin ta jiyo daga waje yana faɗar "Mama ai ba mu rabu ba gani nan na biyo ki."
A kufule ta yo waje tana ƙunduma ashar "Kutuma! Amma yaron nan ka raina ni, bance karka sake ka biyo ni b......"
Sauran maganar ce ta maƙale a maƙogwaronta lokacin da ta fito wajen bukkar.
Ba komai ne ya hana ta ƙarasawa ba, face ganin yara da yawa masu siffar Abdul ɗin sun cika gidan taf, ko'ina ka waiga sune tufafin jikinsu iri ɗaya dana Abdul ɗin, ba dai bambanci sak shi ɗin.
Cike da tsananin tashin hankali Kande ta faɗa ɗakin haɗe da faɗawa kan gadon ƙarfenta tana ɓoye fuskarta, jikinta sai kakkarwa yake.
Ba shakka yaron nan aljani ne, yau ta jangwalowa kanta abinda yafi ƙarfinta.
Daga waje ta ji Abdul ɗin yana nufo ɗakin bai kuma daina kiran sunanta ba ya na kuka.
"Mama Kande ki taimaka min na zauna tare da ke a gidanki." Muryar na fita bibbiyu cikin sautin kuka.
Ƙara ɗungulewa ta yi guri ɗaya kamar an cura ta a gun sai kakkarwa take, ta ma kasa yin addu'a...
Can ta ɗan ji shiru ba sautin yaro Abdul hakan ya saka ta ɗago kanta a hankali.
Ba shiri ta kuma sunne kanta ƙasa saboda ganin Abdul ɗin zaune kan ɗaya gadonta ya na baɓɓaka dariya, ga kuma sautin waɗancan yaran na farko daga waje suna kiranta da neman ta taimaka masu.....
Hmmmm!🤔🤔🤔
To fah readers! Me Kande ta jangwalowa kanta? Da alama fa ta faɗa trkon jinnu.
Miye alaƙar waɗannan aljanun da Abdul da suka zo a siffarsa?
Shin ya Hasina zata ƙare a gaban Alhaji?
Wohoho! Ku dai ku tara da ni a page na gaba don jin ya zata kaya.
Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal
RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*
*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
6Rabiul awwal/23 October.
1442hjr/2020.
DEDICATED TO: Nana, mom Islam,mom Khalil, da sauran masoyan wannan book.
Ina miƙo gaisu ga members na HALITTAR ALLAH CE FANS GROUP
Haƙika ina jin daɗin ƙaunar da kuke nunawa book ɗin nan ina yinku over.
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 33-34
Kande ta shiga ruɗani da rikicewar ƙwaƙwalwa, ba abinda take sai wasi-wasi.
Ita dai tas an ta baro Abdul a jejin farkon gari, kuma yaron gurgu ne saboda haka ko da ace biyo ta yayi tabbas bai isa zuwa nan ba, ajiye wannan maganar a gefe, idan ma shi ne ya akayi ya kasu kashi-kashi? Wannan sai dai aikin aljannu.
Ƙwaƙwalwarta ce ta tsaya cak daga tunanin da take, a firgice ta ɗago.
Ihu ta zunduma don ganin yaro Abdul ya zama zabgege, ya cika ɗakin gaba ɗaya, bata ma iya hango kansa, saboda tsawonsa har kan ya fita ta saman rufin ɗakin, iya cinyoyinsa da sandunansa kawai kake iya gani a cikin ɗakin, sauran gangar jikin tana saman rufin.
Nan take nadamar jefar da yaron nan ta shige ta, tabbas da ta samu hanyar ficewa daga ɗakin ba abinda zai hana ta koma ta ɗauko Abdul ta dawo da shi.
Wohoho! Firgici idan ya amsa sunansa firgici ya kansa ma'abocinsa ya ƙeƙashi ido ya zama jarumin dole.
Irin wannan yanayin ne ya faru da Kande, har bata san lokacin da ta buɗi baki cikin tsawa ba ta ce "Wai wannan wane irin iskanci ne! Me kuke so da ni ne? Idan kashe ni zaka yi ka kashe ni Kawai na huta, ina dalilin wannan....."
Kau! Kau!! Kau!!! Ta ji saukar kyawawan maruka guda uku a jejjere, wanda ko wane mari ɗaya yake a matsayin marin sadaukin jarumi guda uku.
Saukar marukan a kuncinta ke da wuya, haƙoranta biyu na gaba suka yi fitar burgu ɗaga bakinta, sai jini ke fesowa daga bakin.
Take ganinta ya ɗauke har na tsawon daƙiƙu goma, tama kasa tantance a wace duniyar take.
Wata buɗaɗɗiyar murya ce ta karaɗe ilahirin gidan inda ake faɗar "Ke Azzaluma! Ki sani yau ƙaryarki ta ƙare, me wancan ɗan talikin ya yi miki kika tsane shi? Shin laifinsa ne don ya zo duniya a cikin irin wannan siffar? Ubangijin dake sarrafa kowa da komai shi ya halicce shi a haka, me yasa ke baki da imani ne?"
Kande dai ba baki sai kunne, don ko iya muryar kawai take ji, kan dake maganar yana wajen rufin.
Duk da cewa mutanen karkara basu cika tsoron aljanu ba, amma dai a yau Kande ta tsure iya tsurewa, saura kaɗan ta saki fitsari don tsoro.
Wata kakkausar murya ce ta ci gaba da cewa "Ba kowane mutum ba ne ake wulaƙantawa don an gan shi kamar a banza, da kin san ko wanene yaron nan da irin arziƙin mahaifinsa, tabbas da ba ki yi gigin ɗora ƙazamin hannunki a kan shi ba, bare har ki dinga dukansa."
Cikin dakiya Kande ta ɗago kai ta ce "To don Allah wanene kai? Meye alaƙarka da Abdul? A Iya tsawon mako biyun da muka yi tare da shi a nan bansan shi da matsalar jinnu ba..."
Wata iriyar dariya aljanin ya bushe da ita, mara daɗi sauraro, sannan ya ɓace ɓat, amma bata daina jin dariyar ba.
Ai da gani ya ɓace ta runtuma da gudu zuwa wace ta na ihu duk ta fice daga hayyacinta.
Kamar daga sama ta ji wata Muryar ƙananun yara na faɗar "Ba ki kai matsayin da zaki yi min wannan tambayar ba mutuniyar banza! Amma zan baki amsa a haɗuwarmu ta gaba."
Daga haka ta ji ɗif, dama gudu take, ta na zuwa ƙofar fita daga gidan, suka yi kaura da Zaliha da ke shigowa a hanzarce, har sai da Zalihan ta baje