Showing 3001 words to 6000 words out of 42870 words
abinci, amma ya ƙi, acewarsa ya na sauri ne.
Ficewa ya yi aransa ya na Faɗar "Ga abinda nake so nan ka hanani ci, sai wani abincin banza zaka ba ni?, ka ga shege mai ɗan banzan wayon tsiya duk lokacin da muka yi yunƙurin kashe ɗan neman yaronga sai ka ga kamar ana hwaɗa mai."
Daga haka ya bar gidan gaba ɗaya, sai da ya yi nisa da gidan ya fita layin gaba ɗaya sannan ya faka motarsa gefe, tare da janyo wayarsa ya kira yayansa Sani ya shaida masa abinda ya faru.
Buɗar bakin sani sai cewa ya yi ".......
RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹
*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 5-6
Buɗar bakin Sani sai cewa ya yi ‘’Ka ga shegen mutum koh?, to ko ya ƙi ko ya so sai mun ga bayansa shi da wannan mummunan ɗan nasa.’’
Huci ya yi, sannan ya rufe zancensa da cewa ‘’Mu haɗu gida anjima da dare, sai mu tattauna maganar tare dasu yaya Bily don ko bata taɓa saɓuwa bindiga a ruwa.’’ Ya na gama faɗa ya kashe wayarsa a hasale, da alama shi yafi sunusi saurin zuciya da ɗaukar abinda ya faru da zafi.
Alhaji sunusi na ganin ɗan uwansa ya sauka a layi, kawai sai ya juya cike da baƙin ciki ya hau motarsa ya wuce, amma ya ɗau alwashin sai ya ga bayan ɗan uwansa Munir da ɗansa kwaya daya jal a duniya, domin kuwa su suka fi dacewa da cin gadon wannan dukiyar ba wannan nakasasshen ba.
A can gidan Alhaji Munir kuwa, bayan sun gama cin abinci shi da ɗansa, sai ya tashi ya shiga ɗakinsa don hutawa, bayan ya kai Abdul ɗakinsa ya ba shi tsarabar da ya zo masa da ita.
Bayan fitarsa ne Abdul ya fiddo alawarsa da wan mahaifinsa ya kawo masa da zimmar zai sha, kawai sai ya ji kamar an fisge alawar daga hannunsa an yi jifa da ita ƙasa.
Akan dole ya haƙura, domin ka'idarsa ne da abu ya faɗi ƙasa haƙura yake da sha ko cinsa, ba don komai ba, sai don baya iya durƙusawa ya ɗauko shi.
Faruwar hakan ke da wuya Abdul ya gyaɗa kansa alamar rashin damuwa, ya buɗe ledar da Abbunsa ya kawo masa ya ciro ice-cream ɗinsa ya na sha.
Da dare Alhaji Munir ya shirya ya hau motarsa ya nufi unguwar miyatti Allah, da yake a can gidan iyayensa yake.
Ko da ya je gidan ya tarad da sauran yayyensa su biyar a gidan, kasancewar kusan wannan lokacin shine lokacin zuwan kowannensu gida domin su gaida mahaifiyarsu.
Bayan sun gaisa da hajiya Inna ne, ya fito tsakar gidan ya samu yayyensa suka ƙara gaisawa cikin mutunta juna da nuna ƙaunar junansu.
A nan ya kalli Alhaji Sunusi ya ce ‘’Yawwa yaya Sunusi, ɗazu ka je da magana na ce ka bari sai mun haɗu gida koh?."
Ya fada da sakin fuska.
Sunusi ya kalle shi fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce ‘’Hakane, mu je waje mu yi maganar.’’
Alhaji Munir ya shiga gaba, Alhaji Sunusi na binsa a baya, ya na masa wani kallo mai cike da tsana, a ransa ya ce ‘’Na tsane ka Munir, me yasa duk wani buri nawa da duk abinda nake so kai Allah ya tattara ya bawa?, dole sai mun ga bayanka, bari dai mu gama da wannan ƙaramin ƙwaron.’’
Haka ya ci gaba da sake-sake da zancen zucinsa, har suka isa wajen suka nemi guri suka zauna don tattauna maganar.
Bayan ya gama shiryawa Alhaji Munir zance, suka ajiye Magana akan gobe ya je ya same sa a inda yake siyar da motoci, don karɓar wasu daga cikin kuɗaɗen.
Daga nan suka miƙe, Sunusi ya je ya tarar da sauran yayyensa kuma abokanan makircinsa suka ci gaba da ƙulle-ƙullensu na yanda za su yi nasarar hallaka ƙanin nasu tare da ɗansa domin su mallaki dukiyarsa, yayinda Alhaji Munir ya je ya tarar da yaya Mizbahu suka ci gaba da hirar zumuncinsu, da yake shi Mizbahun kwata-kwata ba halinsu ɗaya da sauran 'yan uwansa ba, shi kam ya'na son ƙaninsa Munir da zuciya ɗaya, sabanin yayyensa da suke zaune da Munir ɗin da biyu.
Da misalin ƙarfe tara da rabi na dare suka watse, ko wannensu ya nufi gidansa, amma shi Alhaji Sunusi ya tafi da tunanin ko Abdul ya sha alawar? Shin ya mutu ko yana raye?
A haka ya ƙarasa gidansa cike da jiran tsammanin ganin wayar ɗan uwansa domin ya shaida masa labarin mutuwar ɗan nasa.
¥¥¥¥¥¥¥¥
Bayan kwana biyu, Hajiya Haseena ce zaune a falo ta na ta famar tunani, to me Kulu ke nufi, kar dai ta manta da zancensu?, ta ji shiru har yanzu, hakurinta ya kusa ƙarewa, ita fa ta tsani wannan yaron kamar yanda ta tsani mutuwarta, shi yasa take jin daɗin rashin haihuwarta a gidan nan har yanzu, domin bata so ta haifi ɗan da zai kalli wannan nakasasshen ya ce masa yaya, ta fi son sai ta ɓatar da shi sa'annan ta zuba tata zuri'ar, yanda za su mori dukiyar da kyau.
Ganin wannan ba zai fitar da ita ba, ya saka ta ɗaga waya ta kira Kulu mai adashen sharri.
Bayan sun gaisa ta ke cewa ‘’Wai Abbukiyata mi kika nuhi halam?, kwana biyu na ji shiru bayan kesan na riga na biya kuɗɗin wanga aikin, to in baki iyawa na, ki dawo min da kudɗaɗena, in biɗi wanda ka iyawa.’’
Ta na gama faɗa ta kashe wayarta, ba tare da ta jira cewar Kulun ba.
Har za ta shige ɗakinta ta jiyo sallama a ƙofar falon, juyowa ta yi ta na faɗar "Wa'alaikumus salam, shigo."
Yayarta Safiya ce ta shigo da sauri ta ƙarasa gun ta, ta na faɗar "Oyoyo oyoyo!! Sannu da zuwa yaya."
Jan ta ta yi suka shige cikin ɗakinta domin su tattauna a sirrance.
Ba su jima da shigewa ba, Baba direba ya shigo da Abdul falon ya na sallama, dawowarsu kenan daga makaranta, jin shirun ya yi yawa yasa ya dubi yaron ya ce "Abdul yaron kirki mamakka bata kusa ƙoƙarta ka ida shiga ciki."
Da to yaron ya amsa, sannan ya yunƙura ya tattara dukkan ƙarfinsa ya isa gaban 2sitter dake falon, ganin ba kowa gashi tun a makaranta cikinsa ke murɗa masa, kawai sai ya yi dabara ya haye kujerar ya kwanta ya na sauraren cikinsa dake masa ciwo sosai, sai hawaye ke fita a idonsa.
Lafewa ya yi luf, ya na tunanin da ya saba, domin tun ba yanzu ba tunani ya auri ƙwaƙwalwarsa, Ga shi dai yaro ne mai ƙarancin shekaru, amma matsalar da yake fuskanta koda yaushe ta haddasa masa yawan tunane-tunane.
A ransa yake tunanin Mammansa bata sonsa ko kaɗan, domin bata kula da shi, ko don ya na gurgu ko makaho ne take masa haka?, Ko da yake ba ita kaɗai ce ba ta sonsa ba, ya lura har makaranta yara tsokanarsa suke, wasu ma tsaronsa suke, ba mai son zuwa kusa da shi idan ba nakasasshi 'yan uwansa ba, sauran duk ƙyamarsa suke, Abbunsa ne kaɗai ke sonsa, shi kaɗai ne yake rungumarsa har ma ya lallashe shi idan ya na kuka.
Tuna wannan da ya yi ya saka ya ce a ransa "In Abbuna ya dawo zance ya cire ni daga makarantar ban son karatun na gaji."
Haka ya cigaba da rirriƙe ciki ya na kuka har bayan shuɗewar wasu mintuna masu yawa, sai ga Hajiya Haseena ta fito yayarta Safiya na biye da ita a baya sai dariya suke ƙyalƙyalawa da gani kasan ta mugunta ce, wannan na nuna kenan wata munakisar suka ƙulla a cikin ɗakin.
Dai-dai lokacin da suka zo tsakiyar falon, idon Safiya ya sauka akan Abdul da sauri ta runtse idonta ta na faɗar "Innahu min sulaimanu wa Innahu bismillahir-rahmanir rahiim, ku ka ganinmu ba mu mu ka ganinku ba."
Shi dai Abdul bai ce uffan ba, sai ƙuri da ya yi mata da idonsa ɗaya.
Hajiya Haseena ce ta ƙaraso gabansa ta saka hannu ta murɗe masa kunne ɗaya ta na faɗar "To baƙin maye, kallon ya isa haka, kurwar yayata kur, ka ci kanka ka sha baƙin ruwa."
Ta na gama faɗa ta sake masa kunne suka nufi hanyar fita falon Safiyar na faɗar "Tab! Lallai Haseena kina ƙoƙari, haka kika zama da wanga yaro? Ke bai ma baki tsoro da dare?"
Dariya Haseena ta ƙyalƙyale da ita ta ce "Yayata ke cika tsoro, ni ai ban ma yadda mu haɗu da shi da dare sai bisa dole, ke san ko in Babanai na nan har ga jikina nake ja nai ina mai wasa?"
"Uhmm! Lallai iyawa kikai, ni dai sai an jima bari In tahi, kafin nakasasshen ɗan ga naku ya samin hawan jini."
Ta na gama faɗa ta yi gaba abinta.
Shi kuwa bawan Allah Abdul ya na nan inda suka bar shi, sai matsar ƙwalla yake, zafin ya haɗe masa biyu, ga ciwon ciki ga wannan zaluncin da matar babansa ta masa.......
Follow me on Wattpad @ ummu inteesar
RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹
*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 7-8
Ko da ta dawo ma wucewa ta yi abinta, ko kallon inda yaron yake bata yi ba, bare ta ji dalilin kukansa.
Sai can wuraren ƙarfe huɗu da rabi na yamma sannan ta fito jiki na rawa, ta turawa Abdul kekensa zuwa ciki ta kira Lami 'yar aikinsu ta ce "Lami ki yima yaronga wanka, ke ga Babanai ya kusa dawowa."
Ta na gama faɗa ta juyowa ta koma inda ta fito.
Lami ce ta masa wankansa tsaf a bathroom ɗin dake ɗakinsa, bayan ta kammala ta shirya shi cikin ƙananun kaya.
Ganin yanayin yaron ya sauya daga yanda ta saba ganinsa, ya sa ta dube shi ta ce "Abdul mika damunka?"
"Yunwa nika ji anty, kuma cikina ka ciwo." Ya bata amsa.
Cikin alamun tausayawa da mamaki ta juya ta nufi kitchen don nemo masa abinci, mamaki take ya aka yi Hajiya ta bar yaronta da yunwa haka? Kuma baya da lafiya amma da alama bata ma sani ba.
A haka har ta ƙarasa kitchen, ta samu su Ladi masu aiki a kitchen sun gama girki ta ce Su zubowa yaro Abdul zai ci.
Jiki na ɓari Ladi ta ɗauki lafiyayyen filet ɗan madai-daici ta shaƙe masa shi da cous-cous da miya haɗe da naman rago akai, ta miƙawa Lami.
Ƙarba ta yi ta juyo ta nufi ɗakin Abdul, an yi Sa'a Hajiya bata falo don haka ba a samu wata matsala ba.
Sauke shi ta yi ƙasa kan carfet, sannan ta miƙa masa kwanon, sai ta ga har hannunsa na kyarma gun amsawa, hakan ya nuna tsananin buƙatarsa ga abincin, nan take ya fara ci hannu baka hannu ƙwarya.
Jinjina kai ta yi cikin tausayawa, ta juya zuwa boys quaters da yake can ne mazaunin 'yan aikin gidan, ta ɗauko masa maganin ciwon ciki ta kawo masa.
Bayan ya gama cin abincin ta ba shi ya sha sannan ta kwantar da shi, nan da nan barci ɓarawo ya yi awon gaba da shi.
A haka Abdul ya ci gaba da rayuwa cikin tsana da tsangwamar matar uba da ƙiyayyar yayyen uba.
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
Waye Alhaji Munir?
Sunansa na asali shine Munir Abbas.
Mahaifinsa Alhaji Abbas tsohon ɗan kasuwa ne, yana da yara Goma sha uku.
Matansa biyu, Saratu da Sa'adatu, Saratu ce uwar gida tana da yara Goma, maza biyar mata biyar.
Bilya shine babba sai Sani, Sunusi, Bello sai Mizbahu.
Acikin ƴaƴanta mata kuwa uku sun mutu saura biyu Hajara da Halima suke nan suka rage mata.
Yayinda Sa'adatu take da ƴaƴa Uku, namiji ɗaya mata biyu, Munir shine babban ɗanta sai Hadiza da Fatima.
Alhaji Abbas ya aurar da duka ƴaƴansa mata, yayin da ya aurar da wasu daga cikin mazan, ya na zaune da iyalinsa a unguwar ƙofar kaɗe can cikin gari.
Yaransa sun taso cikin haɗin kai da ƙaunar junansu, da kuma kyakkyawar tarbiya da suka samu daga iyayensu.
Lokacin da Alhaji Abbas ya fuskanci tsufa ya taso masa, sai ya ɗauki ƴaƴansa maza ya saka su a harkar kasuwancinsa, manyan su ke kula masa da shagunansa, ƙananan kuwa ya rarraba su a shagunan abokansa suna masu jiran shago, daga cikin waɗanda ke shagunan abokansa akwai Munir, mai gidansa ya na sonsa sosai saboda gaskiya da riƙon amanarsa, bayan wani dogon lokaci Munir ya bunƙasa har ya tsayu da ƙafafunsa ya buɗe shaguna guda biyu inda yake siyar da yaduka da atamfofin mata, a dai-dai lokacin ne kuma ya samu aikin gwamnati, bayan kammala digirinsa.
Lokacin yana da shekaru ashirin da bakwai a rayuwarsa.
Ya samu aiki a asibitin amanawa na jihar Sokoto, inda yake bangaren gwaje-gwajen jini.
Ya ji daɗi sosai, duk da albashinsa a lokacin ba wani mai yawa ba ne, a haka ya daure, domin da babu gwara ba daɗi, wannan aikin da yake bai hana masa yin kasuwancinsa ba, da ya dawo daga gun aiki yake wucewa kasuwa.
A lokacin ne kuma ya haɗu da wata budurwa mai suna Zulaiha ta waya, sai dai Zulaiha ba mazauniyar jihar Sokoto ba ce 'yar jihar Taraba ce, da farko bai san ko ita wacece ba, daga ta yi kuskuren number ta Kira shi, shikenan ya kamu da ƙaunarta, su na gaisawa a waya matsayin abokai lokaci zuwa lokaci, sai daga baya ya bayyanar mata da soyayyarsa, ba musu ta karɓa da yake ita ma tun ranar farko da suka fara waya ta ji ya kwanta mata a rai.
Shi a tunaninsa duk 'yar gari ce sai da tafiya ta yi nisa, sannan ya tambaye ta wace unguwa take anan Sokoto ya na so zai zo su haɗu.
A lokacin ne take shaida masa ita ba 'yar nan ba ce, ta na zaune a jalingo ne ta jihar Taraba.
Lokacin da ya ji wannan labarin sai jikinsa ya yi sanyi laƙwas, har ya fara sarewa da soyayyarta, sanin a yanzu ba zai iya tafiya har can ba, idan ma ya je ba lallai iyayensa su amince masa auren wacce ba 'yar gari ba.
Amma saboda tsananin ƙaunarta da yake haka suka cigaba da soyayyarsu, tare da alƙawarin cewa watarana zai zo jihar Taraba su yi zancen aure.
Watarana Munir ya shirya ya je Taraba ya gano Zulaiharsa bayan kwana biyu ya dawo gida cike da murna.
Bayan shekara biyu iyayensa suka shirya zuwa Jalingo don nema masa auren Zulaiha, duk da sai da aka kai ruwa rana, kafin iyayensa su amince masa da batun auren.
Sun isa jalingo lafiya, sannan sun samu tarba iya tarba, da karammawa daga fulanin Jalingo, kasancewar garin da nisa dole sai da suka kwana biyu a ranar na uku suka juyo cike da murna, su na ji a ransu haƙiƙa ɗan su ya yi mata, ya samu natsattsiya mai tarbiyya, daga can aka sako ranar aure nan da shekara ɗaya.
Murna ce fal ran Munir da Zulaiha, ganin suna daf da cika burinsu na zama ma'aurata.
Bayan shekara ɗaya aka sha shagalin bikin auren Munir da Zulaiha.
'Yan uwan Zulaiha suka yo tattaki har jihar Sokoto, don rako amaryarsu ɗakinta.
Bayan amarya ta tare a gidanta dake unguwar Nakasari bayan school of nursing, suka ci gaba da shimfiɗa ƙauna da soyayyarsu, zaman lafiya suke sosai ba hayaniya bare tashin hankali kasancewarsu masu haƙuri da juna.
Kwanci tashi asarar mai rai, su na nan a haka, har aka share shekaru biyar ko ɓatan wata Zulaiha bata taɓa yi ba, nan fa abin duniya ya dame ta, Munir ɗin ne ma mai lallashinta da lallaɓa ta, yana kwantar mata hankali da cewa ai haihuwa nufin Allah ce, wata rana za su samu.
Da ire-iren waɗannan maganganu yake samu ya na ciwo kanta a duk lokacin da ta tashi hankalinta akan wannan maganar.
A dai-dai lokacin ne kuma arziƙin Munir ya bunƙasa, domin yanzu ya na da babban shago a tsohuwar kasuwa inda yake bada sarin atamfofi, da wasu shaguna guda huɗu a sabuwar kasuwa ya zuba yara a ciki, inda suke sayar da kayan kitchen saura kuwa, suke siyar da yadukan maza.
Haka rayuwa ta cigaba da gudanar masu, suna cikin sukuni sosai, a shekara ta bakwai ne Munir ya canza gida daga Nakasari suka koma sama road commissioner quarters, domin zuwa lokacin Allah ya tarfawa garinsa nono, ya zama hamshaƙin ɗan kasuwa har ya fara siyar da motoci ga kuma aikinsa da yake, an ƙara masa matsayi a shekarar da ta gabata.
A lokacin ne kuma 'yan uwansa suka ƙullace shi a ransu, suka fara yi mi shi hassada da baƙin ciki, domin duk ya fi su nasibi a harkar kasuwanci saboda riƙe, gaskiya su ko da suka saka zamba sai abin nasu ya lalace, har aka kore su daga shagunan, sai shine ya ɗora su akan dukiyarsa su na kular masa da ita.
Da yake ba masu amana ba ne, sai suke yin yanda suka ga dama da dukiyar, har ta kai wata rana suka haɗa kansu akan cewa kawai za su kashe ɗan uwan ne ta hanyar da ba wanda zai gane, domin su ci dukiyarsa tun kafin matarsa ta haihu.
Akan wannan tsarin suka ci gaba da tafiya, kullum su na cikin ƙulla masa gadar zare, da ya ƙetare wannan sai su shirya wata, yayin da shi kuma yake zaune da su da zuciya ɗaya.
Duk a cikin yayyensa Mizbahu ne kaɗai ba shi da burin cutar da ɗan uwansa, ganin haka ya saka su huɗu suka haɗe kansu tare da ware mizbahun daga cikinsu kullum ce masa suke "Kai dai wallahi ka yadda zucciyarka kare ya ɗauka, ɗan uba ai ba abin so na ba."
Shi ko sai ya ba su amsa da cewa "Na ji dai, ni ina da imani, sannan ban taɓa yarda a haɗa kai da ni a zalunci ɗan uwana ba, ku dai da kuka ga kuna iyawa sai ku yi, amma ina mai maku nasiha da ku ji tsoron Allah."
Cikin wannan lokacin ne kuma wataranar Alhamis Alhaji Abbas ya tashi da wata zazzafar rashin lafiya, akan haka ya saka aka tattaro masa kan ƴaƴansa ya masu nasiha tare da gargaɗi akan riƙe amanar junansu da haɗin kai ko bayan ransa.
Bayan ya sallame su kowa ya watse washe gari ya cika, sai saƙon