Showing 33001 words to 36000 words out of 42870 words
ido yake.
Sister Aysher ce ta lura da damuwar da yaron ya shiga, ta matso tana faɗar "Abdul me kake nema ne?"
Idanunsa suka cicciko da ƙwalla ya ce "Sandunana nika biɗa ban ga su ba."
"Sanduna kuma?" Cewar Mahmud da mamaki a fuskarsa.
Abdul ya ce "Eh, hitsari nika ji, ina son in tai in yi amma ban ga sandunana da nika tahiya dasu ba."
Duk da basa fahimtar Hausar yaron sosai, amma sun fahimci cewa da sandunan yake tafiya.
"Hakan na nufin yaron gurgu ne?" Mahmud ya faɗa a ransa.
Dr Yasir ya matsa kusa yana duba ƙafafun yaron, nan fa ya shiga damuwa, ya juyo kan Mahmud ya ce "Yaron nan fa gurgu ne, da dukkan alamu ƙafar tasa bata samun kyakkyawar kulawa, saboda yanda ta fara lalacewa, yana da buƙatar kyakkyawar kulawa cikin gaggawa."
"Hmmm!" Mahmud ya sauke ajiyar zuciya tare da faɗar "Gashi ina sauri yanzu nake so na wuce Kaduna ya za'ayi kenan?"
Suna cikin maganar sister aysher ta goya Abdul a bayanta, ta kai shi banɗaki ya yi fitsari.
****
Yasir ya ce "Idan ba damuwa kabar shi anan, ni zan san yanda za'a yi, zan kuma sama masa sabbin sanduna, in yaso daga baya ka dawo ayi maganar....
RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*
*AND NOW*
*HALITTAR ALLAH CE*
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
PAGE 43-44
Ajiyar zuciya Mahmud ya sauke, sannan ya janyo ledar hannunsa ya miƙa wa sister aysher abincin da ya siyowa yaron ya ce "Mun manta anata zance,ki bashi abincin nan ya ci yanzu."
Juyawa ya yi ga Dr Yasir ya ce "Mu je office ɗinka sai mu ƙarasa tattaunawa a can."
A tare suka fice daga ɗakin, suka bar sister aysher tana bawa Abdul abinci.
Bayan isar su office ɗin, Dr Yasir ya zauna kan kujerarsa, shi kuwa Mahmud tsabar damuwa ko zama bai samu yi ba ya ce "Ina jinka Dr yanzu me kake ganin za'a yi akan matsalar yaron nan."
"Kamar dai yanda na faɗa maka daga farko, a ganina kabar shi anan mu zamu cigaba da kulawa da shi har zuwa lokaci da zai fara samun sauƙi, in ya so idan ka kammala uzurorinka sai ka zo ka tafi da shi." Cewar Dr Yasir.
Huci ya yi kaɗan tare da furzar da iska cikin damuwa ya ce "Shikenan zan tafi na bar amanar yaron a hannunka, amma don Allah ka kula sosai, ina matuƙar jin tausayin yaron nan saboda yanada special needs, zan tafi na barshi anan ne kawai saboda na yarda da kai sosai, kuma akwai buƙatar yaron ya samu kulawar likitoci a yanzu, da nake ganin idan na ce zan tafi dashi zai jiggata a hanya ne, da ba don haka ba ai....
Shikenan dai, don Allah ka kula da shi sosai."
"Ka kwantar da hankalinka insha'allah zan yi abinda ya dace." Cewar Dr Yasir.
Nan Mahmud ya masa Sallama ya fita jiki a saɓule, da har zai kuma leƙawa ɗakin don ya ga yaron, sai ya ji ba zai iya kuma kallarsa sannan ya tafi ba shi ba, don haka ya juya tare da ɗaukar motarsa ya fice daga asibitin gaba ɗaya.
@@@@@@@@@
Hajiya Hasina kuwa rayuwa ta mata daɗi yanzu, sai nishaɗi take abunta.
Kusan rabin kadarorin Alhajin yanzu duk sun zama nata, don kuwa ta saka shi yasa hannu a takardun wasu filayensa da gonakinsa cewar ya mallaka mata su...
Sai bushasharta take, a yanzu ko kasuwa Alhaji baya fita sai da izinin ta.
Ganin ta samu wannan damar ya saka ta fara tara ƙawayenta a gidan.
Kulu da ada take tsoron zuwa gidan, yanzu kanta tsaye take zuwa duk lokacin da ta ga dama, wani zubin ma sai ta yi sati a gidan, sannan ta tafi.
Ɗakin Abdul ada shi ne ya zama na ƙawayen hajiyar duk sanda suka zo gidan.
Yau ma kamar ko yaushe, zaune suke a falo suna hirarsu ta duniya da ƙyaƙyata dariya, a gabansu abinci ne kala-kala sai ci suke suna nishaɗi.
Binta Angulu (ɗaya daga cikin ƙawayen Hajiya Hasina) ta ce "Gaskiya Hajiya kina burge ni, dubi yanda kika juya alhajinki son ranki, nima gaskiya ato a kai ni wurin bokan ga in samu a mallake min Alhaji Tanimu, ke san duk cikin zawarawana babu wanda ya kai shi kuɗi duk da dai mummuna na.."
Gabaki ɗaya suka saka dariya, Hajiya Hasina ta ce "Ai gaki ga
Kulu nima ita takkaini, don ma ban tashi komawa ba, da tare muka tahiya a koma yimin wani aiki."
Fiddo ido waje Jummai Jaɓa ta yi tare da cewa "Wani aiki kuma! Wai kuna nufin Duk mallakar Alhaji da kinka yi bai ishe ki ba, sai kin haɗa da wani aiki?."
Dariya Hasina ta yi ta ce "Ba ki ganewa, akwai wani aiki guda da yar-rage gabana."
"Wane aiki kenan?" Cewar Kulu.
"Ke dai a yi sha'ani kawai, in lokaci yayyi ji kikai." ta mayar mata da amsa.
Tana gama faɗa ta miƙe ta yi cikin uwar ɗakanta, su kuma suka ci gaba da kallon Tv.
@@@@@@##
Tafiya yake a mota amma hankalinsa yaƙi kwanciya, sai tunanin halin da yaron zai iya shiga bayan baya nan yake.
Har ya durfafi hanyar fita garin, ganin ya kasa samun nutsuwa yasa ya juyo zuwa Asibitin.
A dai-dai lokacin da Yasir ya ɗaga Allura zai masa, shi kuma ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo.
Da sauri Yasir ya juyo, ganin mai shigowar ya saka ya zazzaro ido alamun mamaki.
"Mahmud kai ne?"
"Ni ne Dr, hankalina ya kasa kwanciya shi ne na zo na tafi da shi." Ya bashi amsa.
Nan fa Yasir ya shiga bashi baki da nuna masa illar tafiya da shi a cikin wannan halin da yake, amma Fur Mahmud ya ƙi ji ya kafe sai ya tafi da shi.
"To idan ka tafi da shi ina zaka ajiye shi? Kai dai Gwauro ne bare kace zaka kaiwa matarka shi, kuma ba zaka iya kula da shi ba saboda aikinka, yaya kenan?"
"Hajiyata zan kaiwa amanarsa...."
Tun bai ƙarasa ba Yasir ya katse shi da cewa "Ka dai san halin Hajiya sarai, kafi ni sanin yanda ta tsani talaka da Musakai amma...."
Hannu ya ɗaga masa alamun ya isa ya ce "Koma dai menene ita ce Mahaifiyata na san za ta fahimce ni, Malam cire masa wannan drip ɗin zamu tafi......
RUKY I LAWAL❤️❤️❤️❤️
*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*
*AND NOW*
*HALITTAR ALLAH CE*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
PAGE 45-46
Jiki a sanyaye Dr Yasir ya cirewa Abdul drip ɗin, bai kuma cewa komai ba, saboda lura da ya yi ran abokinsa ya ɓaci da maganarsa.
Shima Mahmud ɗin bai kuma cewa kanzil ba, ya ɗauki Abdul zuwa motarsa.
Abdul ya kalle shi ya ce "Yaya ina zamu na?"
Murmushi ya sakar masa ya ce "Abdul gidanmu zan kai ka, ai nasan zaka so zuwa Kaduna koh?"
"Lah! Kaduna ta cikin state and Capital da anka koya muna a NURSERY?"
Abdul ya faɗa cike da fara'a.
Sosai ya bawa Mahmud dariya, sai da ya ɗan dara sannan ya ce "Ita fa, da alama baka taɓa zuwa ba koh?"
Ya tambayi yaron dai-dai lokacin da ya gama dai-daita zamansa a gaban motar tare da kunna ta.
"Eh yaya ban taɓa zuwa ba ba......" Sai kuma ya yi ɗif kamar wanda wuta ta ɗaukewa.
"Ba me ba Abdul?" Mahmud ya tambaya.
"Na mance abinda nika son cewa."
Murmushi Mahmud ya yi a ransa ya ce "ƙuruciya kenan."
Ji yayi yaron ya ƙara shiga ransa, duk da shima zancen gaskiya daurewa kawai yake yana kallon yaron, tun yana tsoronsa har ya ji ya fara sabawa da ganin halittarsa.
A haka ya ci gaba da jan Abdul da hirar da ta shafi danginsa yana tuƙi, amma bai yi nasarar samun wani labari da zai haska masa waye Abdul ɗin ba, domin kuwa an riga an shafewa yaron tunanin ahalinsa gaba ɗaya.
Sai gab da Magriba Mahmud ya fara shiga garin Kaduna, ko da ya isa unguwarsu an idar da Sallah don haka kafin ya ƙarasa ya tsaya massalacin farkon layinsu ya yi Sallah sannan suka ƙarasa gida.
Ko da ya shiga falonsu Hajiyarsa bata nan, da alama tana sama.
Anan ya ɗaga waya ya kirata.
"Hello Hajiyata Barka da dare."
Shiru ya yi alamun ana magana a ɗaya ɓangaren, zuwa can ya ce "uhmm! Hajiya ai na ƙaraso gida."
Ya kuma yin shiru, ba jimawa ya yi murmushi ya ƙara cewa "Allah da gaske Hajiyata yanzu haka ina falon ƙasa, sauko ki gani."
Daga haka ya kashe waya tare da yin 'yar dariya ya ce "Hajiyata kenan! To banda abin Hajiya miye abun mamaki ma a cikin dawowata yanzu?."
Bayan kamar mintuna biyar sai ga Hajiya ta fito cikin shigarta ta alfarma tana washe baki.
Shi kuwa Mahmud yana zaune kan kujera ya bawa ƙofar ɗakin hajiyar baya, don haka bayansu kawai take iya gani.
"Welcome My Son, kai da wanne yaro ne zaune?" Ta faɗa a lokacin da take takowa zuwa inda suke.
Da sauri ya juyo yana washe haƙora ya ƙarasa gare ta tare da durƙusawa ya gaishe ta.
Cike da fara'a ta amsa shi tana nufar kujerar da yaron ke zaune, burinta shine ta isa gaban kujerar don ganin wane yaro ne wannan ya zo ya zauna mata kan kujera haka.
Ko kusa bata kawo tunanin cewa Mahmud ya zo da yaron ba, ta zata irin yaran nan ne masu tsaurin ido.
Ganin ta nufi gun gadan-gadan yasa cikin Mahmud ya ɗuri ruwa, sai yanzu ne yake ganin girman wautarsa ta zuwa da yaron gidan...
Tun bai ƙarƙare tunaninsa ba ya ji Hajiyarsa ta tsunduma ihu tare da runtse idonta da ƙarfi, a lokacin da Abdul ɗin ke faɗar "Mama ina yini?"
Ido a rufe ta ce "Son fitar mun da wannan yaron daga nan pls."
Kasaƙe ya yi kamar bai ji ba, jin shirun ya fara yawa ya saka ta yi tunanin ko Mahmud ɗin ya je fitar da yaron, kawai sai ta buɗe idonta.
Wani ɓacin rai ne ya ziyarci zuciyarta a lokacin da ta sauke idonta kan Abdul, shiko sai rarraba ido yake kamar an koro shege daga lahira.
Tsawa ta dakawa Mahmud wanda ba iya Abdul kaɗai ba, har shi Mahmud ɗin sai da 'yan hanjinsa suka kaɗa ta ce "Ban ce ka fitar mun da wannan nakasasshen yaron ba? Su ma masu gadin nan bansan amfaninsu ba, da suka bar wannan yaron ya shigo mun har falo, amma zan gamu dasu ne." Ta yi ƙwafa.
Daƙyar ya tattaro nutsuwarsa ya ce "Ki yi haƙuri Hajiyata ni ne fa na shigo dashi nan."
Wani irin kukan kura hajiyar ta yi ta yi cikin Mahmud gadan-gadan tare da balbale shi da Masifa.
Faɗar take "Wannan wane irin iskanci ne? Sarai ka sani cewa na tsani ganin nakasasshi bare kuma wannan da dukkan Alama ba iya nakasa kaɗai yake da ba, harda talauci."
Jiki a sanyaye Mahmud ya ce "Don Allah Hajiya ki saurare ni, wannan yaron yana matuƙar buƙatar taimakon mu, yanzu idan kika kore shi fa ko tafiya ba zai iya yi ba, saboda gurgu ne, na ɗauko shi ba tare da sanin hakan ba, sandunansa kuma suna can yashe a inda na ɗauko shi..."
Zama ta yi tana huci ta baza kunnuwa tana jin tatsuniyar da ɗan nata yake gayamata.
Ganin ta zauna ya saka masa ƙwarin gwuiwar ci gaba da magana.
"Yanzu dai Hajiyata don Allah ki taimaka ki barshi ya zauna anan...."
Tun bai gama rufe bakinsa ba ta daka masa tsawa "Wai baka da hankali ne son? Ni ce zan zauna da wannan abun anan gidan? To kasani ko kwana ba zan barshi ya yi anan ba, yanzun nan zaka mayar dashi duk inda ka ɗauko shi, waya sani ma ko aljani ne."
Durƙusawa ya yi a gabanta yana mata magiya, "Don Allah Hajiya ko sati ɗaya ne ki barshi ya yi, zan nema masa sanduna daga nan sai na mayar dashi."
Duk wannan magiyar da yake bai saka Hajiyarsa jin tausayinsu ba, daga ƙarshe ma miƙewa ta yi, ta ce "Bari ma ka gani, in kai ka kasa."
"Hanne! Hanne!!"
Ta ƙwalawa mai aikinta kira.
Da gudu hanne ta fito tare da faɗar "Ranki yadaɗe gani."
Cike da tsanar yaron ta nunawa Hanne shi da hannu ta ce "Fitar mun da wannan abun daga nan."
Cike da mugunta ta nufi Abdul da tun ɗazu ya ke kuka, ta kinkime shi kamar kayan wanki ta watsar a wajen sashen Hajiyar.
Mahmud na ganin hakan ya tashi rai a ɓace ya nufi kofar fita, Hajiya na kiransa amma ko waiwayowa bai yi ba.
A ƙofa suka haɗu da Hanne ya aika mata wata muguwar harara, tare da yin ƙwafa mai nuni da zaki gane kurenki.
A ɗarare Hanne ta yi ciki, don tana Masifar tsoron wannan fitinannen boss ɗin nasu.
A zuciye ya fice yana neman inda aka jefar da yaron.
A dai-dai lokacin ne kuma wayarsa ta hau ƙugin neman agaji, ya zaro ta daga gaban aljihu ya duba, wani uban tsaki ya ja cike da jin haushin mai kiran.
Shi sam ma ya manta da abinda ya maido shi garin cikin gaggawa, ya manta da alƙawarin da ya yiwa masoyiyar tasa saboda tsabar tashin hankalin da ya shiga yanzu.
Wayar ya kashe gaba ɗaya tare da mayar da ita aljihu ya ci gaba da neman yaro Abdul....
RUKY I LAWAL CE❤️🌹🌹
*HALITTAR ALLAH CE*
🧑🏻🦼🧑🏻🦼🧑🏻🦼🧑🏻🦼🧑🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYGAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*
*AND NOW*
*HALITTAR ALLAH CE*
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
PAGE 47-48
Sai da ya ɗan yi tafiya kaɗan sannan ya hango shi yashe a gefe yana kuka.
Cike da tausayin yaron ya ƙarasa gurinsa, durƙusawa ya yi ya juya masa bayansa ya ce "Abdul hau na goyaka."
Ba musu Abdul ya haye bayansa yana cigaba da kukansa mai taɓa zuciya.
Miƙewa ya yi ransa a jagule yana cin takaicin irin wannan halin na Mahaifiyarsa a ransa.
A haka ya nufi motarsa ya sanya Abdul ɗin cike tare da janta ya bar gidan.
Tunda ya fita bai zame ko'ina ba sai ƙofar wani katafaren restaurant, fitowa yayi daga motar, da har zai shiga da Abdul ɗin cikin gidan abincin, sai ya tuna cewa ashe fa ba zai iya tafiya ba, sannan akwai al'umma da yawa a cikin gidan abincin, zasu iya tsorata da halittarsa.
Tuna hakan da ya yi yasa ya kalli Abdul ya ce "Abdul ka jira ni anan zan siyo ma abinci, ai kana jin yunwa koh?"
Da sauri ya ɗaga kansa yana faɗar "Eh."
"Yawwa to ka jirani a nan, me kake so na siyo maka?"
Ya faɗa yana masa murmushi.
Cike da fara'a Abdul ya ce "Ni komai ma ina ci yaya."
Murmushi ya kuma yi ya ce "Shikenan bari na shiga na fito yaron kirki."
Motar ya sakawa lock sannan ya shige cikin restaurant ɗin yana saka muƙullan motarsa a aljihu.
Shi ko Abdul yana ganin shigewar Mahmud ciki ya shiga rarraba ido a gaban motar, nan ya ƙyalla ido ya ga wayar Mahmud ɗin da ya manta a motar ya ɗauka.
Cikin sa'a kuwa bai sakawa wayar lock ba, don haka Abdul ya ɗauka ya shiga buga Games kamar yanda yake yi a wayar Abbunsa lokacin da yana gida.
Can bayan kamar mintuna goma sai ga Mahmud ya dawo, buɗe motar yayi ya shiga a nan ya tarar da abinda Abdul ɗin ke yi da wayarsa, sai a lokacin ma yasan yabar wayar a mota.
Murmushi kawai ya yi ya ce "Abdul ashe ka iya Game haka?"
"Eh," Abdul ya ce yana dariya.
"A'ina ka koya har ka iya?." Ya faɗa a ƙoƙarinsa na sake bugun cikin yaron a karo na biyu.
"Na iya, ai ina yi a wayar Ba...." Sai kuma ya yi shiru.
Nan fa yayi iya ƙoƙarinsa domin ya ji wani abu daga bakin yaron wanda zai haska masa rayuwarsa ta baya, ko ya gano danginsa ya maida shi gida, amma Abdul ya kasa tuna komai bare ya faɗa, bisa tilas Mahmud ya haƙura.
A haka suka koma gida, ko kallon part ɗin Hajiya bai yi ba, ya wuce zuwa ɓangarensa ɗauke da Abdul a bayansa, hannuwansa kuma suna ɗauke da ledojin abincin da ya siyo masu.
Yana shiga ya kullo ƙofar part ɗinsa da makulli suka shige ciki.
®®®®®®®©©
A ɓangaren Hajiya Hasina kuwa faka
Motarta ta yi a ƙofar gidan bokansu, fuskarta ɗauke da alamun damuwa ta kalli Kulu dake zaune a gefenta ta ce "Ni fa ke ga abinda yassa ban son zuwa wurin bokan ga, kullum sai ka isko layi kamat bone."
Murmushi Kulu ta yi ta ce "Hajiya ki yi hanƙuri, suma nan duk buƙatassu takkawo su kamar dai ke..."
Sosai Hasina ta kara cika kamar ta fashe, yaushe Kulu ta rainata har haka?....
RUKY I LAWAL CE❤️❤️❤️❤️
*HALITTAR ALLAH CE*
🧑🏻🦼🧑🏻🦼🧑🏻🦼🧑🏻🦼🧑🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYGAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*
*AND NOW*
*HALITTAR ALLAH CE*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
PAGE 49-50
Banda raini kamar ita Kulu zata gayawa wannan maganar "wai duk buƙatarsu ta kawo su?"
Ɗaga kai ta yi ta kalli matan da suka yi tururuwa a gurin tana kallonsu a rene, waɗannan kucakan matan ne Kulu ke haɗawa da ita?"
Siririn tsaki ta ja tare da maida hankalinta ga Kulu tace "Waɗanga mata in banda ɓidat a sani kiran sallah da Usur mikkawo su nan, banda ɓacewa? Ni banga abinda zuwa wurin boka yat ctinana musu ba, tunda duk suturarsu a koɗe take..."
"Mtsw!" Ta koma jan tsaki a karo na biyu.
"Ku ji matag-ga wai mai bunu ga gindi ka kai gudumuwat gobara ai duk taron zani-zaka na, duk waku-waku na ɓatattu, ke ma banda bala'i mi zuwa wurin bokan zai ctsinana miki...." Kulu ce ke wannan zancen a ranta kafin ta ɗago ta kalli Hasina dake tsumayen amsarta ta ce "Ke dai bari Hajjiya wanda ya yi nisa ai bai jin kira, kuma shi ɓatacce bai gane kan ɓata yake sai ya hwaɗa cikin kwatamin nadama."
Dariya sosai Hasina ta dinga yi na tare da ta lura cewa yaɓa mata magana ne Kulu ta yi ba.
Sai can ta