Showing 18001 words to 21000 words out of 42870 words
RAYA SU CIKIN AMINCI, SU TA SO DA ƘAUNAR JUNANSU, SU ZAMA MASU AMFANAR DA AL'UMMA, AMEEN YA RABBI🥰🥰
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 23-24
Mutane basu sani ba cewa murna ya kamata a taya su ba jaje ba, don kuwa murna ce fal ransu, yanzu abu ɗaya ya rage masu shi ne; su kawar da ƙaninsu don su mallake dukiyarsu, sai dai fa har yanzu da sauran rina a kaba, kuma har yanzu tsugunne bata ƙare ba wai an sai da akuya an sayi kura, domin ko da sun kashe shi za'a raba gado kuma dole za'a ajiyewa yaron dukiyarsa har a gansa, tunda ba a da tabbacin ya mutu ko yana raye.
Suna cikin wannan damuwar ne suka hau teburin shawara bayan sun haɗu a gidan Hajiya inna....
Yaya Bilya duk yafi su ɗaukar zafi, don haka ya kada baki ya ce "Ba abinda yafi kyau sai mu maida hankali mu nemo yaronga mu kashe shi tun kahin wankin hulla ya kai mu dare, don ko wanga aikin namu, shi aka kira da tufkar makaho ta gaba ta baya na warware wa."
Sani ya saki ajiyar zuciya ya ce "Gaskiyakka yaya, dole sai mun yi da gaske, tunda aikin namu a sirrance muka yinai, yanzu dai a ganina mu hanƙura mu ci gaba da biɗat yaron, tun da yanzu Munir ɗin a hannunmu yake sai yadda muka so mu yi da shi."
Sunusi ya gyaɗa kai yana faɗar "Hakane, sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba."
Da haka suka ci gaba da tattaunawarsu har zuwa wani tsawon lokaci, Mizbahu na daga gefe yana kallonsu, duk da ba ya jin me suke tattaunawa, ya san ba alkhairi suke ƙullawa ba.
Bai ce da su komai ba, sai fatan shiriya da ya bisu da ita.
¥¥¥¥¥^¥^¥^^¥¥¥
A can gidan Alhaji Munir kuwa bayan saɓanin da suka samu shi da matarsa, ta bi shi har ɗakinsa ta lallaɓa shi tare da ba shi haƙuri, kuma ta nuna masa bata damu da marin da ya mata ba, da haka ta shawo kansa ya yarda da ita, sannan ta sanar mishi ta kai report ɗin ɓatan Abdul a Marna police station ne.
Ya bata haƙurin marin da ya mata, ta kuma yafe masa cike da sakin Fuska ta ce "Bakomai mijina, na sani ka mare ni ne a cikin zafin zuciya da kuma kiɗima, ɓatan ɗa ai ba wasa ba ne, musamman mai lalura irinta Abdul."
"Nagode sosai Hasina matar albarka!." Ya faɗa cike da sakin Fuska, duk da cewa ba walwala ƙwata-ƙwata a tattare da shi tun lokacin ɓatan yaronsa.
Abinda bai sani ba shine; Hasina fa bata yafe masa da zuciya ɗaya ba, ta ƙudurce a ranta sai ta ɗau fansar wannan marin da ya mata, ko da za ta yi yawo tsirara.
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
Abdul kuwa tun a ranar da ya tabbatar ba shi da wani mai ceto ko majiɓinci al'amarinsa, duniya ta masa ƙunci, ya rasa inda zai fake ya ji daɗi, shi kaɗai a dokar daji ba ruwa ba abinci, sai dai ya yi 'yan tsince-tsincensa a ƙasa yana ci, ko kuwa ya kakkabo kunnuwan fure ya ci, ruwa kuwa sai Sa'a yake haɗuwa da ruwan kududdufi ya sha, ga shi lokacin ƙarshen bazara ne, ba a fara ruwan sama ba, don haka ne ba wata inuwa mai daɗi ko wani damshin laima da zai zauna ya fake ya ji daɗi, a haka ya ci gaba da tafiya in ya gaji ya zauna ya huta, tunani kala-kala yake har tunanin da ya girmi ƙwaƙwalwarsa a wannan yanayin sai da ya yi shi, bai haɗu da kowa ba bare a samu mai taimaka masa ya maida shi gida gun Abbunsa...
Wani lokacin haka zai zauna yana kuka yana kiran "Abbuna! ka taho ka taimake ni, yunwa zata kashe ni, ga shi bansan hanyar komawa gida ba."
¥¥¥¥¥¥^^
Ranar wuni na uku, Hasina ta nemi izinin mijinta, a kan cewa zata je duba wani ƙanin mahaifiyarta dake kwance a asibiti.
Kai tsaye ya amince mata don ba ya zaton ƙarya daga gare ta.
Tana fita bata zarce ko'ina ba sai gidan abokiyar cin mushenta, da yake a ranar ma ta ƙi yarda Direba ya kai ta.
Ɗaukar Kulu ta yi suka wuce can wani ƙauye dake gaban bafarawa estate domin a can gidan bokan Kulu ya ke.
Isar su ƙauyen Dundume ke da wuya, suka kutsa can ƙarshen garin inda gidan bokan yake, daga nesa da gidan suka yi fakin motar sannan suka ƙarasa ciki da ƙafa.
Layi suka tarar mata ne birjik waɗanda suka kauce hanya, kowacce jira take layi ya zo kanta.
Nan suka hau layi, har bayan shuɗewar awa layi bai zo kansu ba.
Hasina ta kalli Kulu da damuwa a fuskarta ta ce "Ni hwa na hwara gajiya, ke san hwa ƙarya niwwa Alhaji cewa zan je duba Kawu Basiru a asibiti, yanzu dana daɗe an samu matsala, yana iya kiran inna, ita ko ke san kwafsamin zata yi, bata iya ruhin asiri ba."
Kallonta Kulu ta yi da ɗan murmushi a fuskarta ta ce "Abukkiyata ki kwantat da hankalinki, saura kaɗan ai mu kai ga layi, ke san dama shi aski in yattaho gaban goshi ya hi zahi."
Tsagaitawa ta yi tana kallon Hasina don ta ga yanda ta karɓi zancen, jin ba ta ce komai ba kuma har yanzu da alamun damuwa a fuskarta, yasa ta ci gaba da cewa "Habah Hajjiyata! Ki ƙara hanƙuri, yanzu so kikai mu koma ya ci gaba da tuhumarki ɗanai har ya gano ke kinka ɓatar da shi? Ko so kikai Abdul ya samu mai maisai gida?"
Jin tambayoyin da Kulu ta watso mata yasa hankalinta ya yi mugun tashi, haƙiƙa ta yi ragon azanci da bata saka an kashe mata shi ba; ga shi yana son zame mata alaƙaƙai ƙadangaren bakin tulu.
Don haka dole ta haƙura har zuwa lokacin da layi zai zo kanta.
Bayan shuɗewar mintuna sha biyar, layi ya zo kansu, suka faɗa bukkar bokan..
"Salamu alaikum."
Hasina ta faɗa cikin ɓarin baki, domin ta tsorata da yanayin gurin.
"Ke la'ananna!" Boka ya daka mata tsawa ya na faɗar "Ba a min sallama a nan, don ko ba aminci kinka zo nema ba.."
Jikin Hasina ne ya fara rawa da ta yi arba da mummunan mutumin dake zaune a gabanta, kasa yin magana ta yi, sai Kulu ce ta yi magana cikin ƙarfin hali ta ce "A yi hanƙuri boka bata sani ba ne."
"A kiyaye gaba, in ba haka ba, in maida mutum kiyashi..."
Cikin ɓarin jiki Kulu ta ja hannun Hasina ta danƙwafar da ita suka zauna tare a gabansa..
"Meke tafe daku."
Ya faɗa cikin sauti mara daɗin sauraro.
"Dama Abukkiyata ce na rako don ta kawo kukanta gare ka, tana so a mallake mata mijinta, kuma a......"
(Wa'iyazu billahi! mata mu ji tsoron Allah, idan kina da wata damuwa a zuci, ki miƙa ƙoƙon bararki zuwa ga mahaliccin wannan zuciyar, haƙiƙa ya fi ki sanin damuwarki, kuma shine kaɗai zai magance miki, zuwa gun boka ba zai amfanar dake komai ba, face ya saka ki a halaka da taɓewa, ya maidaki mushrika.)
Hannu bokan ya ɗaga mata alamun ta dakata, sannan ya tada kansa sama kamar mai nazarin wani abu, can ya dawo da fuskarsa ya zubawa Hasina jajayen idanunsa ya ce "Na sani, ki na son a mallake miki mijinki ne, ya bar damunki game da ɓacewar ɗa nai, shi ko ɗan a nisanta shi daga gida kuma a shahe mai tunanin gida da kowa da ya sani a ƙwaƙwalwarsa koh?"
Cikin alamun mamaki ta gyaɗa kanta sama alamar tabbatarwa.
Bayansa ya juya, ya ɗauko sauran tarkacensa sannan ya kuma juyowa kamar yanda yake da.
Bukkar ce ta yi shiru baka jin komai, sai 'yan surutan da bokan ke yi ƙasa-ƙasa, yana yiwa kansa kirari.
Wasu ƙullukan gyallaye ya ciro guda biyu, ya miƙa mata ya ce "Wannan na jan ƙyalen ki saka masa a ruwan wanka, ki tabbatar ya yi wanka da su, sannan garin maganin ya bushe a jikinsa, na shuɗin ƙyallen kuwa ki tabbatar kin saka masa a abinci ya ci, yana ci magana ta ƙare."
Cike da murna ta karɓi ƙullukan ta saka a jaka tana godiya, a ranta ta ce "Alhaji ƙaryarka ta ƙare, sai na nuna maka ba a taɓa Hasina a zauna lafiya, don ko kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha. Ja da ni tamkar ka yi kashi gonar fara ne, ka san kuwa zata rama."
Mintsinar da Kulu ta mata, ita ta dawo da ita hayyacinta.
Kallon bokan ta yi ta ce "To boka yaron fa?"
Dariya sosai ya bushe da ita, can kuma ya gimtse kamar bai taɓa dariya ba, ya ce; "Maganar yaron nan ki bar ta, asiri baya tasiri a kansa sosai, sai dai yanzun nan zan miki aikin da zai mantar da shi kowa nasa, kuma zamu saka tsanar gida a ransa, ta yanda ba zai waiwayo ba, ke ko labarin jihar nan ba zai kuma son ji ba bale ya dawo."
Murna ce ta gama kashe Hasina.
Wani ɗan kasko ya janyo mai kama da tukunya na ƙasa, wanda ya kusan cika da wasu ruwan asiri, ya ajiye shi a gabansa.
Wasu surkulle ya karanta sannan ya shafi saman ruwan da hannunsa, sai ga hoton taswirar Abdul ta bayyana a saman ruwan.
"Ku matso ku ga ni."
Ba musu suka matsa ya nuna masu ruwan ya ce "Ko ba wannan ba ne yaron?"
Gyaɗa kai ta yi bata ma samu damar yin magana ba, ganin Abdul zaune cikin rana ƙwayam, yana sharar ƙwalla duk ya lalace a cikin kwana biyun nan.
"Madallah!" Ya faɗa sannan ya ciro wata tsabga dake kusa da shi, ya kuma karanta wasu surkulle sannan ya shauɗa tsabgar a kan hoton Abdul ɗin.
Take yaron ya yi wata uwar zabura daga zaunen da yake ya miƙe kamar zarararre...
Kallonsa su Kulu suka yi da alamun rashin fahimta.
Shi ko gogan ya taƙarƙare ya kwarara wata uwar dariya dake barazanar tsaga masu kunne.
Sai da ya yi mai isar sa sannan ya gimtse ya ce "Aiki ya kammala, wannan zaburar da kika ga ya yi ta tabbatar da cewa aikin ya tafi yanda ake so."
Cike da tsananin murna Hasina ta zaro kuɗi daga jakarta masu ɗan dama ta ajiye masa, sannan suka miƙe suka bar cikin bukkar zuwa waje; inda har yanzu akwai layi na wasu ɓatattu daga cikin mutane dake jiran fitowar su.
Takawa suka yi har gun da Hasina ta faka mota suka shiga.
Sai kuma a lokacin ne ta duba agogon hannunta, zazzaro ido ta yi ganin agogon ya buga ƙarfe biyu da rabi na rana, ita da ta baro gida sha biyu da rabi, ga shi yanzu awar ta biyu a waje bata ma je asibitin ba.
Cikin hanzari ta ja motar ta nufi cikin gari, a nan ƙofar asibitin specialist sokoto ta sauke Kulu, tare da bata kuɗin napep ta ce ta ƙarasa gida, ita tana sauri ne, zata shiga asibitin a gurguje ta dubo shi ta juya, gudun kada asirinta ya tonu.
Ba musu Kulu ta sauka ta hau napep zuwa gida; da yake ita tana girmama duk wani aiki na mugunta da kuma kare kai daga zargi.
A gurguje Hasina ta dubo kawo Basiru, sannan ta juya zuwa gidanta, domin ta san Alhaji na nan bai fita ba.
Ko da ta isa gidan ta tarar da 'yan sanda suna bincike, don haka cikinta ya ɗuri ruwa, fargaba ta kamata, kamar ta juya ta bar gidan ta ji, amma bata da mafita face ta tsaya ayi duk ya ce za'a yi; ta sani dai kushewar baɗi sai baɗi, mai rabon ganin baɗi kuwa sai ya kai, don haka ta shige cikin gidan kai tsaye.
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
A ranar wuni na uku Abdul ne tafe a galabaice, ɗan idonsa ɗayan ma ya fara gani disishi, saboda yunwa da ta masa mugun illa, ga shi tun jiya yake cikin tsanani, ya yi-ya yi ƙwaƙwalwarsa ta tuna masa wani abu game da shi amma ta kasa.
Jin ƙafarsa ta yi tsami, yasa ya nemi guri ya kwanta, da yake yamma ta riga ta yi.
Ko banza ma ƙafar ba wani warkewa ta yi ba, kasancewar ba a jima da yin aikin ba wannan ƙaddarar ta farmasa, ga shi ya daina shan magani, wannan yasa ƙafar ta ruruce masa, ɗan taka ta da yake yi a da ma yanzu ya kasa..
Yana nan kwance yana sauraron ƙafarsa har barci ɓarawo ya ɗauke shi....
Wani bafatake ne ke gangarowa cikin jejin, yayin da ya baro ƙauyensu ya nufi birni mafi kusa don kasuwancinsa.
Ya ɗan yi nisa acikin tafiyarsa, ba abinda yake sai tunanin da kuma fatan ya isa kan babban titi da wuri yanda zai samu mota zuwa cikin garin da za shi.
Bai yi aune ba sai ji ya yi ya yi tuntuɓe da abu mai ɗan nauyi.
Dubawar da zai yi haka ya ga yaro kwance kamar yana barci.
Ɗan ja da baya ya yi yana faɗar "Auzubillahi minas-shaiɗanir-rajim!"
Lura da ya yi kamar yaron na neman taimako, ya sa ya matsa yana dudduba shi, a lokacin kuwa Abdul na kwance ne a ɓarin fuskarsa dake a shafe don haka mutumin bai gano komai ba.
Sai da ya birkito shi, da niyyar ya taɓa ya ji ko yana a raye? Sa'annan ya lura da halittar fuskarsa, duk da gun ya kwaso ƙasa sosai, hakan bai hana mutumin gane mummunar halittar yaron mai ban al'ajabi ba.
Ja da baya ya yi da ƙarfi ya na faɗar "Innahu min sulaimanu wa Innahu bismillahir-rahmanir rahiim!"
A dai-dai lokacin ne Abdul ya buɗe idonsa ƙwaya ɗaya ya kafe mutumin da ido, sai ƙifƙiftawa yake......
More comment more typing.....
In har bansamu comment mai yawa ba tabbas zaku ji hiru, sati ɗaya ba typing😒🤷🏻♀️
Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal.
Vote share and comment...
RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹
*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*
*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
22safar/10 October.
1442hjr/2020.
DEDICATED TO: YARAN ALBARKA;
AFFAN, ABDUL DA IKRAM BABYNA.
ALLAH YA RAYA KU CIKIN AMINCI KU TASO DA ƘAUNAR JUNA, YA SANYA KU CIKIN SHIRYAYYI MASU SHIRYARSUWA, MUCH LOVE YARAN ALBARKA🥰🥰 Mommynku na ɗago maku hannu🙋🏻♀️
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 25-26
Daƙyar mutumin ya tattaro duk jarumtarsa ya ce "Mutum ko aljan?"
Abdul na jin wannan tambayar da sauri ya ce "Mutum ne hwa."
Don baya son mutumin ya tafi ya bar shi; don ko yau ce ranar farko da ya saka ran zai samu taimako daga wani, haka ita ce ranar farko da ya yi arba da wani mahaluƙi bayan ya riski kansa a jeji.
Cike da ƙarfin hali mutumin nan ya matso ga Abdul yana tambayarsa Wanene kai? Daga ina ka ke? Ina iyayenka ko 'yan'uwanka? Me kake kwance a cikin wannan jejin kai kaɗai?"
A jere ya jerowa yaron tambayoyin.
Maimakon ya ba shi amsa, sai ya yunƙura ya miƙe zaune ya na faɗar "Dan Allah taimakamin da ruwa da abinci, yunwa nika ji ƙwarai."
Mamakin mutumin ne ya ƙaru fiye da farko, ba tare da ya yi magana ba ya janyo salkar ruwan dake cikin kayansa, ya miƙa wa yaron.
Karɓa Abdul ɗin ya yi ya tada ita, bai ajiye ba sai da ya shinye ruwan tas, ka na ganin yanayin yanda yake shan ruwan zaka san an daɗe ba a haɗu ba.
Tausayinsa ne ya shiga ran bawan Allan nan, a take ya ji a ransa cewa zai taimaki wannan yaro, don ko da gani ka san ya na neman taimako.
Salkar Abdul ya ba shi ya na cewa "Na gode Baba, saura abinci."
"Yaro yanzu bani da abinci a tare da ni, don ina cikin halin tafiya ne, amma ta shi mu je gidana ka ci."
Jikin Abdul har mazari yake ya ɗauki sandunansa tare da miƙewa ya ce "Baba mu tahi."
Girgiza kai kawai mutumin ya yi, ya shiga gaba Abdul na biye da shi a baya.
Ganin cewa in ya biyewa tafiyar yaron Lallai sai sun yi dare a hanya; kasancewar ƙauyen nasu da ɗan nisa, ya saka ya duƙa ya cewa Abdul "Hau bayana na goya ka."
Ba musu yaron ya haye dama ya gaji, sanin ba shi da wanda zai kokawa damuwarsa ne ya saka ya dangana.
Tafiya mai nisa suka yi sannan suka isa ƙauyen, lokacin har an kira sallar magriba, don haka mutumin ya ja Abdul suka je masallaci...
Bayan idar da sallar ne suka ƙarasa gidansa.
"Assalamu alaikum." Mutumin ya yi sallama a ƙofar gida.
Daga ciki wata mace ta amsa "Wa'alaikumus salam, Muryar waye na ke ji kamar mai gida?"
"Ni ne kande." Ya bada amsa a lokacin da yake shiga cikin gidan Abdul kuwa na biye da shi a baya kamar jela.
Ita ma Kande lokacin ta matso tana cewa "Mai gida lafiya kuwa ka dawo, kai da ka fita fatauci."
"Wani muhimmin al'amari ne ya dawo da ni, yanzu dai kawo mana abinci."
Ba musu ta juya, ta nufi madafa ta ɗebo tuwon dawa da miyar kuɓewa a samira ta kawo ta ajiye masa, a lokacin har ya shimfiɗa tabarmar kaba a ƙasa, a ƙofar ɗakinsa ya zaunar da Abdul.
Ruwa ta je ta ɗebo sannan ta dawo ta zauna ta na faɗar "Mai gida wannan yaron fa daga ina?"
Domin ita sai a lokacin ta lura da yaron da ke zaune tare da shi; kuma duk da cewa duhu ya sauka ba ta gani sosai, amma ta san ba ɗaya daga cikin yaranta ba ne.
Zama ta yi gefen tabarmar cikin alamun mamaki ta ce "Mai gida wannan yaron daga ina?"
Murmushi ya yi ya ce "Wani bawan Allah ne a hanya na tsinto shi, shi ne dalilin dawowa ta gida don na ajiye shi a nan na juya."
Kallonsa ta yi a ɗage, bata ce komai ba, Allah ya sa ma a duhu ne bai lura ba.
Abdul da ya wanke hannunsa zai fara loma ya ce "Mama ina yini?"
Ba dan ta so ba, ta karɓa da ƙalau don ta na shakkar mai gidan nata.
Abdul kuwa ya shiga zuba loma, hannu baka hannu ƙwarya haka yake cin abincin, da ka gani ka san yunwa ta masa kamun kazar kuku.
Sai a lokacin Kande ta haska fitila ta na faɗar "Bari na haska na ga yaron."
Torch light ɗin da ke hannunta ta haska tare da saita fuskar Abdul ta dalla masa ita da gayyah.
Abin da ta gani ne ya saka ta zabura ta yi zumɓur ta miƙe tsaye tare da ja da baya, ta na faɗar "Na shiga uku, yau na ga abin da ya fi