Showing 21001 words to 24000 words out of 42870 words

Chapter 8 - HALLITAR ALLAH CE COMPLETE

11 Jul 2025

2201

ƙarfina, mai gida ina ka samo wannan dodon?"

Inda sabo Abdul ya saba da wannan sunan da mutane ke masa, don haka ko kallon ta bai yi ba ya ci gaba da zuba loma; don ko ya daɗe bai haɗu da lafiyayyen abinci irin wannan ba.

Ɗaki ta shige jikinta na kakkarwa don ta tsorata ainun, jikinta sai ɓari yake.

Bukar ya miƙe tare da kallon Abdul ya ce "Yarona ci gaba da cin abincinka ina zuwa ka ji?"

Bai jira amsar yaron ba ya bi matarsa Kande zuwa ɗakin don ya fahimtar da ita.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Isarta falon ke da wuya ta zauna kan kujera kusa da Alhaji tana faɗar "Alhaji ka gane ni sai yanzu ko? wallahi....." Domin yi ta yi kamar bata san da wanzuwar 'yan sandan a falo ba.

Kallonta Alhaji ya yi, maimakon ya tamka ta a waccan maganar sai ya ce "Hasina ga jami'ai sun zo bincike kan ɓacewar yaronmu."

"Yaronka dai." Ta faɗa a ranta.
A fili kuwa yaƙe ta yi haɗe da kallon 'yan sandan ta ce "Sannunku da zuwa."

Babba daga cikinsu ne ya kalle ta ya ce "Yawwa Hajjiya, zamu miki wasu 'yan tambayoyi idan babu damuwa."

Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi; wanda da Alhaji ya ajiye hankalinsa tabbas zai jiyo ƙarar bugawarsa.

"Ina jin ku." Ta faɗa a ɗan sanyaye, alamun damuwa sun bayyana ƙarara a fuskarta.

Ɗan sandan ya ce "Yawwa! Tambayar farko da zan miki ita ce "Me ya hwaru yinin ranar da anka sace Abdul?"

"Iya kat sani na dai babu abinda ya hwaru da shi a ranar; don lahiya lau mun ka ci abinci dare, kuma da kaina nit rakke shi har ɗakinai, sai da nig-ga ya kwanta nit hito." Hasina ta faɗa.

"Ok." Ya faɗa, ɗayan ɗan sandan dake gefen shi ya rubuta.

Sannan ogan ya ci gaba "Ma'aikatan gidanga sun shaida muna cewar; a daren ranar kowanensu kwana mai nauyi yat kama shi, kamar waɗanda suka sha ƙwayar barci. Haka kuma sun shaida muna a washegarin ranar ke ce mutum ta farko da kinka lura yaron bai gidan, kuma ke kinka shelanta cewa ya tsere ne daga gidan, shin ya anka yi kissan yaron tserewa yay-yi ba sace shi anka yi ba?"

Wata mummunar faɗuwar gaba ce ta ziyarce ta, har sai da 'yan hanjinta suka murɗa tsabar tsoro.

Ita sai a lokacin ma ta lura ashe falon cike yake da duk ilahirin mazauna gidan tun daga kan mai gadi har mai shara kowa na nan, hakan yasa ta ƙara burkicewa.

Nan fa zufa ya fara tattartsowa a kowace kafar ga shi dake jikinta, dama ance mara gaskiya ko cikin ruwa ya yi jiɓi.

Inda-inda ta fara yi "Am dama.... Dama na ta shi ne na je ɗakin yaron don Duba lahiya tai, sai nigga wayam bai nan, nan fa nit ruɗe nit shiga kiran ma'aikatan gidan don su tanyan biɗa tai...."

Ta na kaiwa nan ta dakata, ɗan sandan ya ce "Uhmm! Ina jin ki, ya an ka yi kissan tserewa yayyi ba sace shi anka yi ba? Kuma mi anka yi mi shi da har zai sa ya tsere daggidan Ubanai da yaka mugun so? Yaron da adda tawaya ga ƙafa, taya ya iya tserewa ba wanda yajji ko sautin sandunanai yayin da yaka tserewar?"

Waɗannan tambayoyi ya kuma watso mata.

Hasina fa ta ruɗe iya ruɗewa, don kuwa ko da wasa bata yi tunanin za'a iya zuwa wannan matakin ba, da ta tanadi kalamai don wannan ranar ; ga shi ita ba gwanar tsara abu kai tsaye ba ce sai ta ga wuya.

Ganin asirinta ya na gaf da tonuwa ga kuma Alhaji da ya kafe ta da ido tun lokacin da ta fara amsa tambayoyin, ya saka ta miƙe ta na faɗar "Don Allah ku min uzuri in shiga ciki in hito, kun ga yanzu niddawo ina da ɗan uzuri."

Ogan ya ga rashin gaskiya ƙarara a idonta, don haka ya dakatar da ita da cewa "Hajjiya da ke taimaka ke ba mu amsa sai ki shigewakki, mu ma ta shi za mu yi."

Bata saurari ɗan sandan ba, ta wuce da sauri zuwa cikin ɗakinta, ƙirjinta na lugude.

Ta sani muddin ta bari Alhaji ya gano tana da sa hannu a wannan al'amari tabbas kashinta ya bushe; don ko a kan Abdul zai iya komai ciki kuwa har da sakinta; ga shi ita ko bata gama cika burinta ba a zaman gidan.


Ganin ta shige ya saka jami'an suka miƙe su na faɗar "To Alhaji mu zamu tahi, sai mun dawo."

Ogan ya juya ga ma'aikatan dake zaune gun shiru kamar ruwa ya ci su, ya ce "Kuna iya tahiya, amma ku sani kowane lokaci mu na iya dawowa, don ko ba za mu taɓa barin case ɗinga ba, har sai mun gano mai laifin, an hukunta shi."

Alhaji Munir dake zaune gun ya yi tsit, kamar ba ya nan tun shigowar Hasina sai a lokacin ya miƙe ya na cewa " To officer Nagode sosai, sai kun zagayo."

Su ma godiyar haɗin kan da aka ba su suka yi, sannan suka fice daga gidan cike da zargin Hasina don ganin yanda ta rikice, tabbas ruwa baya tsami banza.

Bayan ficewar su ma'aikatan suka watse kowa ya koma bakin aikinsa, Baba Direba ya koma kan bencinsu ya zauna, sai fara'a yake, tabbas addu'arsa ta fara karɓuwa, don ga shi alamun rashin gaskiya sun fara bayyana ga Uwargidan ta su, Lallai ko ba ita ce da laifin duka ba, to ta na da masaniya ko sa hannu a cikin wannan aika-aikar.

Dama tun lokacin da aka sace Abdul ya duƙufa da addu'ar Allah ya tonawa koma waye asiri, sannan ya kare Abdul a duk inda yake idan ya na raye; don ko ya shaƙu matuƙa da yaron, shiyasa ya fi duk ma'aikatan gidan damuwa da ɓatan yaron.

Alhaji kuwa bayan ficewar su komawa ya yi ya zauna, ya na mamakin yanda ya ga matarsa ta rikice, haƙiƙa idan ba kuskuren fahimta ya yi ba, ya ga kamar hankalinta ya tashi matuƙa, duk wata alamar rashin gaskiya ta tabbata a gare ta.

"To me hakan ke nufi? Ta na da saka hannu a ɓacewar yaronsa?"

Zuciyarsa ta bijiro masa da tambayoyin, nan take hankalinsa ya tashi, sai kuma ya shiga girgiza kai yana ƙaryata zuciyarsa.

A bayyane ya ke faɗar "Ina ba zai yiwu ba! Matata ta na da amana, ba za ta taɓa iya cin amanata ba."

Ganin wannan ba mafita ba ne ya yanke shawarar bin ta cikin ɗakin, don tabbatar da zarginsa ba gaskiya ba ne.....



More comment more typing........


Na ji shiru zaku ji shiru...

Idan na ga guntun sharhi zaku ga guntun page next😹😹





Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal





RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

26safar/14 October.
1442hjr/2020.

DEDICATED TO: ALZAZ GROUP🥰🥰

Mutanena wannan page naku ne, ku ji daɗin ku dashi🥰🥰

So da ƙauna mara iyaka, ina ƙaunar ku fisabilillahi🥰🥰

Da fatan Allah ya ƙara haɗe kanku.






________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_


*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*


PAGE 27-28

A cikin ɗakin ya same ta ya shiga watsa mata tambayoyi cike da tuhuma.

Sosai antar cikinta ta kaɗa, daƙyar ta samu dabarar fitar da kanta, a ranta ta ce "Cab! Lallai ya zama dole a gare ni na yi gaggawar amfani da maganin nan da boka ya ban tun kan tusa ta ƙurewa bodari."

Ta yi iya bakin ƙoƙarinta a wurin ranar domin ta samu Alhaji ya yi wanka da ruwan maganin, amma abin ya ci tura, don kuwa cewa ya yi shi ba wani wanka da zai sake yi yanzu, a kan dole ta haƙura domin ba ta so ta takura shi har ya ɗago jirginta.

Sai dai ta saka mi shi ɗayan maganin a abincin dare ya ci, hakan ya saka ta tsananin murna, tare da fatar ta samu irin wannan nasarar a gobe.

¥¥¥¥¥¥

A can gidan Bukar kowa bayan ya bi matarsa ɗaki ya shiga lallaɓata a kan ta daure ta riƙe masa yaron nan, faɗar yake "Kande ki yi haƙuri ki riƙe yaron nan amana, shi ɗa na kowa ne idan kika taimaki wannan watarana Allah zai kawo wanda zai taimaki ƴaƴanki a lokacin da suka yi nisa dake."

"Habah! Mai gida ka gane mana ni bance bana son riƙe shi ba, halittarsa nake tsoro, da ace gurgu ne kawai ko kuma wani lafiyayyen yaro ka tsinto da zan fika farinciki ma, amma ni dai gaskiya tsoron wannan dodon nake." Ta mayar masa da amsa.

"Haƙuri zaki yi Kande Allah ya kan jarabci bayinsa ta ko wacce fuska don ya gwada imaninsu, shima wannan ai *HALITTAR ALLAH NE* haka Allah ya tsara halittarsa, ba shi ya yi kansa ba, meye laifinsa don ya zama nakasasshe? Hallau ma bamu san meya rabo shi da gidan iyayensa ba, barinsa cikin jeji shi kaɗai hatsari ne sosai shiyasa na kawo maki shi, kin san 'yan magana sun ce ka taimaki na ƙasa gare ka sai Allah ya taimake ka."

Ɗagowa ta yi ta kalle shi a ɗage ta ce "Mai gida gaskiya ni ba zan iya riƙon wannan dodon ba, haka kurum ya tsorata ni cikin da....."

Kafin ta ƙara sa ya tari numfashinta da tsawa "Dakata Kande! Bar ganin ina lallaɓaki ki ce zaki zo min da raini, yanzu sai inci mutuncinki, yaro kuma dolenki ki riƙe shi umurni ne ba shawara ba, gobe-goben nan zan juya idan ya zo in na tafi ki yanka shi."

Ya na gama faɗa ya fice a kufule ya koma gun Abdul.

Ita ko Kande tun lokacin da ya daka mata tsawa jikinta ya hau rawa tamkar mazari, ta tsorata ainun, don ta san halin mai gidan nata da fushi, idan abin ya motsa masa kowa sai ya ji ajikinsa.

Cikin hanzari ta bi shi waje tana ba shi haƙuri.

Lokacin kuwa tuni ya iso gun Abdul da ya gama cin abincin ya sha ruwa, sai dai da alama bai ƙoshi ba, don kuwa sai rarraba ido yake, ko bai faɗa ba ka san ƙari yake so.

Bukar ya kalle shi ya ce "Abdul baka ƙoshi ba koh?"

Da yake tun a hanya yaron ya gaya mai sunansa.

Gyaɗa kai sama ya yi alamar "Eh."

Bukar ya ɗauki kwanon tare da miƙewa zai je madafa don ƙarowa yaron abinci.

A dai-dai lokacin Kande ta fito, cikin ɓarin baki ta ce "Mai gida kawo na ɗebo masa."

Ko kallonta Bukar bai yi ba ya wuce abinsa, don kuwa ta mugun ɓata masa rai.

Sai da ya kuma cikowa yaron kwano da abinci ya kawo masa.

Miƙawa Abdul kwanon da yake ya yi dai-dai da shigowar yara maza guda biyu a gidan.

Ɗayan ba zai wuce sa'ar Abdul ba, ɗayan kuma zai kai shekara sha huɗu.

Kai tsaye suka nufo gun Babansu suna faɗar "Sannu da dawowa Baba, ashe baka tafi fa?."

Wani mummunan kallo ya aika masu, sai dai abinda ya yi shi ake kira aikin banza harara a duhu, don kuwa ba su ma lura da yanayin fuskar tasa ba saboda duhu, sai ji suka yi ya ce "Eh, da kun ɗauka na tafi, shiyasa kuka fita yawon shashanci a gari? Ashe haka kuke idan bana nan koh?"

Sanin halin Baban nasu yasa suka shiga inda-inda daga ƙarshe Basiru ya yi wuf, ya ce ashe baƙo muka yi?"

Domin sai a lokacin ya lura da yaron dake cin abinci, saurin waigawa Badaru ya yi don ya ga baƙon da ya ji ƙaninsa ya faɗa.

Cikin sake fuska Baban ya ce "Na samo maka aboki ne Basiru."

Daɗi sosai yaron ya ji ya tafi da gudu gun Abdul ya rungume shi ya na jin daɗi, har ya na faɗar "Yau shimfiɗa ɗaya zamu kwana."

Baya da sanannen ciki a kan yanda halittar Abdul ɗin take.

Bayan Abdul ya gama cin abincin, Bukar ya tasa shi gaba da tambayar garinsu, 'yan'uwansa da dalilin zaman shi a jeji.

Nan fa Abdul ya saka masu kuka, don kuwa ya yi-ya yi
Ƙwaƙwalwarsa ta tuna masa wani abu game da shi ya kasa, shi dai ya san yana da iyaye amma ya manta komai game da su, sunansa ne kawai bai manta ba, don haka ya ce "Baba na mance komi, ni ban ma san kowa anni ba."

Shiru ya yi alamar tunani, can ya ce "Na san dai ina da Uwaye, amma dai na mance komi."

Haka Bukar ya yi iya ƙoƙarinsa ya sa Abdul ya tuna wani abu ya gaya masa, amma abin ya ci tura, a kan dole ya bar zancen, don ba ya son tursasawa yaron, ya ƙudurce a ransa idan ya dawo daga fatauci zai sake tambayarsa, ya san zuwa lokacin yaron ya sake sosai.

Daƙyar Kande ta shawo kan mijin nata, ta nuna masa ta amince ta kuwa gane kuskurenta, amma a ranta faɗar ta ke "Ba dai gobe zaka tafi ba? Kana tafiya zan kora ɗan banzan dodon nan, waya sani ma ko aljani ka kwaso mana, garin kwashe-kwashenka? Haka kawai ka ɗebo mana ƙamaya-maya? Ai ba zai yiwu ba."


Tun da asuba kowa na gidan ya tashi, Bukar ya ja yaransa maza zuwa masallaci, da yake shi mutum ne mai riƙon addini dai-dai gwargwado.

Har zuwa lokacin su Badaru ba su ankara da fuskar Abdul ba, kasancewar har lokacin da duhu.

Sai bayan sun dawo ne da haske ya fito suka gan shi, nan fa hankalin Badaru ya tashi, Kande ma ta ƙara ruɗewa, ashe munin halittar yaron nan yafi yanda take tunani, duhu ne ya saka bata gani sosai ba.

Shi kam Basiru bai wani damu ba duk da cewa a farko ya ɗan tsorata kaɗan, amma da yake shi yaro ne ƙarami, sai bai damu da hakan ba, shi murna ma yake ya samu aboki, ga shi daga daren jiya zuwa yau har ya ɗan saba da Abdul ɗin.

Da hantsi Bukar ya tara iyalan gidansa ya basu amanar yaro Abdul, tare da jaddadawa Kande ta yi haƙuri ta riƙe masa amanar yaron Kafin ya dawo ya maida shi gidansu, sannan ya tafi.

¥¥¥¥¥

A ɓangaren su Alhaji Bilya kuwa, sun baza koma sai neman yaro Abdul suke ta ko ina, sun baza yaransu don su nemo masu shi.

Ga kuma dukiyar ƙanin nasu da suka shiga ragarza-gaza don kawai sun san sun asirce shi baya iya masu magana.

¥¥¥¥¥¥¥

Da misalin ƙarfe tara na safe Hajiya Hasina ce a banɗaki ta na haɗawa Alhaji ruwan wanka; Abunda bata saba yi ba.

Amma da yake ta san abinda take son ƙullawa ne jikinta ke ɓari gun aikin.

Haɗa mi shi ruwan ta yi, sannan ta ɗauko maganin ta barbaɗa kaɗan yanda ba zai sauyawa ruwan kala ba, sannan ta fito ta na kwarkwasa kamar wata kilaki.

Gefe gado ta same shi zaune, ta matso ta na cewa "Alhajina ruwanka sun zama ready, wanka ɗai yarrage ma."

Miƙewa ya yi jiki ba kuzari ya ce "Na gode matar albarka, bari na fito."

Ya nufi ban ɗakin ya na takawa a hankali kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki, da ganin yanayinsa ka san ya na cikin matsananciyar damuwa, don ko duk ya rame ya yi baƙi, ɓatan tilon ɗansa ya taɓa shi matuƙa, ta yanda da har abinci baya iya ci sosai, baya da wata sauran nutsuwa, farinciki ya ƙaura daga gare shi.

Bayan shigewarsa, Hasina ta zauna gefen gadon tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, a ranta take faɗar "Munir ƙaryarka ta ƙare! ka na gama wannan wankan ka zama ƙarƙashin ikona sai yanda na yi da kai, ni ko na maka alƙawarin zan juya ka kamar waina a tanda, yanzu lokaci ne da zan ɗau fansar marina da ka yi a kan dodon ɗanka."




More comment more typing.......


Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal






RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

28safar/16 October.
1442hjr/2020





________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_



*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*


PAGE 29-30


Tana nan zaune ta kafe, ƙofar da ido sai zuba wani shu'umin murmushi take har zuwa lokacin da ta ji ya turo ƙofar banɗakin, Alamun ya gama zai fito.

Ƙara gyara zamanta tayi tare da faɗaɗa murmushinta ta ce "yawwa! Abu ya yi daɗi an bawa mayya jiran gawa."

A hankali ta furta maganar.

"Mi kika cewa ne matar albarka?" Ya faɗa yayin da yake takowa zuwa gunta.

"Ah! Babu komi Alhajina, hat ka gama wankan?"

"Eh." ya ce a taƙaice.

Daɗi ne ya lulluɓeta, sai kuma wata zuciyar ta ce mata "Idan zubar da ruwan ya yi fa?"

Dam! Ta ji ƙirjinta ya buga.

Kallonsa ta yi ta ce "Am! Alhaji nit ce da ruwan da nit zuba ma kayyi wanka ko?" Ta tambaya cike da zullumi.

"A'a tusshesu niyyi..."

Da ƙarfi ta miƙe tsaye tana zazzaro ido waje "Tussuwa hwa Alhaji? Kamar wani ƙaramin yaro?" Ta faɗa.

Yanda yanayinta ya canza kai tsaye ya matuƙar ba shi mamaki da dariya, duk da baya jin zai iya dariya yanzu, sai dai ya ɗan murmusa; kasancewar tun da ya fara wankan yake jin wani sabon yanayi ga ƙai-ƙaiyi da yake ji ajikinsa, hakan yasa bayan ya gama wanka da ruwan, ya ɗebi wasu tsabtataccin ruwa ya ɗauraye jikinsa, ko ya daina jin ƙaiƙayin.

Sai da ya wuce gaban madubi ya tsaya sannan ya ce "Wasa ni kai miki, ina ni ina tussa ruwan da yau aka fara haɗa min?"

Wata uwar ajiyar zuciya ta saki har sai da ya juyo ya kalle ta, kamar zai tambaye ta kuma ya share.

Murmushin mugunta ta yi ta ce "Ina zuwa Alhaji."

Da Gama faɗa ta fice daga ɗakin zuwa na Abdul da ba kowa a ciki yanzu, ta rufe ta hau ɓaɓɓaka dariya tana cewa "Na kama babban kihi, Munir ka dawo ƙarƙashin ikona yanzu muddin ruwan maganin sun bushe ga jikinka."

Wata mahaukaciyar dariya ta kuma bushewa da ita, wacce da akwai mutane a kusa da falon tabbas da sun jiyo ta.

Kulu ta kira ta shaida mata ta gama aiki sannan ta ɗora da cewa "Gobe ki taho gidana da sahe kahin ya hita, ki ga ikon Allah."

Sun yi nisa a wayar ta tuna da Alhaji yana shiryawa a ɗaki.

A hanzarce ta kashe wayar ta fito zuwa ɗakin.


¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

A can gidan Bukar kuwa, bayan tafiyarsa rayuwar Abdul na tsakanin yanayi biyu, farinciki da damuwa.

Don kuwa tun bayan tafiyar tasa, Kande ta saka Abdul a gaba da hantara, muzguna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login