Showing 12001 words to 15000 words out of 42870 words
sa a dace, dama tuni munka gama magana da likitoci, rashin lahiyar ga tashi nat tsaishe mu da an daɗe da mai aiki."
Dogon numfashi Salamatu ta ja ta sauke sannan ta ce "Hmmm! To Allah ya sawwaƙa!, Allah yasa ayi a Sa'a, ko wagga lalurar ya samu ya rabu da ita ai an rage tunda waccen matsalar Halittarsa ce a haka."
Daga haka suka rufe wannan hirar aka zaro wata, har bayan wani dogon lokaci sannan Salamatu ta yiwa Hajiya sallama ta tafi.
Bata wani tsaida ta ba, dama abu ga mai jira, don tun ɗazu take jin ringing ɗin wayarta harma ta duba ta ga Kulu mai adashen sharri ce, amma ba halin ɗagawa, domin ko giyar wake ta sha ba za ta karɓa kiran Kulu a gaban yaya Salamatu ba.
Bayan ficewartan ne ta ƙule cikin ɗakinta sannan ta kira Kulu a waya, anan Kulun ta shaida mata ga ta nan zuwa gidanta yanzu domin ta samo masu wata hanya da take ganin za ta sada su da cikar burinsu ba tare da kowa ya zargi komai a kai ba.
Hajiyar ta ji daɗin wannan albishirin ba kaɗan ba don haka ta ce "Sai ke taho Abbukiyata ta kaina!."
Ta na gama faɗa ta kashe wayar, ta gyara zamanta a gefen gadon ta na jin wani nishaɗi, ta zaƙu Kulu ta zo ta ji wace kitimurmurar ta ƙullo, don ta san ƙawar tata ba dai iya makirci ba.
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥€€
A bangaren su yaya Bilya kuwa, zuwa lokacin fa abin ya dame su sosai ta yanda wannan matsalar ta ƙi ci ta ƙi cinye wa, don haka suka yi shawarar komawa gidan bokansu don neman mafita.
Su uku ne zaune a gaban bokansu wanda suke kira da malam ilu, kowanne su ya tanƙwashe ƙafafuwa su na sauraren bayaninsa.
Malam ilu ya kalle su ya ce "Wan ga yaron da kuke gani sai ku bar shi kawai, ga dukkan alamu asiri bai tasiri ga jikinai sosai, don na hanga na hango ban ga alamat nasara ba, kullum sai tahiyar hawainiya ake, ana tahiya ana dawowa baya, na rasa dalili, amma ku bar maganar yaron hannuna ni nissan wadda zan yi da shi, yanzu ku maida hankali ga uban ko kuna nasara."
Yaya Bilya ya gyara zama ya ce "To Allah ya taimaki malam, yanzu...."
Bai gama maganar ba Boka Ilu ya katse shi cikin tsawa "Sau nawa zan ce maka wanga ba aikin Allah na ba? To ka kiyayi gaba, in dai ana gabana ba a kiran sunan Allah balle a nemi taimako daga gare shi, sai dai ka kira rauhanai."
"Ayi hanƙuri Allah ya huci zucciyar Malam bai sakewa, yanzu ma mantuwa ce." Sani ya faɗa murya na rawa, domin ko da suke mazaje amma sun razana da furucinsa.
Shiru suka yi ba wanda ya kuma gigin magana can, Ilu ya kalle su ya bushe da wata mahaukaciyar dariya, sai da ya yi mai isar sa sannan ya dubi Bilya ya ce "ina jinka ci gaba da maganakka."
Cikin sanyin jiki Bilya ya ce "Yanzu abinda muka so, a mallake muna Alhaji Munir sai yadda muka yi da shi, ina ganin iya haka ɗai ya ishe mu."
Wata dariyar Ilu ya ƙara kecewa da ita sai da ya kwashi 'yan mintuna kafin ya tsagaita ya ce "Ka ga la'ananne, maƙi hukuncin Allah! Wato so kake ya zama kuka juya akalarshi da dukiyarsa koh?"
Sunusi ya yi karaf ya ce "Hakan ko Malam."
"Ta kwana gidan sauƙi." Boka Ilu ya faɗa, tare da cewa yanzu ku tashi ku tahi, bayan kwana biyu gudanku ya dawo ya amsammuku magani, abinda yassa ban baku yanzu ba, ina son sai na yi dogon bincike akainai shiyasa."
Miƙewa suka yi su na faɗi to mu muntahi sai mun dawo mai baƙar aniya."
Dariyar jin daɗi ya yi sannan ya ce "Ku ɓace min daga gani mutanen banza la'ananni."
Ba musu suka fice daga turakarsa suka nufi motarsu.
A hanyarsu ta komawa gida yaya Bilya ke ta mita wai don me Malam Ilu zai dinga ce masa la'ananne? Shi fa ba la'ananne ba ne.
Da alama dai maganar ta masa ciwo sosai.
Dariya sosai 'yan uwansa ke masa, can Sunusi ya ce "Haba yaya Bilya! To dama kai minana in ba la'ananne ba? Ka tuna hwa wagga ba hanyar Allah ta munka biyo ba, sannan in ba la'ananne ba, wa ka son hallaka ɗan'uwa nai saboda dukiya?"
Sauran suka amshe zancen da cewa "Eh wallahi ko gaskiyarka Sunusi dukanmu la'ananni ne."
A haka suka ta zancensu su na dariyar jin daɗi har suka isa gida.
¥¥¥¥¥¥¥¥
Da yamma Kulu mai adashen sharri ta zo, suka kitse magana ita da Hajiya Hasina sannan ta bar gidan da alƙawarin idan ranar aiwatar da aikin ta zo za ta dawo.
Dama bata yawan zuwa gidan domin basa so a ankare da manufarsu, shiyasa suka fi yin waya, idan dai ka ga Kulu a gidan to Babban abu ne ya kawo ta.
Bayan sati ɗaya suka shirya zuwa Kano don kai Abdul gun aikin ƙafar da za'a masa a National othapedic hospital Dala Kano.
Bayan isar su garin ba a wani jima ba a ka kammala komai na shirye-shiryen aikin nasa.
A wata ranar Lahadi aka samu nasarar yi masa aikin ƙafar, sai dai fatar Allah yasa an yi a Sa'a......
More comment more typing.......
Karku manta, idan na ji shiru kuma zaku ji shiru😹🤷🏻♀️
Follow me on wattpad @Ruky_I_lawal
RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹
*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 17-18
Masha'allah! An yiwa Abdul aikin ƙafa kuma aiki ya yi kyau sai dai fatan Allah ya tashi kafaɗunsa.
Tare da Hajiya Hasina da kuma Ladi mai aiki a ka tafi, su ne masu kula da shi a asibitin, a kullum kwana duniya sai Ladi ta je masaukinsu a nan Kano ta dafo masu abinci ta kawo masu asibiti.
An sarƙafe ƙafar Abdul ne a cikin wasu ƙarafuna, shi dai ga shi nan kwance ne kawai shi kaɗai ya san irin zogi da raɗaɗin da ƙafarsa ke masa.
A haka suka ci gaba da jinyarsa har bayan watanni huɗu zuwa biyar sa'annan aka sallame su bayan ya ji dama.
Alhamdulillah! Aiki ya yi kyau domin ko da aka sallame su Abdul ya fara taka ƙafarsa, amma bisa ga jagorancin sanduna guda biyu.
Sai da suka kwana biyu a masaukinsu na Kano suka huta, bayan sun kammala dukkan shirye-shiryen su suka hau mota zuwa Sokoto, da yake tun shekaranjiya Alhajin ya kira direbansa ya zo don maida su gida.
Sai da suka shafe a wanni shida suna tafiya kafin suka iso Birnin Shehu daular Usmaniyya, direban bai zame ko'ina ba sai sama road, a ƙofar gidan Alhaji ya tsayar da motar tare da danna horn, da gudu mai gadi ya zo don buɗe ƙofar, amma sai da ya fara leƙowa ya ga ko suwaye tukunna, sannan ya je ya wangale masu ƙofar gate ɗin suka shige.
Sai da direban ya dai-daita tsayuwar motar, sannan suka fara fitowa, ma'aikatan gidan ne suka yi caa! don kawo gaisuwa a ciki harda mai gadi.
Faɗar suke "Sannu da zuwa Alhaji, kun sha hanya."
"Yawwa sannu, da hwatar mun same ku lafiya." Alhajin ya faɗa.
"Ya jikin Abdul? Da hwatar an yi nasarar aikin?" Suka tambaya.
A dai-dai lokacin ne kuma Hasina ta taimakawa Abdul ya fito daga motar tare da tsayuwa kan sandunansa.
Kafin Alhajin ya ce wani abu, Abdul ya bayyana tsaye a gabansu, don haka gaba ɗayan su suka haɗa baki cike da mamaki suka ce "Masha'allah lahiya ta samu, Allah sa lafiyar ta ɗore."
Alhajin ya amsa da Amin, Hajiya ta dubi Abdul ta ce "Ɗana mu shiga ciki ko?"
Gyaɗa mata kai kawai ya yi, ta shiga gaba ya na biye da ita a baya, ya na takawa a hankali, Ladi na take masa baya har zuwa Babban falon gidan, sai da Hajiya da Alhaji suka shige ɗakinsu, sannan ta ja Abdul zuwa ɗakinsa ta cire masa kaya tare da nuna masa yanda zai yi wanka sannan ta fice daga banɗakin.
A gaban walldrop ɗinsa ta tsaya, ta shiga duba masa kayan shan iska wanda za su dace da yanayin, domin a na tsaka da yanayin zafi.
Wata ƙaramar t-shirt da wando tree-quater ta zaɓar masa ta ajiye masa su a gefen gadonsa inda zai iya ganinsu, ka na ta wuce zuwa kitchen don ganin ko sauran abokanan aikinta sun gama girki?
Ai kuwa ta je a sa'a domin har sun kammala komai tuni, sanin cewa masu gidan na hanya, don haka ta samo ɗan madai-daicin plate ta shaƙewa Abdul shi da abincin sannan ta fice zuwa ɗakinsa.
Ko da ta ƙaraso ɗakin ya fito daga wanka ya na kiciniyar saka wandonsa ya kasa, yana jin an buɗe ƙofar ya yi saurin komawa gefen gado ya zauna tare da saka hannayensa yana kare jikinsa, wai shi kada a gane masa jikinsa.
Hakan ya bawa Ladi dariya ba kaɗan ba, sai da ta ɗan dara sannan ta isa gabansa tare da ajiye plate ɗin abincin ta na cewa "Ɗana Abdul kawo wandon in gyara maka shi."
Ba musu ya miƙa mata ya na sussunne kai ƙasa alamun dai ya na jin kunya, damar abinda dai akwai pant a jikinsa.
Ƙarba ta yi ta gyara masa kana ta ce "Abdul ɗinmu an girma, ka hwara jin kunyata koh?, Uhmm! Maza ka taho ga abinci na kawo maka, ka tabbatar ka canye shi duka."
Tana gama faɗa ta juya ta bar ɗakin.
Zama ya yi ya ci abincinsa a tsanake.
¥¥¥¥¥¥¥
Bayan kwana uku da dawowarsa daga jinya suka fara jarabawar ƙarshe a makaranta, wato dai da sun kammala ya ƙare primary kenan.
Cike da tsananin murna Abdul ke zuwa makaranta don rubuta jarabawarsa ta ƙarshe, daɗi yake ji sosai ganin zai ƙare ya huta da shiga cikin mutane dama Abbunsa ya masa alƙawarin da ya gama primary shi kenan ya gama boko, hakan ne silar farincikinsa.
Bayan wani ɗan dogon lokaci suka kammala jarabawar za'a je hutu, bayan kammala bikin ƙare makarantar.
A ranar da za'a masu bikin ƙare makarantar Alhaji Munir da kansa ya je tare da Abdul har makarantar don karɓo sakamakon jarabawarsa, tare da Hajiya Hasina suka je, Baba direba ne ke tuƙa su har makarantar.
Tun kusan ƙarfe goma na safe aka fara gudanar da shagalin bikin, ko'ina ka duba 'yan makaranta ne birjik sanye cikin uniform ɗinsu, wando kalar blue black sai riga ligh blue kowa a tsaftace sai murna yara suke ga iyayensu a gefensu.
Bayan malaman makarantar sun kammala jawabansu, aka fara kiran ɗalibai masu hazaƙa don gabatar da shiraruwan da aka shirya, duk da cewa Abdul baya gari lokacin da ake ta rehazal, amma a kwana ukun da ya dawo sai da aka saka shi a shirin muhawara.
Don haka aka kira Abdul tare da sauran 'yan team ɗinsa da team ɗin da za su gabza don gabatar da Muhawarar tasu.
An shirya Muhawarar ne a kan maudu'in shin da Manomi da likita wanne ya fi muhimmanci a rayuwar ɗan adam?
Abdul ya na team B team ɗin da za su kawo hujjoji a kan cewa Likita ya fi Manomi muhimmanci a rayuwar ɗan Adam.
A tsanake Abdul ya fita zuwa tsakiyar filin ya na gyara tsayuwa akan sandunansa, har zuwa lokacin da saura suka gama kawo hujjojinsu, dama shi ne last speaker na team ɗinsu, sai da aka zo kansa sannan ya fara zazzago hujjoji dake cike da hikima kamar wanda aka tsarawa a takarda, alhali shi ya tattaro hujjojinsa da kansa, kuma cikin kwana uku ya gama bitarsa.
Ya na zuwa a kan hujjarsa ta ƙarshe ya miƙa abin maganar tare da komawa gefe cikin sauran 'yan uwansa ɗalibai, nan fa hall ɗin ya kaure da tafi, ji kake raf! raf!! raf!!!
Mutane sai mamakin baiwar yaron suke Gashi dai gurgu amma hikimarsa ta zarta shekarunsa.
Alhaji Munir da Hajiya Hasina suna zaune kusa da juna a ɗan gaba kaɗan, a bayansu suka jiyo wani mutum na magana da ɗan uwansa yana cewa "Gaskiya yaron ga ya cika mai hikima, Gashi dai gurmu na ga Halittatai mai muni da ban tsoro amma kuma hikima tai ta hi shi yawa, ko wane uba zai so ɗanai ya samu irin wagga baiwa ta ilimi."
Duk da cewa Alhaji ya ji zafin aibanta masa halittar ɗa da aka yi, amma hakan bai hana shi murmusawa ba, domin ko ba komai sun gano irin baiwarsa da hikimarsa, sannan sun yaba da hakan, Allah shine abun godiya.
Bayan dawowar Abdul mazauninsa bada jimawa ba aka fara kiran ɗaliban da za'a karrama tare da basu kyautuka.
Kyauta uku Abdul ya karɓa a jere, ta farko da ya karɓa ita ce kyautar ɗalibin da yafi kowanne ƙwazo a makarantar, ta biyu kyautar ta ɗaya da yi a cikin ajinsu, ta uku kuma kyautar ɗalibin da yafi ko wanne ladabi a makarantar, ga shi ya ciwo wa team ɗinsu kyautar Muhawarar da aka yi.
Zuciyar Alhaji Munir cike da farin ciki suka dawo gida, haƙiƙanin gaskiya ya na alfahari da ɗansa.
Ita kuwa Hasina idan ranta ya yi dubu to ya ɓaci, zuciyarta cike da baƙin cikin wannan nasarar da yaron nan ya samu, sai dai ba ta isa ta nuna ba, saboda gurin wasa ake wasa gurin bindiga waye ƙyastu?.
Abdul ma ya yi farin ciki sosai, sai dai sun yi kukan rabuwa shi da Sadik, da wannan damuwar ya dawo gida.
Bayan dawowarsu gida, Hajiya Hasina cike da ƙuncin zuciya ta dannawa Kulu mai adashen sharri kira, ta ce "Kulu ki hwara shirin aikin nan namu kwanakkin ga nika son a ƙaddamar da shi."
Bata saurari Kulu ba saboda yanayin da take ciki kawai sai ta kashe wayarta.
Lokacin da Alhaji Munir na Kano gun jinyar ɗansa, su Bilya suka koma don karɓo magani gun boka, bayan dawowarsa, suka yi nasarar barbaɗa masa a waina, suka je da ita kasuwa ya ci.
Tun daga ranar Alhaji Munir ya susuce a kan harkar kula da dukiyarsa, sake masu ita yake yanda suke so, komai su yaya Bilya suka ce baya musawa, saboda asirin dake tasiri a jikinsa.
Ganin wannan nasarar da suka fara samu, sai suka afkawa dukiyarsa da ɓarna suna masa shigo-shigo ba zurfi.
¥¥¥¥¥¥^¥¥¥¥
Bayan kwana uku da faruwar hakan Alhaji ya yi tafiya zuwa kwatano don saro wasu atamfofi.
Baƙar Rana....
Wataranar Talata da misalin ƙarfe uku na dare, sahu ya ɗauke duniyar ta yi tsit, baka jin komai sai kukan tsuntsaye.
Hajiya Hasina ta sulale cikin sanɗa ta je gun gate bayan ta gama karɓa waya, dama ta sakawa ma'aikatan gidan maganin barci a abinci sun ci, ko wannensu ya ɓingire, ta je ta buɗe masu ƙofa suka shigo ciki .....
Wasu matasa ne guda uku fuskarsu rufe take ruf da face mask baƙa.
Cikin sanɗa suka tsallake mai gadi da ya baje a gun ya na barci kamar matacce suka wuce zuwa cikin babban falon.
Ɗakin da Abdul yake kwance ciki ta nuna masu tare da komawa ɗakinta ba tare da ta yi magana ba, da yake tun safe sun kitse maganar, kuma bata son wani ya ji muryarta.
Abdul ya na tsakiyar barcinsa mai daɗi, kawai sai ji ya yi an rufe masa hanci da wani ƙyalle, tun daga nan bai kuma sanin yadda aka yi ba...........
More comment more typing......
Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal
Vote share & comment..
*RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹*
*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼👨🏻🦼
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*
*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 19-20
Bayan sun shaƙa masa maganin kawar da hankali, suka tabbatar ya yi barcin sai ɗaya daga cikinsu ya duƙa ya saɓi yaron a kafaɗar ya yi gaba, yayin da ɗaya daga cikinsu ya shiga dudduba ko'ina don nemarwa yaron sandunansa, bai wani sha wahala ba, ya hango su a kusurwar gado inda Abdul ɗin ke ajiye su duk lokacin da zai kwanta barci.
Cikin hanzari ya ɗauko su sannan suka bi bayan ɗan'uwansa cikin sanɗa har suka fice daga gidan.
A mota suka sami ɗayan har ya shimfiɗe Abdul a bayan mota.
But suka buɗe suka sanya sandunansa a ciki, sannan suka zagaya, ko wannensu ya buɗe gefe ɗaya suka shiga suka saka yaron a tsakiya.
Shigar su ke da wuya Gumush ya ja motar da ƙarfi ya hau titi, sai sharara uban gudu ya ke kamar zai bar duniya.
Kasancewar dare ya raba lokacin shiyasa garin ya yi tsit kamar ba wani mahaluƙi a ciki, wannan ne ya basu damar tiƙar gudu da mota son ransu domin ba kowa a kan kowanne titi, har suka fice daga cikin garin ba su haɗu da wani mahaluƙi ba.
Haka suka wantsu suna sharara gudu a tituna har zuwa lokacin da suka fice daga jahar gaba ɗaya.
A 200 yake tafiya hakan ya saka tafiyar da za'ayi a awa biyar suka yi ta a cikin awa uku kacal.
Zuwa lokacin sun fice daga Sokoto da Zamfara sun kama hanya ɗoɗar, ƙarfe shida na safe suka isa ƙanƙara, gangarawa suka fara yi zuwa cikin surƙuƙin daji, sai da suka yi nisa sosai, ganin haske ya fara hudo sararin samaniya ya sa suka faka motar, sannan suka fito ɗauke da yaron da har zuwa lokacin barci yake bai farka ba, ɗayan ya ɗauko sandunan Abdul suka shiga cikin wata duhuwar bishiyoyi, inda zai yi wuya a ankara da shi, sannan suka jefar da shi a gun, sandunansa suka watsa masa kusa da shi, sannan suka juya da gudu suka bar gun, suna nufar motarsu.
Bayan sun isa bakin motar sai da suka dudduba suka tabbatar ba kowa a gun sannan suka shiga motarsu tare da bata wuta, suka fice daga jejin gaba ɗaya suka hau titi ɗoɗar dan juyowa cikin gari.
Da suka yi ɗan nisa a tafiyarsu, Gumush ya kira Mai adashen sharri ya sanar mata aiki ya yi kyau.
Kirari ta hau yi masa tana faɗar "An gaida ranke-ranke hitilar sheri, duk kihin da yasshiga komakka ya zama nama, ka ga mugu ɗan miyagu, aikinka na kyau Gumush, sai kun taho ansar kuɗɗin aikinku, na san dole Hajjiya ta muku kyauta me tsoka."
Gumush kuwa daɗi ya gama kashe shi, shi ma kirarin ya mata sannan suka kashe waya, ya ci gaba da murza sitiyarin motar cikin nishaɗi.
Bayan sun kashe wayar, cikin zumuɗi Kulu ta kira Hajiya Hasina ta shaida mata