Showing 36001 words to 39000 words out of 149666 words
Sulaiman ya ce yana so?
"Da alama kam"
"Toh me kika yanke?"
Ta ɗago jajayen idanunta tace
"Dole su rabu idan na cigaba da kallonsu tare zuciyata zai iya bindiga Samha, dole ko in sakata
ta rabu da shi ko kuma in san hanyar da zan bi gidansu su san wacece ita! Ko yana sonta ai ba
shi zai aurar da kanshi ba ko?"
Kai Samha ke gyaɗa wa
"Wannan haka yake, shawarar nan yayi kuma ki sameta ki ja mata warning mai girma ta tsaya
matsayin ta"
A hakan suka yanke don har ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi da Afeefah da safe kuma
tana tashi bacci wanka kawai tayi ta fito kaman an ce ta leƙa waje ta hanjeshi tsaye da ita, ko
abinci bata ci ba ta zauna parlor tana jiran Afeefar ta dawo don ta lura abin nasu gaba yake,
bata gama tunanin ba sai ga Samha da gudu ta ƙira su suka nufi ɗakin Afeefar...
***
Tana zaune kanta haɗe da ƙafafunta tana aikin zub da hawaye kawai ta ji an banko ƙofan
ɗakin, suka tsaya suna ƙarewa ɗakin kallo kan Sadiqa ta nufi wayanta da ke zaune gefenta
"Kutt! Yaushe kika yi waya? Na dai tabbatar ba da ita kika zo gidannan ba"
Kayakinta Samha take dagawa tana cewa
"Mommy yau dai kam Yaya da kike yabo ya watsa miki ƙasa a idanu duk wa zai saya mata su
bargo har da su heather in ba Yaya ba? Dubi ƙwalamar dake ɗakin nan? Mommy anya ba
asirce shi tayi ba?"
Ita dai tana tsaye tana kallonsu duk da zuciyarta da ke dukan sakwara ta kame bata firgice ba,
Sameera ta je ta fusgo ledojin da Sulaiman ya kawo mata tana zazzage kayakin ciki idanunta
cike da kwallah.
"Shikenan wallahi tambaɗe mana take shirin yi a gida, wani namijin ne zai na kashewa mace
kuɗi haka ba tare da ta bashi komai ba?"
Sadiqa ce tayi maganan tana ganin turaruka da dogayen riguna masu tsada da mahaifiyar
Sulaiman ta bata.
Sameera ta katse ta
"Ko dai asiri ta yi musu ba yaya sadiqa in tambaɗe wa ne kenan har da Yayanmu kalli wayan
nan kalar text messages dake ciki na tsantsar soyayya don tsabar rashin kunya da nuna cewa
ta isa dashi ma kin ga sunan shi gatsau tayi saving saleemullahi"
A fili ta fara karantowa mommy wasu inda yake tabbatar mata da zai iya jurar komai a kanta
kuma zai jajirce har sai ya ga sun samu cikar burin su na kasancewa karkashin inuwa daya.
"Ya isa haka sadiqa"
Mommy ta faɗa jiri na kwasarta ta samu wuri ta zauna, har Dishi Dishi take gani saboda yadda
kanta ya sara ashe salim zai iya tsallake maganar ta? Yanzu idan da basu lura da wuri ba tayi
amfani da wannan dama ta kashe mata shi fa? Da gaske maita na tafiya da aljanu? Ai kuma
duk inda Aljanu suke akwai asiri kenan dai tun farko ma asiri ta mishi ta sa ya kawo ta
matsuguninsu?
"Lallai saleem! Ni yaron nan zai nunawa ɗan yau ne shi? A kan mace? Macen ma Mayya marar
galihu da tushe haɗe da asali mai kyau? Allah ya isa na a banza ya ɗauke shi? Ni saleem...?"
Sai ta kama hawaye, hankalin Afeefah ne ya tashi ganin mommyn na mishi hawaye bata son
masifar hawayenta ya taɓa shi ko ta wani ɓangare da sauri ta isa gaban mommyn ta zube a kan
gwiwowinta
"Don Allah Hajiya ki yi haƙuri kar ki mishi kuka, wallahi yana jin maganarki yana kuma tsoron
fushinki, Ni ce mai kuskure ni ce na nemi ya sayamin kar ki yi fushi da shi domin fushinki bala'i
ne a tare da shi..."
Tauuuu sadiqa ta ɗauke ta da mari
"Kin san hakan amma kike hure masa kunne ya saɓa mata? Kin san abin da ɓacin rai daga
gareshi zai iya ja mata?"
Samha da ta janyo jakar da saleem ɗin ya shigo ya ajiye mata ta zazzage komai na ciki tana
cewa
"Wallahi yarinyar nan so take ta raba mu da ɗan uwanmu Mommy, kalli uwar tsarabar da ya
kawo mata a ɓoye ko ke bai kawo miki irin hakan ba bare mu... Farraku take shirin yi mana
daga karshe ta sa ya kora mu daga gidan nan"
"ƙira min saleem sadiqa"
Da wayan Afeefar ta ƙira shi, ringing ɗaya ya ɗaga a hankali ya kira sunanta sai ta duƙar da kai
hawaye na gangaro mata jin muryarshi.
"Yaya Salim Sadiqa ce Mommy ke son ganinka"
Runtse ido yayi da ƙarfi gabanshi na faɗuwa, bai shirya ba! Bai shirya tashin hankali a yanzu ba
ba yanzu ba da yake jin son Afeefah yayi mishi yawa a zuciya.
Da sauri ya juyo kan motar dama bai yi nisa ba ya dawo wani irin parking yayi ya sauƙa ya nufi
sashen Boys quaters ɗin yana Adu'ar Allah ya sa kar mommy tayi mata wani abu, sai kace-
nace ya same su suke yi ana ta maida magana, Afeefar na tsugune kaman mai neman gafara
tana kuka.
Gaban mommyn ya je kusa da Afeefar shima ya duƙa kawai ba tare da ya furta kalma ko guda
ba.
"Saleem"
Ta ƙira sunanshi ya amsa ba tare da ya kalleta ba
"Ɗago saleem ka kalleni, ka ɗago ka tabbatar min da kai ke tura duk wani saƙo da na gani
wayar yarinyar nan, da gaske kai ne kake son wannan marar cikakken asalin?"
Ya runtse ido wani irin nauyin Afeefah yake ji kaman yayi yaya, baya so baya kaunar ta ke jin
furucin ɓatanci daga ahalinshi zuwa gareta musamman mahaifiyarshi.
"Mommy ni ne, Son ta nake kuma aurenta nake Son y...."
Wani irin mari ta ɗauke shi da shi, karo na farko kenan da ta kai hannunta jikinshi don shi yaro
ne mai tsananin biyayya a gareta.
"Maimaita!"
Ta daka mishi tsawa ya sake cewa
"Mommy ina ƙaunarta, kuma aurenta nake buri"
Wani marin ta sake dauke shi da shi, ba shi kaɗai ba har su sadiqa sun tsorata basu taɓa
tunanin za ta iya kai hannunta jikinsu ba don ita Allah yayi ta da tsananin son yaranta, hawaye
take yi ta sake cewa saleem ya maimaita
"Mommy... Mommy da gaske zuciyata ta kamu da Soyayyar Afeefah da ba na tunanin ko wani
hukunci za'a yi min zai sa ta fita daga ciki, mommy kila sai kin cire zuciyar gabaɗaya daga
kirjina za ki daina jin harshena na furta kalmar ƙauna zuwa gareta..."
Wani irin kuka Sameerah ta fashe da shi, a yanzu ta yarda ta yarda ba wani asiri don tabbas
abin da take ji a kan Sulaiman shi ke azabtar da Saleem tunda har zai iya mayarwa mommy
magana sau uku, Mommy ta sake ɗaga hannu zata mareshi sadiqa ta riƙe hannun tana hawaye
"Mommy ba shi za ki daka ba ga Mayyar da ya kamata ki kassara chan, wallahi Afeefah sai kin
bar gidan nan ba za ki tarwatsa mana gida ba"
Afeefah dai ta rasa yanayin da take ciki, wani irin ƙauna da tausayin saleem ne suka sake
mamaye zuciyarta ko tunanin inda za ta nufa in sun kore ta bata yi, damuwarta saleem idan
suka raba su basu mishi adalci ba, shi ya cancanci bautar ta na aure har mutuwa.
"Saleem!"
Mommy ta kira shi karo na ba adadi muryarta har yanzu da wani irin mamaki, idanunshi da suka
sauya ainun ya ɗago ya kalleta tamkar ba soja ba wani irin rauni ya bayyana karara a fuska da
idanun nashi.
"Saleem!!"
Ya amsa a hankali
"Saleem!! Sau nawa na kira ka?"
A hankali yace
"Uku"
"Wannan ba aikin hankali bane na asiri ne, amma ko da asirin ai ka san matsayi na a wurin ka
ko? Ka san ni wacece ko?"
"Mommy ke mahaifiyata ce kina da darajar da babu wanda yake dashi a wurina duk faɗin
duniyar nan. Kin isa da ni kuma na san za ki so farin cikina! Mommy a yanzu ba na jin ina da
wani buri da zai haifar min da farin ciki kaman Afeefah, ban san sadda sonta yayi min wannan
kamu ba don ba ya shawara kan ya shiga wallahi ina sonta! Ba zan iya rarrashin zuciyata ba
don so bai san rarrashi ba..."
"Afeefah Allah ya isa tsakanina da ke! Allah ya isa"
Mommy ta faɗa tana kuka. A lokacin hawayen da saleem ke danne wa suka gangaro ya ɗago
ya kalli mommyn zai yi magana ta daka mishi tsawa a kan ya mata shiru
"Aure kake so zan ɗaura maka aure da yar ɗan uwana Sabreena da take sonka tun bata san
kanta ba, amma soyayya, magana ko zancen aure tsakaninka da wannan yarinya saleem har
Abada, ko bayan raina ne Allah ya isa ban yafe ba! Wallahi wallahi sai na iya tsine maka ka
sake shiga huldar yarinyar nan ko a hanya kuka haɗu ban yafe ba ka mata ko da sannu ne... In
har ni na haif...haifeka Saleem sai dai in kana da wata uwar za ka iya"
A razane yake kallonta, ta share fuskanta ta dubi Samha
"Je ɗakina ki ɗaukomin akwatin da ya fi kowanne girma"
Da sauri ta tafi, Sameera zuciyarta ne ke tsitsinkewa a yanzu tsoro ne ya rufeta, wlh tana iya jin
irin abin da saleem da idanunshi ke runtse yake ji a yanzu, gabaɗaya jijiyoyin kanshi sun
mimmiƙe girgiza kai take yi
"Mommy don Allah ki dakata! Ki tsaya kar azabar yayi mana yawa... Ki barta don Allah ko bai
aureta ba ta z..."
Sadiqa ce ta kai mata duka
"Kema asirce ki tayi don ƙaniyarki? Wallahi ta gama zaman gidan nan"
A lokacin Samha ta shigo da wani cream trolley.
Mommy ta karɓa ta jefa mata
"Na tsani ganin ko inuwar ta ne, ku gaya mata ta tattari duk taeukucenta ba na son ganin ko
ƙyallenta a gidan nan kar ma ta dawo cikin dare ta kama wani biya... Har Abada ko magana ta
yi wa dana sai na tabbatar ta kare rayuwarta a gidan yari"
Ko gwada roƙon su bata yi ba don ta san ko sama zai haɗu da kasa a yanzu mommy ba zata
amince da hakurin ta ba, kuka mai sauti take yi jikin saleem ne ya fara rawa, ba zai cigaba da
sauraron kukanta ba ba zai iya ganin tafiyar ta ba, zuciyarshi tamkar zai fashe saboda tsoro da
fargaba in ta fita ina za ta je? Wa ta sani a duk faɗin Kaduna? A hankali ya miƙe jiri na kwasar
shi a dafe da gini ya cigaba da tafiya har ya bar ɗakin zuwa lokacin da gaske yake hawaye,
hukuncin Mommy tamkar zare mishi farin ciki tayi a wannan rayuwa, tamkar ta kulle shi ne a
magarƙamar da ya fi kowani magarƙama duhu da azaba.
Afeefah ta haɗa komai nata, wayar da saleem ya saya mata kawai ne ke riƙe hannun mommy
kan suka tasa ta gaba har wajen gate, ta jima tsugune a wurin tana kuka kan ta miƙe ta share
fuskarta ta ja akwatin ta fara tafiya.
"Hasbunallahu wani'imal wakeel...! Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Abin da take ta nanatawa kenan tana share hawaye ta yi tafiyan da bata san adadi ba har ta fito
wani babban hanya dake dauke da ababen hawa fiye da cikin unguwar da ta bari, nan ma
miƙawa kawai tayi ta cigaba da tafiya ko biyar babu a hannunta, ta fi awa biyu tana tafiya janye
da trolley ɗin lokaci lokaci ta kan share hawaye masu zafi dake zuba mata, a daidai wani wurin
ba da hannu ta tsaya ta ɗaga kai ta kalli garin, mutane ne ke ta hada hada kowa harkar
gabanshi yake yi, daidai wutan ya nuna ja motoci suka tsatsaya wani daga gaba yayi kokarin
kin bin doka sai hatsari ya faru a wurin tuni go slow ya wani irin haɗuwa.
Tana tsaye har lokacin rike da akwatinta kamkam sam bata san me za ta yanke ba, bata san ya
za tayi ba kaman an ce ta ɗaga kai sai idanunta da suka zama wasu iri tsabar kuka suka shige
cikin nashi daidai yana sauƙe glass, kallon seconds biyar suka yi wa juna ya ɗauke kanshi ya
mayar gaba yana tsaki, ita kam bata dauke kai ba sai take jin kaman ta je ta roƙe shi ya taimaka
mata ko da ya haɗa ta da Sulaiman ne, amma kuma Sulaiman ai bai san wacece ita ba idan su
ma suka kore ta fa? Innalillahi wainna ilaihi rajiun ta sake faɗa hawaye na silalo mata daidai ya
sake kallonta idanunshi suka sauƙa kan hawayen a lokacin suka samu hanya ya ja motar ya bar
wurin.
Juyawa tayi ta cigaba da jan trolley ɗin dama ta sani bashi da kirkin saleem, babu mai kirkin
saleem ma a duniyarta shi kaɗai ta sani mai kirki, daidai ta zo gaban galaxy mall da ta gani
rubuce sama za ta wuce sai tayi karo da wata mata, baya baya matar tayi za ta faɗi Afeefar tayi
hanzarin sake akwatin ta riƙe ta
"Subhallah! Ki yi haƙuri"
Ta faɗa cikin dasasshiyar muryarta, sai ta ga matar ta kasa tsayuwa numfashinta na ta kai
komo ga ta dai cikin shiga na alfarma har da jaka a hannunta
"Lafiya Aunty? Ko baki da lafiya ne?"
Take ta tambayar cike da damuwa matar ta kasa magana.
Hankalin Afeefah ya tashi, kar ta mutu yanzu ma a ce ita, ya zata yi? Ba Za Ta iya barin ta a
nan ba a haka yadda take duk ta fice hayyacinta ta jike jagwaf da gumi Dukda sanyi ake. Wani
tunani ne ya faɗo wa Afeefah ta yi hanzarin karbar jakar matar tana cewa
"Aunty taimakon ki zan yi ba sata zan miki ba bani da ko biyar da ba zan taɓa jakanki ba"
Buɗewa tayi ta samu ɗari biyar bata tsaya tunani ba ta tari abin hawa ta sanya matar a ciki
itama ta shiga mai machine ɗin ne ya dauka mata akwatinta tana ce mishi
"Asibitin dake kusa don Allah"
"Sannu, Sannu"
Take ta maimaitawa matar gwanin tausayi sai taji tana yi wa Allah godiya da ya barta da
lafiyanta ko ba komai ta tsira da shi, a haka suka isa wani private hospital ya shiga da su har
ciki aka dauƙeta emergency zuwa lokacin bata numfashi.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*018*
Sai da ya bar gida da motar ya fahimci gas din Ac ɗin shi ya ƙare, hakan ya ɓata mishi rai don
baya son buɗe glass na mota yana tuƙi, a haka ya tafi Asibiti yayi abin da zai yi a ranar wuraren
sha biyu ya bar asibitin ya nufi gida, a daidai babban titin da zai ɗauki hanyar cikin unguwar su
na Barnawa hold up ya riƙe shi, a dole ya sauƙe glass saboda zafin da yake ji.
Karon farko da idanunshi suka sauƙa a kanta bai gane ta ba sai da ya ɗan yi focusing na
seconds kan ya gane ta, wannan yarinya ce da ya taɓa ceta from poison, wannan yarinya da
saleem ke so, sam bai yi tunanin wani abu ne ya tsayar da ita a wurin ba sai a karo na biyu da
ya mayar da idanunshi wurin suka sauƙa a kan trolley dake gabanta, idanunta ya sake mayar
da ido sai ya fahimci ta yi kuka sossai, horn ake ta danna mishi hakan ya sa ya ja motar yayi
gaba wayanshi ya zaro ya shiga neman Layin salim sai dai har 2missed calls ya mishi bai ɗaga
ba shi da ya tsani kira sau biyu ya kan ce ai duk uzurin da mutum ke yi in ya zo ya ga na farko
zai bi ba sai ka ta jera kira kaman marar aikin yi ba, a kira na uku saleem ya ɗaga sai dai ya
kasa magana.
"Saleem are you Okay? Whats wrong with ur voice?"
Saleem ya kasa magana don shi kaɗai ya san me yake ji, Ryan bai taɓa jin Muryar abokin nashi
a haka ba, dole ya nemi wuri yayi parking
"Saleem Mommy ce?"
Yayi uttering
"Uhmm Ryan Mommy ta kori Afeefah ban san wani irin hali za ta faɗa ba, mommy tayi
alkawarin tsine min na sake ko da magana da Afeefah ne bare yunkurin taimako aure ko
soyayya, she's too young Ryan she's too young! Na san tana chan all alone, scared and
disturbed idan wani abu ya same ta fa? Its all my fault da na fara son ta Its my fault..."
Hawayen da yake yi ne ya sa ya datse lips ɗin shi da ƙarfi sai kawai ya katse wayan.
Kunna motar rayann yayi yana jin wani abu a ƙasan ranshi, tausayin Saleem ya rufe shi haɗe
da damuwan jin halin da yake ciki bai taɓa jin abokin shin haka ba, saleem da ko haɗe rai baya
yi. Fuskarta yake gani a idanunshi ashe kallon taimako take mishi, steering ya ɗan buga da tafin
hannunshi yana zagayowa inda ya barta sai dai neman duniya bai ganta ba, har parking yayi ya
sauƙa yana takawa da kafa ya zazzaga bata nan. Bakinshi ya ɗan taɓe kaɗan yana shirin
juyawa wayanshi yayi ringing.
Zarowa yayi sai ya ga Driver ɗin Mamminshi ne, dagawa yayi
"Ado ya aka yi?"
Ya fitar da maganan yana lumshe ido sam ba zaka san yana da damuwa ba ko hankalinshi ya
ɗan tashi don fuskar bai nuna ba ko da wasa.
"Oga akwai matsala ne, Hajiya ce!"
Tuni ya ware idanun a take suka sauya ya fara nufar motanshi yana ji Ado na mishi bayani wai
ya kaita sayayya kuma yayi ta jira bata fito ba ya shiga ciki kuma yayi neman duniya bai sameta
ba.
"A ina ne?"
"Galaxy mall"
Yana kusa da wurin ƙarasa wa kawai yayi
"Ka ƙirata?"
Ya jefawa Ado tambayar Ado yayi saurin duƙar da kanshi don ya san fushin Rayyan a take sai
ya haukace, idanunshi sun yi mishi kwarjinin da ba zai iya kallon cikinsu ba
"Ban fito da waya ba"
Wani irin kallo ya watsa mishi lip ɗin shi ma sun yi nauyin buduwa bare su sake furta ko da
kalmar A.
Wayanshi kawai yake dannawa ya shiga ƙiran layinta sai dai ringing na duniya ba'a ɗaga ba,
tracker ya shiga na Find my Iphone tuni ya ga location da take, a maimakon hankalinshi ya
kwanta sai hankalinshi ya sake tashi ba za ka sani ba amma in ka ƙura mishi ido zaka ga
hannayenshi har rawa suke idan kuma ka taɓa za ka ji sun yi sanyi tamkar ƙanƙara to baya
cikin lafiya kenan.
Mota kawai ya shiga ya ja tafiyar mintuna goma ya isar da shi asibitin yayi rough parking ya
sauƙa ya nufi ciki, a gaban nurses station ya tsaya
"An kawo wata elderly woman yanzu! Where is she?"
Da ɗan karfi yayi maganan don ya ga mace ɗaya ce kawai ta mayar da hankali kanshi tsawar
da yayi ya sa duk suka juyo, kofan emergency kawai ta nuna mishi ya nufi wurin kawai ya tura
ya shiga.
"Excuse you! Baka san ba'a shiga nan bane?"
Id card ɗin shi ya fitar ya nuna musu idanunshi na kan Mammi da suke ta ƙoƙari wurin ganin
sun ceceta ya furta a hankali
"The patient is experiencing end-stage renal disease(ESRD) nd she's diabetic i hope ba ku yi
kuskuren komai a kanta ba"
Ja da baya wanda ke rike da drip yayi don ba ruwan masu sugar bane, Id card ɗinshi kuma ya
tabbatar musu da waye