Showing 54001 words to 57000 words out of 149666 words

Chapter 19 - Haihuwa Da Hanji

Unknown   

16 Mar 2026

4426

'yar haki tana kishingida.
"Sannu! Ko zaki ƙara magani?"
"Kayya bar zancen maganin nan Afeefah, je ki kira min Yayanku nayi ta gwada layinshi bana
samu tun bayan asuba da ya shigo nan muka gaisa ban sake ganinshi ba"

Idanu ta ɗan waro gabanta na faɗuwa, Dukda ta san ta inda Sashenshi yake amma bata taɓa
gigin shiga ba to me zai kai ta? Yanzu ɗin ma jiki a sabule ta miƙe ta fice daga ɗakin, Abeeha
bata nan tun safe taje gidan jiddah za ta raka ta asibiti wai bata jin daaɗi da ko ita zata iya zuwa
amma ita har yanzu ganinta baƙuwa a gidan take, ko ba ma haka ba ina zata iya da wannan da
ba'a mishi gwanintar? Mutum sai faɗin rai da masifa... Da kyar ta ɗaga hannu tayi knocking
kofan parlorn sai dai shiru babu amsa, ta sake yin knocking karo na biyu nan ma shiru, a
hankali ta tura kofar da sallama a Bakinta ta shiga yana kishindige very relaxed a cikin kujera,

parlorn da hasken shi ba sosai chan chan ba sai tashin kamshi yake, kaman waya yake yi
amma ba da wayar da ta saba ganinshi dashi ba gabanshi system ne shima a kunne kaman dai
aiki yake yi ya tsaya amsa wayar.

Daga ɗan nesa ta tsaya kanta a ƙasa tana jin yadda yake magana wane wani sarki, murmushi
tayi a chan ƙasan ranta take raya dole Mammi ta kira shi Saraki don shi komai nashi ya fi yanayi
da jinin sarauta, bayan ya gama wayan ya ɗan kalleta ba tare da ya ce komai ba ya ɗauke
idanu itama jin shiru ya sa ta ɗago ganin ya gama wayan ta ɗan ƙara taku biyu sai ta rasa me
za ta ce.

Da kyar ta iya haɗa kalmar sunanshi akan lips ɗinta
"Yaya Saraki..."
Ɗagowa da yayi ya kalleta ya sa maganar datsewa, bai san ya ɗago ɗin ba don yadda ta kira
sunan sossai ya dake shi, bayan Mammi bai yarda ya ji sunan bakin kowa ba amma jinshi a
Bakinta sai ya rasa me yake ji ma, haushi ne ko takaici ko bacin rai? Tsam ya miƙe ya nufo ta.

Idanu ta shiga zarewa takunshi na tafiya da bugun zuciyarta har ya matso dab da ita yace
"Maimaita abin da kika ce?"

Shiru tayi ta kasa magana idanunta da suka yi raurau alamun kuka ko wani lokaci ta ɗauke
daga kanshi jikinta na tsuma ta ciki, kusan seconds huɗu kan ya ce
"Allah ya so ki, da kin maimaita sai na fasa miki baki ke Mammi ce da za ki kira ni Saraki? Wani
Yaya Saraki...!"
Ya sake maimaitawa yana ɗan harararta.

"Me?"
Ya faɗa yana dan gyara tsayuwa idanunshi tsamm a tsaye a kanta ko a jikinshi.
"Yaya..."
Wlh sai ta kasa cewa Rayyan ɗin tayi tsai tsammm sai ma ta fasa kiran sunan da ɗan saurin
baki tace
"Mammi ce wai ka je!"
Ta juya za ta fice yace
"Tsaya!"
"Ba ni da suna ne? Ko da gini kike magana?"
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."
Ta faɗa kaman za tayi kuka chan ƙasa, sarai ya ji ta
"Ga musiba tsaye gabanki ko?"
Girgiza kai tayi, tsaki ya ja yace
"Bar nan"
Da sauri ta fice.

Sai da ta ganta tsakiyar babban parlor kan ta dafe kirjinta tana sauƙe numfashi, Rayyan na son
kasheta da ranta, yaushe ya iya ma dogon magana haka bata sani ba, shi da komai ko oho ne
me yasa zai saka ta a gaba yayi ta razana ta!

Jiki a sabule ta ƙarasa wurin Mammi
"Wai yana zuwa"
Zama tayi kawai bata sake cewa komai ba, mintuna basu wuci uku ba sai gashi gaban Mammin
kawai ya ƙarasa ya fara taɓa temperature ɗinta, numfashinta baya fita yadda ya kamata
hankalinshi tashi yayi, a take yace su tafi asibiti duk yadda Mammin za ta ƙi ya nace ya dubi
Afeefah yace ta ɗauko mata mayafi, da sauri taje ta ɗauko duk sai ta shiga damuwa ganin
yadda hankalinshi ya tashi, kuma dai a fili Mammin bata yi tsananin da ya kamata ya ɗaga
hankalin nashi haka ba, bata zauna ba itama gyalen da ta ɗaura a kanta na Jersey ta warware
ta yafa akan doguwar rigar atamphar dake jikinta ta bi bayansu, a gaba ya saka mammin ta
buɗe baya ta shiga suka fice daga gidan.

Tafiyar mintuna ashirin ya kai su asibitin shi ya sake kama mammin suka yi inda za'a duba ta
don ya riga yayi call, tuni suka karɓeta don a yi mata gwaje gwaje a tabbatar da babu abin da
ya sake tsananta ko chanzawa.

A reception ta zauna idanunta na kan yatsun ta sai adu'ar samun lafiya take yiwa Mammi mata
mai kirki da mutunci, macen da ta zame mata uwa kuma garkuwa a yanzu.

"Afeefah...!"
Da ɗan karfi ta ji an kira sunanta har bata san ta ɗago a razane ba sai...




🖤Gureenjoh🖤

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*25*

Sulaiman kaman zai kama hannunta haka ya tsaya gabanta yana kallonta.

"Da gaske ke ce? Ashe zan sake ganinki Afeefah? Ina kika shiga? Kin san irin neman da na
miki?"

Idanunta na sauƙa kanshi ta miƙe tsaye, ganin irin kusancin su ya sa ta ɗan yi taku biyu baya
fuskarta a sake tace
"Ina nan Dr. Allah ya haɗa ni da mutanen kirki"
"Afeefah me yasa ba ki zo office na ba? Me yasa ba ki neme ni ba da mahaifiyar saleem ta kore
ki?"
Idanunta ne suka cika taf da kwallah a hankali tace
"Ban san inda zan sameka bane ban san sunan asibitin ku ba ko in ce ban riƙe ba, ko ma na
riƙe ba ni da ko biyar da zan hau abin hawa in ce a kawo ni"

Idanu ya ɗan runtse kaɗan ya buɗe da sauri sai ya ga kaman za ta iya ɓace mishi any moment
"Ina kika shiga to? Waye ya taimake ki?"
"Na haɗu da mutanen kirki sun tallafeni daidai lokacin da na buƙata kuma suna riƙe ni tamkar
ɗaya daga cikinsu yanzu haka ina makaranta"
"Alhamdulillah!"

Zama yayi saboda a lokaci ɗaya daaɗi da baƙin ciki duk suka haɗu mishi, itama ta zauna a
hankali ya ce

"Afeefah har Dutsen-wai na je nemanki"
Da sauri ta ɗago ido suka haɗa idanu ya gyaɗa mata kai alamun tabbaci.
"Gidan kawu ka je?"
Kai ya gyaɗa cikin nuna damuwa ya ce
"Abin da muka tarar ba karamin tsoro ya bamu ba Afeefah, ban so ba, ban san hakan zai
kasance ba da ban yi ganganci da kuskuren tafiya da manya na ba"

A lokaci daya ta zama very confused sun je gidan kawu? Me suka tarar? Me yasa yaje da
wasu?.

"ko da ban furta miki ba kin dai san Sonki nake ko Afeefah?"
Lumshe ido tayi kalamar na sauka mata wani iri a zuciya.
"A lokacin da na samu labarin tafiyar ki i was very disturbed na ɗauka chan gida za ki koma, ko
da na koma gida na samu mahaifiyata da labarin ban gama bata ba Abba ya shigo ya ji zancen,
dama ya matsu kuma da maganan aurena dole ya haɗa ni da Yayyenshi kuma ya kafa hujja ne
da cewa a musulunce ma bai halatta namiji ya fara taran mace ba tare da sanin iyayenta ba..
Dole ta sa muka tafi tare da su ba don na so ba"

Hawaye ne ya zubo mata a kan fuska ta ɗan yi murmushi mai yanayi da wani ciwo a ƙasan rai
ta ce
"Sun ji kunya ko? Na tabbatar ba su amince maka ba kuma ba za su taɓa amince maka ba..! Ka
yi haƙuri, da na san za ka aikata hakan da ni da kaina na faɗa maka wacece ni kafin ma ka je"

Ya ɗan haɗiye wani abu mai ciwo a hankali yace
"Afeefah sun yanke min hukunci mai girma a yanzu haka ina da aure, an ɗaura min aure last
week saturday amma har yanzu zuciyata ke take so, ke take marararin rayuwa da ba wata ba.

Na haƙura na karɓi auren ne saboda ban san inda zan ganki ba ban san inda zan sameki ba, a
ina ne gidan da kika koma? Idan kin ga da takura za ki iya dawowa wurin Umma na tabbatar ita
me riƙe ki ce tamkar ɗiyar da zata haifa a cikinta"

Rayyan ne ya fito sai idanunshi ya faɗa kan su, a kan hawayen dake bin ƙuncin ta ya ɗan tsayar
da idanun kan ya ɗauke kai ya zo ya wuce su kaman bai gane su waye ba, Afeefah da suka
haɗa ido ta sa hannu ta share hawayen fuskarta ta dubi Sulaiman
"Zan tambayi Mammi zan zo in gaishe Da Umma! Amma batun soyayya don Allah ka ajiye shi a
gefe Dr. Kai fa ka gayamin irin abubuwan da Kawu ya muku na ba da kunya, taya za ka yi
convincing iyayenka su sake komawa irin gidan chan?"

"Zan iya Afeefah kawai ki ba ni dama!"
Ta girgiza kai
"Aurenka fa?"
Zai yi magana ta ce
"Ka yi haƙuri Dr. Yanzu ba lokacin wannan maganan bane marar lafiya muka kawo"

Shigowar Abeeha da Jannah ne ya sa ta ƙarasa share fuskarta ta ƙirƙiro murmushi ta saka,
suka ƙaraso kusa da ita
"Afeefah ya jikin Mammin?"
Ta ce
"Da sauƙi sossai amma tunda Ya Saraki ya shiga da ita ba'a fito da ita ba"
"Amma Yaya Rayyan ɗin yanzu muka wuce shi a waje yana waya"
"Eh shi kadai ne ya fito"
Gaisawa suka yi da Dr. Sulaiman yana mamakin jin ana ambaton Rayyan, gidan su Rayyan ta
koma?

"Afeefah ko zan iya samun Layin da zan yi magana da ke?"
Ya faɗa yana kallonta, kallonta Abeeha tayi sai ta ɗan yi murmushi tace mata
"Dr. Sulaiman kenan!"
Shima ta juya tace
"Yayyena ne Addah jannah da Adda Abeeha"
Murmushi yayi lallai Afeefah ta samu wurin zama idan har ta sake da ahalin haka sun zama
tamkar jininta ya tabbata ba zata iya barin su ta dawo wurin ummanshi ba yadda ya ci buri.

"Dr bamu natsu ba har yau bamu samu mun je mun sayi waya ba, bari na baka layina za ku iya
dinga gaisawa kan ta samu nata"
Godiya sossai yayiwa Abeehar, ta bashi contact ɗinta ya tafi da sauri ta juyi wurin Afeefah tana
murmushi sai ta ga damuwa a kan fuskarta, dafa kafaɗarta tayi
"Ya dai?"
"Adda wai Shima aure yayi last week saturday"
Duk sun ji maganar wani iri amma sai suka dinga nuna mata babu komai kila ba rabonta bane
ko kuma Allah ya kaddara za ta zama matarshi ta biyu bata san ta cewa Abeeha ba

"A yaushe kenan? Aure last week Adda Abeeha kina tunanin ko shekara daya ne zata amince
ya mata kishiya a kusa haka?"

"Duk ba mu san tsarin Allah ba, mu yi Adu'a kawai duk abinda ya kaddara daidai ne"
Ta gamsu amma har lokacin ranta na suya da abinda kawu ya aikata, kenan akwai ɗan sunnar
da zai aureta a duniya kenan? Waye zai yarda ɗan shi ya auri irin ta matukar za su bincika asali
da tushenta?

Bata san Rayyan ya dawo ya wuce ba chan sai ga shi sun fito da Mammi, duk Miƙewa suka yi
suna mata sannu tayi murmushi
"Duk rigimar Saraki ne amma jikin nan bai kai zuwa Asibiti ba, Jannah ya jikin naki?"
"Da sauƙi Mammi, sannu Allah ya baki lafiya"
Ta gyaɗa kai.
Idanunta ta kai kan Afeefah dake ta murmushin yake
"Afeefah kina lafiya? Na ga damuwa a fuskarki"
"Babu komai Mammi sannu da jiki"
Kai ta gyaɗa ba wai don ta yarda ba suka nufi mota, ƙin shiga motar Rayyan tayi don wlh tsoron
ko motsi take a gabanshi, motar Jannah ta tafi suka haɗu su uku suna hirarsu har gida.

A babban parlor suka yi masauki don Rayyan ya riga su isa kuma ya shigar da Mammi ciki ko
da ya fito a babban parlorn ya tsaya yana nuna su da yatsa
"Ba ku parrots ba? To in ga watan ku ta shiga ciki tana damunta da surutu ko wata taje tana
saka ta gaba da kukan banza ku ga abin da zai faru"

Yana kai nan ya wuce abin shi basu motsa ba sai da ya ɓace Abeeha da Jannah suka tafa suna
sheke wa da dariya, Afeefah na murmushi.

"Mutum yayi ta muzurai kaman a filin daga yake"
Jannah ta faɗa, Abeeha tace
"Ai ke baki ganin komai tunda yanzu kin bar gidan nan da sauƙin ki"
Jannah ta girgiza kai
"Kema kin san babu wani sauƙi wlh sai dai in ban yi wani abin ba Ya Rayyan bai game shi ba ya
je har gidan auren nawa ya zane ni tsaff"
Ita dai Afeefah bata ce komai ba idanunshi kawai take gani, a hankali ta ɗan yi murmushi tana
girgiza kai.

Jannah bata tafi ba sai dare, sun sha hira sun ci sun sha, kuma sai da suka cika Mammin da
surutu don yana fita daga gidan suka yi ɗakin suna bata labarin gargadinshi tana dariya ta dubi
Afeefah
"Afeefah ke ce me kukan banza kenan? Me aka yi miki za ki zo ki min kukan?"
"Ba ayi komai ba fa Mammi"
"Afeefah ki faɗa min damuwarki wlh ina hangar damuwa a tattare da ke"
Kanta ta duƙar Mammi ita uwa ce, uwar ma ta wannan baudadden mutum ai dole ta san
expression na kowa.

Abeeha tace
"Mammi Dr. Sulaiman yayi aure shima ashe"
Mammi ta kalli Abeeha kan ta kalli Afeefah tace
"Auren ne ya dame ki ɗiyata? Kin ga fa duk abin da Allah ya hanaka ba rabonka bane wanda
kika ga kin samu shi ne rabon ki, in shaa Allahu za ki samu miji na nunawa sa'a"
A hankali tace
"Mammi ba auren shi bane damuwata"
"Toh menene Afeefah?"
"Mammi bana tunanin zan auru, Musulunci ya yarda a auri mace don kyaunta, dukiyarta ko
nasabarta, sannan bincike a aure kaman dole ne a musulunci akwai dangi na ƙwarai da za su je
bincike a kaina su yarda su bar ɗan su ya aureni? Mammi kin ji abinda su Sulaiman suka samu
kawu suna yi a kan layi? Kin ji abinda aka fada musu a kaina daga shigar su kauyenmu?"
Hawaye ne ya tsinke mata ta fashe da kuka tana jin ciwon Taɓon ta da bata tunani har Abada
zai gogu.

Jannah da Abeeha har sun fara tayata hawaye don idan ka ji yadda take maganan za ka san
abin na mata ciwo kwarai da gaske..

"Afeefah zo nan"
Mammi ta ƙirata, Miƙewa tayi ta isa kusa da ita Mammin ta ɗora ta akan kafaɗarta tana shafa
mata kai.
"in shaa Allahu Afeefah sai kin auri mijin da kowa sai ya ji sha'awar kasancewa ke, nagartaccen
namiji kuma mai tarin ilimi da baiwa na musamman, kawunki ko mutanen garinku ba su isa sun
shafe abin da Allah ya rubuta ba, ko kin manta Allah da kanshi ya faɗa mana yana fitar da
mummuna cikin kyakyawa ya kuma fitar da kyakyawa cikin mummuna? Ba fa a suffa ko sura
ake magana ba ana magana ne akan hali da ɗabi'a. To ki sa a ranki mijin da Allah ya zaɓa miki
yana nan kuma idan lokaci yayi za ki aure shi ba makawa kar ki wani damu kanki kin ji?"

Kai ta gyaɗa cike da gamsuwa
"Na gode Mammi"
"na ƙara ji sai na Buge bakin godiyar"
Murmushi duk suka yi don da wasa tayi maganan.


*****

Hajiya Hussaina tun fa tana tunanin abin na Saleem da Sabrina wasa ne har ta fahimci da
gaske ne, domin yau tana zaune a parlor Sabreenar ta sauƙo ta ɗan kalleta tace
"Sannu Mommy"
Bata jira ta amsa ba ta wuce kitchen ta samu Talatuwa na aiki, ta ce
"Talatuwa me kike dafawa?"
"Tuwo ne da miyar egusi shi mutanen gidan suka ce a dafa musu"

"Toh bari ki ɗora min fried Rice da kaji iyayena za su zo ganin ɗakina ba zan tarbesu da tuwo
ba"
"Amma S..."
"Kin yi abinda nace ko sai na bi ta kanki? Har kin isa ja da ni typical 'yar aiki? Toh wallahi ki
kiyaye ni"

Sadiqa da ke shigowa ne tace
"Haaa me ke faruwa da ihu haka?"
Talatuwa ce ta mata bayani sadiqa ta kalleta sama da kasa
"Amma ba ki da hankali yanzu su Gajen ne baƙi da har za'a dafa musu kaza da wani fried Rice?
Dama shi suka saba ci a gida?"
Sabreena ta riƙe baki tana kallonta na seconds kan tayi wani murmushi kawai ta juya fuuuuu ta
fice.

Mommy na nan zaune tana tunanin wannan lamarin da bata gane kanshi ba bare ƙasan shi ta
ga wucewarta kamar iska, ba'a fi mintuna biyu ba sai Ga saleem rike da belt nashi na sojoji ko
mommy bai kalla ba ya shiga kicin ya ya kuwa samu Sadiqa ya rufeta da dukar kawo wuka....




🖤Gureenjoh🖤

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Ku lallaɓa wannan kaina ciwo wallahi kaman zai faɗi*

*26*

Ihu take yi sossai na neman agaji, shi kuwa tamkar wanda ake zuga shi dukan ta yake kaman
an aiko shi cike da wani haushi nasu da dama yana kwance ƙasan ranshi, Mommy da ta shigo
da gudu ne ta riƙe belt ɗin a tsorace take cewa

"SALEEM! SALEEM!! Me haka? Me ya hau kanka? Sadiqa fa kake yi wa wannan duka kaman
wanda ya kama ɓarawo? Sadiqa fa ba sameerah ko Samha ba?"

"Na kula rainin sun ya fara yawa ne, kuma wallahi kaɗan na mata ko kallon banza ta sake yiwa
Sabrina ta gani bare zagin iyayenta sai na yi ƙasa ƙasa da ita, marasa kunyar yara kawai..."
Yana kai nan ya wuce fuuuuu mommy dake tsaye kaman an dasa ta jiri ya kwashe ta ta tafi
zaune.

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun me ke faruwa?"
Sadiqa da baƙin ciki kaman ya kasheta tana dukunkune gefe tana kuka sossai don ba laifi ta
bugu ta ce
"Me kuwa mommy? Duk wa ya ja mana? Wlh babbar alamar tambaya ne akan yarinyar nan
dama ni ba sonta nake ba kika saka shi dole aurenta yanzu wa gari ya waya? Tun fa ba'a je ko
ina ba mommy wlh ba zan iya zama da yaya a wannan gida ba, ni zai daka? Akan Sabreena da
take ƙanwar ƙanwar bayana?"

Samha ta je ta kama sadiqa a tsorace take don jikinta duk rawa yake, ita dai Sameera bata ce
komai ba ta juya ta fice, zuciyarta rawa yake kuma a cunkushe yake tana ji Mommy na fashewa
da kuka tana tambayar me ke faruwa ita ta kasa gane komai me ya hau kan ɗan ta? Ko ci
kanku bata ce ba.

Samha ce ta taimakawa sadiqa da ruwan zafi yayinda ta dawo parlor wurin Mommy ta zauna
suka yi shiruuu ita mommy tana tunanin me ya kamata tayi? Me yake faruwa ita bata gane
komai ba, Sabrina ta sauƙo tana waka ta wuce su zuwa kitchen ta tabbatar Talatuwa ta ɗora
mata abinda tace kan ta dawo ta haura ko kallon su mommyn bata yi ba.

"Ashe yarinyar nan macijin sari ka noke ce?"
Mommyn ta faɗa cikin mamakin duniya da ya rufe ta. Ina hijaban? Ina ladabin?
"Mommy me ta yiwa yaya saleem? Ki dubeshi a kwanakin nan kaman ba shi ba duk ya zama
wani iri ga faɗa da masifa ga saurin duka mu da tun muna kanana ma bai dake mu ba sai
yanzu?"
Samha ce me maganan zuciyarta har lokacin yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login