Showing 9001 words to 12000 words out of 149666 words
basu yarda cewa komai Allah ne yake yi ba.
Afeefah Kowacce rayuwa akwai ƙalubale ciki ke kuma ta ki kalar ƙalubalen kenan, amma fa na
faɗa na sake kar ki saka hakan a ranki saboda babu mai kashewa da raya wa sai ubangiji, duk
kuma wanda kika ga ya rasa ransa tabbas lokacin shi ya riga ya ƙare ne ko da sanadi ko babu
dole babu maƙawa sai ya tafi, tsakanin ki da su Adu'a ne shine zai ba su tabbacin irin ƙaunar da
kike musu. Afeefah mahaifiyarki ba za ta so ta ga kina zub da hawaye ko kin ƙuntatawa kan ki
saboda ƙaddarar da ba ke kika ɗorawa kan ki ba, kaman kowace uwa ni ma zan baki shawara
ki saka zuciyarki gaba, ki yi Adu'a ki kuma jajirce ki zama tamkar bishiyar gamji sara ko sassaƙa
ba su isa su hana ki toho ba"
Jikin Aunty zee kawai ta faɗa tana shesheka da kyar ta lallasheta ta bar kukan kan ta ɗago
"Na miki alƙawari in shaa Allahu Aunty za ki yi alfahari da ni nan gaba, ba za ki taɓa kuka a
kaina ba"
"Allah ya amince hajiya ta"
Dariya Afeefah ta saki jin ta kirata hajiyarta wadda babban burinta kenan ta zama shahararriyar
'yar kasuwa don tana so tayi kuɗi saboda wani dalili nata. Ƙaurin kamawar leda da suka ji ya sa
ta tashi da gudu taje ta sauke tukunyar alelenta daga kan gano tana furta
"Aunty alele na so yayi mana buƙulu"
Aunty zee na dariya tace
"Hira ta yi daaɗi ba, duba ki ga Allah ya sa bata yi komai ba"
Sun ci sa'a bata yi komai ba sai na ƙasan guda biyu da ledar ya ƙone nan ta zuba musu tare da
Auntyn ta zuba na uncle a kula suka zauna suka ci tare suna hirar su gwanin sha'awa bayan
sun gama ita ta yi wanke wanke, ko da ta dawo kan taburman hoton Aunty zee ta bata
"Gashi na bar miki, ki ajiye a wurinki"
Murmushi ta saki kan ta karɓa tana godiya.
Wasa wasa cikin Aunty zee ya shiga watan haihuwa, ta ɓangaren Afeefah tana nan tana
ƙoƙarin karatu ka'in da na'in don 2nd term da suka koma ita ta ɗauki na ɗaya kuma 3rd term
nan suna ƙare ta tare da ita za'a zana Junior waec ta tafi ss1, a yanzu hatta turanci ya zauna a
bakinta ba kaman baya ba da bata wani jin komai, duk wani sayayyar haihuwa tare suke zuwa
saboda a hankali ciki ya sa Aunty zee ɗin ta shigar da Afeefah cikin business ɗin ta, wani
lokacin ta kan aike ta ita kaɗai ma kasuwa wurin customers ɗinta kuma ta zo ta raba wa clients
ɗinta kayan, asusu Aunty zee ta yi mata ta kan ware ladar ta na kasuwanci ta saka mata ciki
duk da Afeefah ta nuna ita bata so, tufafi, karatu da kuma cima sau uku da ake bata ya wadatar
da ita. Amma Aunty zee ta nuna hakan shine adalci kuma ko nan gaba zata iya anfani da
kayanta idan buƙatar hakan ta taso.
A yau Aunty zee take cika wata tara da kwana tara kuma a ranar ta kwana da labour mai zafi,
hankali tashe da asuba suka tarkata asibiti har da kishiyarta da ta zo ta kwanan musu
kasancewar tun da abin ya fara mijin ya ƙirata, ta fi kowa shiga damuwa an ƙarbe ta zuwa ɗakin
haihuwa sai jiran abin da hali zai yi, duk Afeefah ta fi ruɗewa babu abin da take tunawa vividly
sai irin wahalar nakudar da innarta tayi ƙarshe daga ita har babyn suka koma wannan abu ba
zata taɓa mantawa ba, duk kuma ta ga mai ciki sai hantar cikinta ya kaɗa a yanzu Allah kaɗai
ya san halin da take ciki na tsoro da fargaba duk adu'ar da ta zo Bakinta ita take yi.
Sai Azahar Allah ya taimakesu midwifes ɗin da suka karɓi haihuwar suka fito suna musu albishir
na ta samu 'yan biyu mace da namiji faɗin kalar murnar da suka yi ɓata baki ne. Karo na
barkatai kenan da Afeefah ta ke kai idanunta kan yaran hakwaranta duk waje, yaran gwanin
sha'awa kaman ta Haɗiye su, sam bata san Aunty zee ta farka ba sai ji ta yi tana furta
"Suna ba ki sha'awa ko Afeefah?"
Da sauri ta juyo tana dariya
"Sossai ma Aunty zee, sannu kin farka? Ya jikin?"
Ta ɗan saki murmushi.
"Masha Allah, jiki Alhamdulillah"
Ta furta hawaye na gangaro mata Dukda tana sauƙa sai da ta ji ɗuminsu kan wannan
wahalallen baccin ya yi awon gaba da ita amma yanzu da ta farka sai take ganin kaman
mafarki, kaman ba'a gaske ba ita ce yau da shekaru arba'in da biyu a duniya kan Allah ya nufe
ta da ganin ƙwanta? Har biyu kyautar Allah? Bata san wani irin godiya za ta yiwa mahallicinta
ba don ko yau ta faɗi ta mutu ta san ta bar bayan da za su iya tunawa da ita su yi mata Adu'a,
bata san daaɗin haihuwar ya kai har haka ba a ganinsu da take kawai ji take kaman ta rabu da
baƙin ciki har abada matukar suna kusa da ita.
A hankali Afeefah take kokarin ɗaukar su ta kaiwa uwar, daidai shigowan kishiyar Auntyn
"A'a Afeefah me haka? Sabbin haihuwan kike ɗaga su anyhow? Wa kika tambaya da za ki ɗaga
su?"
Yadda take maganan zaka zata wani gagarumin abu Afeefar ta aikata don har ta tsorata, da ta
kurawa matar idanu sai ta fahimci kaman akwai dalilin maganar nata amma bata wani mai da
hankali ba don Aunty zee ta amsa mata
"A'a hamdiyya ai Afeefah ba yarinya ba ce da zata kada yaran baki san ko yanzu ta yi aure zata
iya haihuwa ba? Getting to 18yrs ba wasa ba"
"kin ga Aunty sabbin haihuwa ne kuma ji da abin mu muke ko kuda bama so ya taɓa su bare
wasu da idonsu idon sabon jini su ke Sha'awa"
Da sauri Afeefah ta mayar da idanunta kan matar, Aunty zee ma ta ɗago ta kalleta
"Me kike nufi Hamdiyya?"
"Gaskiya nake faɗa Aunty, hanyar lafiya sai a bi ta da shekara ba za mu so farin cikinmu ya
koma baƙin ciki ba"
Hawaye ne ke kokarin zubowa Afeefah da jikinta yayi wani irin sanyi, bata ankara ba sai ji ta yi
Aunty zee ta ɗora mata yaran duk biyu a kan kafafunta
"Afeefah ga su nan ƙannenki ne, ki riƙe su yadda kike so"
Juyawa ta yi ga hamdiyya
"A kan Afeefah za mu iya samun matsala da ke, ba zan taɓa zuba ido ki tozarta ɗiyata a
gabana ba, kin ga yau na haife su ko? Kuma na san daaɗin su ko? To wallahi zan iya zaɓar
Afeefah sau dubu kan in zaɓe su sau ɗaya. Ki kiyaye kan mu yi uwar watsi da ke a kan 'yata"
"Aunty ni kike yi wa gori a kan wannan mayyar?"
Ko kan Aunty zee ta yi magana Uncle ya shigo, kafin ya tambayi me ya faru Hamdiyya ta fashe
da kuka mai ƙarfi tana yunƙurin fita, da sauri uncle ya tare ta don shi mutum ne da baya son
abin da zai kawo mishi matsala da iyalanshi, yayi kokari ƙwarai wurin haɗe kawunansu ba zai
so ko ma menene ya raba su ba, ban da ma yanzu da suka soma tara zuri'a suke kuma cikin
farin ciki tsantsa.
"Me ya faru hamdiyya? Zainab me ya haɗa ku?"
Aunty zee dai komawa ta yi ta zauna sai hamdiyya ce ta kara karfin kukanta
"Ka yi haƙuri ni ce da laifi na zaci da ni da Aunty duk ɗaya mu ke kuma 'ya'yanta za su iya zama
nawa amma ashe na yi kuskure, in shaa Allah ba zan sake ba"
"Zainab!"
Uncle ya furta sunan cikin rashin jin daaɗi
"Gori kika yi mata?"
"Amma dai ka fi kowa sanin hali na Usman, ban yi mata gori ba kuma ba zan taɓa yi mata ba
don nima babu wayo na bare dabara ta Allah ya ba ni, abin da take shirin shigowa da shi ne ba
zan lamunta ba sam"
Hannunshi dake cikin nata hamdiyya ta janye
"jita-jita bai taɓa wanzuwa ba matukar babu kamshin gaskiya, an sha tare ni ana gargadina a
kan Afeefah amma na ɗauke kai saboda ganin yadda Aunty zee ke ƙaunarta, abin da nake
tsoro an ce suna kaunar sababbin jini to don na ce Afeefar ta yi haƙuri da daukar su har su yi
kwari shikenan na yi laifi...? Ku yi haƙuri bari na je gida"
Tana kai nan ta fice uncle bai ce komai ba don shima karo na ba adadi an tare shi an faɗa mishi
abubuwa dayawa kan Afeefah amma baya bari ya shige shi, sai dai kuma bai ji daaɗin reaction
na zainab ba da sai a bi abin a hankali tunda dai already akwai maganganu kan Afeefar.
"Amma ba ki kyauta ba zainab, na sani kina kaunar Afeefah kasancewar ta marainiya kuma
abin tausayi amma kuma sai ki duba kokarin hamdiyya wurin ganin ta bai wa jininki kariya, tun
fa jiya tana tare da ke ko runtsawa bata yi ba, ko da kika sauka kika fara bacci haka ta koma
gida ta dafo miki ruwan zafi ta biya ta sayo kayan tea saboda kar ki tashi da yunwa babu
abunda zai taimaka miki, ai gyara kayanka baya zama sauƙe mu raba"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Idanunta ta mayar kan Afeefah dake hawaye sossai, rabon da taji raɗaɗin zuciya tun ranar da
uncle ya amince ta zauna da su sai yau.
Yanzu ko da tana cin naman mutum wani bala'in ne da rashin tausayi haɗe da rashin imani zai
sa ta ci naman waennan talikan da isowarsu duniya kenan? Me zai sa ta cutar da 'ya'yan wacce
ta rungumeta ta cicciɓota ta zaro ta daga cikin bala'i da ƙuncin rayuwa?
"Afeefah..."
Auntyn ta ƙira sunanta a hankali sai kuma ta kasa magana duk suka yi shiru tsawon lokaci kan
nurses suka shigo, hakan ya tilastawa Afeefah barin ɗakin kai tsaye fita tayi daga asibiti ta tsare
abin hawa ta faɗa mishi inda za ta, gidan Hamdiyya ta nufa don ta tabbatar a chan za ta samu
Uncle usman da ma ita karan kanta hamdiyyar.
Hasashenta ya tabbata don kuwa ta same shi tare da hamdiyyar yana ta kokarin bata baki tana
tuburewa, maganganu take gayamishi cikin ɗaci da nuna kaman shi ne ai ya zaɓi ya ba
Zainabun ciki har ta haifi 'yan biyu tana mata gori.
"Haba hamdiyya kema kin san da mutum shi ke ba kanshi haihuwa da yanzu mun tara yaran da
bakya zato saboda Zainab macece mai kaunar yara, tun aurenmu na shekara duk inda taji
magani muddin bai saba shari'a ba nema take amma da Allah bai turo ba ba gashi yanzu ta
haihun ba? Ba'a cire rai daga rahamar ubangiji kema kuma ya san dalilin da ya jinkirta naki
namu Adu'a ne kawai da neman zabin alkhairi daga rabbissamawati".
"A'a Usman ai ka fi ƙaunar Zainabun idan da Zainabun ta haihu tun farkon aurenku da baka
auro ni ba, silar rashin haihuwar ne ta saka ka kara aure ba don kana so na ba kuma ta haihun
ai..."
sallamar ta ya katse musu maganar duk suka mayar da hankali kanta.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*006*
"Uncle, Aunty hamdiyya don Allah ku yi haƙuri, ban zo da niyyar wargaza zaman ku ba, na sani
Auntyna ta faɗa miki magana ne saboda irin ƙaunar da take mini amma ni na san gaskiya kika
faɗa, don Allah ki koma asibitin ki cigaba da kula da ita da jariran ni zan koma gida zan cigaba
da jira har lokacin da ya kamata a ce na ɗauke su ɗin"
Cikin wani kalar sanyin murya take maganan, idanunta har lokacin ba su daina zubar da
hawaye ba. Uncle ɗin tausayinta ya ji yayinda hamdiyya ta taɓe baki ta ce
"Toh ai shikenan, ni ba na yi magana ba ne da wata manufa kawai dai ina kare yaran da yanzu
ne muka fara morewa wanzuwar su ba za mu juri dare ɗaya a yi abincin meeting da su ba"
Uncle ne ya katse ta
"ya isa haka, ki tashi ki koma asibitin. Afeefah tashi mu je in sauƙe ki a babur na"
Miƙewa ta yi suka fice daga gidan, har suka iso gidan Auntyn nata magana bai haɗa su ba ta
sauƙa ta shige yayinda ya juya ya koma asibitin.
Bata bari abin ya cigaba da damunta ba ta kintsa gidan tamkar Auntyn na nan ta ɗora girki
marar nauyi ta ci ta zuba saura a kula kan ta ɗan kwanta bacci, har ga Allah ta tsame kanta ne
saboda gudun abin da zai je ya dawo sam ba zata so wani ya yi kuka sanadin ta ba bare
Auntyn ta don haka tana ganin shawarar da ta yanke shine daidai
Sai da Aunty zee ta kara kwana biyu a asibiti saboda postpartum ciwon ciki da ya matsa mata
amma duk da haka sai damun uncle usman take akan maganan Afeefar har fushi ta yi ta matsa
a sallame ta saboda tunanin ta kar Afeefar ta ji an ware ta ko ta sanyawa kanta damuwa, duk
da sun shirya da hamdiyya sai dai har aka yi sallamar hirar arziki bai haɗa su ba don ta matuƙar
jin zafin abin da ta yiwa Afeefar.
Tana sanya kai cikin gidan ta soma kiran
"Afeefah! Afeefah!!"
Da gudu Afeefah da ke zaune a parlor tana kallo ta fito ta rungumeta tana murmushin ganinta,
Auntyn ta ɗago fuskarta sai ta sauke ajiyar zuciya
"Afeefah ni kika yasar a asibiti ko?"
"A'a Aunty ban isa yasar da ke ba wallahi, na bari ne Aunty hamdiyya ta kula da ku ni kuma sai
in kula da gida ba gashi ba gidan ma ya ji daaɗi, da missing ɗin mu da zai yi sai yayi mishi
yawa"
Dariya Aunty zee ta yi tana girgiza kai, a parlor suka ya da masauki kan a natsa ma maƙota da
abokan arziki an fara shigowa barka tuni gidan ya soma ɗinkewa da jama'a nan Afeefah ta
shiga jeka ka dawo.
Zamanta da hamdiyya na kwanaki shidda ba karamin wahala ta sha ba ta kuma danne
zuciyarta, ko Aunty bata bari ta san hamdiyyar tana matukar musguna mata ba ta yadda ko
satan kallon yaran ta yi sai ta yaɓa mata baƙar magana, har tsoron kallonsu take Dukda tana jin
son su tamkar jini da tsokarta ta sha ɓuya tayi kuka sossai na mummunar shaidar da take dashi
don bata tsira ba ranar suna har nuna ta hamdiyya ta saka ake yi saboda kananun maganganu
duk Aunty bata sani ba.
Auntyn Ta yi matuƙar kyau cikin milk leshin ta yayinda yaran suke sanye cikin kyawawan
tufafinsu pink da blue, Afeefah ma cikin leshin da Auntyn ta yi mata musamman na suna
maroon ta shirya ta yi mugun kyau Aunty zee har ajiye ta tayi ta zana mata liner a baki ta saka
ta saka kwalli ta shafa mata powder sai tayi kaman ka sace ta ka gudu, masu hidima da kitchen
ita suke kira tana miƙawa mutane abinci daidai ta zo miƙawa wasu mata kenan da yake ta
bayansu ta zo ta ji ɗayar tana cewa
"Ni kam dai ina tausayawa Zainabu saboda fa da gaske yarinyar da take riƙo rikakkiyar Mayya
ce kuma fa an ce Mayu sun fi zaluntar wanda ya ji tausayin su"
Ɗayar ta ce
"Ni fa ban san yarinyar ba amma kuma ina da labarin tun tana ciki take cin maita, uban ta ma
bai tsira ba haka uwar da ta haife ta, aiko Allah raba mu da irin wannan iri. Haihuwa bata yi rana
ba"
Wani irin abu mai nauyi ne ya taso ya tsayawa Afeefah a kirji tana ji na ukunsu na furta
"za ki gane ta mana wata baƙa marar kiba ta saka leshi maroon, ai daga kallon idanunta da
suke manya kaman kwai kin san za'a ga kurwa da kyau... Allah dai ya hana farin ciki komawa
baƙin ciki"
Gabansu ta zagayo suka ɗan sha jinin jikinsu ganin fuskarta babu ɗigon walwala idanunta da
suka surke zuwa ja ta ɗan zuba musu kan ta ajiye abincin ta juya ta bar wurin.
A karshe dai ba'a tashi suna lafiya ba don wata wai aljannunta sun tashi ai sai ta kashe Afeefah
Mayya ce! nan fa gidan suna ya kachame dayawa suka shiga kururuwa su ma, da ƙyar aka fita
da ita a gidan zuwa maƙota ban da kuka babu abin da take, bata san wani irin tunani zata yi ba
duk ta ji kaman ta sallamarwa duniya farin ciki da rayuwarta sai ta tuna Aunty zee da ta yarda
da ita take kuma bata kariya don yanzu ma ita ce ta nuna jan ido ta sallami kowa da abin da
za'a yi sai ya fi haka, chan kuryar maƙociyarsu ta takure tana kuka sossai bata ji Shigowar
Aunty zee ba amma ta ji hannu ya taɓa ta firgita ta yi ta miƙe tsaye tana girgiza kai
"Wallahi ni ba Mayya ba ce! Ban san ya ake yi ba don Allah ku yi haƙuri ban taɓa cin naman
mutum ba wallahi..!"
A rikice take maimaitawa da sauri Aunty zee ta rungumeta tana hawayen tausayinta
"Ya isa Afeefah! Ni ce! Auntynki ce, na sani wallahi na sani ke ba Mayya ba ce na yarda da ke"
Kuka kawai ta saki mai tsuma zuciya tana yin luff a jikin Aunty zee ɗin.
Jiki a sanyaye duk suka dawo gidan, yayinda abin da ya faru a sunan ya tsayawa Afeefar ta
yadda ko kuzarin taɓa yaran bata da shi, tsoro take ji kar ta taɓa su abu ya faru haka Aunty zee
ta sa uncle usman a gaba tana kuka sossai
"Duk laifin matar ka ne usman da bata fara ba da hakan bai faru ba, yaran nan fa kannen
Afeefah ne amma ka ga yadda take baya baya da su ko taɓa su sai na yi da gaske take yi!
Haba mana ko bata duba komai ba ta duba maraicinta mana wallahi ta ɗauki alhakinta dayawa
kuma ni kam ta daina burgeni sam"
Shiru yayi chan ya ce
"Ki yi haƙuri zan yi mata magana, amma ki dinga dubawa itama hamdiyyar ba don tsanar
Afeefah bane ya sa take hakan saboda kare yaran nan ne ganin tsawon lokacin da muka ɗauka
kafin Allah ya ba mu"
"Wallahi na fi ƙaunarta a kan su, ta cigaba da rayuwa da wannan tsangwamar rayuwarta na
cikin haɗari don Allah zan roƙe ka Alfarma don girman Allah kar ka chanza mata kaman yadda
ka fara mata, ka dubi maraicinta ka riƙe ta kamar yadda za ka riƙe suhail da suhaila".
Hannayenta duk biyu ya riƙe
"Ban tsani Afeefah ba Zainabu, in shaa Allahu kuma zan cigaba da iya ƙoƙarina a kanta"
"na gode sossai Baban 'yan biyu"
Ya saki murmushi ita ma ta mayar masa.
Duk su biyun sun mayar da hankali kanta ta yadda hatta shi uncle ɗin kan ja Afeefar jiki ko ma
ya bata babies ɗin da take matukar so ta riƙe, yau satinsu na biyu kenan a duniya.
Tsaki Aunty zee ta ɗan ja kaɗan karo na ba adadi hakan ya