Showing 48001 words to 51000 words out of 149666 words
kawai na tsince ni gaban kakata wacce ta haifi babana...."
A hankali ta cigaba da basu labarinta tun daga farko har ƙarshe, ta gaji da kuka a kan labarinta
hakan ya sa a yanzu ta danne kwarai bata yi kukan ba sai idanunta da suka rine matuƙa gaya,
bayan ta gama ta ɗago ido tana kallon expression na su Mammin gabanta na faɗuwa zuciyarta
na duka da ƙarfin gaske....
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*22*
Ga dumbin mamakinta dukkansu biyu kuka suke yi, Abeeha kam ma da sauti yayinda Mammi
ke zubar da hawaye, ko kan tayi wani yunkuri Mammi ta miƙe ta iskota ta ɗago ta sai ta sanya
ta jikinta ta rungume tana shafa bayanta, wannan dalili! wannan ɗumin jikin shi ya saka Afeefah
fashewa da sassanyar kuka mai sauti.
Sun fi mintuna goma a haka tana wannan kukan, tuna komai take yi tamkar yanzu ne ya faru ji
take duk mace-macen yanzu ne suke dawo mata sabo, taji tana kewar mahaifiyarta da Aunty
zee, wannan tausayi da kauna da ta gani daga Mammi sai ya tsaya mata a rai ta ji itama tana
ƙaunar matar tamkar mahaifiyarta.
Rayyan da tun kan tayi nisa ya lumshe idanunshi bai buɗe ba sai da ya ga kukan na yawa, duk
tsikar jikinshi jinshi yake a tashe, ko da ya miƙe zaune sai da ya ji kanshi ya sara ya ɗan runtse
idanunshi ya buɗe kan ya ja tsaki ya sauka daga gadon, ya taka ya dafa kafadar Mammi da har
lokacin take rike da Afeefah.
Mammin gabanta ya faɗi tuna yana ɗakin ta tuna labarin Afeefah sai tayi sauri ta saki Afeefah ta
waiga tana kallon yanayinshi, idanunshi ya sauƙe kasa a hankali yace
"Mammi please ki bar kukan nan, you are sick already kukan nan bashi da amfani, dole ne sai
mutum ya rayu da dangi? Dole ne sai sune kaɗai za su baka farin ciki da kulawa? Na Allah na
nan dayawa Mammi..."
Yankewa maganan yayi ya ɗago garin kaucewa idanun Mammi sai nashi suka sarƙe cikin nata,
sama da seconds huɗu yana kallonta kan kawai ya juya ya bar ɗakin.
"Saraki.! Saraki....!!"
Bai juyo ba ya fice, ta duƙar da kanta tana ambatar sunan Allah... Chan ta sauƙe numfashi ta
waigo ga Afeefah da tunda taji sauƙar muryarshi da yadda yake magana da amo kukanta ya
tsaya chakk, haɗa idanun da suka yi ya matuƙar Dakar zuciyarta idanunshi abin tsoro ne a
gareta amma a yanzu sai taga ya zama wani iri duk yadda zata fassara ma'anar kallon nashi ta
kasa, maganan Mammi ne ya dawo da ita tunaninta.
"Lallai Afeefah kin ga rayuwa, haƙiƙa na kaɗu da labarinki abin mamaki kika iya daurewa kika
cije kika tsallake wannan jarabawa duk da kananun shekarun ki, Afeefah rayuwar nan duk
jarabawa ce kuma ko wani lokaci yana da karshen sa, za mu yi ta shan wahala a duniya amma
sakamakon yana hannun Allah kuma ya fi jarabtar wanda ya fi kauna daga cikin bayinsa,
Afeefah ina so ki san idan dai har ni, Abeeha, jidda ko Saraki muna raye a wannan duniya kin
gama kuka, zan cigaba da rikeki har karshen numfashi na haka zan yi musu umarnin cigaba da
kula da ke da baki kariya har nasu karshen numfashin, in shaa Allahu kin gama zubar da
hawayen baƙin ciki Afeefah... Sannu! Sannu da juriya"
Sabon hawaye ne suka cigaba da silalo mata ta sake rungume Mammi tana fashewa da kuka,
Abeeha ta taho ta ɗago ta tana riƙe hannunta
"In shaa Allahu ba za mu taɓa kyamatarki ba Afeefah ai duniya ce idan wani ya ƙi ka dole wani
ya so ka haka Allah yayi rayuwar, ni na yarda ki ƙirani Addah don ko kowa zai guje ki in shaa
Allahu ni ba zan taɓa gudar ki ba"
Sossai take kuka, a ranta Adu'a take tana tuna irin kaunar da Aunty zee ta nuna mata a ƙarshe
ta tafi ta barta, anya ta zama mai adalci? Anya zamanta a gidan zai haifar da ɗa mai ido?
Karshen wahalar kenan ko kuma akwai saura? Duk ta bar wa Allah.
Sossai suka rarrasheta ta natsu kan Mammi ta miƙe tayi sashen Rayyan don duk yana cikin
ranta tun ɗazu, a kwance ta same shi hallau dai idanunshi a lumshe, kai tsaye ta je ta sa hannu
a goshinshi ganin jijiyoyin kanshi raɗa-raɗa a waje, jin hannunta ya sa ya buɗe idanun da suka
sake sauyawa ya zuba mata
"Saraki ciwon kai ne? Ko za ka je asibiti?"
Girgiza kan yayi kaɗan yana yamutsa fuska
"Ba sai na je ba Mammi"
"Saraki in na barka haka dare ba zaka iya bacci ba, ka taimakeni ka je ka ga psychiatrist din ka"
Shiru yayi bai ce komai ba. Ta sauƙe numfashi ta fara duba wayanta cikin mintuna kaɗan sai ya
ji muryarta tana magana da likitarshi, buɗe ido yayi ya kalleta bata damu ba har suka gama
wayan.
"Za ta zo, don Allah ka tashi ka saka wani abu a jikinka mu je parlor"
Ta faɗa cikin kulawa kaman yadda yake damuwa da ciwo da damuwarta, shi ma bai san yadda
zai yi bane, bai san ya zai yi ya hana kwakwalwarshi tsayar da tunanin baya ba, bai san ya zai
yi ya cire tsananin nauyi da damuwar da ke kwance a ƙasan ranshi ba, a duk lokacin da ya
samu sassauci to fa a tsakanin da yake ganin farin ciki da walwala a fuskar Mamminshin ne
saboda baya so yake sakata cikin damuwa amma yaya zai yi?
"Zan zo!"
Ya faɗa a hankali.
Ta juya ta fice da damuwa a fuskarta, bai yi bacci ba a daren jiya dama ya saba da rashin
isashen baccin dare, tun tana kwana dashi har taga yayi girman da bai kamata su cigaba da
kwana ba amma ko bacci take tana tunanin yadda yake tafiyar da nashi daren, ba'a yi mishi
adalci ba amma kuma to ya suka iya ne?
Da kyar ya miƙe ya saka armless vest mai fadi da three quater da ya kai mishi gwiwa, a bakin
gadon ya zauna yana dafe kai har lokacin fuskarshi jazir babu ɗigon fara'a a kan fuskar tashi,
ba'a jima sossai ba sai ga Mammin ta dawo ta kama hannunshi suka fito, a zaune kan kujera ya
ga Dr. Ɗin tashi macece babba da a haife zata haife shi, ganin sun haɗa idanu ya sa tayi mishi
murmushi ya ɗauke idanu, ajiyar zuciya ta sauke har ya zauna ya kishingida ya ɗaura kafa daya
kan daya Mammi ta fita bata ce komai ba.
"Malam Rayyan! Barka da warhaka"
Ido ya ɗan buɗe ya kalleta kan ya amsa.
"Whats happening? Na zaci mun wuce wurin nan duka..! Mafarkin ne?"
Shiru yayi chan dai ya gyaɗa kai
"Am having a sleepless night for almost a month now"
"Me ya faru? Are you taking your pills?"
Gira kawai ya ɗaga don kan ya mishi nauyin da ba zai iya dagawa ba.
Ba don ma ya san darajar likitar ba ba zai kula ta ba, tayi ta janshi da magana dai har ya ɗan
sake ta bashi magani cikin kulawa da kwarewa a aiki.
"Mammi wants me to get married, tana tsoron ta mutu...." Ya ɗan yi shiru zuciyarshi babu daaɗi
sam kan ya cigaba
"ba ta so ta bar ni ni kaɗai ba tare da mata ba and i hate the idea... Me yasa take yawan zancen
mutuwa? Yana damun zuciyata da kwakwalwata kina tunanin zan rayu bayan bata nan?"
Idanu ta zura mishi, Rayyan a cikin patients ɗinta da take gani sama da shekaru talatin yana
daga cikin na daban da take jin damuwarshi tamkar ɗan cikinta, tana tsananin tausayinshi gashi
kuma Allah sai ya sake aiko mishi wata jarabawar akan wata na rashin lafiyar Mammi da
fargabar mutuwar a kowani lokaci, sam bata so Mammin tashi take kawo mishi zancen tunda a
ranshi ya riga ya san kowa zai mutu idan ajalin shi ya zo amma kuma ta taya ta duba raunin da
yake danne wa a cikin zuciyarshi he was already traumatized, yana fama da insomia for so long
ciwon Mammi kuma ya haifar mishi da anxiety tsoro da fargabar barin shi da zata iya yi.
Lallaɓa shi tayi tayi har ya ɗan sake, maganin da ta bashi kuma ya taimaka mishi don kafin ta
tafi ma yayi bacci a kan kujerar, Mammi ta samu
"Don Allah Maman Rayyan ki taimakeni a kan Rayyan, ki daina mishi maganganun da zai ji a
ranshi kaman wasiyya ne, kin san matsalar shi kin san da ya ya girma in ba Allah ba babu mai
iya kawo Rayyan matakin da yake kai yanzu"
"Dr. Ya zan yi ne? Ina faɗa mishi hakan ne saboda ya shirya, ya kamata ya shiryawa hakan
dole zata kasance amma bana Fatan hakan ya kasance bashi da wani kafaɗar, bana Fatan
hakan ya kasance ba shi da inda zai iya bayyana damuwarshi shiyasa nake so yayi auren"
"Amma kin san matsalar da niyyar auren nan ya jawo a baya, a maimakon ya gyara sai
tabargaza da yayi mana har ya zama for months Rayyan baya aiki baya kuma fita ko ina, bakya
tsoron abin da ya faru ya sake faruwa?"
Shiru Mammi tayi itama duk damuwa a kan fuskanta kan ta ce a hankali
"Zan san yadda zan yi likita, na gode sossai da taimakon ki ina fata zai ɗore ko da bana nan"
Murmushi kawai tayi ta taso ta dafa kafadar Mammin ta ɗan bubbuga kan ta fice bata iya ta ce
komai ba.
Hawaye ne ya silalowa Mammin, ita kadai ta san me take ji, ita kaɗai ta san tsoro da fargabar
da bawa kan shiga a duk sadda aka ce maka ga wa'adin mutuwarka Dukda bata yarda ba
amma hakan ya tsaya mata a rai tun shekaru bakwai baya, Dukda ta wani gefen hakan ya
matuƙar bata kusanci da ubangijinta sai dai tsoronta yadda zata tafi ta bar Rayyan, bata jin
yaranta matan saboda basu da matsalar komai amma Rayyan fa? Raunin shi sabo zai dawo
bata son hakan bata Fatan hakan don haka dole ne a gareshi ya nemi abinda zai tallafeshi a
bayanta.
****
Ta ɓangaren Dr. Sulaiman neman duniya ya saka an yi wa Afeefah sai dai babu ita babu
alamunta, police station har uku daban daban ya kai report sai dai babu ko duriyarta.
Tun yana ciwon kai a tsatsaye har sai da ya kwanta don da gaske ya matuƙar damuwa, a
ƙarshe haƙuri umma tayi ta bashi akan ya fawwalawa Allah ya karɓi auren da aka bashi don
Abba ya nuna mishi babu gudu babu ja da baya.
A dole daga ita har ƙannenshi suka fara shirye shiryen auren tunda sati biyu kachal ya saura a
yanzu.
****
A ɓangaren saleem ma duk ya ƙare a tsaye saboda damuwa da tunani, a kullum adu'ar shi a
kan Afeefah ne Allah ya tallafeta ya hanata faɗawa halaka Allah yayi riƙo da hannayenta ya
bata uwar ɗaki na ƙwarai, har yanzu iya gaisuwar ƙannenshi kawai yake amsawa wanda abin
ya dame su sossai ya zura musu ido kawai musamman mommy da ke ta shirye-shiryen aure
ka'in da na'in ita uwar amarya kuma uwar ango.
Sameera na zaune a kan plastic chair a wurin parking lots saleem ya shigo da motar shi ya zo
yayi parking ya sauƙa, bai mata magana ba don ta gaisheshi da safe kuma ya amsa har zai
wuce tace
"Yaya!"
Ya juyo ya kalleta duk tayi wani iri da ita
"Yaya don Allah kayi hakuri da abubuwan da muka yi maka, wallahi na gane kuskurena tun da
jimawa na tuba don Allah"
"Me kuka yi min Sameera? Ai ni dan uwanku ne ba zaku iya min komai ba ko? Sai bare ne zaku
iya yi wa... Babu komai Allah yana gani"
Kuka sossai take yi.
"Allah ya riga ya nuna min iyaka ta ko a haka na gane kuskurena, Yaya in na tuna abin da muka
yi wa Afeefah sai Naji tamkar jayayya muka yi da ubangiji... Za ka yi mamaki yaya idan na ce
maka na san abin da kake ji a ranka, na san zafi da raɗaɗin rashin masoyi domin Allahnta ya
saka mata, a sadda take nan ina samun sauƙi ne kawai da kallonshi amma a yanzu ko arzikin
kallon babu tunda Afeefah bata nan haka kawai ba sakayya bane?"
Idanu ya zura mata duk ta zama wani iri ta rame,
"Sameera wa kike so? Rayyan?"
Ta girgiza kai
"Sulaiman?"
Tayi shiru ya ɗan yi jimmm, kan ya matso ta.
"a haka kawai Allah ya barki ya rama mata, ba yafiyata za ki nema ba ita za ki nema ta yafe
miki"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Ta saukar da kai tana hawaye, tana bibiyar Sulaiman sossai Dukda bai sani ba a haka ta san
auren shi wadda hakan ya sake daga mata hankali amma ya zata yi? Jarrabawarta kenan, ashe
Afeefar ma ba laifi tayiwa ubangiji ba ya zaɓi jarabtar ta ta hanyar da ya so, ba zata taɓa cewa
Sulaiman tana son shi ba amma zata yi Adu'a Allah ya sassauta mata ya kawo karshen shi.
****
Rayyan yayi kwana biyu yana jinya kan ya ɗan sake Dukda ba sossai ba, sam ko a hanya basu
sake haɗuwa da Afeefah ba don bata zauna ba shima kuma ba shiga mutane yake yi ba idan
bashi da lafiya, Abeeha ta ɗauke ta suka yi sayayya sossai wadda Mammi ce duk tayi mata,
suka je aka sama mata makaranta sun ma ƙi karbar ta sai da kyar aka barta SS1 za ta yi waec
kawai SS2, idan tace hankalinta ya taɓa kwanciya irin na kwana biyun nan tayi ƙarya, wani irin
so da kulawa suke nuna mata.
Bata aikin komai don gidan ma'aikata har sun yi yawa sai ka ga daman zuwa kitchen, uniform
da ake jira ɗinka mata bai samu da wuri ba saboda uniforms ɗin school din ba'a Kasar nan ake
yi ba kuma tsakiyar term ne ya ƙare already wanda suke dashi ba'a kawo wani ba, don haka
kullum suna tare da Abeeha kusan duk wanda ya san Abeeha sai ya san Afeefah matsayin 'yar
uwarta.
Gidan Jannah suka je suka sha yinin su itama bata da damuwa kaman dai Abeeha don duk sun
samu nagartaccciyar tarbiya daga mahaifiyarsu.
A yau monday Afeefah ta fito sanye da uniform ɗinta mai dauke da bajin KIS(Kaduna
international school) tayi kyau sossai a uniform din sai kuma tayi kankanta, murmushi ne sossai
fuskarta tana yiwa Mammi sallama Abeeha ce zata sauketa in an tashi sai Driver ya je ya ɗauko
ta, har tana shirin fita Mammi tace
"Afeefah kin mance lunch box ɗin ko kunyar dauka kike?"
Abeeha tace
"Ana kunya da ciki ne? Oya maza yi sauri ki sameni a mota"
Da sauri ta juya bata ankara da akwai mutum ba kawai ta ji ta buga goshinta a kan kirjin shi,
kamshin turarenshi ya sanar da ita waye tun bai ɗago ba a razane tayi baya baya tana ɗago ido
sai suka sarƙe cikin nashi fuskar nan tamau, uban Harara da yake zabga mata ya sa ta nemi
rikecewa...
"Ba ki da hankali ne? Ko ba kya abu da natsuwa ne?"
Dakakkiyar muryarshi ya sauka a cikin kunnenta ai sai....
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*23*
"Ba ki da hankali ne nace!"
Ya sake faɗa da ɗan ƙarfi, in za ta iya tunawa kalaman shi na farko kenan a gareta, kila to bata
da hankalin ne don yanzu ma rikice wa tayi ta rasa me zata ce Bakinta ya kasa furta ko A sai
baya baya da tayi da sauri idanunta da suka firfito farare tass a kanshi.
Ganin Hararar da ya watsa mata yana cewa
"Daina kallona!"
Ya sa tayi saurin ɗauke idon, Mammi ce ta ceceta
"Haba Saraki! Bata san kana wurin bane za ka tasa ta gaba kana zazzare mata ido, kayi haƙuri"
Mammi yake kallo, itama Afeefah jin abinda Mammi tace ya sa tayi ƙoƙarin har haɗa kalaman
haƙuri tace
"Ka..yi haƙuri"
Tsaki ya ja ya wuce ta ya barta da fitinannen kamshin shi, kitchen ta wuce ta ɗauko lunch box
ɗin mai kyau dashi ta fito a sanyaye tacewa Mammi
"Mun tafi Mammi"
Daga haka ta fice a parlorn da sassarfa don tana fitowa ya zuba mata ido, tsaki ya ja bayan
fitan ta ya dubi Mammi
"Meyasa kuka sakata makarantar da ba'a sa hijab kamar ba musulma ba?"
Mammi ta kalleshi
"Yanzu menene aibun uniform din nan?"
Sky blue shirt ne da navy blue blazer da skirt Dukda a gwiwa ne sai dai ta saka socks da ya
haura mata har cinya, cover shoe Black ne kafafunta sai navy blue cap da ta rufe kanta kirip
dashi, neck tie ne me layi layi sky nd navy blue sun yi mata kyau kayan kuma babu inda ke
bude jikinta banda hannayenta da fuskarta.
Baki ya taɓe bai sake cewa komai ba, abin kari mammi ta kira aka kawo mishi ya fara karyawa
a hankali, bayan ya gama ya dube ta
"Mammi auren salim next week friday"
"toooh aure haka kwatsam babu sanarwa babu shiri?"
"Nima jiya ne yake faɗa min"
"Toh Allah ubangiji ya sanya alkhairi ya sa da mu za'a yi"
Ya amsa da Ameen.
Daga nan wani hirar ta shiga yi mishi yana bata amsa a hankali hankali har suka gama ya miƙe
ya bar gidan.
Ƙarfe biyu sai ga 'yan makaranta an shigo, bata samu Mammi a babban parlor ba kawai sai ta
shige ɗakinta tayi wanka ta sauya kaya zuwa doguwar riga Abaya onion colour mai kyau, hula
ta saka ta fito ta nufi ɗakin Mammi jinta take very fresh nd healthy, wani sa'in ta kan tuna salim
da halin da yake ciki sai kuma tace kila ma ya manta da ita, Sulaiman ma kan zo mata rai ko
yaya yake oho bata sani ba.
Da sallama ta tura parlorn Mammi ta shiga ta sameta zaune gabanta abinci ne, farin shinkafa ce
basmati aka dafa amma dibawa aka yi kaman na jinjiri da alama ma da measurement cup aka
gwada don ba zai wuce 1/2 cup ba, sai wani wake green, akwai salad ɗan kaɗan shi ma daga
lettuce sai cucumber da lemon tsami, kaza ce gasashiya 'yar kaɗan itama a gefe sai ruwa.
Murmushi Mammi ke yi tana amsa sallamar
"Barka 'yan makaranta an dawo?"
"Eh Mammi mun dawo, ya jikin?"
"Alhamdulillah, Ki karɓi abinci ki ci sai ki huta ko?"
"Toh Mammi"
Abincin Mammin ta zubawa idanu sama da seconds biyu kan tace
"Mammi idan ba damuwa zan iya tambayar me yake damun ki?"
Mammi tayi murmushi tace
"Babu damuwa Afeefah, ciwo biyu ne ke damuna an haifeni da diabetes na gado don tun ina
shekara biyu aka gane cewa na gaji ɓangaren mahaifina ne da ciwonsu na sugar, matsalar
ciwon sugar idan yayi tsanani yana iya affecting koda to wannan dalilin ne ya janyo na samu
damuwa da koda shekaru tara zuwa goma baya, an ma yi min aiki an chanza duka ba'a dace
ba Afeefah har ma an ba ni wa'adin wata uku shine ƙarshen rayuwata sai kuma gashi da yardar
ubangiji na shekara bakwai bayan nan"
Afeefah damuwa ne sossai ya nuna a fuskarta tace
"Toh Mammi shi ciwon ƙodar yaya yake? Ba'a warkewa ne?"
"Allah ya halicci mutane