Showing 144001 words to 147000 words out of 149666 words

Chapter 49 - Haihuwa Da Hanji

Unknown   

16 Mar 2026

4420

mahaifina ya same shi ba tare
da na zo duniya ba, mahaifiyata ta rasu bisa rashin kula da rashin zuwa asibiti a yayin daukar

ciki zuwa haihuwan gida, kakata shekarun ta ya ja ƙwarai wacce dole a yi mata tsammanin
mutuwa a sadda ta tafi haka Goggona ta tafi bisa sakaci da zaman jahilci da dabbanci da ake yi
a cikin gidanta, bamu san kan mu ba bare mu nemi sanin hakkoƙin da suka rataya mana,
hakkoƙin matayenmu, hakkoƙin iyayenmu bare hakkoƙin 'ya'yayenmu wanda duka sai ta hanyar
ilimi za mu sani, na koma wurin Aunty zainabu ta gamu da postpertum wanda ciwo ne da ake
samun shi bayan haihuwa duba da bata taɓa ba ga yawan shekaru babu wanda ya fahimci
hakan sai da lokaci ya ƙure ta tafi duk ba mu dubi ajalin su ne yayi ba, mun manta Allah ya ce
ba zai taɓa jinkirta ajalin dayanmu ba idan ya zo dole za mu tafi. ku sani na yafewa kowannenku
da wanda yayi min na sani da wanda ban sani ba duk na yafe muku, a wannan gidauniya tawa
tafiyar duk na neman ilimi ne da kuma tsayuwa akan kafafunmu don Allah ina roƙon mazaje da
ku bar matayenku da ma ku karan kanku ku nemi ilimi don Allah ba ya ƙarbar uzurin bawa akan
rashin sani saboda ya mana umurnin nema.

Akwai ma'aikata da za su koyar da sana'o'i ga yara da matayenku su ma ku bar su don zai
amfani wannan al'umma tamu, duk lokacin yaye ɗalibai idan yayi zan zo kuma idan Allah ya
amince za mu dinga raba kyaututtuka da suka shafi sana'ar da mutum ya koya don ya cigaba
daga inda ya tsaya ina Fatan ganin chanji daga gare mu bakidaya na gode"

Wasu hawaye suke yi suna tuna abinda suka mata amma dayake tana da zuciya mai kyau dubi
Alkhairin da ta nufe su dashi, kawu ta miƙawa mic ɗin don ya taso yana son yin magana, a
gaban tarin al'ummar yana kuka ya ba da duk labarin abinda yayi mata da wanda aka mishi ta
sanadiyar son zuciyarshi da yadda ilimi ya sauya shi daga mummuna zuwa kyakyawa har ya
kara da
"An karɓo daga Kasir ɗan Qaisi ya ce, ina
zaune tare da Abud Darda'i a masallacin
Dimashqa, sai wani mutum ya zo wajensa ya ce masa, Ya Abud Darda' i na zo wajenka ne
daga Madinar Manzon Allah (S.A. W) saboda
wani hadisi da aka ce min kana faɗa daga Manzon Allah (S.A. W), kuma babu wata buqata da
ta kawo ni nan sai wannan. (wato jin wannan hadisin) Sai Abud Dar' da'i ya ce,
"Na ji Manzon Allah (S.A. W) yana cewa :
"Duk wanda ya bi wata hanya yana neman ilimi a cikinta, to Allah zai sanya shi akan hanya
daga cikin hanyoyin Aljannah, kuma haqiqa Mala'iku suna sanya fika - fikansu ga ɗaliban ilimi,
don yarda da abin da yake nema, sannan duk wanda yake sama da qasa yana nema wa
malami gafara, har ma da
kifayen da suke cikin ruwa. Falalar malami a
kan mai bauta kamar falalar wata ne a daren
goma sha hudu a kan sauran taurari, kuma haqiqa malamai magada Annabawa ne,
Annabawa kuwa ba su bar gadon dinari ko dirhami ba, kaɗai sun bar gadon ilimi ne don haka
don Allah kar mu raja'a akan boko don shi iya na duniya ne mu nemi lahira kuma mu koyar
komin kankartarsa, ko uwa malama ce akan yayanta kar mu saka finafinai ko waƙa gaba mu ta
rawa da nishadi da yara mu koya musu abinda zai amfanesu a gaba. Ni a karan kaina misali ne
kuma Aya ne ubangiji ya nuna min akan Afeefah"

Duk jikin mutanen wurin yayi sanyi kuma sun gamsu ɗari bisa ɗari da lallai suna da nakasu ta
wannan fannin dole rayuwarsu ya tafi a jiɓance, Afeefah da manyan gari a gefenta mijinta ne da
ya bata support ɗari bisa dari suka zaga wurin tassss ta yabi kyau da tsarin komai na wurin
kuma duk abin bukata akwai.
Kawu ta damƙawa wurin ta ce ta bashi amana ya riƙe mata ya kula da komai yadda ya kamata
bisa tsari shi dai babu bakin magana don ya rasa me zai ce.

Cikin jami'an tsaro masu kula da taron kawai idanunta ya sauƙa kanshi, da sauri ta nufe shi
tana kallonshi shima ita yake kallo a hankali ta nuna shi "Sa'adu? Sa'adu Rabi'u kai ne?"
Kai ya gyaɗa yana murmushi ya gane ta amma bai zaci zata nuna ta sanshi ba ta juya ta kalli
Rayyan ya matso
"Ka tuna shi Ya Saraki?"
"Wannan police da ya ceceki daga sharrin gurbatattun 'yan uwansa"
Za Ta cire zobenta na gwal ya miƙa hannu ya riƙe nata, ya zari kati daga aljihunshi ya miƙa
mishi
"Ka ƙira ni in shaa Allah kyautarka ya fi karfin kuɗi za'a mayar da kai cikin Kaduna da matsayi
mai kyau"
Hawayen murna ya fara yana godiya.

Ko da aka watse taron suka koma gidan Kawu akan za'a saka date na fara daukar ɗaliban da
suka kamata za kuma ta turo waenda za su taimaka mishi wurin fahimtar komai da komai kan a
sakar mishi, a tsakar gidan suka samu an jibge kayan abinci babu abinda babu wanda za su iya
ma watanni goma zuwa ashirin basu nemi kayan abinci ba, a gefe crouches ne da wheelchair
na inna Larai Afeefah tayi saurin kallon Rayyan ya girgiza mata kai yana dan ɗage kafada sai
ya juya ya fice ta bi bayanshi

Za tayi magana jiri ya ɗan dibeta da sauri ya riƙo ta
"Boɗɗi menene? Ba kin ga illar kukan da kika dinga yi ba duk yau kin tarawa kanki damuwa!
Kan na ciwo ne?"
Ya kai tafin hannunshi yana dafe goshinta hawayen ta sake farawa
"Ban san da wani baki zan fara maka godiya ba Ya Saraki... Ko baka faɗa ba na san aikinka ne
Allah ya biya ka ya saka maka da alkhairi ka yi min komai Ya Sa..."
Hannunshi ya sa ya rufe mata baki yana dan ɗauke hawayen da take zubarwa yace
"Kin chanchanci fiye da haka a gareni Afeefah don haka ba komai ba ne, na so ko gidan haya
ne mu kama a gyara wannan amma bai samu ba idan ba damuwa za su dan koma Kaduna ko
ma su je ganin ɗakin ki a Fombina kan su dawo sai a gyare nan ɗin"
Rungume shi kawai tayi ya sa hannu yana dan shafa bayanta kan ta ɗago sai ta sake jin jirin
yamutsa fuska tayi, ya shiga mota don bai kula ba itama ta zaci ma stress ne don haka ta koma
ta musu bayanin za su je Fombina ko sati biyu su yi za'a ɗan gyare nan ɗin kuka kam kawu har
ya rasa hawaye ya rasa bakin godiya a haka suka ɗauki duk abinda za su ɗauka aka adana
kayan abincinsu a daki guda suka ɗauki duk wani abu mai muhimmanci, yaranshi maza
manyan uku da mata shidda na Inna Asabe uku na Inna Larai biyar suka bar garin zuwa
Kaduna.

Kai tsaye gidan Mammi suka yi masauki jannah ta turo abinci ko da Abeeha ta gaya mata da
baƙi suke ta turo daga restuarant, a masaukin baki aka sauke su suna ta mamaki da santin
gidan, Ita dai Afeefah su Suhaila ta ja zuwa ɗakinta ta musu wanka ta duba cikin tsarabarsu da
ta musu na musamman ta fidda kaya ta saka musu suka haɗe babban parlor aka ci aka sha kan
kowa ya nemi makwanci don sun gaji, sai da ta tabbatar sun yi bacci ta watsa ruwa ta shirya
cikin wani Red kayan bacci da yayi mata kyau sossai marabarshi da babu kaɗan ne ta nufi
ɗakinshi...

Yana jingine da gado yana jiranta suna haɗa ido suka Sakarwa juna murmushi mai ƙayatarwa,
yanga tayi ta mishi Dukda kunya dake ɗawainiya da ita barin killer looks da yake binta da su har
ta iso gadon ya fusgo hannunta ya manna ta kirjinshi yana matse ta a lokaci ɗaya suna sauƙe
ajiyar zuciya a tare
A kunnenta ya raɗa mata
"Kina kashe ni da raina Gimbiyata"
Ta ɗan ɗago bai tsammata ba ta haɗe lips ɗinsu kaman jira kuwa ya mirginata kasanshi ya
mata rumfa yana bata wasu kisses da suka sake matar da ita a kaunarshi hannunta na yawo
bisa bayanshi zuwa keyarshi tana mishi susa, gasping air yayi ya raba lips ɗin suka yi murmushi
mai sauti ya sake mayar da lips ɗin yayi mata kyakyawar Kiss

Ta raba fuskansu tana shafa kanshi hancinsu haɗe da juna suna musayar numfashi ta ce
"Na gode sossai Na gode kwarai haƙiƙa Allah ya wanke min zuciya ya ba ni mijin marainiya, ya
ba ni kai ba tare da wayo ko dabara ta ba a koyaushe ba ni da abin faɗa a gareshi sai
Alhamdulillah. Ina roƙon Allah akan duk ranar da za ka haɗu da shi, Fuskarka ya zama mai
annuri da sheki fiye da yadda yake a yanzu, ya rabautaka da karɓar kyawawan sakamakonka a
cikin tafin hannunka na dama sannan ya ce
"I am pleased with you" ya haɗa mu gabaɗaya a aljannah madaukakiya ya ba ni dama da ikon
Zama shubagar matayenka a aljannah. Ina ƙaunarka Ya Sameer...Ina ƙaunarka Ya Rayyan ina
matukar sonka Ya Saraki"
Hawayen dake zuba mata yake bi a hankali da harshen shi yana ɗaukewa cikin wani salo
zuciyarshi ƙal yayi fixing gaze ɗin shi cikin idanunta

"I love you. love you more than anything Afeefah, ban taɓa jin son wani abu yadda nake jin naki
ba, I love you more than myself. I will always love you. I will love you till the end of my time. No
words can express how much love i have for you. I will alwavs be here for you no matter what
kin ji? Babu abinda zan miki da zan ji yayi yawa you are my favorite girl nd my only blessing"
Daga nan ta dafa chest dinshi sai ya koma kwance ta dane jikinshi da kanta ta shiga gigitashi
abinda bata taɓa sakewa tayi ba ta yi shi a ranar ta goge mishi hadda sai gashi yau ma yana yi
mata kuka don ta gama da rayuwarshi in dai ta fannin ne.

Washegari sun tashi da mummunan labari don Uncle Usman ya rasu labarin ya kaɗa ta don
faɗuwarta kawai suka ji hankalinsu ba karamin tashi yayi ba barin ma Rayyan a hannunshi ya
ɗauketa suka tafi asibiti don duk abinda za su yi sun yi matsayin shi na likita ya kasa farkar da
ita yana jin panic akan ciwon Mammi amma bai san Meyasa duk abinda ya shafi Afeefah na
fitar da ragwantakanshi a fili ba, tsoro da fargaba ya sa ya manta yadda ma ake aikin likitacin

sai a asibitin ne aka samu ta farfado nan suke samun labarin tana da shigar ciki kuma razanar
da tayi har ya fara barazana ga ɗan cikin nan ya saka aka yi mata allurar bacci don ta huta
sossai.

'Yan uwanshi sun yi rawan gani da su Sulaiman aka sallaci uncle Usman aka kai shi
makwancinshi dogon takarda da ya roki sulaiman rubuta mishi ya ba Rayyan akan idan ta dawo
daidai sai a bata.

Kwanan ta biyu kan ta dawo cikin hayyacinta tayiwa su Suhail kuka ba na wasa ba don maraici
babu daaɗi ta kuma yi alkawarin rike su fiye da ƴaƴan cikinta har illa masha Allah.

A kwana na huɗun suka juya Fombina, anan ne Kawu suka san basu ga komai ba baki sake
suke bin irin girma, tsaruwa da ma kyaun masarautar irin mulkin da ake shimfidawa ko a
mafarki basu taɓa mafarkin halartar irin wannan wuri ba sai gashi wacce suka raina ta zama
sanadiyar da ake zube musu, sun yi kuka kaman me don sashe na musamman aka sauke su
mai martaba da Ammi suka tura ake musu hidima wane wasu masu kuɗi.

Ammi da mai martaba kaman su hadiye Afeefah jin labarin cikinta, soyayyar mijinta kuwa ya
ninku fiye da yadda yake jinta a da su Suhail sun zama 'yan gata don a take aka tsara musu
dakunansu Mai martaba ya sa aka cike musu wardrobes da kaya Ammi ma ba'a barta a baya
ba don abinda za ta yiwa jikokinta shi take musu har ma sun Fara ƙiran Afeefah da Ammah
Ryan kuma Abbu, school na musamman ya saka su masu musu hidima ma daban aka ware
don Afeefah laulayi mai wahalarwa take.

Satin su Kawu uku suka koma bayan Rayyan ya saya mishi babban waya an hada su da goma
sha tara na arziki suka koma, gidan su ya zama daga cikin gidajen da suka fi kowanne kyau a
garin ɗan daidai kuma a kayace sai ya tuna akurkin da suka warewa Afeefah take rayuwa lallai
Allah ya nuna musu ikonshi sun tuba har sun rasa bakin tuba, a kuma satin da suka koma aka
fara gudanar da aikin gidauniyarta.

Sai ga kujerar Umura da Rayyan ya biya musu har da su Mai martaba za su tafi da su Abeeha,
sun yi murna barin Afeefah da bata taɓa zuwa ba za dai tayi kewan yaranta cikinta na wata
huɗu suna gama second semester exams suka chale ƙasa mai tsarki ranar da ta fara ganin
ka'aba tayi kukan da sai da tayi zazzabi bata taɓa ganin abu me kyau da natsuwa ba irin shi
duk rayuwarta, ta zube wurin ta yiwa iyayenta da yan uwanta da ta rasa Adu'a har sai da
miyaun Bakinta ya kafe, sun yi sati uku chan sayayyan baby kuwa kowa yi yake ba Ryan ba ba
Ammi ba ba su jannah ba, daga Saudi sun tsaya kaɗan a Turkey sun yi sayan kayan ɗakin su
Aisha ana dawowa Nigeria Aka fara hidimar bikin su.




🖤Gureenjoh🖤

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*Wannan shafin naki ne Uwar Ɗakin Damisa namu angon Nyla Ƙani ga Didi kuma Uban Didi.
Nana Halima ko na ce Leemar's delicious mai abincin 'yan gayu...Allah ubangiji ya ƙara miki
basira da hazaƙa ina godiya ƙwarai🥰*

*FINAL PAGE*
*60*

Zaune suke a cikin ƙayataccen hall ɗin da ake shan hidimar bikin Autan Mammi da Autar Ammi
waenda duk yanzu suka zama shalelen Ammi kuma angwayen ma duka 'ya'yanta, Ryan na
zaune bisa wani table riƙe da hannun Afeefah sun yi azabbaben kyau cikin outfit ɗinsu na Soire
party wanda english party ne duk mazan shigar suite suka yi matan english dress, Farin suite
ne jikinshi da baƙin shirt daga ciki bakin takalmi da baƙin hankey da ya ɗan leƙa bakinshi daga
aljihun, gashin shi ya sha gyara ainun fuskarshi sheki yake kowa ya ganshi ya ga cikakken
namijin da yake cikin kwanciyar hankali da jin dadi.

Tana sanye da wani doguwar riga na tsadadden sugar lace da ya bayyana cikinta da ya taso
yayi mata kyau ainun, ta saka gyale da ya tafi da kayan tayi wrapping kanta ta sha make up da
ya matuƙar zama mata wanda mijin nata ke ta bacin rai akanshi don kishi ya sa ko motsi tunda
suka zauna basu yi ba su Saleem sun ta kiranshi ya ƙi zuwa sai Sulaiman ne yake representing
ɗin shi, gabansu Suhail da Suhaila ne shigan ryan shine irin na Suhail haka Suhaila ma irin na
Afeefah sai suka ba da wani kyau mai ma'ana.
Zarah ce da yanzu ta sake saboda janta da su Abeeha ke yi a jiki kuma tayi tuban gaskiya ta zo
ta ja su Suhaila don tana kaunarsu su ma kuma sun sonta, Afeefah ta kalli Ryan

"Ya Saraki..!"
A Shagwaɓe tayi maganan ya kalleta
"Matar Masu Sarauta ya aka yi?"
Yayi maganan yana ɗage mata gira tace
"Eyyaa dubi ana yi wa Adda Abeeha barin kudi in je in manna kaɗan mu yi hoto?"
"Wanda kuka yi kan ku zo nan ya isa ba za ki shiga cikin maza ba"

Ta ɗan ɓata rai har ma nadamar Kwalliyar take ji yadda ya kasa ya tsare dama bikin duk ya
hanata wani hidima yadda ta so cin uwar sabada sai dai ta ga su Samha na yi don duk Fombina
suka zo har Sadiqa da ake hidimar aurensu tare sun zabi su zo nan in za'a ɗaura aurenta sai ta
koma tunda sai an ɗaura na Saleem an kai mishi matarshi zai ba da nata.
Har su kawu sun zo bikin da Inna Asabe sun bar inna Larai a gida, kawu ya sauya ƙwarai
natsuwa ta shige shi haka Inna Asabe da inna Larai babu wannan rawan kan da son zuciyar
sam sam sam.

A bikin ne ma take samun labarin Sabrina da iyayenta inda ta kwaso HIV da ya kasa warkewa
ga talauci da yayi musu katutu ita Gaje garin zuwa boka nema mata waraka ta faɗo daga tsauni
sai gawa aka ɗauka Yaya ne ya zo neman tuba wurin mommy kuma ta yafe musu.

"Assalamu Alaikum warahmatullah"
Wata ƙawar Aisha ce ta yi musu sallama, Afeefah ta kalleta da mamaki don ta kula yarinyar na ji
da uban ta wani ne tun fara bikin sai rawar kai take bata zaci Rayyan zai wani kula ta ba sai ta ji
ya amsa, a take wani abu ya taso mata zuwa wuya wato ita ce bata da kishi shi ya hanata tashi
saboda maza ita kuma tana kallonshi yana magana da wata macen.

"Yayanmu barka dai, mun jima muna kallon irin kokarin ka akan rayuwar matasanmu a
koyaushe His Excerllency ba shi da zance sai taka gaskiya samun shugaba irinka abin alfahari
ne in kuwa da irin ku rayuwar matasanmu ba zai taɓarɓare ba"
Ya san mahaifinta Gomna ne mai ci a yanzu don haka yana martaba gidansu sai ya ɗan
murmusa
"Thank you"
"idan ba damuwa ga wannan na jima ina so na baka ban samu ganinka ba Its a small gift don
Allah kar ka ce a'a"
Ta ajiye wani karamin paper bag tayi murmushi ta juya ta wuce.

Kaman an ce ya kalli Afeefah ta haɗa gabas da yamma kudu da arewa, idanunta har shekin
kwalla su ke, hannunshi dake cikin nata ya ɗan murza don ta kalleshi amma ta ɗauke kai sai ma
ta miƙe chadak ta nufi waje, da sauri ya bi bayanta yana dan kiranta amma bata waiga ba dab
wurin mota ya riƙo damtsen hannunta a hankali ya janyota bayanta ya sauƙa kan kirjinshi yana
dan lekan fuskanta yace

"Tsaya mana Boɗɗi fushi kika yi?"
Fuskarta babu walwala ta janye tare da Juyowa ta kalleshi
"No, Meyasa zan yi fushi?"
"Me yasa kika fito to ina ta magana kin ki kulani?"
Ta kalleshi
"Gashi na kula ka, ina jinka"
Numfashi ya sauke
"It seems kin gaji mu tafi gida"

Ta juya ta nufi motarshi bata ce komai ba, numfashi ya sauke yana ɗan shafa gira ya nufi motar
tuni ta buɗe ta zauna ya shiga shima drivern shi ya ja suka nufi ɓangaren su tunda akwai tafiya
sossai, hannunta ya riƙe ta zame tare da juyawa tana kallon Window.

"Akwai abinda ya faru ne? Ko na miki ba daidai bane?"
"Babu, me kuwa zai faru?"
"Ta ya zan sani Afeefah na ga kina fushi"
Ta ɗan bashi side eye tana sake juyawa
"Ni ba fushi nake ba"
Lip dinshi na kasa ya ɗan lasa har ga Allah bai zaci wai kishi take ba a hankali yace
"Ok"
Ya kalleta sai ya ga ta sake haɗa rai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login