Showing 141001 words to 144000 words out of 149666 words
duka gangarshi
"Uncle Usman!!"
Hawaye na zubo mata babu kakkautawa a hankali yace
"Afeefah?? Ke ce??"
Hannayenta ta sa ta toshe Bakinta tana sakin kuka da gaske su ɗin ne cikin wannan hali?
"Uncle me ya faru? Ina Hamdiyya? Me ya samu aikinka baka da lafiya ne?"
Duk ta rasa ma me zata tambaya shima yana kuka yace
"Ki yafe min Afeefah don Allah ki yafe min na cutar da ke, na kasa rike amanar da zainabu ta
tafi ta bar mini ki gafarceni AFEEFAH"
"Baka yi min komai ba uncle wlh baka yi min komai ba hasali ma ka rike ni da amana tsawon
shekara da nayi a gidan nan baka taɓa hantara ta ba, wlh baka min komai ba ni ban ga laifinka
ba ko da ka zarge ni saboda ina da tambarin tun farko manne a goshina"
"Na kasa amincewa da cewa Allah ne me kashewa kuma mai raya wa, hankali na ya tashi ainun
don bayan mun binne zainab kin dawo mun kore ki sai muka muka je asibiti da su Suhail za'a yi
musu riga kafi a kuma ba mu madarar da ya kamata su cigaba da sha anan ne likitan ya ji
maganan da muke yi da Hamdiyya da maiyya ce ta kashe zainabu yayi saurin taka mana birki
ya kuma shiga yi mana bayanin abinda ya faru da zainabu wanda bamu sani ba, ya ce mata
dayawa suna samun wannan matsala na Postpertum ko a samu taɓuwar mu'amala ko irin
ciwon cikin wasu kam ma har a zaci sun haukace ne, ciwon cikin nata bamu farga da wuri ba
sai da ya mata illah kwarai muka koma a sannan babu abinda za su iya ta rasu. Hamdiyya
kuma dama ta jima tana yi mata hassada tana jin haushin yadda ta samu ciki ita tana zaune
hakika ta yi yunkurin illa ta cikin tun kan su zo duniya Allah na kare su har ta haihu tana ganin
kaman za ku haɗu ku kwashe dan abinda na mallaka da ke da zainabu ga yarana da farin cikin
samuwar su bai ɓoya mini kuma dama ta jima tana sanyawa ranta ba sonta nake ba na aureta
ne kawai don in haihuwa a yanzu da bata haihu ba matata ta haihu ta gama amfani kenan zan
iya sakarta kowani lokaci hakan yasa ta ƙarfafa hassadarta a kanku musamman ke tana amfani
da baƙanta miki tana kuntatawa Zainabu.
A ƙarshe tayi sanadin da kika bar gidan nan anan ta fara rainon azaba ga yarana ba tare da na
sani ba, duka zagi tun basu san kansu ba, ta bar su da yunwa ta bar su cikin ruwan wanka duka
don ba ita ta haife su ba Allah ne ke kare su ban sani ba, a ranan da na san duk abinda take
kullawa na shiga masifar tashin hankali marar misaltuwa musamman in na tuna abinda na yi
miki daga nan jinina ya hau na samu matsalar shanyewan jiki, a takaice Hamdiyya ta tattara
komai ta sayar akan ba zata iya zama da ni ba ga jinya, ga rainon ƴaƴan da ba nata ba kuma
bata da damar haihuwa, ko sati ba'a yi ba na samu labarin mota ta kaɗe ta ta rasa kafafunta ta
kuma rasa rabin fuskarta duk kudin yana tafiya a jinyar da har yau bata warke ba. Kuɗin da
Zainabu tayi ta ajiye miki a asusu da su na tsira sai waenda abokan arziki kan kawo da shi nake
aika yaran nan su sayi abinci su ci ko makota su basu, bana iya yi musu komai ko wanka sai dai
su je su watsa"
Sossai Afeefah ke kuka, Allah sarki rayuwa amma Hamdiyya ta cika azzalumar matar uba kuma
ko a yanzu ta ga ishara, Rayyan Aisha ta kira don Afeefah ta kasa daina kuka hankalinta ba
karamin tashi yayi ba shi ya kira aka dauki uncle Usman yace a koma cikin Kaduna dashi a
kaishi asibiti zai kira Sulaiman kan su juyo.
Su Suhail na rungume da Afeefah suka fito zuwa mota yan unguwar na zuwa su gaisheta suna
ta mamaki har wasu na tambayar ko Afeefahn Aunty zee ce ta gyaɗa musu kai, Rayyan ya
zubar da dukiya don duk wanda ya nuna ya gane ta aka gaisa sai ya mishi kyauta daga nan
suka nufi Dutsen-wai.
"Afeefah!"
Ta kalleshi ya riƙe hannunta ya sa hannu yana share mata fuska yace
"kuka sam bai kamace ki ba, ko don zafin da nake ji a nan ya kamata ki sassauta"
Ya ƙarasa yana nuna zuciyarshi. Ta gyaɗa kai ya ce
"Na san burinki shi ne ki yi kuɗi, ba kuma don wani abu ba sai don ki tallafawa al'umma
musamman na ƙauye irin cikin kauyen ku da ake rayuwa kara zube babu neman ilimi, babu
sana'a ana rayuwa irin rayuwar dabobbi ko zamanin da chan baya, ina so in sanar miki cewa na
ba da wannan gudumawa na buɗe miki Center na farko ina fata ya zama farkon buduwar tarin
alkhairanki... Ina adu'a Allah ya sanyawa gidauniyarki daga na farko har na karshe albarka ya
dafa miki ya kuma isar miki da ladan... Akwai Center da aka gama buɗewa a Dutsen-wai da
Sunanki a yau za'a yi taron kaddamarwa a cikin wannan plaza akwai kayan aiki da malamai na
Musamman da zasu ke koyawa mata sana'o'in dogaro da kai kaman su ɗinki da sauransu
akwai kuma makaranta islamiyya da malaman da muka yi hiring na musulunci da za su tsaya
tsayin daka wurin ganin sun koyawa matan wannan kauye da ma mazan addini akwai kuma
babban masallacin juma'a a kusa da wannan plaza shi kam na Mammi ne ina Fatan duk Sallar
da za'a yi ciki ladar ya isa gareta. Ba ni da alaka da kula da wurin daga yau duk naki ne ga
takardun da ma komai da komai na plaza ɗin kyauta ne na musamman zuwa gareki"
Jikinshi kawai ta faɗa don ta gigice ta rasa ma wani irin abu zata yi, kuka kawai ta saka mishi
yana ta aikin rarrashi za tayi godiya ya manne Bakinta da nashi yana kissing passionatly sai da
ya tabbatar ta daina hawayen kan ya saki yayi pecking goshinta
"Anything for you my baby girl ki sani wannan ɗin mafarin nasararki kenan a rayuwa, duk wanda
ya baƙanta miki a da a yanzu yana a karkashin kafafunki, na ji daaɗi da kika nufi saka musu da
alkhairi bayan sun bi ki da sharri amma ki sani wannan yunkuri naki na basu ilimi makami ne
mai girman gaske a duniyarsu ladar ki sai a wurin ubangiji"
Daidai nan suka isa cikin Dutsen-wai ita ke kwatanta musu har kofan Gidan Kawu Labaran.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
"Last Page na zuwa anjima in shaa Allah. Wlh jiya na yi gajiyar da ban san adadi ba ina buɗe
ido da niyyar typing idon na rufuwa ganin ba zan iya ba yasa nayi bacci and yau ma same thing
zan lallaɓa in ba ku shafin karshe in shaa Allah. Na gode da haƙuri da ni*
*59*
A gaban gidan ta tsaya ta ƙura mishi idanu kaman yanzu ne komai ke faruwa da ita, tana tuna
baƙar wuyar da ta ci daki-daki cikin wannan gida, hawaye ne suka cika mata idanu shaidan na
raya mata ta juya ta koma kawai don basu chanchacanci duk wata alfarma daga gareta ba, da
kyar ta hadiye wani abu da ya tsaya mata a wuya tana tuna ni'imomin Allah a gareta sai ta furta
Alhamdulillah don ko daga fasalin gidan zaka san cewa rayuwa ya ƙara taɓarɓare musu wane
wane don daga inda take tana kallon har kofofin dakunan gidan saboda rushewar ginin ƙasan
dake zagaye da gidan, yunkura wa tayi zata shiga sai ta ga Fitowar wani dattijo a yanayin shiga
da fuskarshi ya nuna kamilalle ne wanda kai tsaye bata kawo ko kusa Kawu Labaran bane sai
da suka haɗa idanu, Chakk ya tsaya yana ƙare mata kallo kaman yadda ita ma take ƙare mishi
kallo.
Sanye yake da jallabiya baƙa har da hula taɓani ka ji hadisi da chasbi riƙe a hannunshi sai wani
littafi da ya nuna mata na addini ne, ya rame kam gabaɗaya ya lalace, shi karan kanshi bai
gane ta ba sai da yaga kallon da take mishi da hawayen dake zuba mata don kaman an yi mata
wankin inji ne, kaman bata taɓa sanin menene wahala ba a rayuwarta, muryarta na rawa tace
"Ka..kawu"
Tana tuna ranar da ta zo da Saleem yayi mata kora irin ta miyagun aljannu da kayan tsubbu da
komai.
"Af...Afee..fah??? Ke ce Afeefah? Da gaske ke c..e?"
Cikin wani irin karyayyen murya yake maganan, ta ɗaga kai sai gani tayi ya iso gabanta ya zube
gwiwowinshi ƙasa da sauri itama ta durkusa yadda yayi suka saki kuka a tare, nata dai bata san
me take ji ba don abubuwa ne suka haɗe mata shaidan na tuno mata duk wani minti da tayi a
gidan cikin azabtarwa yana tuna mata irin muggan kalaman kawu a kanta da rayuwarta yana
nuna mata basu chanchanci komai na alkhairi daga gareta ba ta wani ɓangaren tana jin babu
daaɗin yadda ta zo ta ga inda suke rayuwa da kuma lalacewar da kawun yayi kaman kuɗin
guzuri.
Shi kuwa nadama ce, nadama da kunyar kasa riƙe amana da zumuncin ɗan uwanshi yake yi wa
kuka, kunya mai tsanani da ba zai iya cewa ya taɓa jin irin shi ba yake ji na ɗiyar cikinshi.
"Afeefah idan na ce ki yafe min na so kaina dayawa, na san na yi miki abubuwa masu yawa na
zalunce ki, na ci amanar zumunci, na cutar da rayuwarki fiye da ƙima, na wargaza natsuwarki
har ya kai na kore ki da kaina daga kusa na bisa tarin jahilci da baƙar zuciyata... Ina kallo
matana kowacce take abinda ta so da rayuwarki ana gara ki kaman kwallo, na dauke ki da
kaina na jefawa hukuma ke don kawai ina ganin kin zame min Ƙashin kifi, an zo neman aurenki
har nan na lalata komai saboda kawai wani zargi wanda babu wanda ya tabbatar, saboda son
zuciya irin tamu... A ƙarshe na aurar dake ba tare da na ko yi binciken wanene za ki aura ba,
mecece sana'ar shi, su waye danginshi don kawai sun cika ni da kuɗi sun kuma nemi auren
kawai suke so, tun bayan aurenki da kaddara ta faɗa min bisa neman zuwa wurin ki da nayi na
ci arziki na faɗa hannun 'yan shan jini a ranar na san cewa ke ba Mayya ba ce yadda muke
faɗa, a ranar na tabbatar harkar shan jini da maita ya fi karfin kwakwalwarki nadama mai yawa
ya rufe ni a kullum Adu'a ta shi ne yadda zan ganki kafin ƙasa ya rufe min idanu Afeefah...."
Sossai yake kuka ta mayar da kanta ƙasa tana cigaba da hawaye, hatta Aisha da Abeeha
hawaye suke shi kuwa Rayyan kanshi ya kawar yana jin zuciyarshi na jagulewa.
"Ashe za ki zo inda muke Afeefah? Ashe za ki neme mu?"
Zuwa lokacin makota duk ana maƙale ana kallon me ke wakana Larai da Asabe da ma wasu
yaransu dake gida duk sun fito sai dai ita bata kai hankalinta kansu ba yayinda duk suke kuka.
Hannun kawu ta riƙe tana jin yadda zuciyarta ke kakkaryewa tace
"Dole na nemeku kawu dole duk inda zan shiga ku ne nawa, ko me za ku yi min ku ne dole na
duk duniya ba ni da waenda suka fi ku. Tsoro nake ji... Tsoro nake ji kar ku ƙi karɓa ta.."
"Ko a ya kika zo Afeefah wallahi ba zan ki karbarki ba a yanzu, na tuba na yi nadama mai tarin
yawa, na roki Allah a salloli dayawa akan ya waiwayo mana dake ya sa ki tuna da mu. Don
Allah, Don darajar Allah ki dubi girman shi ki yafe min Afeefah ki yafe min don Allah"
Kai take gyaɗa wa ta kai hannu ta share mishi fuska
"Na yafe maka kawu wlh duk na yafe muku Allah ya yafe mana gabaɗaya"
Inna Asabe ta rarrafo
"Afeefah don Allah ki yafe mana don Allah"
Ta kallesu sai ta ga inna Larai na ja da duwawu kafa ɗaya kam babu gabaɗaya kuma ba sanda
bare wheelchair zubewa tayi tana neman yafiyarta duk ta yafe musu, Rayyan da ya gaji da
kukan ya taho ya ɗaga ta tsaye yana kallon cikin idanunta ya fidda hanky fari tas mai cike da
kamshi ya fara ɗauke mata hawayen fuskarshi babu ɗigon walwala.
"Am sorry"
Ta faɗa a hankali.
Iso aka yi musu sai dai duk gidan an rasa ma taburma mai haske da za'a iya shimfida musu su
zauna, Rayyan take kallo ta juya ta kalli kawu ta sake kallon Rayyan.
"Ko za ka tafi mota ka zauna Ya Saraki?"
Ya harareta ya samu wani dutse ya zauna a kai ta mayar da kanta ƙasa ko wannan kaɗai ya isa
ta yafe musu, wa zai ce Rayyan zai iya zama a irin wurin nan saboda ita? Saboda kawai tana
wurin idan ba don haka ba me haɗin kifi da kaska?
Rayuwar mutanen gidan sossai ya chanza mata ko da ta ji irin neman ilimin da kawu ke yi tun
daga sanadiyar yan shan jini da suka kama shi Allah ya nufe shi da shiriya ta tabbatar da gidan
sun rabauta don ilimi shi ne ginshikin rayuwa, yaranshi duk sun dawo kan hanya sai talauci da
yayi musu matuƙar yawa don Allah ya jarabcesu da babu tun bayan tuban shi abinda za'a ci ma
wahala yake sai dai basu daina neman ilimi ba kuma dayake tuban gaskiya suka yi yana iya
yinshi ya ga an ci wani abu ko da sau ɗaya ne a yini, tayi kuka har sai da Rayyan ya fara yi
mata faɗa ganin da gaske ranshi ya ɓaci ya sa ta daina, ta basu labarin duk abinda ya faru da
ita har kawo yau
"Allahu Akbar... Allahu Akbar kabiran lallai shi mahakurci mawadaci ne kuma mai haƙuri shi
yake dafa dutse... Yanzu Afeefah har 'ya'yan sarki mai tarin daraja biyu ne a gidana ta
sanadiyar ki? Ashe ke ce kike gina wannan tamfatsatsen gini da masallacin juma'ar da babu
irinshi a wannan gari? Allah mai girma Allah mai yadda ya so"
Kawu ke magana cikin hawaye da tabbatar da girman zatin ubangiji.
Kallon Inna Larai tayi tace
"Kawu me ya sameta?"
"Maciji ne ya sare ta mun yi gargajiya har mun gaji kafan ya rube dole muka nemi taimako dai
da kyar muka hada kudi aka yanke kafar sai dai babu kudin ko sanda ne bare kujeran guragu a
dole take yawo a haka da ja da duwawu"
Lokaci Ryan ya kalla ya mata umurnin su tafi ana jiran su wurin taron da suka gayyata, kawu da
iyalan shi duk suka tafi dasu wurin taron kusan duka jama'ar garin suna ɗakin taron barin ma
fankoki dake kaɗa su ya sa sai nishadi suke.
Mai gari ne ya fara yin bayani da kuma godiya ga wacce ta dubi garin ta zaɓi inganta rayuwarsu
ta hanyar ba su ilimi wanda ta wannan hanyar ta riga ta gama musu komai, da ya zo wurin kiran
suna sai ya ce
"Wannan ɗin ba kowa ba ce illa mata ga Ciroma Sameer, Ciroma mai jiran gado kuma Yariman
Matasa na ƙasar Fombina Afeefa..h Afeefah kamal??"
Sai yayi saurin kallon matar da ake cewa ita ce Afeefahn, duk yan garin ido suka zuba mata
suna mamaki da ikon Allah, wasu kunya na rufe su a yayinda tayi murmushi ta miƙe ta haura
podium ɗin ta karɓi mic
"Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata
ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga
sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar babu mai ɓatar da
shi, wanda kuma ya ɓatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta
da gaskiya sai Allah, shi kaɗai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi
Muhammad bawansa ne manzonsa
ne. Bayan nan ina yi mana Sallama irin ta addinin musulunci shi ne Assalamu Alaikum
warahmatullah"
Duk suka amsa, ta ɗan sauke numfashi
"Ba gixo ba kuma ba mafarki ba haƙiƙa ni din ce Afeefah kamal wacce kuka fi sani da Annoba
ko kuma Mayya a wannan gari, haƙiƙa na jure abubuwa dayawa daga gare ku 'yan uwana,
yayyena, Ƙannene na da kuma iyayena. A baya na zama mujiya cikin tsuntsaye Abar kyamata
da gudu. Abar tozarta wa da wulaƙanta wa, Abar muzantawa a cikin al'umma saɓanin a yanzu
da nake da miji nagartacce nake kuma da surakan girma waenda suka taka rawar gani bisa
inganta rayuwata daga Wacce ta sallamar da farin ciki ta sallamar da jin daaɗi zuwa wacce ta
zama mai cike da buri da alfahari. Da na zauna nayi nazari da tunanin Meyasa nawa iyalan
kuma dangina suka yi min abinda suka yi a baya sai na fahimci babu wani abunda ke damun
ahalin wannan gari na mu sai rashin ilimi da sanin daidai. Na fahimci mun samu tawaya da
koma baya a wannan ɓangaren iyayen babu bare su tarbiyatar da yara akan daidai, a sadda na
sake zurfafa tunanin me zan yi na taimaki al'ummata sai na ga babu abinda ya fi dacewa irin in
wayar mana da kai in taka rawa wurin ganin mun samu ilimi har ma muna aiki dashi, in ga cewa
wata mace ko wani yaro bai ɗanɗani irin ɗacin da na ɗanɗana ba, in ga cewa yadda rayuwata
ta inganta kowa ma a yankina rayuwarshi ta inganta gobenmu mu samu tsatson da za mu yi
alfahari da su daga wannan gari namu.
Ya ku 'yan uwana musulmai ku sani cewa
addinin musulunci addini ne na ilimi. Umarni
da neman ilimi shi ne farkon abin da Allah
Maɗaukakin Sarki ya umarci Annabinsa
(S.A.W) da shi, yayin da ya saukar masa da
faɗinsa :
)اْقَر ْا ِباْس ٍم َر ِّبَك اَّلِذي َخ َلَق! َخ َلَق اِإْلْنَس اَن ِمْن
َأْل
َعَلَم4 اَّلِذي َعَّلَم ِباْلَقَلِم3 اْقَر ْا َوَر ُّبَك ا ْكَر ُم2 َعَلٍق
.[١ - ٥ :( ]العلق5 اِإْلْنَس اَن َما َلْم َيْعَلْم
Ma'ana : (Ka yi karatu da sunan Ubangijinka
da ya yi halitta. Wanda ya halicci mutum daga gudan jini. Ka yi karatu kuma Ubangijinka shi ne
mafi karamci. Wanda ya sanar da alqalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba). (Alaq : 1 -
5)
Addinin musulunci ya kwaɗaitar da mabiyansa akan neman ilimi, domin ba zai yiwu mutum ya
bauta wa Allah ba sai da ilimi. Allah madaukakin Sarki yana cewa :
)28] (ِإَّنَما َيْخ َش ى الَّل ِمْن ِع َباِدِه اْلُعَلَماُء:فاطر
TA].
Ma'ana : (Kaɗai waɗanda suke jin tsoron Allah daga cikin bayinsa su ne masu ilimi)
Idan na ce zan kawo muku faɗar Allah da kuma hadisan da suka yi magana akan ilimi da
amfaninsa gare mu za mu kwana bamu ƙare ba amma tabbas da akwai ilimi da duk ban
fuskanci abinda ya faru da ni a wannan kauyen namu ba, Ajalin