Showing 138001 words to 141000 words out of 149666 words
bayyanuwar shi ba tunda an tabbatar wa
Makama cewa asirin ba mai karyewa bane don kogi aka jefa aka ba wa tsuntsu wani ya fire sai
gashi ya dawo kuma da wata mace.
Anan suka yanke hukuncin aura mishi zarah da haɗin Bakinta na daga ta aure shi sarki yayi
murabus za su kashe shi su kashe sarkin sai su karbi sarautar har dan Zarah ya girma,
kwatsam ta fahimci Fulani Afeefah na da juna biyu, hankalinta ya tashi ta aikeni wurin mai
maganinsu inda ya bani magani na kawo sai dai duk abinda aka bata bata ci har sai da Fulani
ta yi mata wasu maganganu da suka raunata zuciyarta ta sha fura, a cewar mai maganin sai
bayan sati ma zata yi ɓari kar ma a zarge ta tunda da wayon ta ba zata bari a lokaci ɗaya ta
zubar da cikin ba dayake Allah ba azzalumin bawan shi ba akwai rabon kamatan dumu dumu
bisa laifukanta sai cikin ya ɓare a ranar dole aka san me ta ci kuma a ina ta ci inda daga ranar
Ciroma Sameer bai bar su sun shaki iska ba.
Ya kama ni aka dinga min horo iri iri bai bar ni ba sai da na faɗi komai na kuma kaishi wurin mai
maganin aka kama shi... Ku yafemin don Allah ku yafe min na tuba wallahi umarni kawai nake
bi don tsira da rayuwata"
Cikin kuka mai tsuma zuciya ta ƙarasa.
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..! Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Abinda ke tashi kenan a fadar duka matan sarki kuka suke yi mai tada hankali yayinda mai
martaba ya runtse ido yana jin hawaye na sulmiyo mishi, ashe kashe mishi yaro suke niyyar yi
shiyasa take kanainaye shi da kissa da komai take cusa mishi son auren Zarah da Sameer? Ya
gode Allah da ba'a yi auren ba da ba zai yafe wa kanshi ba.
"Wallahi na yi nadama tun ba yanzu ba amma tsoron hukuncin Fulani Adama ya sa na kasa
daina basu magani, yarana sun mutu duk a gobara na auri mata sama da biyar duk suna gudu
su bar ni don na kasa basu haihuwa, tun mutuwar yarana na yi nadama amma ban san yadda
zan yi ba a gafarceni"
Tsohon ke fada. Fulani Aminatou tace
"Allah ya isa! Allah ya isa tsanina da ku duka wallahi Allah ko da ni kaɗai ce zan yafe muku ku
shiga aljannah ba zan taɓa yafe wa ba"
Fulani Salima ma Allah ya isa take jerawa cikin kuka mai ciwo, mai martaba hawaye kawai yake
yi haka Ammi dake jin mutuwar yaronta ya dawo mata sabo.
"Babu aure tsakaninka da Zarah har Abada Ciroma, ku kuma wannan kaɗai ya ishe ku tsoron
Allah, wannan kaɗai ya kamata ya ishe ku ishara.... A tube musu duk wani rawanin zuri'arsu ku
kuma shaida na yanke igiyar aurena da Adama a dibe su a kaisu kurkuru mafi azabtarwa na
wannan masarauta kan a yanke musu hukuncinsu.... A tabbatar basu samu natsuwa ko
kwanciyar hankali ba"
"An gama ranka ya dade"
Sarkin dogarai ya zube ya amsa kan wasu majiya karfin suka shigo suka saɓesu ko damar
magana ba'a basu ba, kunya da dana sani marar amfani na rufe Adama komai ya kare mata a
lokacin da bata yi tsammani ba.
Rayyan ya dubi Afeefah dake kuka ya girgiza mata kai a hankali yace
"Na gode Afeefah. Na gode kwarai ta sanadiyarki asirinsu ya karye idan baki manta ba duk
ayoyin da kike yi wa Saleem a tare muke sha Dukda ban san da zaman wani asiri a jikina ba,
Kin ba ni babban dama ta sanadiyarki na samu faɗa wa Mammi abinda ta jima tana son ji na
wanene ni kafin mutuwarta. Ba zan taɓa manta wannan taimako naki ba na gode"
Ammi ta rungumeta tana kuka. A haka aka watse zaman fadan mai martaba sai riƙe shi aka yi
zuwa sashenshi tuni Rayyan ya maƙala mishi ruwa don ba karamin hawa jinin shi yayi ba.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*58*
Alhamdulillah komai ya cigaba da tafiya normal bayan nan, ta cigaba da lectures ɗinta cikin
kwanciyar hankali kuma tana samun duk wani kyautatawa daga zuri'ar na mijin nata kaman
yadda shima yake kara samun kusanci da iyayenshi, Mai martaba ya sha jinya kan ya warke ya
tara matan yayi ta basu haƙuri a ganinshi komai ya faru ne sanadin aurenshi da suka yi, sun
nuna haka ƙaddarar su take sai dai Fatan Allah yayi musu sakayya akan Adama, Zarah da bata
san komai ba sai da aka warware daga farko ji tayi duniyar yayi mata zafi damuwa yayi mata
yawa ta tattara ta koma wurin mahaifiyarta da dukkansu har yan uwanta kunyar abinda
mahaifinsu ya aikata ya sa ba sa iya ko fitowa, Ammi bata neme ta ba haka Aisha don tunda
har ta yi niyyar auren Rayyan ne don ta cutar dashi su ma suka ji ba za su iya cigaba da hulda
da ita ba amma Aisha tayi kuka kaman ta mutu, ta ɗauki zarah kaman 'yan biyunta ne bata zaci
hakan daga gareta ba.
Maganan yanke hukunci sai da suka yi wata biyu suna cikin na uku garƙame cikin azabtarwa
kan aka yankewa Fulani Adama hukuncin kisa ta hanyar rataya, Makama da asirinshi ya dawo
mishi ya haukace damuwarshi kawai a barshi yayi ta tafiya ji yake kaman kwakwalwarshi zai
fashe idan bai shiga duniya ba dukan da yake yiwa Madaki yasa aka raba musu ɗaki, shi
Madaki da sauran hadiman an yanke musu life imprisoment iyalan su sun yi kuka kaman ba
gobe amma bahaushe ya ce tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan yi wa dukan tsiya.
Soyayya tsakanin Saleem da Aisha yayi nisa don har ya turo mai martaba yace za su yi fixing
rana sai a haɗa da na Ameer da ya kasa komawa da Abeeha dake shirin gama makaranta,
Jiddah dai da tayi mugun kewan su sai dai a haɗu a yi ta waya. Yau ya kama ana ya gobe
Afeefah za ta gama First semester examination ɗinta kuma Rayyan ya tabbatar mata a satin za
su fara shirin tafiya Kaduna don ta matsa mishi sossai akan komawa ga su Suhail da kuma su
kawu Dukda shi baƙin cikin kawun bai taɓa wankuwa mishi a rai ba sai dai bai hanata ba don
haka mai lalle ta nema Ammie ta turo mata har sashenta.
Tana zaune da dogon wando da wani shirt Black na ma Rayyan ɗin ne daga ganin girman da
yayi mata amma ta fi jinta comfortable ciki, ta ɗaura Black dan kwali a kanta an gama lallen kafa
da hannun duk an saka leda su Aisha na gefe suna ta hirar su da ta shafi rayuwa har jan ya
kama aka cire mata sai aka zana mata baƙi a bayan hannun don ta ce jan kawai ya isa a
kafafun yarinyar kwararriya ce kuma lallen ya mugun kamawa yayi maroon sharrr kaman ka
sace kafafun in ka gani, Rayyan ne yayi sallama ya shigo duk suka mishi sannu da dawowa
daidai an gama baƙin kenan ya tsaya yana kallon hannun kan ya ce
"Wai tunda na bar ku kina nan wurin zaune?"
Ta karkata kai fuska a ɗan Shagwaɓe tace
"Kwalliyar kenan sai wahala duk yunwa ma nake ji babu hannun cin"
Ya kalli hannun nata sai ya nufi kitchen, Aisha da Abeeha suka kwashe da dariya suna tafawa
"Sai da ke Matar mijinta"
Aisha ta faɗa tana dariya.
Abeeha tace
"Ku tashi mu tafi yanzu bai wuci abinda zata ci ya je nema mata ba kan ya dawo ya kora mu ko
su makanta mu gwara mun yi ta kanmu salin alin"
Afeefah na ce musu su tsaya ko ta kanta basu bi ba suka tarkata suka tafi sai gashi ya dawo
hannunshi rike da wani plate.
"Duk ka kora min 'yan hirar Ya Saraki..."
"Dama wani amfani suke dashi a gareki idan ina nan? Babu so Haaa ki ci abinci"
Murmushi ta saki tana bude baki ya saka mata Nan-bread guda biyu da ya sanyo a plate ɗin da
curry chicken da ya zuba a gefe, da hannunshi yake bata yana tabbatar da bai ɓata mata jiki ba
har ta ƙoshi ya bata ruwa ta sha kan ya shiga duba lallen.
"Kin yi wa lallen nan kyau ainun Boɗɗi na"
Tayi murmushi tana sake kallon lallen
"Ko kuma shi ya min kyau dai ko Ya Saraki?".
"Wai dama baki sani ba?"
"Mene?"
"Ado biyayya yake miki, Kwalliyar da kanshi ke kike mishi kyau ba shi yake miki kyau ba.."
She's just blushing don bata gajiya da sauraron dadadan kalamanshi yana ɗan wuya ya sake
bakin don haka idan ya sake yana zubowar tana amfani da damar ta adana a cikin zuciyarta ta
yadda ko baya nan in ta tuna fuskarta kan zama ya cika da tarin murmushi.
Washegari kuwa aka kai ta paper yadda aka saba motoci biyu har gaban exams hall su jira ta
gama a dawo da ita gida, yau ko da ta fito bata gansu ba, daga jikin hall ɗin ta tsaya sai ta ga
call nashi tayi picking ya ce mata ta taho yana kallonta fuskarta cike da fara'a ta nufi motar
nashi don a yau da kanshi ya zo ɗaukar ta.
Idanunshi da ya zura mata tun tahowarta ya lumshe a sadda ta yi masauki gaban motar
kamshinta mai sanyi da natsuwa na ratsa shi
"Hey Assalamu Alaikum"
Ta furta a hankali tare da miƙa mishi hannunta ya ɗan murmusa kan ya miƙa nashi ya shigar
cikin nata yana kallon tsakiyar idanunta ya furta
"Wa'alaikissalam warahmatullah"
Cire hannunta ta so yi sai ya gimtse yana mata kallon baki isa ba kuma ai dariya ta ɗan yi, ya
miƙa hannu gefenshi ya zaro wani rose Red nd green dake fidda sassanyar kamshi ya miƙa
mata.
Da hannu ɗaya ta karɓa ta kai hancinta tana lumshe ido fuskanta ɗauke da murmushi tace
"and this?"
"I am bribing you a ban dama in fitar dake outing”
Dariya ne ya ɗan kufce mata
"seriously? Ai na zaci saurayi da buduruwa ne ke fita date ba mata da miji ba"
Tayi tambayar tana wara fararen idanunta a kanshi ya kai hannunshi ɗaya kan kumatunta ya
shafa
"Babu laifi a hakan.... Afeefah ki na da kyau fiye da duk wani abu mai kyau, kina da daraja fiye
da duk wani abu mai daraja a kullum soyayyarki ƙara yawa take a zuciyar Ryan, I will always
love you again and again...kullum sabunta kanshi soyayyar ki ke yi so i have to be very caution"
Tayi murmushi mai cike da tarin alfahari tana sake shinshuna kyawawar furen dake hannunta.
Motar ya ja suka fice daga makarantar.
"Kin ce za ki yi sayayyar su Suhail should we start with the shopping ko mu je ki sha ice
cream?"
Tayi murmushi tana sake jin alfahari zuciyarta fal godiyar Allah tace
"Lets start with the shopping"
Kai tsaye shopping din ya kaita a tare suke tafiya hannunshi rike da nata ɗayan yana tura chart
na shopping din ita kuma tana duba abinda zata ɗauka.
Tsaye yake sai dai bayanshi a jingine da stall ɗin kayayyaki inda suke babu wasu yawaitar
mutane, ita ke sayayya shi ya zuba mata idanu yana aikin kallo, sanye yake da full Black Jean
nd top ya saka facing cap da ya zauna mishi sossai saboda mutane kar su gane shi, takalman
kafafunshi ma bakake ne, hannayenshi duka a zube a aljihu... Don tun dazu suke tsaye wurin
choculates ɗin tana ta rawan ido.
Ta ɗauko wani choculates tana dubawa sai kuma ta ɗan ɗago karab suka haɗa idanu kusan
karo na biyar kenan a take ta Shagwaɓe fuska tana kallonshi ya ɗan saki smile yana ɗage mata
gira guda
"ya dai? Na miki ne?"
Ya ƙarshe da wani kayataccen murmushi...
"Ni ya kamata in ce haka ai tun da ni ake ƙarewa kallo.. Ni Allah watarana har muni na sai ka
binciko"
Ta faɗa cikin yanayin da ya saka shi faɗaɗa murmushin shi, choculates na hannunta ta ɗaga
sama
"Ina son picking wa su suhail wannan yayi ko? Ko me kake tunani?"
Very naughty yana ɗan lashe lip ɗin shi na ƙasa ya furta
"I am thinking of kissing you..."
Hannu ta saka ta rufe baki tana zazzaro ido ya saki dariya mai sauti kan ya yunkura ya nufe ta,
kalle kalle ta fara kan ta yunkura kuwa da gaske yayi pecking lips ɗin nata hannunshi na ɗan
manna ta da jikinshi.
"Ya Saraki waje fa muke"
"Ina ruwana"
Ganin yana ta kallon fuskarta ta san zai iya aikata abinda ma ya fi haka don haka ta janye ta
saka choculates ɗin tace su tafi ita kam ta gama, sai murmushi yake mata don ta bashi dariya
yadda take zare ido kaman yayi komai ne gaban mutanen, shi ya biya kuɗin suka fice.
Sossai suka zazzaga ya kashe ta da tarin soyayya wai murnar kamallah exams sai dare suka
koma masarautan, a sayayyanta har su Ammie ta yiwa don haka tana idar da isha ta fito
hadimarta tayi saurin karbar manyan ledojin hannunta suka nufi sashen Ammin don shi bai
shigo ba tukuna, ta shiga sashen Ammin da sallama sai idanunta suka sauƙa kan zarah dake
tsugune ƙasa sanye da hijabi tana kuka sossai.
Gefe ta samu ta zauna bata ce komai ba har zarahn ta gaji da kukan ta fara roƙon su yafiya duk
ta rame tayi duhu. Ammi ta sauke numfashi tace
"Zarah ki daina kukan nan haka ni kam na yafe miki, wlh ban taɓa bambanta ki da Aisha ba
Dukda na ji mamakin ƙudirinki a kaina amma tunda kin gane kuskuren ki Allah ubangiji ya yafe
mana gabaɗaya"
Aisha ma tace ai ya wuce. Ta kalli Afeefah zata yi magana Afeefah tace
"Ni dai baki min komai ba wlh zarah. Allah ubangiji ya cigaba da ɗora mu duka bisa turban
gaskiya"
Suka amsa da Ameen kan ta miƙe ta fice suka bi ta da kallo.
Afeefah ta gaishe da Ammie ta amsa cike da kulawa tana tambayarta exams
"Alhamdulillah Ammie mun gama lafiya"
"Allah ya ba da sakamako na alkhairi, yanzu sai shirye shiryen tafiya Kaduna ko?"
Kai ta gyaɗa Ammie tace
"Masha Allah, Allah ya nuna mana. Akwai saƙo zuwa da safe za'a kawo miki sai ki duba ki ga
idan akwai abinda kike son ƙari ko chanji duk sai a yi"
Godiya tayi sossai kan ta miƙawa Ammie ledar hannunta daidai Rayyan ya shigo kenan tana
cewa
"Ammi mun je shopping ne sai na ɗauka muku da Abeey"
Ta miƙawa Aisha nasu.
Ammie ta buɗe ledar Dukda duk wani kyauta da za'a yi mata tana da halin yin fiye dashi amma
kyautatawa abu ne mai daaɗi kwarai kuma ta ji daaɗi har ƙasan ranta Leshi ne mai tsadar
gaske sai turare shima designer na Abeey, Abeeha da Zarah dogayen riguna ne egypt Abaya
sai yan abun ciye ciye tarin choculates. Shi karan kanshi Rayyan fuskanshi ya nuna jin daaɗi
ainun Dukda tare suka Saya amma ko kusa bai san har da su Ammie ta yi wa sayayyar ba sai
darajar ta ya ƙaru a idanunshi barin ma da ya ji adu'o'in da Ammie ke yi mata anan ya fahimci
duk kudin iyaye kyautata musu na saka su farin ciki kuma hakan Allah ne kadai ya san irin ladar
da zai baka bisa wannan murmushi da ka sanya su aiko ya ƙudiri aniyar cigaba da ganin
wannan murmushi na Ammie, Sai kusan goma suka bar sashen.
Bayan kwana biyu da gama exams ɗinta suka fito a shirye tsaff cikin shiga na alfarma, tafiyar
har da Abeeha da Aisha don duk sun gama exams motoci shida ne ya kaisu Airport yana riƙe
da hannunta cike da kulawa da so da kauna har suka sauƙa a filin tashi da saukar jirgi na
Abuja, anan ma motocin alfarma bakaken prado sai sheki suke da securities ne suka zo ɗaukar
su ya san aikin mai martaba ne don haka babu wani dogon nazari suka shiga zuwa gida, sun
samu gidan a cike su Saleem da sisters ɗin shi ga Sulaiman da matarshi da Twins su fauza ga
jidda an shirya musu abinciccika iri daban daban kasancewar tafiyar mintuna 40 ne ba wani
gajiya suka yi ba nan Sulaiman da Saleem da kuma Rayyan suka zauna sitting room yayinda
'yan matan suke ta hira a parlor babu wani nuna bakunta ko rashin sanayya kaman 'yan uwa.
Sai wuraren isha duk bakin suka tafi Aisha ta sauƙa ɗakin Afeefah na ɓangaren Mammi yayinda
su Afeefah suka sauƙa sashensu.
Washegari da safe suka fito a shirye tsaff suka shiga wannan motocin nan a jere suka Lula sai
Anchau Shigowar su Layin su Aunty zee suka jera gabaɗaya securities ɗin suka fiffito aka buɗe
musu kofa za ta sauƙa ya riƙe hannunta yana kallon gidan da ya fara ganinta ciki a sadda ta
sallamar da Rayuwa, ita kanta tana tuna ranar da aka yi yunkurin kashe ta a wannan gida, tana
tuna rayuwarsu da Aunty zee tana iya tuna ranar da ya fara tare ta a cikin jikinshi lokacin da ta
yanke yin mai Dungurun gum da rayuwarta Wai HAIHUWA DA HANJI a sadda ta sallamar cewa
barin ta duniyar shine maslaharta idan har ta tafi ai shikenan babu mai kallonta bare yayi mata
sharrin maita ko zama annoba.
Idanunta cike da hawaye ta kalleshi ya lumshe nashi cikin su fuskarshi babu walwala yace
"Kin ga dalilin da ya sa bana so ki zo ko?"
Ta mayar da kanta ƙasa ta san kuka kam sai ta yi shi kuma abinda baya so kenan sam.
"Ki min alkawari ba za ki yi kuka ba"
Tayi shiru bata ce komai ba, ya zame hannunshi yana sauke numfashi sai ta juya ta sauƙa ta
nufi kofar kyauren gidan da ya tsufa mata ainun kaman ba gidan Aunty zee ba da yake fes fes,
jama'ar unguwa dayawa sun fita suna kallon wanda ya zo don jiniyar masu take musu baya ya
ja hankalinsu sossai.
Sanye take da wani dakakken purple lace mai shegen tsada an yi mata dinkin Borno style
straight skirt da bubu da yayi mugun kyau ta zuba accesories gold ne daga wuyanta zuwa
hannunta mayafinta ya zauna mata sossai hannunta rike da wani sabon designer bag da ta
dauka cikin kayan aurenta da har lokacin suke gidansu na Kaduna don bata tattare ba, sai
takalmin ta mai ɗan tudu wannan vibe ɗin na manyan mata kuma hajiyoyi yan gatan mazajensu
shi take bayarwa har ta tura kofan gidan ta sanya kai da sallama.
Wasu yara biyu ta gani suna wasa sanye da wasu kaya da suka fi yanayi da tsumma sun yi
dukun dukun macen gashinta kaman wanda yayi shekara bai ga ruwa ba, kafafunsu babu
takalmi, ganin ta yasa suka tsaya suna kallonta kamannin fuskokin su yasa taji tayi bursting to
tears, gabanta na tsananin faɗuwa ta ce
"Suhail...! Suhailaah???".
Abeeha ce ta dafa ta ganin tana ƙoƙarin faɗuwa saboda jirin da ta ji ya ɗauketa a lokacin da
suka amsa, waennan su ne yaran Aunty zee? Su Suhail ne haka? Innalillahi wainna ilaihi rajiun
"Ina Babanku?"
Cikin maganansu suka ce
"Yana ɗaki kwance ba shi da lafiya"
Da sauri ta nufi ɗakin da yake kwancen babu komai cikin ɗakin sai tantagaryan siminti, me ya
faru? Ta fara tambayar kanta kan ta isa inda yake kwance kan taburma idanunshi a buɗe yana
kallonta ta