Showing 6001 words to 9000 words out of 149666 words
saman dami,
idan ka ga na mutu lokacina ne ya yi. Ke tashi mu tafi."
Ta watso ma Afeefahn sauran kalaman nata tana kallonta, tun farkon rasuwar mahaifiyarta
Aunty zainabu da ita kaɗai ce ƙanwar mahaifiyarta ta so karɓar ta sai dai kakarta ta ƙi har ma ya
kai ga sun yi rigimar da ta sa tayi matukar fushi, sau ɗaya ta taɓa zuwa ta duba ta a gidan
kakartata sai lokacin da take wurin innarta ma ta zo ta duba ta, haka ma tana gidan kawu ta zo
sau biyu sai dai bata taɓa wuce awa ɗaya ba tana ganinta ta kawo mata tsaraba ta tafi don wani
kauye gaba da su sossai take.
Duk da chan ta san Afeefahn na cikin damuwa sai dai bata san ya kai har haka ba, ganinta a
yanayin da ta sameta ya matukar ɗaga mata hankali.
"Afeefah da ke nake yi!"
idanunta da kaman za su faɗo ta saisaita ta miƙe da sauri ta shige akurkin ɗakin nata. Wani
tunani da ya ɗarsar mata ne ya sa ta nemi gefen kayanta ta tsuguna, hawaye ne ya cika
idanunta Aunty Zee ce ta shigo tana ƙarewa ɗakin kallo cike da tausayawa ta duƙa gangarta
tare da dafa kafaɗarta
Kaman ta karanci yanayin da take ciki da tunanin da zuciyarta ke yi.
"Sau tari ƙaddarorin da ke zagaye da mu su ke taimaka mana wurin tabbatar da imaninmu ko
akasin hakan, ina so ki zama tuwon hatsi mai yawan juriya, dukkan tsanani yana tare da sauƙi.
Mu tafi."
Taya ta tayi suka haɗa yar Ghana most go ɗinta da babu wasu kayan kirki suka fice, bata damu
da ko sallaman su Baba Larai ba su ma kuma dariyar Allah ya tura ƙeya suka bi su da shi don
yanzu Afeefahn bata da anfani a rayuwarsu.
Tasha suka tafi suka hau mota, ita dai jikinta ya matuƙar sanyaya damuwar da ke ranta ko kusa
bai ragu ba saboda tsoron kar wani abu ya sami Auntyn nata da take ji da, ya haɗu da bata taɓa
shiga mota ba a rayuwarta don bata taɓa barin garin nasu ba wannan ne karo na farko, bata
san akwai titi kwantacce irin hakan ba sai da suka ɗauki titin cikin garin Anchau daga kauyensu
chan cikin Dutsen-wai na Kaduna state, tun tana kalle-kalle har bacci ya sure ta, sai ji tayi Aunty
zainabu na tashinta tana bude ido ta ga har sun iso inda za su sauƙa ba ma su isa tasha ba don
Auntyn gidan ta na daga wajen garin Anchau duk under kubau LGA of Kaduna state ne, sauƙa
suka yi ta ɗauki kayanta a kai suka gangara layin har zuwa gidan, layi ne na masu matsakaitan
ƙarfi da rufin asiri gidan Auntyn ba wani babba bane sai dai ciki biyu ne da parlor sai tsakar gida
da take da tarin shuke-shuke.
A madaidaicin parlorn ta yi mata masauki ta buɗe karamin frigde ɗinta ta fiddo mata ruwa
"Sha ruwa bari na samu na ɗora mana wani abu ko? Sannu. Ki sake jikinki a nan babu mai
takura miki in shaa Allahu kin ji?"
Kai ta gyaɗa tana yaƙe dai, bayan ta sha ruwan ta fita zuwa kicin na tsakar gida don kamawa
Auntyn nata aikin da take yi Dukda ta ƙi tace ta je huta amma sai da ta saka mata hannun suka
shiga yi tare tare har suka gama, shinkafa fara da Miyar jajjage da tayi ta saka mata a filet
"ɗauka ki koma ƙasan mangoron chan ki shimfida taburma sai ki ci"
Yadda ta ce haka tayi Auntyn ta kawo mata ruwa again tuni ta yi nisa a cin abincin.
Aunty zainabu dai na ta kokarin haɗa na mijinta don ta san yana gab da shigowa shima cin
abincin ranan, dama daga ita sai shi ne gidan Dukda ta fi shekaru goma da aure sai dai har
yanzu bata haihu ba, ya sake aure bayan ita amma ba gida daya suke da matar ba itama dai
har yanzu babu wani labari na haihuwa kam suna kuma zaman lafiya sossai.
Tana ƙoƙarin kai loma yana sallama, ta amsa ya ɗan yi turus yana kallonta gabanta ne ya ɗan
faɗi don ganin fuskanshi ya ɗan sauya ko da ta gaishe shi da kalma ɗaya ya amsa kan ya nufi
ciki yana kiran zainabu...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Ba lallai ku ji ni anjima chan ba saboda wani uzuri na so pls bear with me ku riƙe wannan as na
chan anjima ɗin tunda Its already friday.*
*004*
A wurin ta cigaba da zama jiki a saɓule har dai Aunty zainabu ta fito tana kallon fuskanta da har
ya ɗuri ruwa saboda ƙuna daga gefe zuwa ƙasan idanunta, Allah ya taƙaita ma bai taɓa idanun
ba ta ce
"Har kin gama ci Afeefah?"
"Eh Aunty na gama"
Ta faɗa a hankali don yanayin Auntyn bai mata yadda suka dawo ba idanunta kaman ta yi kuka.
"Bari na ba uncle ɗinki abincinshi sai na zo mu tafi gidan mai mazari ya duba miki wannan ƙunar
kar ya zama miki damuwa"
Daga haka ta yi kitchen, Afeefah ta miƙe ta shiga parlor zuwa ɗakin da ta ajiye mata kayanta
daidai ta sauya hijabi zata fito ta ji mijin Auntyn nata murya a sama yana magana
"Babu inda za ki da ita zainabu idan ba mayar da ita inda kika ɗauko ta za kiyi ba"
Itama Auntyn a sama ta amsa shi
"sai dai kuma idan za mu bar maka gidan tare da ita Usman"
"Zainabu...!"
Da mamaki ya ƙira sunan don a zamansu ba zai ce ga sadda ta ɗaga mishi murya ba sai yau.
Kuka ta fara
"Haba Usman na fa faɗa maka maganan nan a wurina bashi da matsuguni, Afeefah ɗiyar
yayata ce daidai take da tawa wacce zan iya haifa a cikina tana cikin matsi da takurar rayuwa
ina tsoron nima Allah ya kama ni a kan banzatar da rayuwarta don Allah ka kalleta da kyau ka
ga depression na neman kasheta tun a kananun shekaru..."
Ya katse ta
"Zainabu ba wai 'yar uwarki na tsana ba ina tsoro ne, ina tsoron abin da zai je ya zo daga nan
Anchau har Dutsen-wai babu wanda bai san da labarin yarinyar nan ba, ko kwanan nan ta ci
kurwar wani matashi a kasuwa kowa tsoron hulda da ita ya ke sai ni zaki ɗauko ta ki kawo min
cikin gida?"
Tana kuka sossai tace
"Wallahi duk babu gaskiya a lamarin mutane Allah ba zan taɓa yarda Afeefah zata yi maita ba,
babu mai mutuwa sai wadda kwanakin shi suka ƙare idan ko don ka zauna da mutum kwana ya
ƙare ka zama maye ne da dukkan mu nan Mayu ne don idan baka rasa iyaye ba ma ka rasa
makusanta. Idan dai har Afeefah zata bar gidan nan zan bita mu tafi tare ba zan iya sake mayar
da ita gidan labaran ba wallahi"
Numfashi mai karfi ya sauƙe
"shikenan zainabu ai sai ta zauna, amma duk abin da ya je ya zo babu ruwana"
"Babu ma abin da zai faru sai alkhairi"
A lokacin Afeefah ta sulale ta maƙale jikin gini kamar kadangaruwa ta chusa kanta cikin
kafafunta, bata ga laifin mijin Aunty zainabu ba rayuwarsu yake karewa da ya wajaba a kanshi
amma Meyasa ita ta zama Mayya? Taya aka yi ta zama Mayya? Amsar da ta kasa ba kanta
kenan har yau bata ma san Shigowar Aunty zainabu ba sai dafa ta da tayi ta ji, ta ɗago kai
"Aunty don Allah ki yi haƙuri ki mayar da ni gidan kawu zan cigaba da juriya ni karan kaina
hankalina ba'a kwance yake ba, tsoro nake ji ina tsananin tsoron kar wani abu ya same ki ta
dalilina ba zan iya yafe wa kaina ba..."
Kuka ne ya ci karfinta Auntyn ta share mata hawaye
"bawa baya taɓa wuce ƙaddarar shi Afeefah babu wanda ke da ran wani a hannunshi face
ubangiji don Allah ki kwantar da hankalinki kin ji? Ba zan taɓa iya sake barinki ki zauna wurin
'yan uwan mahaifinki ba muddin ina numfashi. Tashi mu je"
Tashi tayi suka fice daga gidan suka je aka saka mata maganin ƙuna a wurin kan suka dawo.
Washegari suka sake fita dayake Aunty zainabu yar kasuwa ce tana saya da sayarwa sossai
babu wanda bai santa ba a unguwar da ma unguwannin da suke maƙotaka tana saya kuma ta
sayar, hatta kayan jikinta in zaki ce kina so ta kan iya cirewa ta sayar miki haka take bata zauna
ba, shiyasa take da rufin asirinta a karan kanta makaranta suka je aka yi wa Afeefah interview
da kyar aka barta a js2 duk da shekarunta sun wuce ajin, private ce da bai wuci dubu shidda ba
termly don haka Aunty ta karbi sample na uniform suka tafi kasuwa ta yanka mata yadi aka ba
tela akan zai ɗinka kan su gama sayayya, sayayya sossai ta yi mata da saida tayi ta zub da
hawaye tana da sauran gata ashe bata sani ba soyayyar Aunty zainabu ya shige ta tamkar
yadda zata so mahaifiyarta.
Da kaya sossai suka dawo niki niki, a ɗakin Aunty zainabu inda Afeefahn take suka ya da zango
nan ta sake shirya mata kayanta dama ta cire nata masu ɗan dama suka tafi da su kasuwa aka
rarrage mata yadda zai ƙarbe ta duk na gidan kawu zubarwa tayi.
Rayuwa ne mai cike da natsuwa da kwanciyar hankali ta shiga gudanarwa gidan Aunty zee da
uncle usman, tun yana tsoro har ya sake barin ma da ya ga Afeefar yarinya ce mai kwazo,
natsuwa da hankali ga ibada da son karatu boko da arabi komai na gidan yanzu ita ke yi don
babu wani yawa bata bari Auntyn nata tayi komai muddin tana nan, haka a makaranta malamai
sai yabawa kwazonta suke don tana da ilimi kuma akwai saka kai, suna ganin ma a karshen
shekara za'a iya bari tayi Junior waec ta tafi ss1 in dai aka tafi a yadda take a yanzu, haka
islamiyya tana kokari sossai kusan kowa ya san ta a unguwar saboda yadda Aunty zee ɗin ke
nuna ta matsayin ɗiyarta.
Sauri sauri ta gama shiri don ta so makara ta fito goye da school bag ɗinta, fuskanta ya fito fess
a cikin sky blue hijabin makarantar kyaunta ya sake bayyana na ainihin Black beauty, skin ɗinta
har wani sheki yake na samun natsuwa, fararen idanunta take warawa ta inda za ta hango
Aunty zee sai dai bata ganta ba, a parlorn ta tsaya ko zata fito daga ɗakin uncle usman ta samu
ta mata sallama sai shi ta ga ya fito ta ɗan duka ta gaishe shi ya amsa cikin natsuwa
"Dama uncle ina son yin sallama da Auntina ne ko ta koma bacci?"
"Eh ai tun da ta fito ta ga kin kamalla komai tana komawa ta sake bingirewa da bacci"
Afeefah tayi murmushi
"Toh shikenan na wuce makaranta"
"karɓi"
Ta matsa ta karɓi ɗari biyu da yake miƙa mata
"Sai kin dawo a mayar da hankali"
Ta amsa tana ficewa da murmushi fal fuskarta kaman ba Afeefar da ba da take yawo da
tsananin damuwa da hawaye a ko da yaushe.
Ko a makaranta natsuwarta bai kau ba, sam ba zaka ganta tana wasa ba koyaushe littafi na
hannunta tana dubawa har ta fara presenting abubuwa a assembly da participating a wasu
programs na makarantar, bata da ƙawa har yanzu don duk ajinsu ba sa'annin ta shirin exams
ake don haka yau revision ƙarfe sha biyu suka tashi ta nufo gida cikin natsuwa.
Sai dai ta samu babu kowa, ta karɓi key a maƙota ta shiga sai da ta zare uniform ɗinta ta sauya
da wasu kananun kaya wando ne da dogon riga da ya zo mata har gwiwa kan ta ɗaura
dankwalin ta fita zuwa kicin, abinci ta ɗora musu tana mamakin inda Aunty zee ta tafi don bata
ce mata za ta fita yau ba kuma kila wani abu ne dai ya taso a chan cikin dangi, ita dai ta san
suna da dangin nesa nesa ta ɓangaren mahaifiyarta amma su ma ba wani karbarta suka yi ba
ko daukar ta da muhimmanci Dukda ita kanta Aunty zee ɗin ba ta su take ba abinda ke gabanta
ma ya fi karfinta.
Tana sauƙe faten doyar sai ga su sun shigo
"wannan kamshi haka me ake dafa mana ne Afeefah?"
Aunty zee ta leƙo kicin ɗin tana tambaya
Dariya Afeefah tayi
"Aunty faten doya ne fa, amma ya Naji muryarki kaman ta marasa lafiya?"
Tana zama a kujeran tsuguno ta janyo filet ta miƙawa Afeefahn, Afeefah ta karɓa ta shiga saka
mata kan tace
"Eh Afeefah ban jin daaɗi ki taya ni murna kin kusa samun kanwa ko ƙani"
Wani irin zaro ido Afeefah tayi kan ta saki ihu tana rungume Aunty zee ɗin sai ta hau hawayen
murna, zuciyarta tamkar takarda haka take jinta oh ashe Aunty zee na da rabon ganin 'ya'yanta
a duniya?
Ita Aunty zee ture ta tayi tana share mata hawaye tace
"duk na murnar ne? Yanzu na gama share wa uncle ɗinki da ma ɗayar Auntyn taki da suka tasa
ni gaba suna kukan farin ciki shine kema za ki fara? Oya ni sa min abinci in ci cikina kaman ana
yasa"
Tana murmushi ta ƙarasa saka mata ta dauka mata zuwa gindin bishiyar dake ba da iska mai
ni'ima, taburma ta shimfida mata kan ta ajiye mata abincin taje ta kawo mata ruwa tuni ta yi nisa
a cin abincinta.
Dukda karatu da Afeefah ta saka a gaba saboda tana son fitowa da sakamako mai kyau a term
ɗin don Aunty tayi alfahari da ita hakan bai hana ta jajirce wurin kulawa da Aunty zee ɗin ba, ko
tsinke in ta ga zata ɗaga za ta karɓe duk abin da take so ko a hira tayi maganan Afeefah za ta
yi kokari wurin ganin ta dafa mata shi tunda uncle usman bai Gaza da gidan ba ko ta wani
ɓangare, kishiyar Aunty zee ɗin ta kan zo sossai tun samuwar cikin itama da ita ake haduwa
ana ririta cikin Dukda Afeefah dai jininsu bai wani haɗu da matar ba tunda iyakarsu gaisuwa, ko
hira Aunty zee ke yi da Afeefah in dai ta sa matar bata amsawa ita dai Afeefah bata damu ba
tunda babu abin da ya haɗa su duk kuma a je a zo bata wuce awanni biyar zuwa goma a gidan
so bata damu ba sam.
Kaman yadda ta ci buri ranar hutu sai ga Afeefah da position 3rd ta yi murna kwarai, haka ta
dawo gidan da farin ciki. A tsaye ta samu Aunty zee tana tattare kayan da Afeefah ta wanke da
safen don shigarwa ciki sai ji tayi an rukunkumeta
"Aunty ki taya ni murna"
Result ɗin ta miƙa mata
"Masha Allah, Alhamdulillah yarinyana kai ya fara ja Allah ubangiji ya sa ki fi haka ya dafa miki a
dukkan lamuran ki, Allah ya nuna mana ranar da wannan karatu zai anfanemu ina fata za ki yi
kokarin ci gaba da tafiya a haka next term mu ga First rubuce wannan wuri"
Kai ta gyaɗa tana ta dariya.
****
Aunty zee ce zaune tana ta aikin kallon Afeefah dake yi musu alele don yau da sha'awar shi ta
tashi hakan ya sa tana furta wa Afeefah ta hau yi, tana aikin cike da tsafta tana kuma jefawa
Aunty zee ɗin hira kaɗan kadan da ya shafi islamiyya da kuma boko da suka koma sati huɗu
kenan.
A ranta take raya abubuwa dayawa game da Afeefah ɗin tana da matuƙar buri a kan rayuwar
Afeefah yadda take very jovial bata fata nan gaba ko ma menene ya karya ta, tana adu'a yadda
ta samu farin ciki ta dawwama a haka haske ya cigaba da bibiyar rayuwarta, bata san me gaba
ya tanadar ba amma tana mafarkin ganin Afeefah a kololuwar matsayi cike da kwanciyar
hankali, danne tunaninta da ya so juyewa ta yi tana cewa Afeefah
"Wai kuwa kin san kamanninki har ya ɓaci da Yaya Aisha?"
Afeefah ta ɗago ta kalleta yau ne karo na farko da maganar mahaifiyarta ya fito daga bakin
Aunty zee ɗin
"Na zaci da babana nake kama don mutane kan ce ina kama da inno(kakarta da ta rasu)"
Miƙewa Aunty zee ta yi ta shiga ɗaki ta ɗan jima sossai kan ta fito da wasu hotuna hannunta, a
lokacin Afeefah ta koma kan taburma ta zauna ta bar alelen ya dafu gefenta Aunty zee da
cikinta har ya turo sossai ta zauna.
"Jini ne kawai tsakanin ki da inno amma kamanninki tsaff Yaya Aisha ne, kin ganta nan lokacin
bikinta ne da babanki"
Karo na farko kenan da zata ga mahaifiyarta sai ta ji zuciyarta ya cika da rauni, hannunta na
ɗan rawa ta sanya ta karɓa hotunan da ne Black and White matar da ta kasance mahaifiyarta
da bata sani ba zaune sanye da zani da riga tare da Ali goggoro, hawayenta ne suka tsinke
ganin yadda matar ta zauna tamkar ta kirata ta amsa, da gaske hatta yatsun hannu da na kafar
ta irin na mamanta ne, baƙin fatarsu mai sheƙi, manyan fararen idanunsu, tsinin hancin su,
karamin bakinsu da fararen hakwaransu hatta dimple guda ɗaya da maman nata ke dashi a
gefen hagu itama tana da shi.
Raɗaɗin maraici ne ya mamaye zuciyarta, in ba mutuwa ta zama dole ba wa zai so maraici?
Maraici ma irin nata marar gata da tushe? Maganganun mutane a kan iyayenta take tunawa sai
taji kaman yanzu ne ake jefanta mugayen kalamai, tsintuwa da hantara a kan waenda duk
duniya idan da za'a ce me take buƙata ayi mata ko da abu na ƙarshe ne za ta zaɓi su yi rayuwa
na har abada amma ake mata Ƙazafin kashe su, anya zuciyarta za ta taɓa warkewa? Anya za
ta iya yafewa masu alhakinta?
Ɗago raunannun idanunta tayi ta Kalli Aunty zee
"Aunty don Allah yaya maita yake? Ya ake yi? Yaya mutanen su ke? Kila baka sanin sadda
kake yi in ba hakan ba ta ya zan zaɓi wannan rayuwa akan iyayena? Kila ko cikin fitan
hayyacine ake yi ko? Menene ribar yin? Suna yin kuɗi ko Aunty? To me yasa ni ban yi ba?
Yanzu wannan pure soul ɗin ni na kasheta ko?"
Duk ta rikice ta rasa me zata ce, kalaman suna zuwar mata ne kawai ba tare da ta san fitan su
ba, kuka ne ya kufce mata, kukan da ke fita daga ƙasan zuciyarta na ciwo da raɗaɗi...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Ku yi ta Adu'a mu ƙare a haka ina jin karsashin typing, ina jin daaɗin comments ɗin ku Allah ya
bar ƙauna*
*005*
Hannunta ta riƙe cike da tarin tausayinta da kuma ƙaunar da take jin tana mata fiye da ƙima ta
shiga cewa
"Na san ba ki kashe kowa ba Afeefah, ƙage ne kawai da Ƙazafi irin da jahilai daga cikin
al'ummar mu, ƙarancin ilimi yayi yawa ta yadda mutane suke kasa yarda komai daga Allah ne, a
ƙarƙarorin mu ne musamman wanda babu addini sossai za ki samu ko tuntuɓe bawa yayi sai an
faɗi dalili da silar shi