Showing 66001 words to 69000 words out of 149666 words
mutumiyar kirki ce Mammi, kina daga cikin sahun 'yan aljanna in shaa Allah... Hakika kina
da zuciya mai kyau wanda Allah ne yayi miki kyautar shi don samun irinki sai an tona"
Murmushi kaɗan kawai Mammi tayi zata yi magana Afeefah tayi saurin cewa
"Mammi ki bar roƙo na kin yarda da ni ni kuma in shaa Allahu ba zan ba ki kunya ba, wlh har
raina na amince kuma zan yi iya kokarina in ga na ba da abinda ake so"
Rungumeta kawai Mammi tayi cikin farin cikin da yake ratsa zuciyarta.
****
Shi kam Rayyan daga masallaci ya mayar da Saleem gida bayan yayi ta mishi tuni akan
mahaifiyarshi da 'yan uwanshi irin muhimmancin su a rayuwarshi duk yana ji amma amsawar
wani iri, bai damu sossai ba don shima zai taya abokin nashi da Adu'a yana kuma da yakinin
duk abinda yayi farko yana da ƙarshe musamman abinda ba don Allah aka yi shi ba.
Daga nan gidan Jannah ya wuce, tana zaune kawai ta ji ana knocking ta tashi taje ta buɗe sai
ta ganshi tsaye, murmushi ta saki tana mishi sannu da zuwa ya amsa yadda ya saba musu ya
shiga ya samu wuri ya zauna, cikin mintuna kaɗan ta cika gabanshi da kalolin abubuwa su
snacks da su abinci kan ta dawo ta zauna
"Barka da juma'a Yaya"
"Barka dai ya gidan?"
Ta amsa da farin ciki
"Lafiya ƙalau ya su Mammi?"
"Alhamdulillah"
Ya faɗa yana shan zobo don yana matuƙar kaunar zobo bayan ya sauƙe cup ɗin ya kalleta
"ba ki da wani damuwa ko?"
Kai ta gyaɗa
"Babu komai Yaya"
Ya ce
"Masha Allah"
Miƙewa yayi ya zare kudi ya ajiye mata dukda tana aiki godiya tayi ta mishi ta raka shi har mota
ya tafi ta dawo tana murmushi ya kan yi hakan tun bayan aurenta, haka kawai sai ta ganshi zai
zo ya duba ta ya tabbatar tana lafiya ya ajiye mata kudi ya tafi.
Gida ya nufa kai tsaye, bai je Sashenshi ba don la'asar ya kusa yana so ya duba Mammi kan ya
fita yayi sallah sai ya dawo ya huta gabaɗaya, ko da ya shiga yanayin wurin ya ɗan zubawa ido
Dukda ya fahimci Mammi ta yi hawaye sai dai idanunshi da suka shiga cikin nata ya ɗan ji wani
yanayi da har bai ɓuya ba, seconds ya kwashe yana kallonta kan ya ɗauke kai sai ta miƙe ta zo
zata fita muryarta na cracking tace
"Sannu da dawowa"
Bata jira amsarshi ba ta wuce don ganinshi kaɗai tausayi yake bata.
Ɗan shiru yayi kan ya taɓe baki yana ɗaga Kafada ya isa wurin Mammi
"Mammi why did you cry? Yarinyar chan ne ko?"
"Ni ce dai na sakata kuka ba ita ta saka ni ba, ka dawo?"
Bai ja zaren zancen ba yace
"Eh, hope baki ji yunwa ba?"
"No ban ji ba, na san ma Abeeha ta kusa shigowa ko na ji ma zata zo ta sama min wani abin
you should rest"
Kai ya gyaɗa ya ɗan jingina da kujera yana lumshe ido
"Ni ko ina son yin wata magana da kai"
Buɗe idanun yayi yana kallonta
"Saraki ka tuna kai ka ce in zaɓa maka mata ko ma wacece za ka aureta in dai ni ce na zaɓa?"
Ɗan shiru yayi kan chan dai ya gyaɗa kai.
"Toh mun samu Mata Saraki"
Bai wani nuna ya ji daaɗi ko zumudi ba sai ma runtse idanu da yayi ya ɗan buɗe.
"Baka tambayi wace ba kuma a ina?"
"Mammi ke fa kika shirya wannan aure duk abubuwan nan ba lallai sai na ji ba ayi duk abinda
ya dace kawai"
"haka za ka aureta baku fahimci juna ba? Ai ba'a haka dole za ka nuna mata itama macece
kaman sauran mata ka bata darajar ta na neman soyayya da ma kyautatawa da kan shiga
tsakanin saurayi da budurwa"
Idanunshi kawai ya zubawa Mammi don jinta kawai yake baya tunanin zai iya yin ko abu guda
cikin wanda ta lissafo.
"Mammi kin fa san duk ba zan iya wannan ba"
"Toh na ji amma ka san wacece yarinyar? Ka dai san ba zan zaɓa maka wacce na san bata
dace da kai ba ko? Kuma ka yi min alkawarin ƙarbar ta yadda take ko?"
Ya ɗan matsa kaɗan ya riƙe hannunta
"Mammi duk zagaye-zagayen nan na menene? Kin fa san yadda na ɗauki girman alkawari
wallahi zan amince, wacece?"
Yadda take ta zagayen ne yasa ma yaji yana son sanin wacece haka.
"Afeefah ce!"
Ɗan shiru yayi yana tunani don sai ya ji kaman ma bai san sunan ba, amma duk inda ya zagaya
a kwakwalwarshi mace ɗaya tak ya sani da wannan suna, mace ɗaya da ya sani kuma
buduruwar abokinshi ce salim.
Da sauri ya kalli Mammin yana girgiza kai
"A'a Mammi ki samo wata ba wannan ba"
Da zuciya ɗaya yayi maganan kuma kai tsaye.
"Ban gane in samo wata ba, Meyasa?"
"Mammi ni wannan ta yi min yarinya wlh ba na son hauka da raini, sannan Mammi buduruwar
saleem ce fa! Ta ya zan fara zaman aure da ita?"
Murmushi Mammi tayi a maganan nashi na farko
"Ina saleem ɗin? Ina yana chan yayi aure yana zaune da matar shi? Ko ma bai yi aure ba ba
zan amincewa Afeefah ta auri saleem ba ba kuma don shi a karan kanshi ba sai don
mahaifiyarshi ba zan so ta koma inda zata sha wahala ba shiyasa na zaɓa mata kai ina da
yakinin za ka kula da ita har karshen numfashi"
Tayi maganan cikin tabbatarwa, duk ya ɗan ruɗe mata kaman zai yi kuka ya fara magiyar ta
chanza wata shi dai wannan yarinya bata mishi ba.
"Ba fa zan fasa ba Saraki sai ka bani kwakwarar hujjar da zan gamsu ban da buduruwar
saleem, ban da kuma baka sonta itama bata son ka dukkanku za ku koyi son juna idan zama ya
haɗa ku, banda kuma tayi yarinya don kaima ka san ba yarinyar bace"
Hangota kawai yake a idanunshi yana son tuna menene kuma aibunta wannan idanu farare
manya da take zarowa duk sadda yayi magana yake hangowa kawai, da ɗan sauri yace
"Mammi baƙa ce!"
Dariya Mammi ta fara tana girgiza kai ya kwaɓe fuska shi da gaske yake
"Yaushe kuma ka fara zaɓar kala? Kenan ni da babanku bai aureni ba kenan ko kuma da Su
Jannah ba za su auru ba"
"To ai ku daban ne ita daban Mammi"
"Ka san Allah idan ba legit hujja zaka kawo ba, maganan nan babu fashi ka fara shiri... Saboda
yanayin jiki na ba za mu ɗauko wani hidima ba ɗaura aure kawai za'a yi ayi walima kowa ya
shaida ta tare"
Duk yadda ya so ya zamewa Mammi ya kasa, don komai ya ce tana da amsa har aka kira
la'asar ya tashi ya tafi, ta bishi da kallo tana murmushi idan ta ga yana hira da ita haka hakan
na yi mata matukar daaɗi a rai, ta kan rasa Meyasa baya son Magana alhali ya iya ba bai iya
ba, kawai dai ya zauna shiru ya fi mishi ko mahaifin su Jannah da yana raye sai dai ya ji dariyar
ta ba zai ji maganan Sarakin nata ba yayi ta tsokanarsu kenan tana shigarwa Sarakin don shi
bayan ita wasa da sakin fuskanshi babu mai gani gwara ma saleem da suka shaku sossai
shima don salim ɗin ya karanci halayenshi ne tsaff kuma ya iya zama dashi.
Tana fata ko ba yanzu ba ya so Afeefah ya sake mata fiye da yadda ita take ganin wannan side
ɗin nashi, hannu ta ɗaga tana roƙon Allah ya nuna mata wannan rana da zata miƙa shi ɗakin
matarshi.
Daga nan ta miƙe ta shige don alwalar la'asar, bata yi ƙasa a gwiwa ba da daren ta sa driver ya
kaita gidan ƙanin mahaifinta Uncle Musa dattijo ne sossai shima kuma natsatse mai tarin ilimin
boko da arabi yana da zuri'a kuma duk zaman lafiya suke da su Mammi, sossai ta mishi
bayanin Afeefah ta kuma roƙi da su je su nema mata aure a wurin dangin mahaifinta don a fita
hakkin su, bata so su bada komai amma tana son A karɓi auren Afeefah daga shakikanta. Ya
gamsu shima kuma yayi na'am da hakan sun yi hira sossai don tana kwana biyu bata je ba sbd
jikinta shi ne ma ya kan zo har gida ya duba ta haka yaranshi da wasu jikokinshi, bata bar gidan
ba sai da suka tsayar zai yi tattaki da kanshi da babban danshi su tafi Dutsen-wai su nemi a
basu ranar auren daga nan sai a fara shiri.
****
Mommy ce kwance a kan gado tsabar damuwa da tunani da ta sakawa kanta ne ya sa jininta
hawa sossai, su Samha ke zagaye da ita a yanzu ɗin ma hawaye take zubarwa na tausayin
Saleem da damuwar halin da yake ciki wanda ta yarda laifin ta ne amma me yasa su Yaya za
su rama alkhairinta da mugunta? Me ta musu da zafi haka?
Bata gama tunanin ba Sabrina ta shigo ɗakin ta samu wuri ta zauna
"Sannu Hajiya mommy ashe kuma jiki ya ƙi?"
Mommy ta danne tace
"Eh amma Alhamdulillah"
"Toh Allah ya kara sauƙi dama Saleem ne ya aiko ni"
Yadda ta kira sunan sai da suka daga kai duk suka kalleta.
"Wai cewa yayi ku koma wanchan tsohon gidan na gado ya riga ya tashi 'yan hayan yana son
yayi renovating nan, kin ga yanzu mun yi yawa ga iyali zai fara tarawa ga su Gaje gininsun ya
tsofe cikin ko wani minti zai iya rufta musu suma dai duk nan za su dawo"
Galala suke kallonta da kyar mommy ta iya cewa
"Saleem ɗin ne yace haka?"
"Ai kin san ban san yan hayan ba bare in tashe su, shine yayi komai kuma ya tabbatar min kar
ku wuce yau don gobe masu aikin za su fara zuwa"
Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga sulmiyo wa mommy da su Samha, Sameera ce ta iya
daurewa ta miƙe tsaye ta fara hada kayan mommyn don ba zasu zauna ba, gwara su tafi ɗin
babban matsalar dukkansu babu mai aiki cikinsu karatu suke yi, mommyn sai kallonta take tana
jin tururin zafi a zuciyarta tuni Sabrina ta fice, mommy tashi tayi ta fito kai tsaye ta haura saman
su ta buga, su Samha duk suka bi bayanta jikinsu a matuƙar sanyaye sai da tayi mintuna biyu
kan aka bude saleem ta ƙura wa ido sama da seconds goma kan tace
"kai ka ba matarka saƙo ta ba mu?"
Kai ya gyaɗa
"Duk abinda tace haka ne!"
Jiri ne ya kwashe ta ya yunkura zai tare ta ta ture hannunshi ta juya da sauri ta sauƙa su Samha
ta cewa su hada kayansu duk suka hada suka fito a motar sadiqa suka zuba duk abubuwan
buƙatar su ta ja suka fice daga gidan dukkansu suna kuka, basu sake jin tashin hankali ba sai
da suka iso gidan duk 'yan haya sun lalata shi komai dai sai a hankali kuma dakuna biyu ne da
parlor sai kitchen duk jiki a sanyaye suka zauna a parlorn mommy na dafe da kanta har lokacin
kuka take yi.
"Mommy..!"
Sameera ta kira sunanta.
Sai ta ɗago ta kalleta
"Kina jin zafi a ranki ko? Kina jin ciwo da raɗaɗi ko? Kina jin baƙin ciki da tsantsar damuwa da
tashin hankali ko?"
Mommy tace
"Ba sai na faɗa ba Sameera abin da nake ji ba zai misaltu ba ni saleem ya ɗaga daga gidan shi
zai dawo da surukanshi? Ni fah? Ko a mafarki ban taɓa zato ko tsammanin saleem zai iya juya
min baya a kan mace ba"
"Mommy in faɗa miki gaskiya? Laifin ki ne, dukkanmu muna da laifi a abin da ya faru... Mommy
kin yi tunanin inda Afeefah ta nufa da muka kore ta? Gwara mu muna da nan kuma ko ba komai
muna da junanmu amma ita kaɗai ta fita bata da kowa bata da inda zata je, kin tuna irin
wulakancin da muka mata? Ashe alhakin da muka raina zai iya bibiyarmu, kin tsane ta ne
saboda saleem yana son ta kina ganin son nan da yake mata zai sa ya bijire miki kika zaɓa
mishi wacce kike ganin ke ce da riba sai kuma akasin hakan ya faru. har yanzu kina ganin laifin
Yaya da kika mishi dolen karbar wacce bai taba so ba? Kina ganin laifin Yaya da ƙarfi da yaji
yana kuka yana komai kika raba shi da Masoyiyar shi? Mommy ina jin zafi ina jin ciwo ina ji a
zuciyata cewa duk wannan abinda ya farun alhakin yarinyar nan ne, Allah ya jarabceni da
azabar so na ji yadda itama ta ji a sadda muka raba ta da nata savior ɗin, na ji kwatar abinda
yaya ya ji a kanta amma muka hadu muka nufeta da sharri har da ƙagen lalata da samari wlh
idan ba mu neme ta mun nemi yafiyarta ba to kadan kenan muka fara gani"
Dukkansu maganganun sameeran sun shige su barin ma mommy da Samha dake ta kuka,
gaskiya Sameera ta faɗa bata kyauta ba kuma duk laifin ta ne da tun farko ta kwaɓe su ba zasu
yi ba amma bakin alƙalami ya riga ya bushe sai dai su tari gaba, tana tuna irin abubuwan da
suka mata tana tuna irin yadda taje ta haɗa ta da maza don tayi rayuwa saboda kawai an ce ne
ita Mayya ce sai ka ce jahilai waenda basu yi karatun islama ba sun ci zarafinta baiwar Allah,
sai gashi Allah ya nuna musu ɗan Adam ko ya yake mai daraja ne a gareshi, ya nuna musu
ikon shi a kan bayinsa.
"A ina za mu sameta mu nemi yafiyarta a ina zan ganta Sameera?"
"Wannan sai Allah mommy, yanzu ina so ki daina yiwa yaya kuka mu dukufa Adu'a da sadaka
Allah ya karkato da hankalinshi mommy adu'ar ki karɓaɓɓiya ce a gareshi ke kika ɓata ke ya
kamata ki dukufa ki gyara"
Ta gamsu sossai kuma ta fahimci karatun duniyar, ta fahimci ayar da Allah ya nuna a kanta don
haka gwagwalanta ta cire ta ba sadiqa akan su je su sayar su musu sayayyan duk abinda za su
buƙata haka suka fice kasuwa suka bar su su biyu da Samha da har lokacin jikinta kaman an
zuba mata ƙanƙara.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*31*
A hankali kwanaki ke ja har ranar da Uncle Musa ya yanke da za su tafi Dutsen-wai su samu
kawu, shi da yaranshi manya biyu sai Driver suka ɗauki hanyar, tafiyan awanni kaɗan ya sada
su da kauyen, kusan abin da ya faru da 'yan uwan Sulaiman hakan ce ta faru amma dayake ya
riga ya sani suma kuma sun sani so basu wani damu ba.
A kofar gidan Labaran suka yi parking motar su biyu suka fito suka bar uncle ɗin cikin mota,
gidan da rabin shi a zube a ƙasa suka ɗan zubawa idanu suna mamakin me ya kawo Rayyan
har nan neman aure? Daga ka ga gidan zaka san suna fama da masifar talauci, buhuhuna ne
da suka zama jajazir aka kare ɓangare guda na gidan dashi, ga yara nan dukunkun rabin su
tsirara suna ta wasa a kofar gidan, daga gefe wasu matasa ne suna shaye-shayensu ko a
jikinsu, ɗayan na shirin turawa a kira musu mai gidan sai ga kawu Labaran ya fito a zuburen shi
ganin mota ya sa ya taka birki
"Lafiya?"
"Ƙalau sai Alheri, Malam Labaran muke nema"
Kanshi ya nuna
"Ga ni"
Girgiza kai babban da sunanshi Mansur yayi wani abu sai bakauye Dukda wasu kauyukan
mutanen cikinshi akwai kara da girmama baƙo haka kuma mutane suna suka tara, amma babu
gaisuwa babu komai bare iso ko ruwa kawai a yi abinda ake so.
"Mun zo ne akan maganar 'yar wajenka Afeefah"
Uncle Sanusi ya faɗa, tun ma kafin ya gama kaiwa aya Kawu ya katse shi
"Wace Afeefah? Ai mu bamu da Afeefah a zuri'ar mu kap"
Uncle Mansur yace
"Afeefah 'yar wajen ƙaninka?"
"Ah Annoba zaka ce sai na fi ganewa, ai na jima da sallamar wa duniya ita ko a chan ne tayi
muku wani abin ba wurina za ku zo ba ita za ku kama babu ruwan Labaran Ah to"
"Malam ka natsu mana ka ji bayanin da muke tafe dashi"
Uncle Mansur ya faɗa da ɗan zafi don yana da faɗa shi, Buɗe kofan da Mahaifinsu yayi ya fito
ne ya sa suka yi shiru, uncle Musa ya miƙa mishi hannu suka gaisa ya ce
"Ba wani abu bane ya kawo mu illa nemawa jikana, ɗan wajen su auren 'yarka Afeefah, mun zo
ne da batun na gani ina so idan babu damuwa zaka iya ba mu rana sai mu zo a ɗaura aure"
"aure??"
Ya faɗa yana sake kallonsu Dukda sun yi zubin masu hankali kuma kaman suna da kuɗi amma
wani gida ne zasu yadda dansu ya auri Afeefah? Kila dai basu san wace ita ba, zayyano musu
wace ita da mutanen da ta kashe ya shiga yi har abinda ya sa ta bar garin
"Duk mun san da hakan"
Uncle Sanusi ya faɗa.
"Kuma kuka yarda ɗan ku ya aureta?"
"Eh a haka yake sonta, bama buƙatar komai daga gareka ita ɗin ma ba sai ta dawo nan ba
auren kawai muke so ka bamu da kanka kuma mutanen garin nan su shida zaman aure zata
cigaba da yi ba dadiro ba kaman yadda kuke ta faɗa"
Numfashi ya sauƙe ai tunda babu abinda suke so shikenan kila ma suma manyan mayun ne
don waenda basu ji tsoro ba bayan jin labarinta ai basu da maraba da mayun, kuɗi har dubu
hamsin suka bashi a cewar na gani ina so ne. Ya hangame baki yana kallon uban kuɗin kaman
faɗa ya karɓa yace tunda sune zasu zo su gaya mishi kawai randa suke so a daura, suna ta
mamaki shi ba ruwanshi da bincike ko wani abu tunda ya ga kudi kawai ya ruɗe, suka tsayar da
nan da wata guda a haka suka yi komai daga tsaye suka shiga mota suka juya suna mamakin
ƙarantar mutumin.
A chan wurin kawu kuwa kaman zai kifa ya shiga gidan
"Asabe, larai ku fito ku ji abin mamaki wai na kwance ya faɗi"
Duk waje suka yo larai ta kasa shiru
"Wannan uban kudin fa malam daga ina haka?"
"Nima duk kaina ya kulle, wasu ne suka zo yanzu a mota wai sun zo neman auren Afeefah
wannan kudin na gani ina so ne suka bayar"
"Afeefah dai???? A mota?? Wannan uban kudin kawai na na gani ina so ne? Kuma ka amince
musu??"
Duk a jere suka jero tambayoyin cike da tashin hankalin hassada.
"Toh ko ban basu ba ai zasu iya auren tunda ba gabanmu take ba tunda suka ba da wannan a
na gani ina so ki yi lissafin nawa zasu bayar sadaki?"
"Amma malam Afeefah annoba Mayyar taya zata yi aure ta bar yaranmu zaune? A dandi fa
take basu sani bane?"
"Sai da na basu labarinta tsaff kuma sun ce sun ji sun gani"
Wani irin abu ne ya taso ya tsayawa inna larai a makogoro Ah ba zai yiwu ba, sam Afeefah bata
chanchanci auren mai kuɗi ba dole ta san yadda zata yi zama bai ganta ba.
Ko ta kan bayanin da kawun ke tayi bata bi ba shi lissafin zuwan kuɗin shi