Showing 3001 words to 6000 words out of 149666 words
dama na san aje aje sai ta fara yiwa mutane dauki ɗaiɗai shiyasa ban taɓa
sayan abincinta ba, yarinyar da riƙaƙƙiyar Mayya ce an ce ma ita ce mataimakiyar shugaban
Mayu yanzu?"
Ko motsi bata iya ta yi ba taji an damketa zuciyarta kaman zai fito waje ba na tsoron abin da
mutane zasu iya yi mata ba sai na tsananin tsoron mutuwa, mutuwa na daga cikin abinda a
yanzu yake gigitata dole duk mai imani ya tsorace mutuwa a yanzu yaron nan ke mata magana
a yanzu ana cewa ya mutu? Ta yaya? Meyasa sai da ya sayi abinci a hannunta?
Wani mai ƙirar ƙarfi ya hankaɗata tsakiyar mutanen
"Ke tsallakeshi sau uku ki sakar masa kurwa yanzu wallahi ko mu sheƙa ki barzahu.."
Yayi maganan da karaji yana zaro wuƙa mutane suka fara kananun maganganu masu zaginta
na yi, wasu har labari suke bayarwa na ta kashe iyayenta ai maitar gado ne tun a ciki ta fara
kisa, hawaye masu zafi ne suka shiga gangaro mata a sadda take tsallakeshi a dole, kalaman
da suke shiga kunnuwanta sun yi mata girman da ba zata iya ɗauka ba, abin tashin hankalin ma
shine yaron bai tashi ba, ya tabbata ya riga ya rasa ransa ko kan ta gama fahimtar kanta har
tayi wani yunƙuri an rufe ta da duka, ko yunkurin kare kanta bata yi ba don a yanzu ita ma ta fi
ƙaunar mutuwar da rayuwa, da kyar wasu dattijai suka kwace ta fuskanta har ya fara sauya
kamanni wasu sassa na jikinta na zubar da jini, kwanukan inna larai da kulolinta an yi daga
daga da su, ko kasheni ka ɗaukanta (lalitar kuɗi) bata gani a jikinta ba.
Wani irin deep kuka take yi mai taɓa rai, dattijon ta kalla
"Don Allah baba ka bar su su kasheni kawai nima ina so in huta, don Allah ku bar ni su kasheni"
Abin da take ta maimaitawa kenan tana gunjin kuka ya riƙo hannunta
"Ki natsu yarinya babu mai kashe ki, shima kwananshi ne ya ƙare ya mutu kiyi hakuri ki tashi
mu raka ki gidan ku"
Cikin in-inaa take cewa
"in naje gi..gidan ma ba..ba tsira z..Zan yi ba kuɗin inna larai da kwanukan ta duk babu"
Ta sake rushewa da kuka, tausayinta ne ya kama su suka haɗu suka tasa ta gaba har gidan,
kawu suka fara nema ko da ya fito da kallon tsana ya shiga bin ta.
"Yau kuma magana kika janyo min ko? Kayan uban wa kika sata ko uban wa kika kashe??"
Dattijo ɗaya daga ciki yace
"A'a malam labaran ya kamata ka fara tambayar raunin jikinta ne amma damuwarka wani abu
daban? Ka san yaran zamani da kansu a koyaushe baya gayamusu daidai akwai wani yaro da
ya sayi abincin 'yar wajenka yana cikin ci sai Allah ya turo da ajalinshi a take ya tafi shine suka
yi yunkurin kasheta a cewar su ita ce ta cinye kur..."
Tuni ya katse su
"Ai da kun barsu don ni baku burge ni ba sam, da kun barsu don ko rantsuwa nayi ba zan yi
kaffara ba ita ce nan ta kashe shi, sai ki shiga ai ki jira zuwan iyayenshi tunda ba kowani
mahaukaci bane zaki mishi asarar rai ya barki ki sha ba"
"Ashshaa amma...."
"Babu ruwanku! Tunda kun kawo ta zaku iya tafiya" ya cigaba da mita kaman zai ari baki
yarinya ba jari zata kawo mishi ba, ba auruwa za tayi ba babu wani amfanin da take mishi sai
cin abincinshi amma kullum bacin ranta ya fi na kowa a ranshi.
Dattijan suka juya suka tafi ita kam kanta ƙasa zuciyarta na wani irin karta, hawaye kuwa sun ki
kafewa a idanunta kafafunta da suka matuƙar yi mata nauyi take kokarin ɗaga wa ta shiga cikin
gidan taji an fusgo ta har tana taga taga zata faɗi wuyan hijabin jikinta aka shaƙo
"Ina kudina da kayana?"
Kakari take don ko numfashi ta kasa shaƙa, idanunta da suke manya suka sake fitowa ainun
sun rine sun chanza gabaɗaya.
Inna larai ganin zata yi kisa ya sa ta Hankaɗata bata damu da kokawar saisaita numfashin da
take tayi ba ta daka mata tsawa
"nace ina kuɗina?"
"In...nn..a B..ban san ya ak...a yi ya fice daga ji..jikina B.."
Hayewa ruwan cikinta tayi ta shiga ɗirkarta kaman an aiko mata ita
"kaman kuwa yadda ya fice baki sani ba haka sai na rabaki da numfashinki baki farga ba, wlh
dukan kuɗina yau sai na yi miki shi"
Ko karfin kare kanta bata dashi sai da dukan yayi yawa ne kawu Labaran da ke kishingiɗe yana
sakace haƙorinshi ya fito ya ɗaga inna larai
"ke kar ki yi min kisa a gida"
Yana kai nan ya juya ya bar wurin ta cigaba da sababi da zage zage karshe ta tafi ta barta nan
yashe.
Yaran gidan bayan sun gama kwasar dariya kowa ya kama gabansa
Inna Asabe ma na girki tana zaginta da tsine mata don yau ta yi mata asarar tallar yamma
tunda yanzu ko ta fita ba su da tabbacin akwai mai sayan abin hannunta irin wannan suncewar
zani a kasuwa da tayi musu, ta fi mintuna goma a kwance a wurin kan da rarrafe ta shiga
akurkinta ta faɗi bisa taburma tana kuka kaman ranta zai fita.
Ko mintuna biyu bata yi da shiga ɗakin ba tana yashe a inda take ta soma jin hayaniya tamkar
ana yaƙi, idanunta sun kumbure ko iya buɗewa da kyau bata yi, bata san ya aka yi ba sai ji tayi
an janyota tamkar tsumma an fitar da ita, sama sama take jin mutane na ta hayaniya tana
hangar sanduna da makamai na tashi sama ana ikirarin kasheta kaman yadda ta kashe musu
ɗa matashi, bata san ashe rigimar har su kawu ya shafa ba don sun rantse in ba'a fita da ita ba
gidan gabaɗaya za su ƙona, tashin hankalin da bata taɓa shiga ba ta shiga a ranar, bata san ya
aka yi 'yan sanda suka iso wurin ba don ana ta janta tamkar kaya ko takarda Muryar kawu na
ihun kar su ƙona masa dukiya ita suke so don haka ga ta nan su kashe ta. Fusgar ta aka yi aka
wulla ta motar 'yan sanda suka ja suka yi ofishin su da ita...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*003*
Bayan tsawon lokacin da ba za ta iya cewa gashi ba ta ji sauƙar ruwan sanyi a kanta duk da ta
farka sai dai bata da kuzarin ɗaga ko da yatsar hannunta ne.
" In ba kema da ja wa kai ba ina ke ina cin maita don janyowa mutane bala'i ki mutu a ce ai ba
ma aikinmu ne yadda ya kamata. tashi my friend"
Ya ƙarasa yana kai mata kafa.
Laluɓe take har ta samu ta miƙe zaune gajimare ya rufe mata ido bata iya ganin komai.
Maƙogoronta da ke bushe ko miyau ba ta iya haɗiyewa sai kartar ta yake da kyar ta buɗe baki
ta ce
"R..ruwa..a don Allah"
Ruwan ya tura mata ta ɗauka ta afa a baki har kwarewa take sai da ta sha sossai cikinta ya
murɗa don dama babu komai ciki ai sai amai tana jin ɗan sandan na zaginta amma ba za ta iya
tsayarwa ba ya riga da ya zo, a lokacin idanunta sun washe tana gamawa ya tasa keyarta ta
kwashe ta share wurin cikin layi.
A lungun cell ɗin ta raɓe tana ta aikin riƙe ciki saboda yunwa, ɗaya dan sandar ya taso yana
ƙare mata kallo
"Ya dai?"
"Yunwa nake ji"
Murmushi yayi yana gyaɗa kai yana sake ƙarewa halittarta kallo Dukda rama ya yi mata yawa
ainun albarkatun jikinta na daidai shekarunta ba su ɓuya ba sam.
"Zan sayo miki abinci amma kin san gomnati ta hana aikin banza ko? Nima za ki rama min"
Sam bata wani fahimta don yunwa ba ta da hankali samm kai kawai ta gyaɗa ya fice chan sai
gashi da filate ya miƙa mata ta fusga ta shiga ci hannu baka hannu ƙwarya sai da ta fara koshi
tukuna ma ta fahimci ashe gari ya waye kenan a cell ta kwana gashi har ana batun ƙiran sallar
azahar tsabar rashin gata babu wanda ya neme ta, ta tabbatar ko shekara zata yi nan kawu ba
zuwa zai yi ba bare ya cire kuɗin shi yayi belinta don sun ce sai an ba su kuɗin mai za su sake
ta...
Bayan ta gama ta roƙi za tayi sallah basu hanata ba ta rama duk waenda aka bi ta. A nan ta
cigaba da zama ita daya har dab Magrib wani matashin ɗan sanda ne ya shigo yana dubanta
"Ya Sunanki?"
"Afeefah"
"ba ki da kowa ne da zai zo yayi belinki?"
Ta girgiza kai
"Ni marainiya ce kawu na kuma na san ba zai taɓa zuwa ba ko shekara zan yi"
'dan shiru yayi
"Afeefah za ki iya komawa gida da kan ki?"
Ta gyaɗa kai
"tashi ki tafi to zan biya kuɗin belin naki, bana so dare ya sake samunki a nan muna da
gurɓatattun 'yan sanda bare har kin bari kin ci abin hannun kopur DanJuma sai ya dawo, kuma
ba ni da ƙarfi ko ikon kare ki"
Hawaye ne suka cika kumburarrun idanunta ashe akwai masu zuciyar imani da tausayi a cikin
'yan sanda? Godiya tayi ta mishi har da kuka a lokacin da zata fita ta ce
"Menene sunanka?"
"Sa'adu. Sa'adu Rabi'u"
"Allah ya dube ka ya shiga cikin lamuranka ya dafa maka"
Amsawa yayi ta fice da sauri lunguna tayi ta bi a tsorace kar ma ta haɗu da kopur Danjuma har
ta isa gida.
"Uban wa yayi belinki?"
Kawu dake kofar gida ya daka mata tsawa
"Su...su suka sake ni"
Takalman shi ya wuwuro ya jefa mata
"shegiya natacciya dama shiyasa ake cewa mutum maye mana in ya cika naci, kin rantse sai
kin kasheni ko? To kafin nan sai na yi ajalinki marar anfani kawai"
Da gudu ta shiga gidan don ya miƙe ya biyo bayanta kaman zai faɗi.
Ɗakinshi ya shiga ya haɗo tarkacen da ya karɓo na kare kai daga sharrin Mayu yayi ɗakinta
dorinarshi ya samu ya rufeta da duka wai na hawan jinin da ta saka mishi jiya ta kusa ja mishi
asarar rai da dukiya babu wanda ya kula su duk ihu da neman agajinta sai da ya gaji ya kyaleta.
Ya sa aka kawo mishi garwashi ya turbune su da uban hayaƙi mai bala'in ƙauri bayan ya gama
ya tafi ya barta nan yana cigaba da sababi.
Bata san iya adadin lokutan da ta ɗauka a kwance cikin yanayin ba, tun tana kuka da hawaye
har suka ƙafe sai dai zuci na cigaba da zubar da kwalla cikin ƙunci da raɗaɗin da bata san ranar
tsayuwarshi ba, yunwa ne kaman zai yi ajalinta hakan ya sa ta dole ta lallaɓa ta fito, yadda garin
yayi shiru sossai za ka san cewa dare ya riga da ya tsala murhu ta isa akwai sauran gawayi ta
dibo ruwa tana layi ta ɗora, a wurin ta zube tana kallon kicin ɗin babu alamar an ajiye mata wani
abu da zata iya ci, busashen miyau da ya ƙafe a Bakinta ta lalaɓo da kyar ta Haɗiye.
Sai da ruwan ya tafasa ta juye hadari ne sossai a garin don har an fara iska da walkiya sai
dai dayake zuciyarta a kafe yake yasa babu tsoron komai cikin ranta ta shiga ta gasa jikinta
sossai ta fito, kicin ɗin ta koma da kyar ta samu wani kanzo ta ɗan bubbuga ta zuba ruwa yayi
laushi ta ɗauka ta nufi akurkinta tana da ɗan maggi da yaji da mai kaɗan ta saka a ciki ta ci bata
ma gama ci ba taji sauƙar ruwa kaman da bakin ƙwarya, ko da ta kwanta baccin sai ya ƙi zuwar
mata sai tunanin rasuwar yaron jiya take ko wani hali iyayenshi ke ciki? Tana kuma tambayar
kanta da gaske ita ɗin Mayya ce? Da ƙyar bacci da ya fi kowa iya sata ya lallaɓo ya sace ta...
Rayuwa ya ɗauki yi mata zafi a gidan fiye da baya saboda a yanzu tallar bata yi inna larai ta yi
mugun tsanarta don ta karya mata kasuwa hakan yasa ko abin da zata ci a girkin inna larai
gagararta yake, ba'a isa a aike ta ba haka zata dawo da hawaye saboda maganganun mutane
da ma yunkurin illata ta da wasu kan yi, bautar gidan duk ya dawo kanta yanzu har girki ita ke yi
musu su zo suyi rabo kuma a hanata don daga an sauƙe za'a aike ta kan ta dawo an raba in ta
tambaya su ce sun manta da ita, ita dai gata nan amma rayuwar baya yi mata daaɗi ko ta wani
ɓangare.
''Ina ma mutum na da zaɓi kan rayuwarsa! Ina ma a ce bawa ke da ikon rubuta ƙaddararsa! Da
ban zaɓi maraici ba. Duk bala'i na san ko da kowa zai guje ni su ɗin ba zasu taɓa guduna ba" a
hankali take furta hakan wani irin kewa da maraici na taso mata, har ƙasan ranta bata son
yadda ta zama tamkar mujiya a cikin tsuntsaye, bata son wannan suna na Annoba da yanzu
kowa ke ƙiran ta dashi... Kanta a duƙe ƙasa ruwan hawayen da bata rabo da su na sulmiyowa
cikin ruwan kunfar wanke-wanken da take yi wani irin zafin da zuciyarta ke yi kaman zata fito
daga madaukarta
"Wai zama kika yi kina maitar da kika saba na shanye kurwuwowin mutane ba za ki yi ki kawo
mini kwanuka in raba abinci ba?"
Inna larai ta watso mata kalaman cikin hantara.
sharɓe hawayenta ta yi, cikin mintunan da ba su wuce biyar ba ta kammala.
Tattara kwanukan ta yi ta kai gaban murhu ta ja jikinta gefe ta tsaya tamkar jiƙaƙƙiyar kaza da ta
rasa mafaka yayin ruwan sama.
"Ungo sayo min kuka da daddawa."
Kuɗin da ta wullo mata a wulaƙance ta sanya hannu ta ɗauka ta juya tana jefa singallin
kafafunta masu kama da zaren lipton saboda rama tayi waje, ko da ta dawo zaune ta tadda
zuri'ar gidan suna karyawa cikin natsuwa.
"Ga shi inna larai"
Fusga ta yi suka ci gaba da kai lomar zazzafan ɗumamen tuwon dake turiri ita da Inna Asabe
"Abinci...cina fa?"
Ta yi tambayar zuciyarta na rawa. Amsar da take tsoron ji ita ɗin dai ce ta ratsa kunnuwanta.
"Kin ga na manta da ke a rabo, sai ki jira na rana."
Wani irin raɗaɗi ne ya ziyarci idanunta tamkar wacce aka watsawa borkono. Ba ta sauya zani
ba ba kuma ta tunanin za ta sauya ɗin abu ne da ta riga ta sani a kullum idan har za a raba
abinci aka aike ta shi kenan rabonta ya faɗi ƙas.
Ita take kallo sai dai tuni zuciyarta da ƙwaƙwalwarta suka tafi nisan kiwo, hanjin cikinta jin shi
take kamar ana daddatsawa tsananin yunwar da ta kwana da ita. Ba ta da shi ba ta kuma da
wanda zai ba ta babu mai ɗigon tausayinta a gidan a cewarsu mayu sun fi cinye kurwan wanda
ya ji tausayinsu ko ya taimaka musu.
Sauƙar ruwan zafin da ta ji a fuskarta yasa ta sakin ƙarar azaba a firgice ta miƙe daga durƙuson
da ta yi a gabansu tana dirza fatar inda wani irin zafi ke ziyartar ta. A take ta ɗaile, daidai
lokacin inna larain take faɗar
"Wallahi kurwata kur! Maye sai dai ya ci kansa."
Baya ta matsa ta sake zubewa bisa gwiwoyinta hawaye na sake tsinke mata cikin shessheƙa ta
fara roƙon su taimake ta da abinci.
"Inna don Allah ko da loma biyu ne ku taimake ni da ita, cikina babu komai hanjina murɗa suke,
yunwa za ta kar ni."
Kamar dabba haka ta sa ƙafafu ta hamɓare ta ba tare da ta ko damu da raunin ƙunar da ke
jikinta ba.
"Ba za ki taɓa samun nasara a kaina ba, wuce ki fara shirin ɗaura mini abincin rana."
Jiki a saɓule ta miƙe ta nufi wurin murhu, a haka cikin raɗaɗin gangar jiki da zuci ta fara aikin.
Bata yi nisa a aikin ba suka gama karyawa suka kai kwanukan mawanki kowa ya nufi ɗakinsa
don hutawa. Ta rarrafa ta isa bigiren saboda ko ƙarfin miƙewa tsaye babu jikinta tsabar yunwar
dake dawainiya da rayuwarta.
Ɗan sauran wanda suka rage take kwarfewa tana afkawa a bakin salati, ta haɗe da tukunyar ta
kankare ƙasan tana ci tana zub da hawayen tausayin kanta da irin rayuwar da take. Ko kula
inna Larai dake mata gargaɗin kar ta yi mata lamba a tukunya bata yi ba. Ta miƙe ba don ta
ƙoshi ba sai don babu wani abin da zata sake samu ta ƙarasa ta kwalfi ruwa ta afawa cikinta. A
gindin randar ta raɓe cike da fatan sanyin ya taimaki zuciyarta wurin kashe wutar dake ruruwa a
cikinta har take neman kai ta ga kushewarta.
"Afeefah! Afeefah!!"
Sam bata san bacci ya sure ta a wurin ba sai da ta ji ana jijjiga ta tare da kiran sunanta.
"Lafiya kike bacci a nan?"
Idanunta da ba su da maraba da na mashaya saboda gajiya da jigata ta ware tana kallon mai
maganar da muryarta yayi kama da wacce ta sani da jimawa, a hankali sanyi ya shiga ratsa ta.
Sanyin farincikin sanya mace guda da ta rage mai ƙaunarta kaf faɗin duniya a idanunta, tashi ta
yi cikin azama da 'yar fara'a ta rungume ta.
"Afeefah....!"
Kiran sunanta da ta yi tare da fincikar da tayi mata daga rungumar tana ƙarewa fuskarta da ma
jikinta kallo ne ta ji tamkar ta sosa mata inda ke yi mata ƙaiƙayi. Dama me neman kuka ne aka
jefe shi da kashin shanu. "Wa ya yi miki wannan lahanin?" Ita dai ba baki sai kunne don haka ta
ci gaba da kukanta yayin da ta shiga rarrashinta itama hawayen take zubarwa. Da ƙyar Afeefah
ta yi shiru kan matar ta buɗe jakar hannunta ta fiddo biredin da ta yo mata tsaraba. Kamar
mayunwaciyar zakanya haka ta afka masa da ci ba ji ba gani har tana ƙwarewa, matar ta ɗibo
ruwa ta ba ta hawaye na gangaro mata, daidai lokacin da kawu ya fito shirye da alama kasuwa
za shi..
"Labaran ka ji tsoron Allah, wallahi ka kwana da sanin kai ma ba ka fi ƙarfin ƙaddara ba.
Rayuwa da kake yi da 'ya'yanka ƙarƙashin kulawarka ba wayonka ba ne ballantana dabararka,
a yau za ka iya faɗuwa ka mutu, shin za ka so a yi wa 'ya'yanka yadda kake mata?"
Kanwar mahaifiyarta ta jefa masa kalaman cikin jin haushin yanayin da ta zo ta iske Afeefar
Kallon banza ya watsa mata.
"Kina da gida ko Zainabu? Toh ki tarkata ta ku tafi tun kan mu yi ɓacin ɓacina kuma ki daina
haɗa yarana da wannan annobar... Ni ban haifi maye ko ɗaya ba, ban kuma shirya mutuwa ba.
Zaman ma da kika ga tana yi saboda ba ni da yadda zan yi ne, amma yanzu tun da ga ki Allah
ya raka taki gona...!"
Har ya nufi fita ya dawo ya sake kallon ta.
"Af! Idan ƙarshen saduwar kenan to ubangiji ya sa can ta fi miki nan."
Miƙewa tsaye ta yi a zuciye.
"Zan tafi da ita Labaran, dama rashin sani ne ya sa kaza ta kwana da yunwa a