Showing 93001 words to 96000 words out of 149666 words

Chapter 32 - Haihuwa Da Hanji

Unknown   

16 Mar 2026

4422

ta sunna a yanzu haka"

Afeefah ta mayar da kanta ƙasa hawaye na taruwa a idanunta sam bata san sun zo gangarta
ba sai jin mommy tayi ta riƙe hannunta tana sake ƙara fashewa da kuka mai tsuma rai, Abeeha
ma bata yi shiru ba ta kara da labarin irin yadda ta taimakesu akan Saleem.

"Don Allah ki yafe mana Afeefah, haƙiƙa ba mu da bakin neman yafiyarki saboda mun aikata
miki ba daidai ba, mun kasa duba kasantuwarki mace mun kasa yarda cewa Allah ke komai a
sadda ya so na bi dare na raba ki da Saleem karfi da yafi na aura mishi wacce nake ganin ta fi
cancanta ashe ban sani ba ƙabari na haƙa mana... Haƙiƙa na so na ganki ba tare da aure ba
nayi adu'ar Allah ya bayyana mini ke ko ta wani hali in nemi yafiyarki in kuma gyara kuskurena
ashe ke kam Allah ya dubeki ya Musanya miki da alkhairinki... Don Allah ki yafe mana ki yafe
mana Afeefah!"

Sossai duk suke kuka suna neman yafiyarta sai ta nemi rudewa Dukda tayi mamaki amma ta
sani duniya aka ce makaranta.
"Mommy ku daina neman yafiyata wlh tun kafin na bar gidan duk na yafe muku Yaya Saleem ya
wuce yadda kuke zato a wuri na. Ban riƙe ku a zuciyata ba ku daina wannan kukan don Allah".

Samha ta fi kowa bata haƙuri sai Mommy, duk ta nuna ita komai ya wuce a wurinta suka koma
gefe suna ta kallonta ko motsi tayi burgesu take, basu taɓa sanin haka take ba sai a yanzu yinin
da suka yi a ranar suka kara sanin wacece ita kunyar duniya duk ya rufesu na tunanin duk irin
wulakancin da suka yi mata, lallai da gaske ne da aka ce mai haƙuri shi yake dafa dutse har ma
ya sha romonta.

Mommy ta tabbatar Saleem bai san da wannan labarin ba, gab za su tafi ta kira shi a waya
akan ya zo ciki duk jama'ar sun watse a babban parlorn sai Afeefah dake zaune tana duba abu
a waya mommyn ta fito daga ɗaki ganinta yasa tace
"Yauwa ashe kina nan dama ke zan je dubawa kitchen. Yanzu Saleem zai shigo ku gaisa..."

Gabanta ne ya faɗi rabon da su hadu kusan watanni bakwai zuwa takwas kenan, ya rabu da ita
cikin kuna da zafin zuciya tare da hawaye a yanzu zai haɗu da ita matsayin matar aure, matar
ma ta abokinshi me zata ce mishi? Ta san akwai laifin mahaifiyarshi a rabuwarsu amma ta san
dole zai ji zafin samun wannan labari, anya ma zai yi farin ciki da ganinta? Bata gama tunanin
ba ta ji sallamarshi gabanta ya sake faɗuwa ta miƙe tsaye sai suka haɗa idanu a lokacin da take
amsawa da iyaka lips ɗinta.

"A...Afeefah? Ke..ke ce nake gani? Afeefah ba gizo idanuna suke min ba kece tsaye a gabana?
Ta yaya kika zo gidan nan? Ina kika shiga Afeefah? Ina kika shiga...?"
A ruɗe yake maganan idanunshi na cika da kwallah kaman yadda nata ya cika fal da hawayen
ganinshi.

"Ya Saleem...!"
Ta faɗa a sanyaye sai ta kama hawaye.
Sake matsowa yayi kaman zai taɓa ta tayi saurin matsawa baya sossai tana girgiza mishi kai.

"Ka gafarceni Ya Saleem yanzu da baya ba ɗaya bane..."
"Afeefah na san akan mahaifiyata ne wlh yanzu duk sun yi nadamar abin da suka aikata miki,
na tabbatar za kuma su nemi yafiyarki don Kullum adu'arsu shine mu ganki mu nemi
yafiyarki...ko babu komai a yanzu za mu cika burinmu za mu cika alkawarinmu na mallakar
juna..."
Daidai lokacin Rayyan ya sanyo kai parlorn he just stood there fuskarshi kadaran-hadaran yana
kallonsu.

Hawaye take yi sossai
"Lokaci ya riga ya ƙure ya Saleem, kayi hakuri Allah bai nufa na zama rabonka ba. Ni din yanzu
matar aure ce."

Jikinshi yayi wani irin sanyi wani tashin hankali da damuwa na lallaɓo wa ya rufe shi murya na
shaking yake furta
"A..a..aure Afeefah? Aure kika yi? Da waye? Me..me yasa?"

Idanunta ne suka shiga cikin na Rayyan da sauri ta kawar heartbreat ɗinta na kara gudu ganin
kallon da yake mata.

"Ka sa a ranka ƙaddara ce ta zo haka, amma ni matar aure ce don Allah ka ajiye zancen alaƙar
da ta riga ta wuce Ya Saleem"
Daga haka tayi saurin wucewa sashensu ta barshi kanshi a matukar kulle, idan bai ce ya
matuƙar kaɗuwa da wannan zance ba yayi ƙarya zuciyarshi raɗaɗi ya shiga mishi, saboda
rauninshi tuni hawaye suka shiga zubo mishi haƙiƙa ya so Afeefah kaman ranshi har gobe yana
ƙaunarta amma gashi ƙaddarar su ya zaɓar musu rabuwa aure tayi a sadda yana chan ya rasa
hankalinshi, me yasa bata yi haƙuri ba? Meyasa bata jira ba? Me yasa yayi jinkiri? Tun da ya
dawo hayyacinshi a neman ta yake ko Allah zai sa ya ganta ashe ita kam tana chan tare da
mijinta tana rayuwa mai kyau don ko skin ɗinta ya bayyana hakan.

Mommy ce ta fito ganin yanayin da yake ciki ta kalli Rayyan dake tsaye har lokacin a bakin kofa
hannunshi harde a kirjinshi wanda da alama Saleem ɗin bai kula da wanzuwar shi ba tayi saurin
kama Saleem ɗin ta zaunar taje ta kawo mishi ruwa bai karɓa ba sai ma maganganu da ya fara

"Mommy ta ya kika ga Afeefah? Me ya kawo ta gidan nan? Mommy wai da gaske Afeefah aure
tayi? Aure tayi? A yanzu haka Afeefah ta haramta mini?"
Mommy ta kalli Rayyan ta mayar da idanunta kan Saleem.

"Saleem Afeefah ta yi aure laifina ne duka, laifina ne ta subuce maka ka yafemin ciwon da nake
sakawa zuciyarka ka ɗauki dangana da haƙuri. A gidan nan muka samu Afeefah tana kuma
auren abokinka ne Rayyan..."
Da ƙarfin gaske ya miƙe har yana Buge ruwan hannunta ya faɗi ƙasa
"Rayyan?? Mommy all this while Rayyan na tare da Afeefah? Har ma ya aureta? Rayyan dai
Rayyan Moh'd Khamis??"

Gabaɗaya wani duhu ne ya taso ya rufe mishi gani tsabar wani irin bacin rai da ya zo mishi
juyawa yayi zai fita yaje ya samu Rayyan ɗin sai suka haɗa idanu nan ya nufe shi ya tsaya a
gabanshi.

"Rayyan da gaske Afeefah ka aura?"

Shi karan kanshi ya san yayi mugun ƙoƙari a sadda ya buɗi baki ya furta

"Saleem Afeefah matata ce idan har ka san darajar aure da kuma martabarsa za ka kiyaye irin
kalmanka a kan matata... Ƙaddara ta riga ta raba ku ta bani ita a lokacin da ban yi zato ko
tsammani ba don haka don't Look at me with those eyes dake nuna kaman I betrayed you or
something like that, you should questioned yourself nd your family not me..."
Yana kai nan ya wuce don har ga Allah bai san dalilin da yasa yake ji kaman zai kama da wuta
ba, mommy ya kalla har kaman zai wuce ya tsayar da idanunshi kanta ba zai iya yi mata
magana kai tsaye ba ba kuma don komai ba sai don uwa ce ya juyo ya kalli Saleem dake
kallonshi rai a tsananin ɓace yace in a respectful manner.

"Rasuwa aka yi mana ko ba rasuwa ba muna da darajar da ba za'a tako har nan a ci mana
mutunci ba Saleem, idan ba zaka taya mu baƙin ciki da jajen rasa wani sashe na bangonmu ba
za ka iya zama da kai da familyn ka a gida. Mun gode"
Daga haka ya nufi sashensu ya bar su nan tsaye calmly kaman ranshi ba suya yake ba.

Wani irin duka Saleem ya kaiwa bangon wurin yana yin baya tare da zuba yatsun shi cikin
gashin kanshi kaman zai fashe haka yake ji, su Samha ne duk suka fito a tare da Abeeha jin
salatin mommy.

Ganin yanayin da suke ciki suka shiga tambayar me ya faru? Menene?
Mommy tana zubar da hawaye tace
"Na sake wani kuskuren, da na san hakan zai kasance Saleem da ban nemi ku gaisa da
Afeefah ba! Na zaci zaka yi farin cikin ganinta idan ka ji kuma tana da aure zaka taya ta murna
da Adu'a ka karɓi kaddara amma me kayin nan? Abokinka ne fa Rayyan abokin da ya zama
ɗan uwa ya kuma tsaya mana duka a sadda muke neman tagayyara. Rasuwa fa mahaifiyarshi
tayi ko lafiya bai samu ba me kake yin nan?"

"Rayyan ya ci amanata mommy, ashe ya san inda Afeefah take ya zaɓi ya ɓoye min? Ashe
aurenta yake shirin yi ko da na matsa ya nemo min ita a sadda ba ni da daman hakan saboda
kalamanki ya san inda take ya dinga zurma ni akan ya neme ta ya rasa? Meyasa tun farko bai
ce min sonta yake in sakawa zuciyata hakan ba? Idan ba da wata manufa yayi hakan ba
Meyasa ina zuwa gidan nan bai taɓa nuna min tana nan ko ya bari na ganta ba?"

Abeeha da ranta yayi mugun ɓaci tace
"Ya Saleem baka kyauta ba sam...! Ban zaci ko Ya Rayyan amanarka ya ci zaka iya aikata
hakan kuma ka jefe shi da irin kalaman nan ba. kar hankalinka ya gushe mana... Toh wallahi
Yaya Rayyan ya auri Afeefah ne bisa umurnin Mammi, ya karɓi auren cike da tunanin mai zaka

ɗauki hakan a duk sadda ka dawo hayyacinka... Idan ma ya faɗa maka a lokacin kake nemanta
cewa coincidently sun haɗu a sadda ta taimaki Mammi Mammi ma ta taimaka mata ta kawo ta
gidan nan me zaka yi? Kar ka manta a sannan Allah ya isan mahaifiyarka ke kanka muddin ka
mata magana? Idan da yana da mugun nufi kanka da ba zai ba da gudummawar dinga kawo ka
gidan nan kana ci da sha daga ayoyin Allah ba har ka dawo cikin hayyacinka...idan da yana da
wata manufa ta daban da ba zai bari ku kasance tare da ita a zaman makonkin nan ba don
kaima ka san zai iya kaita ko ma inane... Wallahi ko ni bayan labarin da Afeefah ta bamu na ji
har abada ban bata goyon bayan aurenka ba, Mammi ta zaɓa mata miji kuma ta karɓa hannu
bibbiyu kuma take ibadar aure... Ko da Yaya Rayyan baya sonta a baya bai kyamaceta ba
Dukda ya san labarinta kaman yadda kaima baka kyamaceta ba bambancin kawai mu da
mahsifiyarmu muna sonta kuma muna so rayuwarta ta inganta ashe idan baka godewa Ya
Rayyan ba ba zaka ga baƙin shi ba. Ka je kayi nazarin kalamaina kan ka sake yanke kowani irin
hukunci ne"

Tana kai nan ta juya ta koma ciki cike da jin haushinsu dukkansu, tunanin ta ya tsaya akan ya
Rayyan da banzar zuciyarshi Allah ya sa kar ya sauke akan Afeefar.

Tana zaune bakin gado ta toshe bakinta da gyalen ta tana kuka kawai taji an turo kofan an
shigo, da sauri ta ɗaga idanunta dake zub da hawaye sai suka shige cikin nashi da ya jirkice,
wani irin kallo ya mata da ya sa tayi saurin mayar da idanunta ƙasa tana Miƙewa tsaye.

"Kin raina ni ko? Ni za ki wulaƙanta??"
A hankali yayi maganan. Sai ta ɗago tana cewa

"Kayi haƙuri ban san zai shigo ba, ban san mahaifiyarshi ta kira shi ba da na nemi izini..."

"Shuttt up!! Just shut up Afeefahh"
Ya daka mata tsawa har saida ta tsorata tayi baya baya zata faɗi ta dafe jikin gado kirjinta na
sama da ƙasa. Yau ne karo na farko da taji sunanta a bakinshi Dukda kaɗuwar da tayi hakan
bai hana sunan sake amsa kuwwa cikin kunnuwanta ba da muryarshi.

Shiru yayi yana sauke numfashi idanunshi a tsaye a kanta ya ce a zafafe
"Ko babyn roba na aura, ko 'yar tsana ce ta amsa sunan matar Rayyan Moh'd Khamis wallahi
billahi na fi ƙarfin ta wulaƙanta min aure... A gabana kike cewa aurena dake ƙaddara ce??"

"Ka yi ha..kuri ba haka..."
Juyawa kawai yayi ya fice yana buga kofar da karfin gaske sai da ta sake razana.

"Na shiga uku!"
Ta ambata tana zama bakin gadon.

🖤Gureenjoh🖤

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*Yauwa. Ga Page ɗin ku na yau, it's monday already! ba ni da tabbacin zama available through
out.*

*42*

Zaune kawai yake a kan couch bayanshi na jingine da jikin kujerar idanunshi a lumshe, tun da
ya dawo daga Sallar isha haka yake.
Wani iri yake ji lokaci lokaci ya kan buɗe idanu ya kalli kofan ko za ta shigo amma shiru babu ita
ba alamunta, sai wuraren sha biyu ya miƙe ya ɗan yi shirye-shiryen shi na bacci ya koma gado
ya kwanta sai ya tsinci kanshi da kallon wurin da take kwanciya a kwana biyun yadda inuwarta
ke yi, irin rikicewar da tayi ta rungumeshi a daren jiya hannayenta na yawo a cikin sumanshi da
bayan wuyanshi ya tabbatar da ana lafiya ne ba za ta taɓa iya hakan ba, sai yaji emptiness da
ya rasa na menene, da kyar yayi bacci bayan ya yi overdosing magungunanshi.

Ta ɓangaren ta tana so taje ɗakin amma tana tsoro, kila bai huce ba kar taje kuma ya hau ta da
faɗa ko ya make ta, haka ta shirya ta kwanta a kan gadonta sai ta dinga tunanin moment ɗinsu
na jiya sautin numfashinshi na dawo mata har heart ɗinta na racing a haka bacci ya ɗauketa.

Karfe goma na safen Washegari ta fito a shirye cikin half boubou da skirt na lace cream colour
da mix of dark pink yayi mata kyau sossai ta yafa pink gyale bayan dan kunne da wani zoben
gwal dake yatsanta bata wani saka acessories ba ta fito zuwa babban kitchen ta karbi abincin
su ta kai ta shirya a dining kan ta koma wurinsu jannah da Uncle ya kira mijinta ya zo ya
dauƙeta yau duk su mama ma yau za su koma gidajensu.

Shi kam tun da ya dawo Sallar asuba bacci bai ɗauke shi ba yana zaune kan kujera inda kaman
nan ne wurin zamanshi a ɗakin, as usual idanunshi a rufe ruf bai motsa ba har sai da Abeeha ta
kira shi a waya akan su Mama za su koma gidajensu ya miƙe ya fito suka sake mishi gaisuwa
da ban haƙuri kan suka tafi bayan sun raka su har waje, ya kalleta amma bai tsawalla kallon ba

don haushin ta har lokacin yake ji barin ma da ya kalli yadda idanunta suka zama saboda kukan
da tayi jiya Dukda ba kowa zai lura ba amma shi with a single gaze ya fahimci lids ɗin are
swelled up a little.

Bai koma ciki ba motar Sulaiman ya shigo gidan sai suka isa kan kujerun da aka shirya don
hutawa a chan gefen gidan suka zauna.
"Ya dai? Na ga kaman ranka a ɓace sossai?"
Sulaiman yayi tambayar don a hankali Sulaiman ɗin yayi mugun karantar shi har ma ya zama
kaman Saleem a wurinshi ɗan zaman da suka yi daga aurenshi zuwa yanzu rasuwar Mammi.

"Hakane am just worried sick about one or two things."
Sulaiman ya gyara zama
"Toh fa, menene kuma?"
Nan ya bashi labarin duk abin da ya faru Sulaiman sai yayi murmushi
"Are you jealous?"
"Menene hakan?"
Yayi tambayar kaman bai san me ake nufi da kishi ba.

"Rayyan kana kishin Afeefah ne sossai kayi adu'ar sassaucin zafin kishi, anan dai zan baka laifi
Saleem ko da bai auri Afeefah ba kaman Yaya yake a wurinta sannan Saleem yana da fahimta
am very sure bai san reasons naka bane yasa ranshi ya ɓaci, shima fa mutum ne kaman kai
yana da zuciya a kirji, your words are harsh gaskiya kenan.."

Ya gyaɗa kai
"I know, tun jiyan i wanted to call him amma sai na bari ya huce tukuna. I just lost control tunda
ta furta wai aurena kaddara ne kalaman sun min zafi"

Dariya Sulaiman ya fara
"Kana wasa da So Surgeon General Ryan Khamis, kuma fa babu wani abin zafi a maganan nan
kishi ne kawai irin naka... Ai komai ma mukaddari ne daga Allah ta wani mawaki yace Nufin
Allah ne! Haɗin Allah ne ko da basa so su gani sai anyi! Ka ga kenan dole da kaddara a komai.
I'am advicing kaje ka samu Saleem ku yi resolving issue ɗin nan"

"Kai! ka fa dameni da zancen kishin nan idan ma kishin ne ai ban yi laifi ba a gaban ka na cire
kuɗina na biya sadaki!"
Yayi maganan da iyakan gaskiyarshi yana sake kame fuska Sulaiman yana ta dariya.

Basu jima ba ya wuce, shima ya shiga ya zari key bai ko bi ta kan abin kari ba ya fice daga
gidan kai tsaye gidan su Saleem ɗin ya tafi, bai shiga ciki ba ya kirashi a waya akan yana waje
mintuna kaɗan sai ga Saleem ɗin ya zo ya buɗe kofan motar ya shiga ya zauna ba tare da ya
ce komai ba.

"Ka tashi lafiya?"
Rayyan ɗin ya faɗa, bai jira amsar Saleem ba ya ɗora da.

"Na zo ne in baka haƙuri akan abin da ya faru tsakaninmu we are not perfect in everything
sannan a zaman tare dole watarana a saɓa. A koyaushe kai ke haƙuri da ni I really respect and
appreciate you Saleem kuma ka fi karfin duk abinda kake zato a gareni! Saleem...Billahi ban
ɓoye maka wanzuwar Afeefah a gidanmu saboda son zuciya ko wata soyayya ba don har
yanzu ban sani ba shin ina sonta ko ba na sonta na dai san ban tsane ta ba"
Ya ɗan yi shiru kadan kan ya cigaba
"A lokacin da muke waya da kai akan Mommy ta kore ta na ganta amma ban zaci saboda kora
ne take tsaye a kan titi ba, jin irin damuwar da ka shiga ya sa nayi deciding in koma in ɗauko ta
kafin ka samu masalaha da mahaifiyarka, ko da na koma ban sameta ba a sannan aka kira ni
ba'a ga Mammi ba cikin damuwar rashin ganinta na tafi asibiti ka san halina farin sani damuwa
na ba komai bane illa kar a samu wasu su cuceta ko su zalunce ta sanin bata san gari ba. ko da
na isa asibitin sai na samu ashe ita ce ta taimaki Mammi, from there Mammi ta fara ƙaunarta
har ta mayar da ita gida ba tare da na ce musu komai akan labarinta ba Dukda na san Mammi
da su Abeeha amma ba zan so ta samu matsala a gidan yadda ta samu a naku ba, nayi tunanin
faɗa maka sau ba adadi ina tsoron saka ka cikin wani damuwar don na san in har ka san inda
take ba lallai ka cigaba da yiwa mahaifiyarka biyayya ba, zai iya zama ka saɓa umarnin ta
saboda mace ko kuma shaidan ya ja ka ga fushintan ta hanyar yarinyar, na bari akan daga
baya idan kayi settling komai sai na faɗa maka. Unfortunately abun nan ya zo ya faru
tsakaninka da ex wife ɗin ka da i even called her name to your ears ka nuna baka santa ba
kana da mata..."
Daga nan ya bashi labarin duk yadda aka ɗaura aurensu da Afeefah.

"Na karɓi auren ne saboda Mammi Dukda ta rokeni ya zama saboda Allah zan yi wa Afeefah
komai ko da bata nan zata samu peace of mind na cewa ta barta inda ba zata wulaƙanta ba, na
san Afeefah ce tayi adu'o'in duk da kake using

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login