Showing 21001 words to 24000 words out of 149666 words

Chapter 8 - Haihuwa Da Hanji

Unknown   

16 Mar 2026

4850

zan nemi izininku kafin aiwatar da abin da yake daidai?
Duk cikinku akwai wacce ta isa ta hanata zama a gidan nan ne?"
Ya daka musu tsawa Ranshi ya kai ƙololuwar ɓaci duk mommy ce ta ba su wannan ƙofa amma
ya zai yi?

Gaban mommyn ya koma ya kama hannunta idanunshi kaman garwashi don saura kiris ya fara
yi mata kuka a yadda yake jin zuciyarshi ya ce
"Don girman Allah mommy kar ki koreta, ba zan iya bari ta tafi ba mommy in ta fita a gidan nan
ina za ta je? Musulma ce fa 'yar uwarmu kuma mace, ko don aikina na kare lafiyar al'umma
mommy ba zan iya tura Afeefah waje ba, Don Allah mommy ba don ni ba ki sake nazari akan
hukuncin ki kar ki saka ni yin abin da zai yi hunting ɗina for life please mommy"

Ganin zai kai gwiwar shi ƙasa yana cigaba da roƙon ta ya sa ta riƙe hannunshi suka koma
zaune, wuri guda ta tsurawa idanu sama da mintuna biyu ta sake kallonshi duk ya marairaice
yana roƙonta, Salim a yaranta yana da haƙuri yana kuma da kawaici don da wuya ya roƙe ta
abu ko ya tambayeta ko da kuwa yana matuƙar bukata ko da kuwa buƙatar kuɗi ne, yana
tausayinta ƙwarai gani yake har yanzu bata huta da ɗawainiya ba alhali, gidan gadon su ma
'yan haya ne ciki bai san ya suke kashe kudin ba a haka shi yake daukar ɗawainiyar karatun
ƙannenshi da cin su, tufafin su da ma sauran hidima na rashin lafiya bai taɓa gazawa ba tun da
ya riƙe ƙasa to Meyasa za ta kasa yi mishi wannan alfarma guda? Amma kuma idan yarinyar ta
kashe mata shi fa? Numfashi mai matuƙar nauyi ta sauƙe ta ji ana cewa Mayu sun fi cinye
kurwan wanda ya taimaka musu ya ji tausayinsu kenan muddin yarinyar za ta zauna gidan sai
ta cire wa salim tausayinta? Amma ta yaya?

Ta sake jan ajiyar zuciya cikin gamsuwa da shawarar zuciyarta
"Shikenan Salim na amince ta zauna amma fa ina da sharuɗɗa, sharrudan da zan gindaya
maka wanda matuƙar ka tsallake Allah ya isa ban yafe maka ba"

A firgice yake kallonta, zuciyarshi kaman zai fito waje jikinshi har yana wani rawa don ba ya
wasa da Abin da ya shafe ta, me yayi zafi da Allah ya isa? Da kyar ya iya buɗe bakinshi da yayi
masa nauyi ya furta
"Allah ya isa mommy? Ni??"

Ta gyaɗa kai cikin alamun tabbatarwa tana kawar da idanunta daga kallonshi kar ma ya bata
tausayi kuma ta san muddin ya amince ba zai taɓa tsallakewa umarnin ta ba.
"Sharuɗɗan su ne babu ruwanka da abin da ya shafe ta, za ta zauna zan bata abinci sau uku
kaman kowa, za ta yi aikin da ya kamata a ce kowacce mace na yi saidai duk wani abu da ka
ga na yanke a kanta babu ruwanka, do not question me a kan duk abin da ya shafe ta i repeat!
Magana ta fatar baki tsakanin ku in har ya wuce minti ɗaya ban yafe maka ba, ni zan duba in ga
cancantar saka ta makaranta ko akasin hakan idan zaman ba na ɗore bane dole za ta bar
gidannan ka kuma yanke kowace alaqa tsakanin ku, ko da ko sannu ne"

Ya yi jimmm kanshi ƙasa duk ya damu kan ya sauƙe numfashi
"Shikenan mommy in shaa Allahu zan kiyaye umarnin ki"
Yana kai nan ya miƙe ya bar musu parlorn Ranshi na ƙuna, da yana da mata babu abin da zai
hana shi riƙe Afeefah tamkar 'yar sarki ya ba ta ingantacciyar rayuwa, a yanzu ma bai fidda
tsammani ba ya amincewa mommy ne da tunanin with time za ta sassauto daga kudurinta.

Tuni suka cika parlorn da hayaniya bayan barin shi suna uzzurawa mommyn akan me yasa ta
amince da zaman yarinyar gidan?
"ku yi shiru ku bar ni da shi, ai in bata ga wurin zama ba da kanta za ta fitar da kanta daga
gidan ba sai wani ya kore ta ba."
Ta miƙe ta nufi ɗakin Samha tana jin abin da zuciyarta ke gayamata daidai ne, duk suka rufa
mata baya wane sarauniya da fadawarta.
Suka sameta zaune inda take tun bayan idar da Sallar ta idanunta suna zube a farantin abincin
da ko loma uku bata yi ba saboda tunani da ya ci karfin kwakwalwanta, tsoro ne sossai da
fargaba suka danne yunwar da take ji don rabonta da abinci tun da suka karya da Baaba da
safen a asibiti.

"Ya ma Sunanki?"
Mommyn ta tambaya tana sake ƙare mata kallo.
"Afeefah" ta amsa a hankali.
"Ban san wani kalar tsafin kika yi wa Saleem ba da har karo na farko ya zaɓi bijirewa umarni na
a kanki, amma bari mu ga ko ke kin san hallaci? Zan ja miki federal warning akan yarana don ni
karan kaina ban san abin da zan iya aikatawa ba a kansu, hawainiyarki ta kiyayi ramata idan
kina cin ƙasa to fa ki kiyayi na shuri wallahi ko da wasa 'ya'ya na suka yi ko da ciwon kai ne
hmmmm"

Ta kara hmm ɗin da wani irin siga na razanarwa,
"ana magana ba za ki amsa ba?"
Sadiqa tayi maganan tana hankada ta da kafar ta
A ɗan razane ta gyaɗa kai.
"Tashi in kai ki inda za ki zauna, ki ɗauki farantin nan don daga yau a ciki za'a na baki abinci har
Allah ya raba mu da ke, kuma ba ki isa a saka miki abinci ki bar mana ba don a nan ba ma
almubazzaranci da gumi muke nema don haka dole duk abin da aka saka miki haka za ki cinye.
Shara, mopping da wanke-wanke su ne aikinki. Am I clear?"

Sameera tace
"Kai mommy ke ma ina wannan ina jin turanci? aka ce kin fahimta?"
"Eh na fahimta"
Ta amsa cikin rawar murya.
"Tashi mana ni ki bar min ɗaki, ko za mu tsaya muna jiran ki ne?"
Dole ta miƙe da sauri ta ɗauki kayanta da plates ɗin ta bi bayansu, ta kofan baya suka fita suka
miƙa har Boys quaters jin hayaniya da hira haɗe da dariya kuma Muryar maza ya sa ta sake
tsorata, isan su varender ɗin Hajiya ta shiga buga cikin aihinin main building ɗin ɗaya daga cikin

su ne ya leƙo ganinta ya sa ya koma da gudu ya ƙira sauran suka fito su uku. Ba manya bane
chan matasa ne duka masu jini a jika da fafutukar neman halal, Ishaq shi ne ke musu wanki da
guga sai iliya da shi ne driver sai mudi mai gadi, ganin duk maza ya sake tsorata Afeefah me
hajiyar take nufi? A sama ta ji muryarta tana cewa

"ke! Ga ɗakin ki nan"
Tq nuna mata wani single room dake kan varender ɗin. Da gaske a waennan garadan za ta
haɗa ta, ganin yadda suke kallonta kaman kura ya ga nama ya sa hawaye ɓalle mata a take
tana ji hajiyar na cewa
"Mudi wannan itace mai wanke-wanke da share share za ta zauna a ɗakin nan kar in ji kar in
gani"
"To! To hajjaju in shaa Allah za mu kiyaye"
Suka juya suka tafi suka barta nan tsaye kyam.

"Sannu kyakyawa"
Bata tanka ba sai shige wa ɗakin da aka kira da nata da tayi da gudu ta datse kofan tare da
zamewa a jikin kofan tana fashewa da kuka sossai.

Dariya suka sheke da shi don tayi mugun basu dariya suna shiga ɗaki kuma suka fara gulman
kyaunta, kaman daga sama suka ga an turo kofa da ƙarfin gaske duk razana suka yi sai kuma a
take suka wani irin zubewa ƙasan ganin Saleem riƙe da bindiga muraran, fuskan nan yayi Red
babu wanda zai iya cewa ya taɓa ganinshi cikin wannan yanayin a take jikinsu ya tsume cikinsu
ya shiga ba da ƙarar tsoro suna tunanin me suka yi?

Iliya ke ta maimaita
"Yau mun shiga uku mun lalace allurar ce wallahi ta tashi a kanmu ya Allah ga mu gareka.."
Kuuuuu haka kowa cikinshi ke ba da sauti ganin ya sake haɗe fuskan nan tamau, ya samu
hannun kujera ya zauna tare da ɗora kafan shi daya kan kujerar ya sa bindigar ya ɗan sosa
goshinshi yadda za su sake gani da kyau su tabbatar, ya sauƙar yayi kooking ta ba da sauti tuni
suka maƙale juna suna kakkarwa kaman kadangarun da suka faɗa wuta sai salati suke.

Ya ce cikin dakakkiyar murya
"Menene wannan a hannu na?"
Mudi da yake jin yana shiru saleem zai iya fashe kanshi don an sha ce musu idan allurar sojojin
ta tashi bata da hankali ana ɓata wa sojan rai sai kisa yayi carab ya ce murya na rawa

"Abin kashe mutane"
"sunanta na tambaya!!"
Ya faɗa a hasale da kuma gaske a mugun hasalen yake, Ishaq yayi saurin cewa
"Sunanta bindiga wallahi bindiga sunanta"
"Kun dai san ni soja ne, kuma ina da lasisin harbata ko?"
Sai kai suke gyaɗawa kaman kadangaru
"Buɗe baki za kuyi ku amsa ni malamai"
Tuni suka cika ɗakin da

"Eh, tabbas! Haƙiƙa hakane!"
"To ku buɗe kunnuwanku da kyau ku ji ni, wannan yarinya da Hajiya ta kawo ta nan ko kallon
da ya wuce na seconds kuka yi mata bare magana ta fatar baki ba tare da kwakwaran dalili
baaaa..."

Ya miƙe tsaye ya isa inda suke ya ɗodɗora bindigar kan kowannen su yace da ƙarfi
"Toh tabbas sai ya kwana a lahira!!! Ina Fatan kuna ji na da kyau??"
Suna zare numfarfashin tsoro da kaɗuwa suke amsawa a tare
"Mun gane wallahi mun gane, ba za mu kuskure ba ranka ya dade yallabai"
Ya ɗan matsa baya.
"Kar ku ga kaman ban cika zama ba, gidannan ko ta wani ɓangare ina da abin ɗaukar video a
ɓoye waninku ya gwada saɓa doka ta ya gani..."

Yana kai nan ya juya ya fice bayan ya sake nunnuna musu bindigar a Goshi ai da gudu iliya da
mudi suka fara rige-rigen isa bayi sai zawo...! Ko magana cikinsu babu wanda ya sake yi a haka
baccin dole ya kwashe su dukunkukune da juna.

Ya ɗan jima tsaye yana kallon kofan ɗakin nata bayan fitanshi kan ya wuce, yana tsaye a
balcony ɗin shi na sama ya ga isar mommy da ita wurin abin ya matuƙar damun shi, ta ya
mommy za ta haɗa mace da maza har uku waenda ba muharammanta ba? Tsoro ne ya
mamaye zuciyarshi ba zama yake ba yana matukar tsoron wani abu ya sameta ba zai iya
yafewa kanshi ba, wayanshi ya fitar ya kira Rayyan.

Ringing na ƙarshe ya ɗaga da sallama
"Ya aka yi ne man?"
"I need your advice, ni ne na kawo lu'u lu'u mai tsananin daraja da ƙima sai na rasa inda zan
killace hakan ya sa dole na ajiye a inda ba ni da tabbacin za ta samu tsaro da kular da ta dace
da darajar ta, ban gama nazari ba sai na kyalla ido na hango wasu kananun ɓarayi da basu kai
ko da shakar numfashi ɗaya ba suna zagaye wannan lu'u lu'u da kallon da ban gamsu ba, idan
ba zan iya tafiya da wannan lu'u lu'u ba kuma dole zan tafi wani mataki kake ga ya kamata in
ɗauka?"

Ryan ya ɗan yi shiru na seconds kan ya ce cikin dakakkiyar voice ɗin shi
"Dukkan yanki ba'a rasa ɓarayi kuma ko wani ɓarawo yana da uban gida, idan har kai ne uban
gidan wannan ɓarayi kana da dama da ikon gargaɗi mai zafi irin na asalin maza ba mata ba, ina
mai tabbatar maka daga zarar sun tsorata da gargadin ka ko kallon hanyar da wannan tagulla
take ba za su sake ba"

Lumshe ido yayi
"Na gode"
Ryan ya kashe wayanshi.
Ya ɗan sake nazari kan ya saki murmushi ya juya ya je ya ɗauko bindigar ya wuce sashen.
Dariya kaɗan yayi tuna yadda suke ta zazzaro idanu suka jike jagwaf da gumin tsoro...

🖤Gureenjoh🖤

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Don Allah ku yi haƙuri da wannan yau ɗin nan ban zauna ba wallahi*

*012*

Ta ɓangaren Afeefah anan bakin ƙofa ta ci kukanta har bacci ya sure ta ba tare da ta sani ba,
mummunar mafarki da tayi da Aunty zee ne ya sakata farkawa a razane, fitsari ne kaman zai
zube mata hakan ya sa tayi single kofa guda ɗaya da ta gani a ɗakin sai ta samu madaidaicin
bayi ne, bayan ta gama abinda take ta fito ne ta fara bin ɗakin da kallon tsanaki don wutar a
kunne tarrr kaman rana.

Matsakaicin ɗaki ne a lailaye yake da farin tiles, fanka da bulbs duk suna aiki daga chan dungu
'yar ƙaramar katifa ce da babu ko shimfidi a kai, sai agogon bango da ɗakin ke dashi, time ta
kalla ƙarfe biyu na dare har ma da mintuna ashirin da uku, juyawa tayi ta koma bayin ta yo
alwala ta zo ta sake shimfida dankwalinta ta saka hijabinta ta tada sallah, raka'a shidda tayi a
sujadar ƙarshe ne ta saki kukan dake dukanta a kirji tana jerowa Allah kirari bayan ta jera
sunayen shi masu daraja casa'in da tara ta bi da salati annabi kan ta fara jero matsalolin ta da
neman sassauci ta yiwa iyayenta da sauran 'yan uwanta da ta rasa Adu'a ta roki Allah ya kawo
mata sauƙin rayuwa ya warware mata matsalolin ta ya kuma cigaba da bata zuciyar karbar
ƙaddarar ta a duk yadda ya zo mata. Kusan ƙarfe uku da rabi ta sake kwanciya a wurin sanyin
tiles na ratsa ta har wani baccin ya ɗauke ta.

Ta makara don tana bude idanunta ta ga haske daga Window, da sauri ta miƙe ta shige bayi
tayi saurin yin alwala ta zo ta gabatar da Sallar asuba tana sallame wa bata wani zauna Adu'a
ba don tsoron laifi abincin jiya da ya ƙanƙare saboda sanyi ta cuccusa kan ta fito riƙe da plate
ɗin ta nufi inda ta ga sun fito jiya.

Tsaye bakin kofan kitchen ta ci karo da mommy sanye da hijabi, duk da zuciyarta ya buga haka
ta ƙarasa ta zube a ƙasa tana gaisheta.

"Sannu isasshiya sai yanzu za ki fito? Ban gaya miki aikin ki shara da wanke wanke bane, sai
karfe nawa ake shara a gidan ku?"

Murya a sanyaye tace
"Ki yi haƙuri"
Tsaki ta ja kan ta juya cikin kitchen ɗin
"Talatuwa miƙo mata kayan sharar nan da mopping ta ajiye su chan baya don bana son
kallonta gangar abincin da yarana za su ci ban san me za ta iya jefawa ciki ba ko jini ko tsoka"
Abubuwan sharan wata dattijuwar ta fito mata da su, ta karɓa ta fara share parlorn zuwa dining
area daga nan bayan ta gama ta shiga mopping da goge-goge aiki ba baƙonta bane don
wannan a wurinta mai sauki ne sossai ma, haka zagi ko hantara duk ta riga da ta saba sai dai
ba rayuwar da take fata tayi ba kenan, ba rayuwar da take buri ba kenan tana so ta ga tana
karatu tana so ta ga tana hulda da mutane kaman kowani dan Adam, tana so taga ana hira da
dariya da ita kaman yadda ta samu gidan Aunty zee, sai dai da kaman wuya wai guguwa da
auren nesa.

A gefe ta tsaya tana kallon Talatuwa dake ta aikin shirya abincin mutanen gidan bisa dining
bayan ta gama ta dubi Afeefah tace mata
"Ki zuba turarukan wuta 'yan dai-dai a cikin wanchan abin ki kunna" ta ƙarasa tana nuna mata
burner, show glass ɗin ta tafi a hankali cikin natsuwa ta buɗe ta ɗauko ta saka ta kunna yadda
aka gaya mata ta koma bakin kitchen ɗin ta tsaya tana cewa Talatuwa ta gama..
"Akwai abincin ki na saka miki a plate ɗinki ki ɗauka kije ki ci sai yaran sun gama karyawa tass
sun wuce makaranta ake wanke-wanke"
Da to ta amsa kan ta ɗauka ta fice, a hanya ta gamu da Ishaq so take ta gaishe shi amma
kaman walƙiya haka ya wuce ta, bata damu ba ta shige ɗakin da yake da sunan nata ta rufo
kofan.

Ba za ta ce rayuwa a gidan yayi mata tsanani ba, saboda kwata kwata aikinta bashi da yawan
da zai dameta, tana idar da Sallar asuba take zuwa tayi share share da su goge goge ta ɗauko
abincinta daga nan ta tafi, sai wuraren sha ɗaya take komawa dining ta tattaro duk abubuwan
da suka ɓata na karyawan ta fitar waje ta wanke ta kawo bakin kitchen ta ƙira talatuwa ta
shigar, lokacin ita kuma Talatu za ta fiddo mata da abubuwan da ta bata na rana za taje ta tara
su wurin wanke wanken ta rufe ta ɗauki abincin ranar ta ta tafi, sai bayan la'asar za ta fito tayi
wanke-wanken haka na dare sai wuraren takwas tara. Ba Ta da abokin hira don talatuwa
tsakaninsu ki yi kaza ne kar ki yi kaza ita kuma amsar ta ɗaya a komai to.

Su iliya gudunta suke bata sani ba ko sun samu labarin ita ɗin annoba ce oho, bayan Hajiya da
suka gamu sau ɗaya 'yan mata ukun ko ganinsu bata sake yi ba, kaman yadda bata sake saka
saleem a idanunta ba tun ranar da ya kawo ta zuwa yau da take neman sati uku.
Bata sani ba shin rayuwar zai cigaba da tafiya a haka ne ko zai sauya? Shikenan ta sallamar da
burin ta na yin karatu kenan?Shikenan ta tabbata Mayyar za ta ci gaba da rayuwa ita kaɗai
tamkar a fursuna kenan? Bata da mai bata amsa.

Da misalin ƙarfe biyu na dare chan cikin baccinta ta ji kaman ana buga mata ƙofa, a ɗan tsorace
ta farka sai ta ji ana ambaton sunanta
"Afeefah! Afeefah!!"
Tun ranar da ta sanya kafafunta cikin gidan yau ne karo na farko da ta ji sunanta na fita a bakin
wani hakan ya sake razana ta, da ta kasa kunne kuma sai ta ji kaman Muryar salim a maimakon
ta ji sauƙi sai ta ji tsoro ya sake dabaibaye ta. Me yake yi a kofar ɗakin ta da wannan tsohon
daren? Ashe bai ma manta da ita ba yadda tayi tunani?
Miƙewa tayi ta nufi kofan wani zuciyar na cewa idan kuma hajiyarshi ta ganshi fa? Allah ya isa
fa zata mishi sanadiyarta, sai ta girgiza kai tana dakatawa.

"Afeefah saƙo zan baki ki buɗe don Allah, na san kina jina please buɗe ba zan jima ba"
A hankali yayi maganan amma ta ji shi tsaff kasancewar dare ne, ta gyaɗa kai tana ba zuciyarta
tabbacin saƙo kawai zai bata ya juya ba wani abu bane, da sauri ta je ta buɗe kofan sai suka
tsaya chakk idanunshi cikin nata yana ƙare mata kallo kusan seconds biyar bai ce komai ba sai
ita ce tayi ƙarfin halin ɗauke idanunta daga kanshi ta ɗan duka ta ce
"Ina kwana Ya salim?"
Ɗauke idanunshi yayi ya lumshe su kaɗan ya saki ajiyar zuciya mai dan nauyi, matsota yayi
sossai ta matsa baya tana kallonshi da manyan idanunta, ya leƙa ɗakin kaɗan kan ya dawo
baya, time ya kalla inda seconds ke reading, babbar leda jumbo dake hannunshi ya ajiye mata
don baya so ya shiga ɗakin nata ba da wannan dare ba, kai ko da rana ne ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login