Showing 45001 words to 48000 words out of 212110 words
"inbanji tsoron Allah ba tsoronka zanji? "
Ta wani murguda baki ta rike kugu sannan ta juya ta shige dakin ko minti biyu ba aiba ta fito cikin sleeping dress ta wuceshi, yana zaune sede yaji ta bude dakinshi ta shige da alamu can zata kwana.
Ya dade zaune dan gabadaya gani yake kamar anmasa musanya, dakyar ya samu yayi bacci,
Dasafe tun kafin tafito yabar gidan don wani mugun tsoronta ne ya shigeshi.
Yana zuwa gidan hiya bayan sungaisa ya mika mata Nata kayan sallar, ta amsa ayatsine tace?"Allah yasa albarka "
Badadi yabar gidan kanshi na mugun ciwo,
Shiko fahad karfe 11 da rabi na safe yakira faseelat yafadamata sun sauka taimishi ya gajiya sukai sallama saboda azumi.
Haka faseelat ta bullo da wasu sabbin abubuwa da suka rikita ma khalil kwakwalwa, da yanzu tsoron shiga gida yake inko yashigo har kyarma yake wani lokaci ma da yashigo sede kiji kwammmm! Mashin yafadi daga hannunshi saboda yanda hannunshi ke rawa, ba ruwan faseelat da taji karar faduwar tai ta babbakar dariya se tagama taja tsoki, gaba daya ya rikice idanunshi kullum awaje yana rarrabasu more especially inya shigo gida.
Ranar salla faseelat taci gayu ta turawa fahad, yayi ta kodata don bakaramin haduwa taiba don seda taje kasuwarnan ta zabo materials masu kyau takai akamata dinki,
Yanata aikomata da kisses daga karshe yakirata suka cigaba da waya,
Wan safen salla, khalil ya dauki faseelat a mashin zasuje suyiwa su ummi barka da salla,
Hankalinta kwance shiko yana tuki hannu na rawa, se warning takemasa "wlh kabini asannu don inka kadani Kasa naji ciwo wlh abakin aurenka don dolenka se ka sakeni "
Yayi shiru sede hannunshi daya kara gafgaf yana rawa saboda bacin rai tana kallonshi tana dariya kasakasa da farko tausayi yake bata intana mishi tsiya Amman yanzu haushi da takaici yakebata tana ganinshi kamar ba namiji ba da wani ne da tuni yabata red card dinta ahannu.
Tana ganin an hau titin da ze kaika gidansu tace "dakata, dakata "
Yaja burki ya juyo yazata ko zata gyara zama ne, yana kallonta ta tunzuro baki gaba ta sauka tace "ina zakakaini ne naga munyi nan? "
Yace "gidan hajya zamu fara zuwa sannan muwuce gidanku "
Tana mishi kallon raini tace "wace hjyar? Wai hjya saratu? To banzuwa kaje ka gaida uwarka nima inje ingaida tawa "
Rumtse ido yayi da yanabiye zuciya da tuni yafara jibgarta,
Cikin tsawa yace "faseelat !ya isheki kiyimin duk wulakanci amma karki kara ambatar sunan mahaifiyata "
tace "me zaka iyayi?innafada inba raba ido ba, "taja tsoki da Allah kakara gaba inkaje ka gaida saratun "
ta juya, cikin zafin rai yaja mashin yabi bayanta.
khalil ai hakuri kar amedata gurguwaπ€£
[7/12, 11:00 PM] Maman Mamy: β°β°β°β°β°
*RAGGON MIJI*
β°β°β°β°β°
By
*MAMAN MAMY*
ππ€ *ZINARIYAR GOLDENπ*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
βββββββ
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
βββββββ
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
π
Ώ 3β£5β£
*hakika ina cikin farinciki, na tabbatar ana so na anayi dani, jiya naga dubban comments da wanda ma banganiba, kowa nata fadin raayinshi da hangenshi, ga ruwan adduoi da na sha nida yarana, ina godiya Sosai Allah yabar soyayya*
Cikin zafin rai yabi bayanta ya sha gabanta da mashin tai tsaye ta rike kugu da hannu daya,
Cikin dauriya da fin karfin zuciya yace "ki hau muje gidan ummin"
Tana mishi kallon up and down tace "kayi hanyar ka daban inyi tawa, bana bukatar ka kaini kaji ko dan hjya "
Ta zagaye shi Tawuce ya rumtse ido idanunshi tuni sukai ja sede baze iya bari tayi doguwar tafiya a kafa ba , ya kara danne zuciyar yabi bayanta yakara shan gabanta ,ta game fuska tana kallonshi tace "malan khalil kafara takura ni nace katafiyar ka, aa ko ana dole ne?"
Cikin muryar rarrashi yace "kiyi hakuri ki hau muje kalli titin nan ba abin hawa doguwar tafiya zaki sosai "
Ta wurga mishi harara "to ina ruwanka? Nace karabu dani "
Yace, "Dan Allah ki hau mutafi "
Taja tsoki ta hau babur din tana cewa "ande ji haushi ba zuciya ko kadan kare yariga ya lashe"
Yana jinta yayi kamar be ji taba ya juya yakama hanyar gidan ummi,
Yana zuwa ta sauka ta shige, yayi parking ya kutsa kai shima,
Tana shiga ta yaye hijab" ummi ga khalil nan shigowa fa "
Ummi tace "to bari in dauko hijab dita, "
Khalil yayi sallama ya shiga har cikin daki ummi ta shiga ciki suka gaisa da yatashi tafiya ya aje mata bandir na 50 yace abawa yara,
Ummi tace "to angode sosai Allah yakara budi, aitade hakuri shi zaman aure dole seda hakuri da kai zuciya nesa Allah yabaku zuria dayyiba "
Yace "amin "yanata sadda kai maganar ummi ta dan ragemishi zafin da yakeji kamar tasan tsiyar da faseelat ke shukawa a cikin gidan ,ya tashi ya fita, faseelat se wurga mishi harara takeyi beko damuba ya Saki murmushi yace "ki shirya 6pm zanzo na daukeki "be jira amsar ta ba ya fita.
Shikadai yaje gidan hjya bayan sungaisa take tambayarshi faseelat yace"ai tana gida tundazu "
Hjya tai shiru ta cigaba da hidimunta, tunda yazo ya zauna yaketa sake-sake da tunani, wai miyake damun faseelat ne yau kusan kwana goma sha basa kwana daki daya, ba magana me dadi, batayin duk wani abu da tasaba yi, yayi shiru yana nazari, seya tuna last maganar su datake mashi korafi akan sex, tunanin shi da kwakwalwarshi ya tsaya nan, se kuma ya cigaba da neman mafita, akarshe yayanke shawarar zuwa wajen masu man power na Islamic, yana cikin tunanin hjya tashigo cikin dakin so biyu kenan tana giftashi be sani ba har tazo kusa dashi tana kiran" kai!kai ! "amma bejiba seda ta dafashi ya dago ta tsuramishi ido tace "wai lpy kake? Dukkabi ka rame kafita hayyacinka mike faruwane? "
Yace "bakomi hjya azumine ya medani haka "
tana mai wani irin kallo tace "to yayi tunda bakaso naji damuwarka sede inaso ka kwantar da hankalinka, banison ka shiga wani hali na rasa mahaifinka baniso na rasa ka ,"
Yace "hjya bawani abufa, Ki kwantar da hankalinki "
Tace "Allah yasa "tana kara karemishi kallo,
Yadan kara zama ya tashi yafita be zame ko inaba se alhayat Islamic center, yaje ya siyi kati kasancewar salla ce ba layi yashiga gun malamin, ya mishi bayani a kunyace, malamin yarubuta mashi magugunan sa karfi na maza, khalil ya siya ya nufi gida ya dauki biyu ya shanye su tass yayi kwance yana ta tunani abin duniya duk ya dameshi,
Karfe shidda yaje ya dauko faseelat tunda ya daukota batace uffan ba, saboda itama ummi seda tai mata tata yar nasihar,
Yana ajiyeta yawuce masjid ita kuma ta shige gida, kusan karfe 7: 30 fahad yakirata sukai ta fira har isha, shi ko khalil a daddafe yayi salla ya taho gida saboda yadda yaji yana ta samun erection,
Ko da yazo betsaya shigo da mashin ba ya shiga gida, sam faseelat batasan ya shigoba, sunata firar soyayyar su da fahad,
Tunda khalil yashiga dakin yaji wayar da take tana ta noke murya tana shagwaba da duk wani abu da zeja hankalin namiji, hankalinshi ya tashi, kafafuwansa na kyarma ya samu kujera ya zauna ya dafe kai da hannu biyu, yana tunani "meyasa? Meyasa faseelat takeso ta lalata rayuwar aurensu? meyasa takeso ta jefa kanta a cikin halaka? "
Tunanin shi ne yakatse jin sautin kisses dinta ,ya mike tsaye yana kyarma,
faseelat nakiran "good night have a sweet dreams "
Khalil yashigo tai sauri ta kashe kiran ta mike tsaye tana raba ido dan bataji shigowar shiba,
Tana ta sadda kai shiko ya tsaya yana kallonta, da wani yabashi labari baze taba yarda ba wai faseelat dinshi ce ke fira da wani,
Ya samu dakyar yace "faseelat kinaso kigama da duniya lpya ko? da aure na akanki kike waya da wani kato "
Faseelat ta juyo dasauri ta daga mishi hannu "hehehee,karka kara cewa fahad dina kato kaine de babban katon bashi ba "
Ta rika murguda baki,
Ranshi ya baci sosai, batai tsammani ba taji ya tura ta kan bed yabi bayanta ya fara kokarin cire mata riga suka cigaba da kokawa har ya janye rigar ya danne mata hannuwa ya fara bin jikinta da kisses ,tana ta kuka tana kokarin janye hannuwanta, ko minti daya be dauka ba yayi hanyar shigarta ,abun mamakin shine yanajin shaawar beyi release ba amma yana zuwa shigarta yaji abar ta kwanta, he was very surprised, ganin baze iya ba yasa yatsa yafara kokarin yiwa kanshi hanya don yau yakudurci se yayi sex daita,
Faseelat sede taji yatsa na neman shigarta a tsorace ta kurma ihu yasa hannu ya toshe bakin tadage cincin karfinta ta gartsa mashi cizo, yayi sauri ya dagata yana duban hannun yana nishi, ita ko taja gefe guda tana kuka tana fadin "Allah yaisa, banyafe ba mugu azzalumi, daniska "ta cigaba da kukanta yana samu zafin cizon ya rage ya mika hannu ze kara kamota ta tashi da gudu ta shige toilet
Tana cigaba da kuka tana Allah yaisanta bata yakeba.
Yayi kwance yana tunanin lamarinshi yanzu haka ga abar a mike, to me yahana ya shigeta? Yanata tunani ,
itako tana toilet tana cigaba da bankomai Allah yaisa, dukda shi masoyin bacci ne amma bacci beyi gigin daukarsa ba saboda tashin hankalinda yake ciki, itama tana cikin toilet tana kuka saboda yunkurin rabata da virgin dinta da yayi wanda yanzu burinta be wuce takaishi ga fahad ba.
Har sha biyu bata fito ba ya tashi yaje bakin kofar toilet din Yana kwankwasawa "kifito faseelat dare ne fa kina cikin toilet for many hours ki fito plsss baabunda zanmiki "
tana jingine da kofar tace "baza a fito ba din mugu azzalumi kawai "
Yace "eh naji kifito bazan miki komi ba, kinsan fa toilet matattarar iska ce "
Tace "yo ba kwara iskan ba da mugun abinda kakeson yimin dan zalunci "
Yace "kifito plsss OK tunda bazaki fito ba ni natafi dakina acan zan kwana kifito ni natafi "ya juya yabar dakin,
Seda taji tsit sannan tafito dasauri ta sakawa dakin kuba, ta koma taita rizgar kuka saboda ita kanta tasan abinda take badede bane amma takasa hakura wanda yanzu bama zata iya kwana daya ba batare da jin muryar fahad ba,
Khalil dakyar bacci ya daukeshi batare da yagano abinda ke damunshi ba, itama faseelat dakyar tai bacci,
Da safe har karfe 8 faseelat bata fito ba gashi yanason fita shago, yaje yana kwankwasa mata, seda ya dade yanayi sannan ta tashi tana zumburo baki tazo ta bude tana mishi kallon tsana,
Batare da yadamu da kallon da takeyi mishi ba yace "ki sauri kihada min break fast nayi late "yawuce cikin dakin
Ta tabe baki tai hanyar kitchen, dukda yace yana sauri seta tsiri yin danwake, kuma it take much time, har ya shirya ya zauna jiranta, se kusan 9 saura kwata takawomishi abincin ta dangwarar da plate din Kasa ya dauka yana girgiza kai, don shi dakanshi ke tausayin kanshi, yafara cin abincin,
Tana ta yan gyare gyarenta, tana waiwayowa taga khalil yana cin abincin yana bata fuska yana karkace baki irin ba dadin nan,
Beyi aune ba yaji ta wafce plate din, ya kalleta yace "bani plate dinnan faseelat"
tace "anki abaka ni zaka raina wa hankali insha wuya inmaka girki kazo kanaci kamar yadda jaki keci to kaGama cin abinci na wlh daga yau kanemi wurin cin abinci ko karika shiga kitchen da kanka ka girka "
Yatsura mata ido yana memeta jaki,can yace "faseelat nine jakin? "
Tai dariyar rainin hankali tace "ai gwara jakin ma da kai "
Tai waje ta zubda abincin a dustbin dama dan tayi tsiya tai girkin ba dadi, ta dawo ta dora plate din kan cinyarshi tace "kakai shi kitchen alaramma "ta shige daki yayi galala da baki yana kallonta, ya ajiye plate din yatashi yabar gidan gabadaya,
tagama abubuwan da take tai wanka ta sanya wata yellow din gownt tana zaunawa kan mirror fahad ya kira ta ,abun mamakin shine video call ne ba kamar yanda suka saba ba, batare da wani laakari da ko dankwali babu kanta ba ta dauka ta ajiye wayar setin ta,
Dukansu kallon juna sukarika yi ba wanda yace uffan shi yana zaune akan wata resting chair ne yana sanye da armless riga ,yanata aika mata da kallon love,
ya kure ta da ido yana kallonta especially her boob's and her beautiful face and hair, tayi matukar yin kyau,
Can zuwa ya daure yace "hi! "
Tai murmushi tana gyara gashin kanta da ya jike ya zubo kan fuskarta sannan tace "hi "
Ya cigaba da kallonta tai murmushi ganin be magana ba tace "kayi kyau sosai "
Ya danyi dariya "kinga na kiraki video call ko? "
Tadaga kai tana sunna kai tana mai wani irin kallo
Yace "nakasa hakura ne har nadawo naganki, inason ganin motsin kyawawan lips dinki da ganin ur beautiful body shiyasa na kira I hop banyi laifi ba? "
Tace "laifi? Ai baka laifi "
yayi murmushi "kinyi kyau sosai, se yanxu nasamu natsuwa dana ganki "
Tai dariya tace "thank you "
Yace "kinsan me? "
Tace "a, a sekafada "
Yace "jibi zamu dawo Nigeria "
Ta zaro ido tana jindadi tace "wow im
Very happy to hear that "
Yace "and I want to meet you on that day"
Ta dan rage faraar ta don batasan ko aina zasu haduba,
Seyaga duk ta sauya yace "bakiji dadi ba? "
Tai dariya tace "I'm very happy mana, that I will meet my handsome "
Yace "good yanzu what do you want me to buy for you ?"
Tana murmushi tace "everything kasan komi abunso ne aguna inde daga gareka ya fito "
Yanata kallon yanda take motsa lip dinta yace "I like ur lip "
Tai murmushi "can I have a good kiss from you? "
Tai dariya tana bin lip's dinshi da kallo tace "where? "
Bece komi ba yadora yatsa a lip dinshi,
Ta dan sunkuyar da kai kasa yace "plss mana I'm watching"
Ta dago tai kiss me sauti ta hura masa tana rufe fuska,
ya dafe zuciya tare da fadin "ashsh "
tai ta dariya yana kallonta ko kiftawa babu yace "I love you faseelat "
Tai tsit tanajin dadi namata yawo koina,
Ahankali tace "love you too dear "
yayi murmushi tareda fadin "bye "
Bata iya bashi amsa ba se yatsunta biyu da ta motsa alamun bye, yakashe kiran,
faseelat tai zaune gun tana tunanin ta yadda zasuyi su hadu daga karshe taja tsoki, tace "kawai anan ze sameni se me? "π€·π»ββ
Haka akai 2 days dinnan faseelat batawa khalil girki in ma ya dafa seta dauke ta cinye koba dadi dan kawai yaji haushi,
Kuma kullum se sunyi video call da fahad ba so daya ba biyu ba dan dukkansu jindadin ganin juna sukeyi duk Sun dimauce dukansu,
Kafin ranar da zasu dawo faseelat tasha dilka ta kara kilewa ya fadamata 11am zasu sauka zezo wurinta da marece se dadi takeji kamar ta rafka ihu,
11 am su maman amira suka sauka Nigeria, suna makale da juna as usual suka isa gida sukai wanka suka fita zuwa dauko amira dan daddinta kullum cikin fadawa aisha yadda yayi missing dinta yake, dukda suna waya yana ganinta
Sun dauki lokaci agidan momy sannan ya daukosu suka koma gida, lokacin marece ne wajen karfe biyar saura.
Ya fito daga gida suna waya da faseelat har bakin kofar gidanta, yana zuwa few minutes later tafito daga cikin gidan, tana hango mota Sabuwa dal tagane shine ba bata lokaci ta isa gun motar ta bude ta shiga,
Hmmm kamshin turarenta kawai ya rikita fahad se mayen kallo yake binta dashi itama seta kalleshi tasaki murmushi,
yanajin kamar yajawota ya rungume yace "me kyau kinason kasheni ne ko "
tai dariya ta girgiza kai yace "se kara kyau kike miye sirrin ?"
Tai dariya tace"ai kaine sirrina "
Yayi dariya tace "ya hanya inafatan kundawo lpya? "
Yace "lpya lau "yana lumshe ido
Tace "ina my anti da daughter na? "
Yace "suna lpya suma "
Tace "alhamdulillah"
Duk sukai shiru sunata kallon kallo can zuwa ya fiddo wani dankaramin akwati da kwalin iPhone8s ya mika mata, ta karba tana duba kwalin wayar ta zaro ido tana kallon wayar duka befi 3wks taga tallon ta a insta ba 500,000 ta kai hannuwa ta rufe baki, sannan tabude akwatin sega haddadun zinare da yankunne da sarka da yan hannu takara rufe baki tana mamaki shiko kallonta kawai yake kamar yau yafara ganinta tace "all this for me? "
Ya daga mata kai tace "thank you very much, Nagode Allah yakara tsaremin kai ya kara buda duk kofofin arziki "
Ya lumshe ido ya bude yace "amin my baby "
cikin kasala dan gabadaya ta rudashi yace "me zaki bani? "
Tai karamin murmushi tana sadda kai Kasa tana fatan kar yace tai kissing dinshi don bazata iyayi ba a zahiri,
Yace "koba za aban komi ba? "
Ta dago tana kallon shi tace "me kakeso?"tana rufe fuska, yayi dariya
yace "nothing but you "
Tana jin kunya tace "I'm all yours "
Yace "alright I need your hot kiss that always make me go crazy "
Ta zaro ido ta tunzuro baki "plss not now, I'm feeling shyness ,"
Yace "bazan samu ba kenan? "yana langwabe mata
Tace "I will do that on the phone "
Yayi dariya yana kallonta wai kunya takeji yace "alright bani wayarki naimiki exchange na sim "don yasamu yadan taba ta,
Ta dauko ta miko mishi yahada da hannunta sannan yajanye kamar irin mistake dinnan,yana amsa ya rumtse ido again yadora kan seat jin soft and smooth na hannunta inaga b..... Fa
Tana kallonshi thinking that duk gajiya ce ya sauya mata sim card din yabata sabuwar a hannu yasaka tsohuwar a kwali ya mika mata nan ma yasamu yadan taban batare da damuwa ba tace "thank you "
ya kalleta kawai tace "I'm going inside se yaushe? "
Yace "anytime, "
Tace "OK bye ka kulamin da kanka "
tana mishi wani kallo me kara dulmiya mutum ta fita daga motar,ta shige gida yayi murmushi ya girgiza kai yace "I love you my lady "
Yaja motor yabar unguwar,
khalil isowarshi kenan unguwar yaga faseelat tafito a motar ta shige gida dauke da leda ahannu cikin daukewar wuta yabita da kallo har tashige yakuma