Showing 102001 words to 105000 words out of 212110 words
gyara ciki ta samu jamila nata yagar tsire abunta, hjya ta kalleta tayi bulbul abunta ta wuce ciki tana shiga ciki tafara masifa ita kadai "yo ai dole ki kiba yarinya shikenan se ya biye maki komi kikeso se kinci to me zaya tara ne? "
Tana sababi tana gyaran dakin tafito tana share falon jamila ta dage kafa sama ta meda kan Kujera ta cigaba da cin tsirenta ,
Hjya na Duke na shara take tuno faseelat duk in sunzo koba dauda se anma dakin kwass bazata iya kilga wankin da faseelat ta mata ba gata da kunya in sunzo ko kallon hjya bata iyayi, hjya ta cigaba da shara karo na baadadi kenan da tayi tunanin faseelat,
Har tagama ta kwashe tafita kitchen ta juye abinci a flask ta dawo ta shiga toilet wanka,
Ta fito tana shirin kabbara salla taji jamila na waya "yaya dan Allah taura nakeson ci danbaba ya matsa min "
Khalil yace "OK bari infita in siyo miki yanzu "shide haka yake da ririta mace
Hjya tace "aise kuyi "t a kabbara salla tana salla tana tunani barkatai,
Tana sallamewa bata tsaya ko addua ba ta dauko waya ta danna kiran ummi tana jin nauyi,
Ummi na kwance tana hutawa ta dauki wayar tana mamakin ganin kiran hjya,
Hjya tayi sallma ummi ta amsa hjy tace "kwana da yawa bamu gaisa ba ina diyata? "
Ummi tace "aikuwa ai diyar ki tayi aure shekaran jiyar nan "
Cikin rashin jindadi hjya tace "Allah sarki Allah ya basu zaman lpya da zuria dayyiba"
Ummi tace "amin Nagode sosai "
Hjy tace "to se anjima "ta kashe kiran ,tana cizar lips,
Ummi tabi wayar da kallo tace "nifa ban yarda hjya tayi wani asiri ba I'm doubting about it "
Hjya tagama salla tafito taga jamila tana salla tafita takawo mata abinci ta zuba nata ta zauna awaje ta shimfida tabarma tana ci,
Jamila na gama salla ta bude kular, dasauri ta dade hanci ganin wake da shinkafa, ta meda kular ta rufe,
Ta dauko waya ta kira khalil ya dauka tace "yaya bazan iya cin abincin nanba ka siyomin fried rice a restaurant "
Khalil dake kan mashin yakusa kawowa yace "kuma, to ganinan tafe "
ya juya ya koma yasiyo mata abincin hjya kasa cin abincin tayi ta meda kitchen tazo tabuga tagumi,
Can zuwa khalil ya shigo da ledoji a hannu yazo ya zauna yanama hajiya sannu ta kalleshi tace "yawwa "ya mika mata tata fried rice din, yana niyyar tashi jamila tafito tana ya mutsa fuska ita adole me ciki hjya tabita da ido khalil ya kalleta yace "sannu "
Tazo ta zauna gefenshi ta amshi ledar tafara ci,
Shiko ya dauko natan yaci ya tashi ya koma aiki,
Butsu butsu jamila ta kirashi tace tanason wani abu, haushi har yagama cika hjya ta kunna radionta tanaji don tadena jin kayan haushi.
Bayan faseelat ta gama abincin ta shiga daki tayi wanka tana ta sauri donta shirya tai salla,
Fahad da ya dawo daga masjid ya shigo dakin bataji shigowar shi ba, ya zauna ya harde hannu kan cushion yana kallonta,
Ta gama makeup da shafe shafe ta mike tsaye tana juyowa taga fahad zaune yana kallonta, gabanta yayi mummunar faduwa ta saki towel din dake rike hannunta ya fadi kasa ,ta fiddo ido waje don yabata tsoro,
Fahad yayi mutuwar zaune yakafeta da ido bako kiftawa joystick dinshi na harbawa ,
Batasan ta saki towel dinba ta kalli jikinta taganta tunbur tai tsuwwa tai sauri ta juya baya jikinta na rawa hannunta dafe da kirjinta ,
Fahad yabi bayanta da kallo ,
Faseelat ta tuna bayan ma fa akwai abun kallo tai sauri ta juyo ta duka daukar towel dinta,
Fahad yana dariyar shakiyanci yataso ya rike hannunta yana kara bin jikinta da kallo yace "haba miye duk na rudewa ni da kayana? kibari nakara nazartarki plsss karfa ki manta naga komi har can ciki na sha to miye na boyo ?"
Faseelat jikinta na rawa tace "Dan Allah kabani towel din "
Ya dage kafada yana cigaba da binta da mayen kallo, kawai taida shigewa jikinshi ta makalkaleshi,
Jin hannunshi tai yana massagin hips dinta harwani girgiza su yake,
Ta hadiyi miyau me daci ta rike hannunshi tace "banyi salla ba plss bari nayi kar alwala ta takare"
Yace "ai akwai sauran time bari mu gama sekiyi "ya cigaba da abinda yake
Faseelat ta yamutse fuska tace "to kashi nakeji wlh "
Jin tace kashi ya saketa yana dariya yace "jekiyi ki dawo "
Faseelat ta janye towel din ta dora ta koma toilet shiko ya haye bed yana dariya yasan bawani kashin da zatai "
can zuwa ta fito ya lumshe ido tazo ta bude wardrobe ta dauko carpet da hijab, da riga da sket na material lace pink color tana sauri ta zura ta kabbara salla ,
yana ta kallonta har ta sallame ta juyo ta kalleshi bayan ta shafa addua, ya mata murmushi da fuska ya mata alamun tazo,
Ta dage kafada ta tashi ta linke kayan sallan ta nufi gun mirror fahad ya kira sunanta "honey! "
Ta juyo ya kada kai yace "ba sekin sake kwalliya ba kinyi kyau ahaka, kizo muje muyi lunch "
Faseelat ta dawo wurinshi ta mika mai hannu ya tashi ya sargafa mata kafada suka fito,
Aisha da amira na falo suma yanzu suka fito dan bacci sukai suma duk Sun sauya kaya,
dukkansu sun hadu a dining faseelat tai sarving dinsu,
Ta mikawa su Aisha nasu ta zuba nata a plate daya da fahad taja kujera ta matsa gaf dashi ta koma ta zauna yanata kallonta ta debo alkubus a spoon ta kai bakinshi yayi tsaye yana kallonta tace "open your mouth mana ni zanyi feeding dinka da kaina baniso ka wahala "tanayi tana mai kallon jan hankali,
Kamar wawa ya bude baki ta zuba mishi tana ta bashi yanata kallonta,
Aisha ta cika tai bammm ko abincin takasa ci se aikin kallonsu take,
Wasa wasa har alkubus biyu Sun kare,
Faseelat ta tashi zata kara zubawa ya riko hannunta ya kalli plate din ya kalli cikinshi yana mamaki yace "wai duk na cinye wannan abincin? Honey kinaso in kara kiba ne? "
Faseelat tace "sosai ma, bari nakara maka ai zakayi kyau da kiba "
Yace "noo banason nakara weight ze takura ni, bari na zuba nayi feeding dinki da kaina "
Faseelat ta koma ta zauna ko da ta daga ido ba Aisha har ta bar wurin,
Ya zubo yasa hannu yace "da hannu zan baki fa "
Faseelat tace "se yafi dadi ai "takashe mai ido daya, yana bata abaki har ta koshi daga karshe ta rike ya tsunshi ta tandesu tasss,
Yace "to muje abiya ni lada "
Faseelat ta make kafada ya jata tafara turjewa ,
Ya tsaya yana dariya yace "Allah zan sungumeki gaban princess "ya kalli amira dake niyyar tashi tabar wurin don takoshi ,
Tana barin wurin ya sungumi faseelat akafada tafara harba kafafu yace "dande ki rage min karfi ne kuma senayi "
Ya dirji abishshi son rai sannan ya tashi yawuce toilet, gaskiya fahad abunka yayi yawa 🤣
Faseelat gashinta a baje hannunta dafe da mararta,daga jiya zuwa yau ciwon kugun dole takeyi, ta rumtse ido tana tunani wato shi fahad sex har yafi salla yawa tunda baya gajiya,
Ya fito yana tsane jikinshi da karamin tawul, faseelat tabishi da kallo,
ya zauna yana drying gashinshi ya kalleta ta mirror yace "sannu my kankana se hakuri mijinki hero ne"
faseelat tai dariya ta juyar da kai,
Yana gama shiryawa ya wuce masjid don yin asr ,
faseelat ta yunkura ta tashi dakyar ta shiga toilet ta gasa jikinta tayo wanka, tazo tai salla sannan tafara shirya kanta, tasan halin kayanta yana iya dawowa ya ganta da towel akoma ruwa shiyasa tafara saka single long gown dark green ta zauna gaban mirror, tana zama tafara taje kanta wayar fahad tafara ringing,
faseelat ta tsaya da taje kan tatashi tai wurin wayar tana fatan bad woman ce ta kira, saboda tanason sanin wacece me sunan,
Aiko itace hannunta har rawa yake saboda sauri ta dauki wayar ta kara akunne,
Abinda taji ana fadi yasa hanjin cikinta juyawa,
Muryar babbar mace tana cewa "son dan Allah katsaya ka saurareni ko na minti biyu ne, nasan ban kyauta maka ba ban maka adalci ba amma kayafemin badon hali naba wlh nayi..........
*wasu nata complain wai bekamata ace faseelat tafi Aisha komai ba, kunsan Allah ana samun haka a reality kishiyarki tafiki komi, kuma miji yafi sonta se kaga wasu suna kauce hanya saboda kishi da bacewar hankali,Allah yariga ya rubuta ko ku nawane gun mijinku dole se yafi son wata acikinku, yanzu de babban misali manzon Allah S. A. W da aka tambayeshi wa yafiso acikin matanshi cewa yayi Aisha, amma kuma yana son duk matannashi, khadija R. A) ta rasu amma saboda yadda manzon Allah yake sonta da yawan ambaton ta Aisha R. A) tace tafi kishinta a kan sauran matan, manzon Allah (S. A. W) yana girmama khadija yana yawan ambaton ta har ya zam ko bayan mutuwar ta yakan yiwa friends dinta kyauta saboda girmamata, kungani toni inaga wannan ba sabon abu bane miji yafi son wata, kuma dama ai Allah yafada a kurani acikin suratul nisai (walan tastadi'u an taadilu bainan nisai walau harastum ,fala tamilu kullal maili fa tazaruha kal muallakati, wain tuslihu wa tattaku fa innallaha gafuran rahima) to amin hakuri akwai sakon da nakeson isarwa ne akan haka inafatan team Aisha zasumin hakuri, acigaba da danne kishin nan, nima fa uwargida ce 😃bari ma nabaku labari lokacin da fahad ya mari Aisha akan faseelat seda na kewaya toilet 😂🏃🏽♀kude yi hakuri da abunda ke faruwa*
[8/5, 6:09 PM] +234 815 712 7134: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
6⃣1⃣
Wlh nayi nadamar abunda nai maka kai da mahaifinka, kullum cikin dana sani nake, kayi hakuri plsss kadawo gareni wlh duk cikin diyana nafison ka, bansan yadda zangyara kuskuren da na maka ba,amma ka tausayamin ,na azabtu da rashinka ina bukatar kulawar ka my son.. "ta tsagaita saboda kukan da yazo mata , but she's very surprised yadda ya dauki wayar yatsaya saurare don baya daukar wayarta inma ya dauka da yagane itace yake kashewa duk yayi saving numbers dinta don yarika avoiding kiranta,
Jikin faseelat kyarma ya dauka jin abinda umma ke cewa jin sautin kukanta hawaye suka zubomata zuciyarta na bugawa da karfi magana takesonyi bakinta yakasa fitar da maganar ,
Jin shiru umma tace"plssss ka yafemin, kayi hakuri nasan nacuce ka "
Hawaye sharrrr suka zubo ma faseelat jin uwace kewa danta kuka begging for his forgiveness, muryarta na rawa tace "ya ...fita... masallaci..."
Sanin Aisha bata shiga lamarin tace "faseelat ce? His bride? "
Faseelat ta shanye kukanta tace "ni...ce umma"hawaye na cigaba da kwaranya a fuskarta
umma tayi murmushin jindadi wanda har faseelat seda ta jishi,murya a raunane tace "I'm very happy da naga pictures na bikinku, ina tunanin zaki temakamin wurin shawo kan fahad, na mishi laifi babba na wulakantashi nabarsu shi da mahaifinshi saboda son zuciya ,amma nayi nadamar abinda nai masa tunda dadewa, mahaifinshi be bani damar koda ganinshi ba, after his death na kira fahad nayi zarya gidanshi da office dinshi nabashi hakuri Amman he dont even listen to me,na tura malamai da dama gunshi he didn't look at them, I once come to his wife itama bata saurare ni ba, I don't know what to do, kamar yadda nagani yana sonki sosai dan Allah ina rokonki ki shawomin kanshi ya yafemin tun kafin na bar duniyar "
Faseelat tace "karkice haka umma fahad ze yafemiki ze so ki kamar yadda kowane da yake son mahaifiyarshi kiyi ta masa addua umma Allah ya sanyaya mishi zuciyarshi adduar ki kar babbace, kuma ina rokon karki fushi dashi "
Umma tace "ina ta addua faseelat amma shiru, kuma bana fushi dashi ko kadan don nasan duk ni najawo hakan, Nagode kwarai dagaske "
Faseelat tace "ki kara hakuri umma komai ze zama labari watarana "
Umma tace "Allah yasa Nagode da kika saurareni se anjima "
Ta kashe kiran tana tunani da dama,
Faseelat har suka gama wayar tana hawaye, jikinta ya mutu murus zuciyarta na cigaba da harbawa, wayar na rike hannunta takasa ajiye ta sanin irin balain da fahad Ke ciki tafasa kuka zuciyarta cunkushe numfashinta har daukewa yake,
Bayan fahad ya dawo masallaci dakin Aisha yawuce ya same su sunata labari da amira, shima ya zauna akai tayi don ya debewa Aisha kewa , karfe biyar da wani abu ya fita ya nufi dakin faseelat,
Ya tura ya shiga faseelat da har lokacin tana zaune wurin takasa tashi ta juyo idanunta dake jawur ta zuba su akan fahad tarika kallonshi kamar yau tafara ganinshi,
Abun yabawa fahad tsoro ganin idanuwanta jawur a kumbure ga gashinta dake zube koina gaba da baya,
Dasauri yaida shiga dakin ya isa wurinta yaje ya zukunna gabanta yana gyara mata gashi da hannu yana kallon fuskarta yace "what's wrong with you? Ehimm? "
Hawaye suka gangarowa faseelat tana meda kukan dake niyyar kufcemata tace "Ankira wayarka "
Fahad ya kalli wayar dake hannunta batare da ya damuba yace "answer me first meke damunki kike kuka "
Kanta a sunkuye ta dago tana kallon kwayar idonshi tace "it's the phone "
Fahad yariga yasan baya wani abun banza da wayar shi atata in zata ga abin tashin hankali befi hotunan Aisha da suke birjik ba wasu ma half-naked, aranshi yayi tunanin ko wani Yakira yafadi wani abun tashin hankali, ya anshi wayar daga hannunta ya shiga call log, number bad woman ce sama kuma sunyi kusan 10mnt suna magana,
Kafin ma ya dago faseelat tace "it's bad woman"
Fahad ya dago ranshi bace yace "who ask you to pick my call? Miye ruwanki da kiran da akemin da har zaki dauka eyee?"
Faseelat jikinta mace batare da ta bashi amsa ba tace "hero! Kaine kake kiran ummanka bad woman? Umma ce fa wadda ta dauki cikinka wata tara tai nakudar ka tabaka nononta kasha itace kake avoiding kiranta kai watsi daita just because she did a small mistake? " ta ja ajiyar zuciya ta cigaba da cewa "kasan halinda kake ciki kuwa? Haba hero banyi zaton haka daga gareka ba "
Fahad ya mike tsaye yace "don't interfere in this faseelat stay away from this matter, kuma daga yau karki kara daukarmin waya"
Ya juya zebar dakin ranshi bace,
Faseelat tace "hero mahaifiya ba abar yadda wa bace ba ,kome tayi kuwa, ankarbo daga Abdullahi dan mas ud wani mutum yazo wurin manzon Allah (S. A. W) yace ya manzon Allah man ahakkan nasi bi husni sahabatiy?se maaiki yace mishi ummuka yace summa man? yakara ce mishi ummuka yace summa man?yace abuka "
"Hero yanzu kai ba maganar kyautatawa ma ake ba ka saurare ta ma ka ki baka tsoron fushin Allah? manzon Allah yace yardar Allah na tare da yardar iyaye fushin Allah na tare da fushin iyaye ,hero kar idanka ya rufe ka gaggauta zuwa wurin mahaifiyarka ku dedeta, ayoyi nawa ne a alkurani sukai magana akan yiwa iyaye biyayya saboda mahimmancin yiwa iyaye biyayya awasu wurare da dama daga kadaita Allah se yiwa iyaye biyayya agaba , duba suratul israi daga aya ta 23 da ukku zuwa da 4, suratul ahkaf aya ta 15 zuwa da 17 da suratul...."
Fahad ya daka mata tsawa ta fiddo ido waje tana kallonshi rai bace yace "kimin shiru bana bukatar waazin ki akan wannan matar, ta cuceni ta wulakanta ni saboda son zuciyarta ta rabu dani lokacin da nake bukatar ta har yau kunne na yakanyi ciwo time to time saboda marin da tamin, ita ki naganin tayi abu me kyau kuma ta tursasa mahaifina ya saketa don son zuciya kawai? ki fidda kanki cikin maganar nan faseelat, Aisha shekarar mu nawa tare amma bata taba shiga maganarba hasalima tafini jin zafin wulakanta ni da matar tayi ,idan har baso kike raina yarika baci ba to ki fidda kanki aciki "
Faseelat daketa zubda hawaye tana kallonshi tace "bazan dena nuna maka gaskiya ba umma tayi maka laifi kuma tayi nadama ta nemi afuwarka seka yafe mata wai shin baka yiwa Allah laifine amma kuma ya yafemaka, itama fa mutum ce mace tanada rauni yakamata kamanta baya ka rungumi mahaifiyarka ko zaka samu rabauta "
Idanunshi jawur ranshi bace ba abinda yake tunawa se labarin da mommy tabashi na cewa "bata sonka ko kadan bata kula da kai daddynka shine komi naka shine wanke maka tutu shine wanka shine dariyarka shine duk gatanka "
Jijiyoyin kanshi duk Sun fito zuciyarshi na zafi yace "bakijin magana ta kenan nace kibar maganar ta I'm warning you this is the first and last time karki kara maganar matar nan acikin gidannan inba haka ba I will do something bad "
Ya fita yabar mata dakin, faseelat ta kara fashewa da kuka yanzu idan ya mutu yau fa me zece wa Allah bayada wata hujja akan abinda yake yi,
Fahad gidan yabari gabadaya yana tuki yana fidda huci,
Hjya cikin dabara kar jamila ta kaita karshe ta kira khalil ya dauka da sallama ta amsa tace "khalil kazo ka dauki jamila ku tafi gida kasan baason me ciki na kai Maghreb awaje "
Yace "to hjya ganinan zuwa "
Hjya takashe kiran ta shiga ta samu jamila dake bacci hjya ta bubbuga gefen kujerar jamila ta bude ido tana kallonta hjya tace "ki tashi ki shirya gashinan zuwa zaku tafi gida "
Jamila ta tashi tana ya mutsa fuska ta shiga toilet,
Hjya tace "oh ni saro na daukowa kaina jidali yarinya ba kunya kokadan duk tabi ta fitsare kafarta to Allah ya kyauta "
Jamila kau tunda ta riga tagama gano halin hjya ta kuduri musguna mata,
Gab Maghreb khalil yazo ya dauketa suka koma gida,
Fahad wurinda suke hutawa da friends dinshi ya nufa sabeer se shakiyanci yake mishi sede yayi murmushi,
bayan faseelat ta yi sallar Maghreb ta shiga kitchen ta masu vegetable soup and white rice,
Tana gamawa ta kai musu dining ta koma daknta tayo wanka tayi salla ta saka doguwar