Showing 15001 words to 18000 words out of 212110 words
da kukanta, a sannu ya dagota yana goge mata hawaye, "miye na kuka kuma? Ki shiru plsss kukanki na daga min hankali "
tai shiru tana ajiyar heart yana tallabe da fuskarta yana kallon kwayar idanunta yace "kinyi kyau kanwata "tai murmushi kawai ya Saki fuskar ya kama hannunta zuwa dakinshi,
Tana zaune ya rage kayan jikinshi ya rage daga shi se singlet da wando jumper ya shiga toilet din dakin ya yo brush yadawo ya zauna cin abinci yana ci yana kallonta itama shi take kallo kullum de bazata gaji da yabon danuwanta ba yayi a kowane Fanni, ya katse shirun da cewa
"yasu ummi da auta?"
Tace "lpya lau suke, suna gaidaka "
yace "ai ummi takirani jiya tace zakizo in kula dake "
tai shiru yace"kitashi ki shirya mutafi gidan dijen "
Ta tashi tsaye ya dago ya kalleta har tafita ya girgiza kai a zuciyarshi yace "tunda bazaki bi shawara ta ba ai shikenan "
he have been advising her ta je ta fadawa baba Babba bata san auren amma taki a karshe ma Cewa tai tafara son khalil din ,shiyasa ya kyaleta,
Yana Gama cin abinci ya tashi ya watso ruwa ya shirya suka tafi gidan dije shi da ita da fadila,
Suna isa dije se murna take takawo masu abinci tai nan tai nan, su omer da fadila suka barta suka koma gida a tare, domin shi omer tuni Sun dedeta da fadila wadda dama can tasu tazo daya.
tun daren ranar akafara gyaren faseelat taff,ko sati baaiba takara jin shaawa ta mata yawa, abun mutum baze yarda ba domin har zuba takeyi kamar me mensis, nasan wasu zasu ga cewar novel ne kawai amma it's happening wlh dan wani lokaci irin wannan yanayin harda ciwon mara yake Saki,
Kiri-kiri faseelat bacci nason ga gararta saboda shaawa, itaba abun ta dau azumi ba tunda shaye-shayen da take wasu ma dasu take breakfast, dubarar da tayi shine tadena zama ita daya kullum tana like da fatoum wadda tama girmeta, bata aikin komi tunda taje,
*Bayan 3wks*
Lefe ya Gama haduwa hjy ta kikkira danginta da abokanta da makwabta ganin lefe, ba lefi lefen yayi kyau kuma de anyi kokari wajen kala 45 bag 5, 10 shoe's include bathroom slippers, 6 hijab, kaya de sunyi.
Mutane dodo-dodo ake zuwa ganin lefen dadi kam yakashe hjy domin ita macece meson ace komi Nata yafi na kowa,
bangaren su ummi kuwa tuni anje angano gidan faseelat matsakaicin gida ne, ciki da falo da toilet se waje kitchen store da toilet na waje da dakin khalil falle daya, tsakar gidan beda girma sosai se get dake makale da bangon gidan,
Baba babba yariga yabada kudin yimata furnitures se nanda 10days zaagama kitchen plaza kawai yaje yace ahada mishi all kitchen material, aka hada yana zaune ya Kalli kayan yace akaro, irinsu food flask da jugs set 5, aka hada kayan kusan million daya ba abinda babu har su gas toaster oven d. s.
Ya bada ATM aka cire, suna da motar kai kaya danhaka har kofar gida aka kai kayan aka zubasu a old garage nashi kafin ran jere.
Khalil kau sukan dan taba waya da faseelat amma ba sosai ba saboda rashin lokaci dabata dashi, gaskiya yayi missing dinta dan kullum da tunaninta yake barci.
Bayan sati,
yau faseelat shirin tafiya kawai take, gashi motar haya zata hau dole ta fita da wuri yanzu kusan 7am tana fitowa daga dakin tana kiran "dije.. Dije! Na shirya" sega ya omer
Yana kallonta yadda ta canza yace "zuwa nai muyi bankwana, zan wuce school ne kigaida ummi,Se nashigo daurin aure "
Bata iya bashi amsa ba ta bishi da ido, ganin ranshi bace yake, seta fara tuhumar kanta mima yasa ta fadamishi bata son auren gashi tabarshi cikin tunani, danuwa kenan me hana kansa sukuni saboda matsalar dayan danuwan.
Baffa dan yayar ummi shi yakaita tasha yanata tsokanarta wai ta kode tai kamar aljanna karta je ta tsorata mijinta.
Yana kai ta suka dau hanya,
motarsu ta samu matsala a hanya ga shi cikin daji, sukayi cirko cirko suna jiran su samu wata.
Da kyar suka samu ana daukarsu da dai daya wannan yasa se Maghreb taisa, se murna kowa yake,
harta kwanta kiran khalil ya shigo kamar karta daga se kuma ta daga, ya mata ban gajiya ta kashe.
Washe gari aka kai lefe gidan baba babba mutane suka fara zarya biyadin ma biyadin.
Seda yayi kwana biyu aka kaishi gidansu faseelat, ko kadan lefen be mata ba ,ba English wears ko daya se tarin atamfofi kamar me, haka de taje takai dinki.
yau saura kwana goma auren, kamar daga sama sega wata kawar hjy da suka dade basu haduba, bayan gaishe gaishe, kawar wadda ake kira rakiya tace naji ance danki zeyi aure "
Ummi tace "eh abu yazoma sauran kwana bakwai, "
rakiya tace "naji ance diyar hjy asiya ce wadda ke can kofar durbi wadda kukaje hajj tare "
Hjy ta washe baki "aiko haka abun yake"
Rakiya tace "kina aikinmi, Zaki hada jinin ki da nasu asiya, tobari infadamiki asiya ko kara ta aje alhaji maaruf be tsallakewa nasanta sosai munyi zama unguwa daya kafin su tashi, tariga ta mallakeshi, cewa ma akai danginsu wani lakani garesu inde aka kusancesu to shikenan Sun mallake mutum se yadda sukace, ke mi zaki hada jini da yan niger? Kinsan su da tsirface tsirface da shan kayan matan tsiya kamar danshi aka halicce su, aiba hakanan suke ba "
Hjy tsoro ya da baibayeta jikinta har kyarma yake yi saboda tashin hankali ,tace "aiko wlh dole afasa aurennan, muddin ina numfashi bazaai aurennanba kawai? Wlh rakiya tunda yaronnan yaje ganinta shikenan ya sauya ashe har an fara asirce shi wlh bazeyiwuba sam "
ta jawo wayarta ta kira alhaji,yana dauka tace "alhaji kataho gida ba lpya "
hularshi kawai yasaka ya nufi gida a 360....
[7/12, 10:59 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
1⃣5⃣
Rakiya tace "ni bansan me ya kaikiba duk matan da ke yawo a katsina ga sunan birjik in auren hadin kikeso ki sama mishi a dangi mana amma kinje zakija jubo wa kanki masifa, ke da danki sede kallo dan ita zata zama uwar ke kuma matai"
Hjy ta cire dankwalin kanta tana fifita da hannu wani gumi ne ke tsatstsafo mata tace " wlh rakiya kamar ammin asiri inata tunanin yarinyar da zan turashi wurinta se ita kawai tafadomun kuma naji inason abun amma tunda naga yanata rawar kai naji abun ya siremin, kibari de alhaji ya shigo bazaai bikin nanba wlh "
Rakiya ta tashi tsaye "to nikam zanwuce karya sameni anan Allah ya kyauta"
Dasauri ta zuri ta kalminta tabar gidan.
Baa dade ba alhaji ya shigo dasauri yanata tunanin me ke faruwa,
Yana shiga dakinta ya ganta se kai kawo take tana hada zufa yace "wai lpya de? Mi yafaru NE naganki hargitse "
Ba wani tunani tace "alhaji so nike a fasa auren khalil, kuma a anso masa duk kayansa "
Ya Saki baki yana kallonta yace "kina da hankali kuwa? Yau saura sati biki kike wannan maganar anriga angama komi se kice a fasa?
Ya jawo hannunta ya zaunar daita shima ya zauna yace "inajinki "
Tace "wlh alhaji se anfasa auren nan gabadaya duk gari fada ake danginsu yan asiri ne ni kuma inason dana dan haka dole a fasa shi "
Ya game hannunsa biyu ya saita su akan geme yana nazarinta yace "wannan ba magana bace kide nemo wani abun fadin, kuma aure kamar anyi angama ne "
Cikin tashin hankali tace "alhaji ya zakaimin haka? Inace ni na hada abun to yanzu na raba ai shikenan"
Alhaji ya zuba mata idanuwa he can't seee sense in her brain, yace "hjy are you out of your sense ?"
Tace "ni ban damu ko kakirani mad person amma a fasa aurennan kawai "
Ya tashi tsaye yana tafiya yace "ni inada hankali na inke naki ya bar jikinki, wa zan tura ya tunkari dattijon nan da wannan maganar? Mutane masu mutunci masu halacci, ki gama duk haukanki ki dawo dede na gayamiki, ni na fita wurin sanaata"
yayi tafiyar shi da ido kawai tabishi ita yake kira mahaukaciya, toyayi kyau, ta jawo waya ta kira khalil,
Yana school yayi saurin baro makarantar saboda muryar ta da yaji some how.
Yana zuwa ya shiga dakin yana binta da kallo dan haryanzu bata tashi daga zaunen da take ba yace "hjy lpya? "
Ta sauke tagumin da tayi tace "khalil ni na hada aurenka da faseelat yanzu kuma banason kasancewar sa "
Yace"bangane ba hjy"
tace "nade fadamaka ka gaggauta zuwa kasamu alhaji kace kafasa "
Yayi sauri ya tashi tsaye cikin tashin hankali, how he will live with out faseelat se kawai ya duke akan gwiwoyinsa ya hade tafukan hannayensa yace "hjy Dan Allah kiyi hakuri inma wani abu ya faru be dace kiyi wannan hukuncin ba, kiyi hakuri dan Allah wlh inasonta hjy "
tatashi tai kanshi ta falla mishi mari tareda cewa "shasha kawai katashi kaje kai abinda nace tunkan in saba maka"
Idanuwan khalil cike da hawaye hannunshi daya dafe da kumcinsa ya tashi tsaye ya fita daga dakin yanata zazzaro ido saboda tashin hankali, direct shagon alhaji ya nufa, alhaji naganinshi yasan ba lpy ba ya ja hannunshi ya fito dashi waje, suka matsa can suka zauna kan wani slope,
Alhaji ya fara magana "ka rabu da maganar saratu mutane kawai ke zugata, ita kuma ta dauka ka kwantar da hankalinka ka je ka cigaba da hidimiminka "
Khalil yace "tace dole se anfasa shi inde inason zaman lpy "
Alhaji yayi murmushi "kayi hakuri da abubuwan da zatai tayi komi ze wuce, nide ne me daura auren kuma se an daura "
Khalil jiki sanyaye yabar wurin be koma gida ba har dare koda ya koma ta rufeshi da fada alhaji ne ya saka ta dole tai shiru shikenan ta dauki fushi da khalil da alhaji ta dena bacci da duk wata hidima,
Yau kwana ukku kenan ana jidali amma da alamu de aurennan se anyi shi, danhaka ba bata lokaci ta tafi gidan rakiya suka shige daki,
Hjy tafada wa rakiya yadda ake Ciki rakiya tai shiru can zuwa tace "akwai mafita "
hjy tace "tame? "
Rakiya tace "kawo kunnenki kiji "hjy ta mika kunne rakiya tafada mata, se hjy tai kasake rakiya tace "Allah kuwa hankalinki kwance ba wani tension "
Hjy tace "kuma fa kai Nagode kawalliya shiyasa nike sonki" suka tafa hannu hjy tace "bari natashi na tafi se Kinzo har hankali na ya kwanta?"ta tashi ta tafi.
Shikenan hankali kwance ta cigaba da hidimar biki. Se kuma lokacin ta sakarwa alhaji da khalil mara,
Faseelat da friends nata sunata shirye shirye kuma tunda ta dawo ummi ta cigaba da nata gyaran ,gaba daya faseelat ta rame saboda tunani har yanzu ko digon son khalil babu a ranta tayi adduar tayi adduar shiru haryanzu batajin sonshi, duk wanda ya ganta se yayi tunanin ko rabuwa yasata rama kuma de it's normal thing mafiya yawan amare na rama,.
Yau saura kwana biyu biki yan biki tuni suka fara cika gida mutanen Niger su dije da ammah dasu fadila duk har suniso, anata hidima faseelat tasha kunshi anyi mata relaxer da kitso jelar gashin har kafada,tayi kyau sosai,
shima angon duk ya rame yayi wuri -wuri dashi saboda hidima, abubuwa sunyi yawa,
Yau din kuma akaje akaiwa faseelat jere, anata yaba kyan kayan har dakin khalil ansakawa kujeru da karamin gado.
Gobe NE daurin aure dukda de bawani event amma maza zasuuyi walima ita kuma faseelat yau sukayi setting, wannan yasa duk suke busy khalil rabindshi ma da faseelat tun jiya,
Can bayan Maghreb alhaji yaji duk bejin dadi tunda hjy ta sako fitina hawan jininshi ya tashi hakanan yake shan drugs be kwanta ba, yau abun yayi yawa gida ya dawo ya shige daki ya kulle, bawanda ma yagansa suna can ciki suna hidima,
Yayi kwance yana dafe da zuciyarshi yana meda numfashi,
Sega rakiya tazo hjy saratu ta jawota kofar dakin alhaji dan privacy, suna magana kasa kasa rakiya tace "inafatan kinnyi duk yadda malam yace? "
hjy saratu ta babbake da dariya "yo mi zanjira? Kede Allah yabarmu tare "suka cigaba da magana alhaji yanajinsu, gabadaya tunda suka fara magana hankalin shi ya tashi nan ciwonshi ya taso haikan, yanata meda numfashi yana fiddo, suko su hjy suna Gama magana sukabar gun bayan Sun kamo wata fira daban,
Alhaji ko zuciyarshi kamar zata fashe haka ya keji dandanan yafara karanto hailala yana ta memetawa har ya cika,
Se bayan ishai sosai wajen karfe 10 :30 hjy taje kofar dakin tasan de yanzu yaisa ya dawo ta fara kwankwasa kofar shiru gata kuma a kulle daga ciki, se ta koma ta window ta haska torchlight saboda ba haske dakin seta hango alhaji kwance, tai ta kiran alhaji amma shiru ta kwartsa ihu "ni yau nashiga ukku na Lalace ni saratu alhaji ya mutu "
ihunta yasa duk kowa ya fito su siyama da sauran yanbiki duk suka yo out, kowa nata sallallami suna leka windon itako ta zube kasa tanata ihu, siyama na kuka takira khalil ta fada masa ,hankali tashe yayo gida da temakon zarto aka yanke kubar suka shiga dakin, alhaji de ya mutu, kuka kawai sukeyi ba yaro ba babba dandanan labarin mutuwarshi ta game dangi da yanuwa,
Su ummi tunda akadamata tafara hawaye, Allah kenan me iko akan komi, shine kadai yakeyin komi a duk lokacin da yaso,mutuwa bata da notice kuma baajin alert ko wani sign zuwa kawai take, ana gobe daurin auren dansa shi kuma ya mutu,
Allah yajikan musulmai ya musu gafara.
Su faseelat anbaje kan bed itada friends da dangi labarin aure kawai suke yadda zasu kula da mazajensu se ga ummi da wannan labarin suma Sukai jingum jingum.
da karfe bakwai aka kai alhaji gidanshi na gaskiya, sabon gida inda mutum ke girbar abinda ya shuka.
tare da baba babba akai janaiza bayan sunkoma wurin zaman makoki shi da daya daga cikin wakilan khalil Sukai magana akan daurin aure zaa dagashi se next week,
Waccan dattijon ya juya ya na kallon khalil da kanshi ke sunkuye hannunsa kan gwiwa duk Bayan seconds yana share hawaye, ya girgiza kai.
Hjy saratu da siyama sunsha kuka kuma suna kanshi gidan biki yazama gidan makoki ,bayan kwana ukku da yawa daga cikin yanbiki suka koma gida kafin ran bikin yayinda yan niger tuni sunkoma gida senanda 4 days din.
Tunda abun Yafaru khalil ya sake komawa wani kala dan haryanzu a hurhurce yake, faseelat de takirashi ta mai gaisuwa, har yanzu basu ga juna ba,
*************
Bayan kwana hudu yau daurin aure yan biki tuni duk sundawo abubuwa ake da sanyin jiki,
Taro yayi taro a masallacin abu ubaida, bayan gama salla aka daura auren khalil usman da faseelat maaruf akan sadaki dubu 40 lakadan ba ajalan ba.
Ango khalil ansha tsadaddun hill din corver shoe's hakan yasa ya kara tsayi yasha milk shadda, as usual hular nan na kusa da ido se washe baki yake yana gaiswa da mutane a bangare guda akai walima da hotuna.
Bangaren amarya faseelat ............
yo Anya tayi wanka ma ita 🤔
[7/12, 10:59 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
1⃣6⃣
*dedicated to umar dalha my bazawari 😂 & all golden pen members luv u all*
Faseelat kau kukanta take ta sha tunda garin Allah ya waye bawanda besa baki ba amma taki tai shiru, da yake tana gidan baba babba,dan nan sukayi setting kuma nan zaa dau amarya,
Matasan yanmata irinsu fadila husna da manya irinsu fatouma da rahma Sun sakata tsakiya suna ta kallo kowacen su taci gayu banda faseelat, sun rasa kukan me take saboda cikinsu bawadda tasan batasan auren se fadila kuma bata fadawa kowa ba,
Baaba ta shigo dakin taga haryanzu faseelat bata bar kuka ba taje wurinta ta zauna faseelat ta dago jikakkun eyelashes dinta ta zuba mata amma kanta na a sadde, baaba tace "kiyi hakuri haka faseelat Kowa da kikagani dakin miji seda yaga irin wannan ranar, nasani akwai damuwa saboda rabuwa da iyaye amma hakuri akeyi, yanzu kina ta kuka so kike ciwo ya kamaki ne? "
Faseelat ta girgiza kai ,baaba tace "Tom kiyi hakuri ki tashi kije kiyi wanka tun dilkar safe har ta bushe jikinki kinki ki wanka kitashi, nasan zuwa yanzu an daura aure, kitashi ki shirya kuje gidan ummi wurin waazi kafin dare "
Faseelat hawaye suka kara zuraro mata ta share duk wurin Sun zubamata ido fadila ma ta danyi mata kwalla saboda ita kadai tasan reality na abun,
Rahma cousing dinta yar ban dariya bata da kunya ko kadan tace "baaba kubarta tayi kuka zata je gidan Sandar famfo ku barta tayi "yanmatan suka fashe da dariya,
baaba ta girgiza kai taja faseelat har bakin toilet seda taga shigarta sannan ta bar dakin,
Tana fitowa wanka wata kawarta makeup artist ce tai mata kwalliya, tsantsarar rar kwalliya wadda me karamin tunani baze iya ganinta ba, ta saka lace wanda daka ganshi kasan dole yayi tsada, white and red ga uban stones jikinshi head din ta ja, haka purse dinta da takalminta se tayi gyale da dankwalin lace din, wow sukaita fada, nan fa suka fara shooting pictures cikin farin ciki itako hjyar ko murmushi amma kuma tanayin kyau,
Kawarta ta zainab ta raba gefe ta kira abokin khalil ta fada mashi yazo ya daukesu zuwa gidansu faseelat din ,
Aliyu yaja khalil gefe daga cikin friend yafada mishi zeje daukar su faseelat, khalil ya dade besa sanyin idaniyar shi cikin ido ba, yace bari su shiga motar Mohammed su tafi haka akai har kofar gidan baba babba, aliyu ya kira zainab se gasu sunfito tunda suka fito yake kallonta feeling like going to hug her, suma mazan ita suke kallo sunajin inama tasu ce,
Itako faseelat da dai daya take jefa kafa jikinta a matukar sanyaye