Showing 120001 words to 123000 words out of 212110 words
kenan tashin hankali gabanta ysyi mummunar bugawa tai sauri ta latse kiran ta nufi dayan bedroom din ta tun kafin ta shiga wani kiran na fahad ya shigo.
Masturbation (istimnai) ya zama ruwan dare acikin alumma baga mata ba baga maza ba baga matan aure ba baga yanmata da zawarawa ba kai de bazaka taba shedar mutum ba tunda dole koda kuna kwana a makwanci daya bakomi nasa kasani ba kuma nasan de bazakabishi toilet ba kuyi wanka tare, yanmata da yawa su sukayi dis virgining kansu matan aure da dama basa gamsuwa da mazajensu sunfada harkar istimnai kuma sunsan illarshi, tomuji tsoron Allah de musan yana ganin mu a duk inda muke, kuma yanason masujin tsoronsa da masu kiyayewa saboda takwa,
Innallaha yu hibbul muttakin.
Innallaha maal muttakin,
Yaayyuhallazina amanuttakillaha laallakum turhamun,
Ittakillaha laallakum tuflihun.
Acikin alkurani me girma Allah yata kiranmu damuji tsoronsa kuma yafada mana idan munji tsoronsa ze bamu mafita acikin alamurranmu Allah kakara mana tsoronka amin,
Manzon mu manzon tsira(S.A.w) yace Kuji tsoron allah kamar kuna ganinshi idan ku bakwa ganinshi toshi yana ganinku, bukhary da Muslim.
[8/7, 7:45 AM] SHALELE: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽
*
We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
*Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
6⃣6⃣
Kamar karta dauka tai ta maza ta dauka takara akunne cikin fada yace "wayace ki mata karya?ke zaki iya dawomata da virgininty dinta ne ? "
Murya sanyaye tace "in mutum na aikata laifi kayi iyakar kokarinka wurin dawo dashi kan hanya yanzu idan nace mata bazata dawo dede ba zata shiga tashin hankali sosai maybe ma shedan yakara ingizata ta cigaba amma yanzu nasan zatayi kokarin bari kuma hankalinta ze kwanta "
Fahad yaja dogon tsoki zuciyarshi na zafi bazaka taba gane yadda yakeji ba se wanda yataba samun danuwanshi acikin mugun hali, yace "ta tayar da hankalin nata mana kikai mata wayar bari nadawo zataci ubanta ne"
Faseelat tace "a, a plsss karka mata maganar dagani se ita mukayi maganar bazanji dadi ba kuma zakasa ta cikin zullumi ka barta plsss "
Yakara jan tsoki yace "dukkansu aure zaai musu kowa yahuta"
Faseelat tace "sede safiyya da ita din amma ai salma bata isa aure ba duka fa yanzu take ss1"
Yace "har itadin aita fara menses da anmata aure am very sure bazatai shekara bata haihu ba "
Faseelat tadanyi dariya tace "to ai basuda mazajen se yaya? "
Yace "nanda dan lokaci duk zan samar masu maza, masu bakin jini kawai "
Faseelat takara yin dariya tace "Dan Allah karkayi haka auren dole bakaramin illa gareshi ba baida wata faida barinshi shine mafi aala mata nawa ne sukebin maza da aurensu saboda basusan mazajensu nide nan sheda ce, nawa ne suke guduwa subar auren, nawa ne suka kashe mazan wasu har su tsufa kiyayyar nanan wasu Sun fada lesbians dasauransu kasani bafa temaka musu ne zakai ba tilasta su su auri wanda bashi ne zabin zuciyarsu ba, ko ita lady in batason wannan din abarta har tasamu wani kagade yanzu istimnai ne kawai nangaba ko abun zewuce haka kabi asannu ahankali karkai gaggawa"
Yace "to naji malama, amma kibata shawara taso shi ta rufawa kanta asiri "
Faseelat tace "karka samu damuwa insha Allah zata amince "
Yace "alright bari nabarki kiyi bacci seda safe ki shafamin kan princess "
tace "I will do as u said take care "ta ma wayar kisss ta kashe taja doguwar ajiyar zuciya batai tunanin zeyi sauki haka ba, takai hannu ta taba wuyanta rau yake da zafi, har yanzu takasa fadamishi batajin dadi saboda karta dagamai hankali,tasha pcm ta shiga toilet sede tai alwala da ruwan dumi ta dawo ta shige duvet tana ma kyarkyata ,
Fahad ya dade yanata nazari akan abinda suka tattauna da faseelat se tunanin Mansura yake fuskarta she look decent amma tana aikata aika aika ,
Seda yafara biyawa ya yo masu take away sannan ya nufo gida yariga yasan Aisha tana can tana risgar kuka,
Yana shiga gidan direct bedroom dinsu ya nufa tana zaune kan praying mat tunda tagama salla take gun zaune kanta jikin gadon ta kwantar dashi tana ta hawaye,
yaje ya dora ledar hannunshi saman carpet din da take ,batare da ya sauya kaya ba ya haye kan bed ya kwanta rufda ciki yanajin takaicin aisha saboda shi anashi ganin yana kokari sosai da ze fiddo duk maitar shi akan faseelat dase zuciyarta tayi blasting,he don't know when and how wutar son faseelat kullum kara ruruwa take azuciyarshi, she's beautiful kind and obedient ,dutiful she have good heart as well more of it is she's better than zuma in bed 🤣he must be blinded ,
Aisha tai shiru takurawa ledar gabanta ido tanajin karin takaici yau ko dan hakurin da yake bata bazata samu ba,
Takara hawa sosai tai zaune taki tashi wasawasa har 11:30 amma be tashi ba kuma beyi shirin bacci ba kuma da alamu ba barci yake ba, tafara bawa zuciyarta hakuri "ki daure Aisha kitashi kije ke kibashi hakuri mijinki ne fa masoyinki ko zaki barshi ya kwana acikin bakin ciki? "
Ta tashi jiki sanyaye ta cire hijabin jikinta ta ta dauke dadduman tafita kitchen few minutes ta dawo da plate da spoon da fork tazo ta ajiye ta bude fridge ta dauko ruwa ta dawo tazo ta zauna gefen gadon ta dora hannu a samanshi murya sanyaye tace"yaya kayi hakuri dani plssss, nasan inada kishi amma ina kokari wurin danneshi, kayi hakuri akan abinda nayi dazun insha Allah bazan sake ba but ka tausayamin yaya ka rage wani abu wlh inajin matukar ciwo a zuciyata "
Yayi shiru bece mata uffan ba ko motsi ma baiba idanunshi a lumshe,
Ta kwanta kan shi tace "I'm sorry bazan sake ba I promise you "
Murya dishe yakira sunanta "Aisha! Tashi ajikina karki kara tabamin jiki nima "
Ta tashi zaune ta zaro ido cikeda mamaki yaushe yayanta yafara zuciya da abin?
Tafara hawaye ta riko hannunshi tace "Dan Allah kayi hakuri karkayi fushi dani bazan jura ba "
Batare da ya damu ba yace "leave me alone please"
taki sakin hannun bare ta tashi tace "plsssss yaya farin cikinka shine nawa kayi hakuri katashi wlh bazan iya bacci ba awannan halin "
Ya tashi zaune yana kallonta yace "bakison farin ciki na Aisha da kinason farin ciki na da kinso faseelat she's my happiness inasonta sosai ke kuma ba wacce kika tsana se ita, is she not my wife don me bazanyi waya daita ba, tell me for how many times nake hugging, kissing feeding naki in front of her amma take hakuri ita batada kishi ne kome? "
Aisha hawaye suka cigaba da kwararowa fuskarta wai faseelat is his happiness duk soyayyar data nuna mishi for long periods of time amma lokaci daya ya manta daita,
Zuciyarta na tafasa tace "kadena yimin kome agabanta while nima kadena mata agabana kuma in ita zata iya hakura ni bazan iya ba kuma daita ce a matsayina da abinda zatai se yafi haka "
Hawaye masu zafi na cigaba da zubowa tace mai "nagode sosai yaya da irin wannan soyayyar da kakemin a yanzu inafata anan gaba bazaka manta ni ba kamanta duk soyayyar dana nuna maka, I must hate that girl saboda ita hasken rayuwata ya bace, thanks u so much yaya for everything "
ta sauka daga kan bed din ta fita adakin tana kuka ta koma other bedroom ta zauna kan kujera ta cigaba da kuka hannunta dafe da zuciyarta dake ciwo takoina,
Fahad yayi kasake yana tunanin maganar da yaga ya mata he felt very bad, Aisha bata cancanci haka agunshi ba ta soshi ta mishi biyayya matuka bekamata so da bacin rai ya rufe mai ido ya furta mata wadannan Kalaman ba,
Yaja tsoki (tsoki master🤣) ya tashi yabita tanata risgar kuka ya shiga yana tsaye yajawota ya rungume yanajin tausayin ta sosai yakankameta kam kam ,
Aisha tana kuka tace "I love you yaya sonka a jinina yake dashi nataso tun yarinta plssss kamin koda digon wanda nake maka ne kafin na mu..."
Ya rufe mata baki yanafadin "shitttttttt"!!!
"nima inasonki sosai matata kiyi hakuri what I told you is not from my heart bakina ne kawai ya furta amma ba daga zuci bane, u r my first love kece nafara so kuma I value the love u do to me, kidena kiran mutuwa idan kika mutu ni inyi yaya? "
ta cigaba da kuka he don't have to lie at all kobe fada ba afili maganarshi take,
Ya dagota daga jikinshi yana kallon fuskarta yace " I love you so badly kece bugun zuciya ta Aisha ur my heart stop shedding ur golden tears,"
ya saketa yayi kneeling kasa da fuskar tausayi yace"im very sorry for all I have done to you now and before plss forgive me my wife "
Ta sulale kasa ta rungumeshi tana cigaba da kuka tana kai mishi kisss takoina sannan takara rungumeshi wani abu yaji yana zubo mai a gefen ido he don't know meye yasa hannu ya lakuto ya duba it's tears ya lumshe ido ya bude, hes deeply in love with faseelat amma kuma he love his Aisha too,
Yakara matse ta yana fadin" sorry "
bayan wasu mintoci tai shiru tana ajiyar zuciya ya dagota ya ma fuskar ta kisss ya dauketa just like baby ya fita daita,
a bedroom ya ajiyeta akan bed ya bude take away din ya shairr da yasiyo ya hau gadon yafara bata a baki, ta rika karba tana taunawa kamar filajin,
Tana cikin taunawa ya shafo gashinta hannunshi na kanta ta Kalle shi yace "I love you my heart beat "
Tadanyi karamin murmushi ta dauki spoon takai bakinshi ya bude baki yanata kallonta ta zuba mishi abinci a ciki, ya lumshe ido harda sauke ajiyar zuciya ta kurama beautiful face dinshi ido ta kai baki tai wa gefen cheek dinshi kisss,
Ahaka suka gama cin abinci ya dauketa suka tafi toilet sukai wanka cike da love acan yasamu yadan..... Sannan suka fito,
Shi yajawo mata wata pink rigar bacci yasamata yasa nashi sleeping dress sannan suka kwanta ya jawota ya dorata saman cikinshi,, ba dadewa tai bacci tana ta ajiyar heart, hannunshi a zagaye daita ya dora dayan ma yazagaye ta ya rumtse ido,
Har cikin dare faseelat batai bacci ba har cikin kasusuwanta takejin zafi haka tai kwance tana ta istigfareee,
Da asuba zazzabin ya sauka se kuma zuciyarta datai ta tashi ta shiga toilet taita amai batsaya wa, ta galabaita sosai tasamu ta watsa ruwa dan taji karfin jikinta tai alwala tazo tai salla tai kwance kan carpet takasa tashi ta tayarda su Mansura ba shiri bacci ya dauketa,
har Mansura ta tashi tai salla tana ganinta kwance tasan batajin dadi tawuce kitchen yi musu breakfast,
Se 8 ta farka tabude ido taga haske tangaram ta tashi tanajin juwwwa ta fita kasa, da nufin shiga kitchen ko step bata gama sauka ba ta zauna ta dafe kai cikin muryar wahala ta rika kwalawa lady kira "Mansura! Mansura!! Mansura!!!!! "
Mansura tafito daga kitchen dasauri tana amsa kiran faseelat ta mika mata hannu tace "temakamin kikaini daki juwwa nake gani"
Cikin tausayinta Mansura ta kamata ta tashi ta kwantar da kai kan kafadar Mansura idonta a rufe suka hau sama har kan bed tasamu ta haye kan bed din ta kwanta,
Mansura tace "sannu anty Allah yabaki lpy bari nakira umma nafada mata ta turo family doctor namu "
Faseelat tace "karki fadamata anjima kadan zan warke duk kwanakinnan haka nake amma da rana ana dan samun sauki"
Mansura tace "Dan Allah anty kibari inkira ta kar wani abu yasameki jikinki fa da zafi sosai "
Faseelat tace "zan warke ina amira ki tadata hakanan "
Mansura tace "to amma anty aibaa wasa da lpya ni zankira yaya nafadamishi "
Faseelat ta dafe kai tace "kincika kafiya nace kibarshi shima hankalinshi tashi zeyi idan yaji kuma bawani ciwo ne sosai ba "
Mansura ta juya ta nufi dayan bedroom din tasamu amira tafito wanka ta wuce kitchen ta ida aikinta tanajin ba dadi, tana gamawa takoma dakin faseelat tambayarta ko zata iyacin supergetti omelette da tayi,
Kwance tasamu faseelat ta rufe da bargo tana ta kyarma abun yabawa lady tsoro yadda taga tana makyarkyata,
Kafin tai magana
Wayar faseelat tafara ringing karo na hudu,
Mansura taje ta dauka ganin fahad ne,
murya sanyaye yace "honey yau ko gaisuwar safe babu kuma ina kira anki dagawa? "
Dasauri bakin Lady na in ina tace "yaya anty fa bata lpy tun kwana ukku da suka wuce take rashin lpy taki bari afadawa kowa jiya amai ta wuni yau kuma gatanan kamar ma bata cikin hayyacinta zazzabi ya rufeta "
Hankali tashe yanajin kamar ya bude ido ya ganshi kusa daita yace "u r very stupid seki shiru miye amfaninki ne wlh in wani abu ya sameta se jikinki yagaya miki nonsense"
kittt ya katse kiran hannu na rawa ya latso number marry ya danna mata kira,
Ringing 3 ta dauka takara akunne be jira gaisuwar da take mai ba yace "plsss go-to my home matata bata lpy nikuma bani gari I don't know actual abinda ke damunta ki temaka kije ki dubamin ita kiyi bakin kokarinki doctor "
Doctor mary tace "okay don't worry she'll be fine "
Ta katse kiran tana ma hospital tafito tataho gidan,
Mansura ce tabude mata tashiga ciki tana ta sauri, suna shiga ta yaye duvet din da faseelat ta rufa tafara gwadata jikinta yayi zafi sosai ta Kalli Mansura dake tsaye tace "sister ki samo ruwa da small towel kizo kina shafa mata ajiki "
Mansura ta juya ta shige toilet,
Mary ta duba tafin hannunta ta bude idonta ta duba ta debi jininta sannan tai mata allurai ta tashi tafita ta koma hospital don yin teste din jinin da kuma siyo wa faseelat drugs,
Mansura ta debo ruwan tazo tana shafawa faseelat amira ta zauna tahade kai da gwiwa tana kuka sede Mansura keta rarrashin ta,
Acan japan fahad nagama waya da Mary hankali tashe jikinshi na bari ya kira deputy nashi bayan ya dauka yafada mai yanada patient matar shi bata lpy she's seriously ill dole ze dawo Nigeria ya dubata yaga condition nata saura kwana hudu shi yazo yaida covering aikin, badan Mustafan yaso ba ya amsa mai,
seda yafara kiran daya daga cikin maaikatan jirgi yafada mai akwai jirgin daze tashi karfe 5 na yamma,
Sannan Fahad yaja mota se gida, ya shiga dasauri Aisha ta tashi tsaye tana kallonshi ganin duk baya cikin natsuwarshi, tace "yaya lpy de ko? "
Ya yamutsa fuska yace "faseelat ce bata lpy sosai to nariga nasa aimana booking yau zamu koma Nigeria "
Aisha ta zaro ido tace "aikin fa? "
Ya harareta yace "ana maki maganar lpy wake ta aiki bari naje na shirya mana kaya "
ya juya ya shige bedroom yafara masu parking Aisha takoma tai zauniyyarta ta turo baki gaba tace "dan Rainin hankali macen da jiya tananan tana zuba maka iskanci yau kuma ace bata lpy dukkabi ka rude kamar ance maka ta mutu mtssww "taita dumi itakadai,
Fahad na cikin hada kaya wayarshi tafara ringing ya dauka da sauri ganin mary ce,
cikin farin ciki tace "congratulation sir ur wife is one month pregnant"
He don't expect this nankusa 1month ai kwanakin auren ma ne, he hate pregnancy saboda yana hanashi jindadin rayuwa but he's happy his queen zata haihu nanda 8month,
Yayi murmushi yace "thank you doctor kinada tukwici me kyau inafatan ita she's now safe ?"
Marry tace "she'll be well very soon tanada white fever amma bata bukatar asamata jini zan kaimata wasu drugs yanzu insha Allah zasu temaka sosai but sede hakuri shigar karamin ciki "
Jin tace jini hankalinshi ya kara tashi yace "OK thanks you but kicigaba da kulamin daita I'm on my way to night "
Marry tace "u don't have to worry I will do my best "
Yace "thanks "ya kashe kiran,
He's happy one side one side kuma he's not saboda matsalar da cikin yafara zuwa daita yana wahalar mishi da mata,
Yana murna yakira umma, umma dake driving ta dauka tace "son gani ahanyar gidan yanzunnan Mansura take fadamin faseelat ba lpy "
Yace "ehmm umma" yana sosa kai ya cigaba da cewa "ai doctor tace she's 1 month pregnant "
Batare da jin kunyar maganar ba Umma tace "alhamdulillah this is good news gaskiya dole naiwa doctor din kyauta Allah yaraba su lpy I'm very happy "
Yace "thanks u "
Ya rage murya" umma plsss ki kulamin daita inanan dawowa anjima da daddare"
Umma tai dariya tace "wato ma bazaka iya hakurin 4days dinba to yayi Allah yakawo ka lpy "
Yace "amin thank you "
Yakashe kiran yana farin ciki sama sama yafita pallow yaje ya zauna kusa da Aisha yanata murmushi,
Aisha ta kalleshi tace "ya me jikinne "ganin yanata dariya shi da keda patient,
Fahad yajawota jikinshi yace "dasauki doctor nacan na kula daita, she's4 weeks pregnant "
Gaban Aisha yayi mummunar faduwa nan da nan zuciyarta tafara zafi,
Se tunanin baya ya fadomata tunda taga yadda fahad yasha wuya itama tasha wuya ga cikin amira shiyasa taje akasa mata implant na 2 years, bayan 2years saboda fahad yakara jindadi ta koma aka cire akasamata na 5 years, wanda shi bema sani ba kuma be damu da rashin haihuwar ba sedaga baya yagane be kuma mata fada ba,
Seda yayi 4years jin ze kara aure taje ta cire gashi haryanzu shiru ba ko alamun cikin gashi mommy batasan da maganar ba da hanata zatai, gashi yanzu daga shigowar faseelat zata haihu su zama daya, hawaye suka gangaromata tai sauri ta share kar ya gani tace "I'm happy Allah yabata lpy "
Yace "amin my heart beat "ya mata kisss,
Shiru sukai Aisha nata tunani itama so take tasamu cikinnan,
bayan wani lokaci bacci ya dauke faseelat se bayan azahar ta tashi batama san umma tazo ta tafi ba ta kurawa pop din dakin ido setaji kamar motsi a maratta ta kai hannu sama tai tunanin ko period zezo ta tashi zaune cike da dauriya,
Tana ta kokarin tashi su Mansura suka shigo amira taje ta rungume faseelat tana fadin "anty karki kara kyarma irin dazun kinbani tsoro "
Faseelat tai