Showing 177001 words to 180000 words out of 212110 words

Chapter 60 - Ragon Miji

10 Jul 2025

8331

baki,

mommy tace "sena ci ubanki da shiga maganar manya tashi kidaukomun gyalena ke Aisha da jikka ta ki duba a closet ki daukomun rapar 1k guda 3 tashi maza "


Aisha ta tashi tana share hawaye ta haye sama jim kadan tafito da kayan tabawa mommy tasaka suka fita,

Suna fita sadiya tafashe da kuka tace "Allah yaganar daku gaskiya"

Basu tsaya koina ba se gidan salma suna shiga ta sabo mayafi suka fito a motar ta suka nufi gidan boka gumurzun duniya suka lula kamar zasu tafi jibiya sannan sukabi hanyar datayi dankama suka cigaba da tafiya,

Sunayi suna labari mommy tace "inta haihu aini nabani bare inta haifi namiji shikenan ita zata cigaba da ruling gida in ita wannan banzar bata kara haifuwa ba shikenan natashi atutar babu nayi renon banza"

Anty salma tace "ki kwantar da hankalinki anty kome yazo karshe"

Sunata tafiya suka tsaya a bakin titi suka sauka sukabi wata yar karamar hanya tundaga kan titin kana hango rufin bukkar bokan, bawata tafiya sosai suka iso wurin yana bakin bukkar wurin ba rufi amma bakikirin yake kamar anyi rufin kwano gawani mugun wari dake tashi gawasu layu da kawunan dabbobi gefenshi, tunda suka tunkari wurin suka rikajin ihunshi da maganganun shi da bakaken aljanu wadanda yake musu hidima su kuma suna biya mishi bukatocinshi,

dukkansu ba wacce ta tsorata har gara mommy danshi kanshi bokan abun tsoro ne shirgegen kato ne baki wulik daga shi se dan bante ya rufe kugunshi,

Anty salma ta bude baki tana fadin "gafara de gafara de,"


Suka zo zasu zauna gabanshi nesa dashi,

Tunkan su zauna ya kwasa masu tsawa dukkansu seda suka tsorata muryarshi na amo yace "Allah ya gaza? Ya gaza ne "?

Dukkansu suka rika gyada kai suna fadin "eh yagaza"

ya kwashe da dariya yayi yan surutanshi da aljanu dawani kalar yare,

Duk suka samu wuri suka zauna,


boka ya kallesu daya bayan daya idanunshi kore kore yellow yellow yanata zaresu, ya nuna Aisha yadaka mata tsawa yace "me kkso a musu?"

Aisha ta girgiza ,jikinta na rawa tace "so nake a zubar da cikinta asa mishi tsanarta amma karya saketa yanzu harse ta kamu da ciwon zuciya"

boka ya babbake da dariya "hahahahahahahahaha bukatarki zata biya yarinya amma dan dukununu nason ganin tsiraicinki aljani betau yanason shan maniyinki,aljani mugu yanason ya sadu dake daganan kuma bukatarki tagama biya har'abada hahahaha "

mommy ta zaro ido waje jikinta yana rawa ta kalli salma ta banka mata harara,

Aisha zatai magana mommy tai karaf tace "muna zuwa boka zamuyi shawara"

Yayi ta dumumuwanshi kamar beji taba yanata juya hannuwa,


ta wurga musu harara duk suka mike suka bar wurin seda suka kai gaf titi, mommy ta kalli salma tace "amma wlh salma bakida hankali kirasa wurin wanda zaki kawomu se wannan bakin arnen wanda in ance rabonshi da wanka yafi shekara baa gardama ,ahakan ze kwanta da diyata wlh batayiwu wa dan nasan duk cutukan duniya babu wacce bazaa samu a jikinshi ba "

Salma tace "aa anty bawani ciwo kuma seme dan ya kwanta daita inde bukata zata biya Allah anty aikinshi na lasting wani lokaci mutu karaba"

Mommy tace "keni inason diyata ban shirya ganin gawarta ba bazan bada ita shida aljanunshi suyi wartambe da jikinta ba wancan katon idan yahaye ta na tabbata seta ji kamar bata taba sanin namiji a rayuwarta ba "


taja hannun Aisha tace "mutafi wurin dayan mugani"

Aisha ta riko gyalen mommy tace "mommy kibari plssss "

Mommy ta balla mata harara tace "inbari wancan laanannen Allan ya tumurmusheki? Lalle bakida hankali Aisha nida sauran hankali na"

Taja ta da tsiya suka shiga mota suka bi ta ring road sunata tafiya seda suka bullo cikin batagarawa suka kutsa kai can ciki can wata unguwa daba mutane sosai se daidaya suka faka bakin wani gidan bulo,

suka firfito salma nagaba tanajin haushin mommy ta bude labulen dake wani daki awajen gidan suka shiga,


wani dattijon mutum ne zaune da katon tray da kasa cike dashi ga casbaha yanaja zut zut kai kace ba abinda yake fada casbahar kadai yake ja,

suna shiga yadago yabisu da kallo da daidaya,

suka samu wuri suka russuna,


Sukai tsitttt, ya dukar dakai yayita jan carbi sannan ya dago ya kalli aisha yakura mata ido yace "mijinki yafi son amaryarki, yanzu tanada ciki yakara fifitata akanki?"


Aisha ta girgiza kai kamar kadangaruwa,

yasa yatsa yafara zane jikin kasar yace "ba'ita ce ta kashemiki diya ba dodon matsafa ya bukaci jininta suka bashi, bataiwa mijinki komi ba sonta kawai yake, me kkso a mata? "

tace "so nake yaji ya tsaneta sannan azubda cikin jikinta kuma data kamu da ciwon zuciya ya saketa"


ya cigaba da rubutu yana jijjiga kai,

mommy de shiru tayi wato Aisha seta dau fansa takeso ya saketa lalle Aisha ta azabtu sosai,


bayan lokaci ya dago yace "ze tsaneta bazeso ko hada ido daita ba, sede cikin jikinta baze zubdu ba saboda tana adduoi kuma cikin na yan baiwa ne dole se sunzo duniya sede akwai mafita idan cikin ya tsufa yakai watan haihuwa zakizo nabaki wani magani data fara nakuda ki mata turarenshi cikin kwana ukku yaran zasuyita ciwo su mutu su duka "

Aisha ta daga kai alamun ta yadda,


ya bude wata kwarya dake gefenshi ya dauko magani daya tallin tall kulle a leda ya mika mata jiki na bari ta amsa,

Yace "da kinkoma Gida kiyi turarensa akoina acikin gidan ki tabbatar ya shaki hayakin kafin awa biyu dayinsa daganan kuma aikinki zefara "

Mommy tace "mungode sosai tome zaa bada? "

Yace "zakubada 100k idan wata takwas sukayi zata dawo ta amshi cikon maganinta"

abun yawa mommy sauki da yawa, ta zuge zip na jaka ta fiddo 200k ta ajiye agabanshi tace "ga wadannan idan aiki yayi kyau yaran suka mutu zan kawo maka wasu 200k din "


malam yace "da kyau se kundawo"

Suka tashi suka fita sunata godiya,


Suna fita mommy ta kalli salma tace "keda kinsan wannan yafi sauki kika kaimu can? "


Salma tace "Ai kuma waccan aikinshi yafi lasting kuma dashine har cikin seya zube amma wannan ma semujira lokacin da yace "


Aisha na murmushi tace "nagode anty "

anty salma ta harareta tace "shasha seki meda hankali kiyi yadda yace, kuma kita abubuwan da shegiyar zuciyar ta zata buga karshen ciwo ma"

Aisha tai dariya suka hau mota sunata labari suka koma gidan anty salma daga nan suka dau motarsu suka wuce gidan mommy,

Lokacin marece yayi sosai acan gida faseelat suna zaune da hero a main falo tana jikinshi da shagwaba tace"hero ice cream vanilla essence plss "

yace "akwai fa acikin fridge bari na dauko miki"

Tace "nide bashi ba vanilla nakeso"

Ya dafa cikinta yace "baby kacika shan sanyi ka rage kar mura takama minkai"

faseelat tai dariya tace "yaji plsss yanzu nakeso sena sha nakejin dadi"

Yace "bari nafita na siyo miki bayanshi seme? "

Ta langwabe kai tace "mutafi tare mana kaga senaga wani abun danikeso din "

yace"bafa ki lpy honey kiyi zamanki"

tace "nide senaje "tai kamar zatayi kuka,

yace "no don't cry bari na daukomiki hijab "

ya hau sama ya dawo da hijab tana zaune yasa mata yakamata suka fita,

Suka shiga mota se oasis bakery ,

suna fita ya bude mota yafita yabude mata murfi tafito tana mai murmushi tace "thank you "

suka jera yana rike da hannunta suka shiga ciki,

khalil da yaje siyo musu bread da zasuyi breakfast gobe,yana ciki a upstairs sukuma suna down,

suna shiga tafara dube dube abinda ze burgeta bayan ice cream din,

sega khalil ya sauko seya hangeta, ya kura mata ido tsohuwar soyayyar da yake mata tuni ta dawo,

faseelat batasan dashi ba tana juyowa taganshi, yana payment, ta kalli dressing dinshi yana cikin maroon yadi black hula da takalma black kayan sun masa dede batasan lokacin da murmushi ya kwacemata ba, sannan tai sauri ta juya wurin fahad dake mata magana ita kuma hankalin na wurin khalil da yayi sororo yana kallonsu ganin hannunta cikin na fahad,

fahad zuciyarshi cunkushe yanata kokawa da kishin dake cin shi,

dandanan faseelat ta waiga ta kalli khalil gaskiya she's happy yadda rayuwarshi ta sauya,

khalil yaji yakamata su gaisa ya doso inda suke faseelat na ganin yataho ta daburce gabanta na faduwa,

Har khalil yazo gabansu da murmushi kan fuskarshi ya mikawa fahad hannu su gaisa,

Zuciyarshi na zafi memakon yabashi hannun seya wanka mishi mari

wanda seda khalil yakusa kifewa, idonshi jawur ya dago yasa hannu ya shafo gefen bakinshi yaga jini, ya meda kallonshi ga fahad daketa huci, ya kuma Kalli faseelat tana ta girgiza kai,

Be wata ba ya kaiwa fahad naushi a hanci nan take se jini yafara zuba,kobin jinin dake zuba jikinshi beba da zafin da yakeji yakara wankama khalil mari, tassss khalil ya rama,

Faseelat tafashe da kuka mutanen dake wurin suka taso suka ririkesu suna basu hakuri,

khalil ya fita daga wurin batare da yabibiyi ledar bread dinshi ba,

rai bace fahad ya jawota kiiiiii suka fito daga wurin ya buda mota ya wurgata ciki ya rufe ya zagaya ciki ya zauna, ya fiddo handkerchief yana goge jinin dake kara fitowa daga hancin shi,

faseelat nata kuka ta matso zata rike mai kai cikeda tausayinshi,

Cikin fada yace "karki tabani munafuka ina tare dake ma amma kina yiwa wani murmushi, marar kamunkai banza ballagaza sokuwa"yanata goge hanci yake maganar

tanata kuka tace "call me with every name hero amma wlh ba abinda kake tunani bane wannan shine khalil tsohon mijina"

kalmar tsohon mijina ta tabashi yace "kinsan kina sonshi meyasa kika rabu dashi?kika zo kika shiga rayuwa ta kika sani dole nafara sonki,meyasa baki tsaya gareshi ba tunda u love each other"

takara volume na kukanta tace "wlh bahaka bane ni kai nakeso...."ya katseta da tsawa" kimin shiru"

tai shiru tanata kallonshi yatada mota dagudu ya doshi gida,

daga gidan mommy Aisha ta dauko motar ta tadawo gidan tana ta murna, tunda tashigo taji gidan tsit taje kofar dakin faseelat takasa kunne taji tsit, tace "to ina sukaje? "

tace"amma hakan ma yayi bari nazo nai aikina kafin sudawo nasan kafin Maghreb dole su dawo,

jiki na rawa tashiga daki ta ajiye gyale da waya tafito da maganin taje falo ta jona burner dandanan tai jawur ta zuba maganin kaffff dandanan hiyaki ya turnuke gidan ga kauri dagaji anhada tsurface tsurface dayawa aciki,

ta zare wayar tarika yawo dashi tana turara gidan tana ta murmushi ,

harta gama shiru shiru basu shigoba tace "nabani karsuki shigowa fa "tana ta duba wall clock,

taji budewar gate tasaki murmushi ta tashi ta haye sama,

fahad na ajiye mota yabude yafita dasauri ya shige gida ranshi bace ba bismillah bakomi,

Yana shiga tsakiyar falon yaji kanshi na juyawa, yayi tsaye wuri daya ya dafen kan yana yamutsa fuska,

faseelat ta bude tafito tanajin juwwa na daukarta saboda kukan data sha, tana kuka tashiga gidan yana tsaye yaba kofa baya taje bayanshi tana kuka tace "Dan Allah Hero kayi hakuri bazan sake ba "

yayi mata shiru yanajin maganarta kamar kukan jakai,

ta dawo gabanshi tana kallonshi hawaye na zuba tace "kayi hakuri Dan Allah kadena fushi dani, banjin dadin ganin fushinka naci albarkacin cikin dake jikina "

yanzu a duniya ba halittar daya tsana kamar ta, ganin ta yake kamar karya agabanshi tana mishi haushi ya tsaneta he hate her like hell bayason ganinta bare jin maganarta,

ta bude baki zatai mishi magana ya dauketa da gigitaccen marin da seda ta zube awurin a sume, yaja dogon tsoki ya haye sama yashiga dakinshi, dashi ma yasha turare ya wuce toilet yana wanke fuskarshi da jini yabata yanayi yana kallon madubi seyakeji kamar bashi ba,

faseelat dama gata sauran ciwo tananan kife cikin hijab se 7:5 Aisha tafito tanata rera waka ta Abdul d one "kasani aranka kar infita inka barni abaya zansha wuya"

Tun kan ta sauko daga step ta hangi faseelat kife, ta tabe baki takarasa wurin tana tsaye tace "ke!!! Ke!!! "taji tsit,

ta duka ta dagota taganta sume tace "innalillahi ba yanzu ba my kishiya ina son ganinki a raye "

ta aje ta ta ruga da gudu ta dauko ruwa tazo ta sheka mata,

faseelat ta farko da tari da kuka hawaye masu zafi nabin fuskarta"

Aisha tai fuskar tausayi tace "sannu faseelat meyasa meki ne haka"?

batace mata komi ba tatashi tana dafe da cikinta ta haye sama zuwa dakin hero dinta.
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰







By






*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*




✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/





8⃣4⃣





*Dedicated to Lipton girl (nuriyya) writer ,Allah yakara miki basira sister,yakara hada kanmu*



*gaisuwa da jinjina ga yan golden pen writers association*
👇🏼
*omer dalhat* we miss you,
Beelat
Princess mazadu
Feaner
Deajer one love
Oum deedat
Fatima batula
Fareeedaty
Bintu
Dr fatee
Lipton girl
Ummee yusuf
Harira aliyu
*And all ina maku fatan alheri Allah yakara maku basira yakara hada kanmu*

Golden pen tsintsiya daya madaurinki daya 🤝🏼



Aisha ta tabe baki tace"kya fito yar issss ke matar so kullum kina nuna ke ta Allah ce dan kinga yana sonki yanzu ma gani ina kilbibin naki da kissar zasu kaiki"

Faseelat ta tura dakin ta shiga kwance ta hangoshi ya rufa da duvet ta matsa tana tunkarar bed din dayake kwance,

Kamshinta kadai yaji yaji duk ya rasa natsuwar shi, tunkan ta karaso muryarshi na rawa domin zazzabi ya rufeshi yace "karki sake ki karaso kusa dani I hate you and all about you dan Allah stay away from me natsaneki natsaneki leave my room now"

Tai still, hawaye nata zarya a kumcin ta anya taji dede kuwa bakinda ya saba fada mata so shine yake fadamata tsana saboda karamin laifi wanda be kamata akirashi laifi ba,

taja zuciya muryarta na sarkewa tace "hero it's me fa ur honey ur life kake fadawa haka kadawo cikin hankalin ka kishi be kamata yarika fidda kai tunaninka ba "

kamar ya dade kunnenshi beson jin muryarta yace "who's my life? U? God forbid ni banma taba tsanar wani abu kamar yadda na tsaneki ba just get out from here banason jin muryarki da gwara haushin kare daita "

Faseelat ta zaro ido waje tafashe da kuka batasan lokacin da ta ida matsawa wurinshi ba ta zagaya taga banshi ta haye gadon dasauri ta bude duvet din tana kallon fuskarshi idonshi a kulle ta kai hannu ta tallabo fuskar shi, hawaye na cigaba da zubo mata,

Ya bude ido yana watsa mata kallon tsana, kallon da yake mata yabata tsoro domin tana hango tsantsar kiyayyar da yake mata bata taba ganin kallonnan a idonshi ba yasaba fushi daita jibgarta amma takanga tashin hankali ne da fushi amma ba kiyayya ba,

Hannunta na rawa tace "meke damunka ne? I'm ur faseelat ni kake hadawa da karya? hero me kakeso ka zama? "

yaja dogon tsoki ya kabe mata hannu a fuskarshi dukda yadda yake ba lpy yatashi yajata tana ta turjewa tana kuka tana fadin "plsss kayi hakuri ka saurare ni " ya bude kofa ya turata waje tatai zata kaiwa bango karo tai sauri ta dafe bangon,

Ta waigo tana nishi tana hawaye hannunta dafe da cikinta take kallonshi,

idonshi kasa be kalleta ba yace "don't ever come to my room again I don't want to see you cos I hate you"gammmm ya meda kofar ya rufe,

Faseelat takara fashewa da kuka tana daga murya ta zame tai zaune wurin tana tayi ,

Aisha da tagama salla tana addua tai murmushi tace "yanzu kika fara kuka zaki ji yadda nakeji lokacin da yake wulakantani saboda ke"

Seda tasha kuka sosai sannan ta tashi, ta goge fuska ta shiga dakin Aisha da sallama bakinta,

Aisha ta amsa tana bin fuskarta da kallo,

Faseelat da muryar ta tagama shakewa tace "anty Dan Allah ki kira doctor ya duba hero bashi lpy"

Aisha ta aje remote tace "meyasa me shi ne? "

faseelat tace "zazzabi yake idan likitan yazo ze mishi bayani"

Aisha tace "Tom"

Ta dauki waya zata kira faseelat ta juya ta fita, Aisha ta kira likita tafada
Mai ya kamo hanya,

dasauri ta fita dakin ta shiga nashi yana rufe ta haye gadon ta bude duvet din ta kai hannu wuyanshi zafi rau tace "subhanallahi sannu yaya ga doctor nan zuwa "

yayi shiru ta kalli fuskarshi da tayi jawur tace "yaya meyasa meka a hanci fuskarka duk ta sauya" hankali tashe take maganar,

ahankali yace "I don't know "

Jin karar door bell ta zo zata sauka taje ta bude kofar ya riko hannunta idonshi a lumshe yace "stay with me please "

tace "yanzu zan dawo ga likita can yazo ze duba ka "

Ta cire hannunshi tafita dasauri, tabude wa okato suka hau zuwa dakinshi,

yana kwance okato ke dubashi yaga hancin shi jawur sosai,

Ya rubuta drugs yace "sannu ko,"ya kalli Aisha yace "madam let me gate him the drugs I will be back soon "

ya tashi yafita, Aisha takoma ta zauna, ta meda kanshi a cinyarta tana shafa gashin kanshi,

Faseelat na zuwa daki tayo alwala tazo tayi salla tun kafin tagama taji tanajin sanyi sosai, jikinta kuma tun dazu yayi zafi, bata damu da ciwon ba ta dauko kurani tana karatu,

Khalil ko da yafita yana cikin mota yana tuki yanata doka tsoki ,ya bugi sitiyarin mota yafi sau biyar yanajin mugun haushi da kishin fahad,

daga gaisawa?who knows koshine yarabashi daita ya dauke mata hankali,ina ma zega wanda yake communicating daita a that time, da seya mashi jina jina,


Yanata tunanin irin murmushin da take mishi da taganshi, yasaki murmushi unknowingly, he miss mace me kyau me halin kirki,abunda hjy tayi ya dawo mishi t
Yaja tsoki,

yana zuwa gida ya shiga jamila tataso tana "oyoyo yaya ina breadin? "

Yace "ban siyo ba, zande siyo din"


takura mai ido tace "meyasa mu lips dinka kamar sun kumbura"

Ya shafo wurin yace "nothing na dan bugene, ina khalil? "

tace "yana daki na kwantar dashi yanzu nakeso na goya shi Maghreb ta kusa "

Yace "OK bari nai alwala natafi masjid"


Dakyar faseelat tasamu ta gama karanta suratul mulk ta koma saman bed ta haye ta rufa da bedshit ,

Hawaye masu zafi sunata yawo a fuskarta,


Doctor ya dawo kawo maganin Aisha tabawa fahad,

bayan ishai,

Tareda aisha fahad yayi salla suna gamawa takamashi ya koma kan bed ya kwanta ,

tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login