Showing 174001 words to 177000 words out of 212110 words
kwai takoma daki taci, dukda bawani cin kirki ba,
Da Maghreb tafito ta dora girki don girkinta ne,
sede faseelat bashi ta ciba don cewa tai bazata iyaci ba tace ice cream takeso ya fita yasiyo mata da yawa yaajiye a fridge,
Shi kanshi bewani ci abincin kirki ba yatashi yakoma gunta ,Aisha tagama takoma daki tai shirin bacci, shiru be shigo ba se 12:am yashigo,
fuska ba walwala yaje ya kwanta,yabata baya, tanata kallon bayanshi tace "yaya baka min adalci kiri kiri kafifita faseelat akaina kana shiga hakkina sosai seyanzu zaka shigomin? "
abun yabashi takaici beko juyoba yace "kede anyi marar imani Aisha kin sauya yaushe zuciyarki takoma haka, faseelat bata lpy ko rantsuwa nayi haryanzu baki mata sannu ba, baki jin ko tausayin wahalar da take yanzu haka nabaro ta tana ta makyarkyata wlh daita ce bazata bari na kwana can ba zata barmiki kwanan amma ke dayake bakida hali har korafi kike Aisha! Aisha!! Anya wannan halin naki ze barki zama lpy, cikin data samu samm baki farin ciki dashi sema bakin ciki da kike lokacin da nasameki ai kuka kike,wanda nasan faseelat bazata miki bakin ciki ba don kinsamu ciki ita batadashi ,adalcin da kike cewa ayi bazaai ba, zuciyata ta fison faseelat ba jikinta kadai nakeso ba harda zuciyarta da halayyarta me kyau wadda ke kika rusa taki, inason faseelat ina tsananin sonta insha Allah zata samu lpy kuma zata haihu lpy lau sede masu bakin ciki su mutu "
tun kafin yadasa aya tafashe da kuka me taba zuciya har sarkewa takeyi tana kuka tace "I pray so Allah yadauki raina na mutu tunkafin bakin cikinka yakasheni u hate me yaya tunda kasamu faseelat baka ganin kyaun komi nawa while abaya kasha yabon halina da komai nawa nagode da wadannan kalaman "
haryanzu be juyo ba yace "kin sauya hali ne Aisha kisamu ki medo kyawawan halinki nada kuma koda zaki medosu wlh faseelat tafiki aguna , saboda tana son duk abunda nakeso, tana sonki Aisha ke kina wulakantata taso amira fiyeda tunani donme bazan fi sonta ba nace I love her I love her badly itace rayuwata "
Aisha tatashi numfashinta nason daukewa tafita tana kuka ta sauka falo tai hanyar kitchen,
Jin yadda numfashinta yasauya yasa yaji tsoro tana fita yabita,
ta na shiga kitchen ta dauko wuka ta dagata sama tazo zata sokawa cikinta yayi sauri yarike hannunta,
Jikinshi har rawa yake saboda tsoratar da yayi saura kirisss ya kwasheta da mari, idonshi jawur yake kallonta,
Itako tanata kuka idonta kulle ta gaji da rayuwa gwara ta mutu kowa yahuta,
Ya amshe wukar ya tillar murya sarke yace "Aisha kashe kanki zaki? So kike ki mutu kafira ki dawwama awuta? Aisha meyasa baki amfani da ilimi da hankalinki, nayi zaton maganganun da nake miki zaki koyi wasu abubuwan da nafiso kirika yinsu segashi kinason kashe kanki ki karamin bakin ciki akan rashin amira, waya fadamiki banasonki? I love you so much Aisha"
Se hawaye zarrr a fuskarshi zuciyarshi na zafi yacigaba da cewa "ina sonki sosai Aisha ina kuma girmama sonda kikemin domin ke masoyiyace, kina sona tsakani da Allah na shaku dake ya kike tunanin zan iya jure mutuwarki? donme zaki zabi mutuwa akan rayuwa? Yesss I know myself ina shiga hakkinki ina nuna fifikon son faseelat, meyasa bazakimin uzuri ba meyasa bazaki rokamin Allah in rika adalci tsakaninku ba se kizabi wannan hanyar ?ya kkso nai da rayuwa ta ne ina bakin kokarina wurin dedeta ku amma nakasa kullum nakan roki Allah amma shiru Aisha in kika kashe kanki mezan cewa mommy ta rikeni kamar danta ta goyani tamin duk gata "
(kai wlh makoshina har wani tururin bakin ciki yake)
Aisha daketa kuka zuciyarta na harbawa dasauri numfashinta nayin kasa tazo zata zube yayi sauri ya tallabeta jikinshi,
Yana duba fuskarta ta suma kuka ya kwace mishi ya rungumeta yana kuka wai ya zeyi ne ya zeyi da rayuwarshi,
yasamu ya dauketa ya haye sama daita, ya kwantar daita ya dauko ruwa a fridge masu shegen sanyi yazo ya kwaramata,
taja dogon numfashi ta cigaba da nishi zuciyarta na matsanancin ciwo tanata sheshsheka, a tsorace yakira doctor,
ya zauna ya rungumeta yana kuka yana mata magana "Aisha inasonki sosai dan Allah kiyafemin bazan sakeba"
(shege yo bakai kace ta mutu ba🤨)
Likita na zuwa ta dubata tai mata allurar bacci, sannan tadago fuskarta daure da takaici tace "Sir meyasa ake bata mata rai bayan namaku gargadi Adena bata mata rai ,in aka cigaba da haka very soon zuciyarta zata buga, ku bincika abinda takeso arika yi mata shi batada lpy sosai zuciyarta ta kumbura sannan bp dinta is high kukula sosai, ga wannan drugs zuwa gobe asamo mata su they will help I mean help not to cure "
ta tafi ranta bace yananan dafe dakai har 4:30 na dare sannan yatashi yashiga dakin faseelat tana ta bacci amma jikinta rau yake, yajuya ya fita ya koma gun Aisha,
Da safe Aisha ta farka kusan karfe tara lokacin har yagama bawa faseelat breakfast yayi wanka yana zaune gefenta don yaga bata farka da wuri ba hannunta cikin nashi ya rike, ahankali ta bude ido ta kalleshi,
fuskarshi jawur yace "kimin hakuri Aisha bazan sake bata miki rai ba kiyi hakuri ki rayu ki kara haifamin yara "hawaye suka zubo mishi,
ta lumshe ido tabude tace"kadena kuka yaya ,zansha ruwa"
Dasauri ya debo ruwa yabata tasha yakaita toilet ya wanke ta yadawo yasa mata kaya ta kabbara salla, tana gamawa yafara bata tea abaki,
be fadawa faseelat Aisha bata lpy ba donkar ta damu kanta, itama jikinta yayi tsanani shi yayita jinyarsu duka biyun,
bayan 3days Aisha tasamu sauki seta rika yin girki harda na faseelat,domin faseelat jikinta basauki kullum amai, zazzabi daya sauka yadawo,
in girkin faseelat ne yana dakinta inna Aisha ne har tsakar dare daya falka seyaje ya dubo faseelat hakan bakaramin bata ran Aisha yake ba,
Har akayi week kuma lokacinne akayi bikin sabeer da fatouma, radiya tayi kuka daren amma dan karfin hali wanshekare ita tai musu girkin breakfast ta aika me aiki ta kaimusu gidansu, sam fahad bewani bada gudumuwa wurin bikin ba don rashin lpyar faseelat bata bari ba,
Yau de faseelat yana shigowa da dare wurin 2am wurinta idonta biyu ta riga ta tsaya tayi tunani gwara takoma gida shima yahuta yasamu ya rika aikinshi yadda yakamata,
yana shigowa yaga idonta biyu yaje yazauna gefen bed yakai hannu yataba jikinta yace "sannu honey "
murya irin ta marassa lpy tace "Dan Allah Hero kamedani gida idan nawarke sena dawo"
wani banzan kallo yake jifarta dashi yace "da lpy suka ba nike sena medaki can don baki lpy?meke nan hakan? kiyi hakuri plsss "
Tace "naga kana shiga hakkin anty ko girkinta ne har dare sekaita shigowa kuma nasan hakan baya mata dadi "
yayi shiru yayi kawaicin yayi kawaicin ko Aisha zata dan bashi dan lokaci yarika jinyar faseelat amma ina taki fahimta,
yace "dole narika zarya dan sanin halin da kike ciki, kuma wlh yanzu ko bacci nake tunanin cikin jikinki nake banason wani abu yasameshi, kiyi hakuri zan rage shigowan amma kirika kula da kanki hakan yayi?"
tadaga kai amma badan yayi ba,
yace "Tom seda safe kikula min da kanki"
ya mata kisss aciki ya fita,
Aisha data ji fitarshi ta tashi zaune tayi tagumi yana shigowa ya ganta zaune,
ya hau gadon ya zauna yana kallonta yace "Aisha kiyi hakuri da maganar da zanmiki ki kuma fahimceni "
tanata kallonshi taji me zece kuma,
Ya dafe kai ya furza iska irin maganar ta zama dolennan yace "Dan Allah inaso kibani 1wk inyi jinyar faseelat saboda tana cikin ciwo ahaka kuma kamar bana kyauta miki, ki daure kibani 1wk insha Allah in ma ta samu sauki kafin time din zan dawo "
zuciyar Aisha na kuna take kallonshi wato ita ta mutu wata ta rayu,
Hawaye cike da idonta batare da tabari sun zuboba tace.... ✍🏽
Follow me akwai cakwakiya fa agaba to Aisha zata yarda? Anya zata cigaba da jure wanann rashin adalcin nasa? Me zefaru gaba kubiyo shalele kusha labari,
up up up my brain kici gaba da kawo light please 😂⛹🏻♀🤸🏻♀
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽
We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
8⃣3⃣
*dedicated to me dambu,kinasani jindadi walle ,comment dinki nasani dariya sosai nagode Allah yabar soyayya😘me dambures🤣azubo mana idan ya gama turara 😂,*
*manzon Allah (S. A. W) yace wanda yaje wurin boka ko dan duba Kuma ya gasgata shi hakika ya kafirta abunda aka saukarwa manzo (S. A. W)* muslim
👇🏼
*Manzon Allah (S. A. W) yace wanda yaje wurin boka ko dan duba ya tambayeshi wani abu bazaa karbi sallar shi ba ta kwana arbain* Muslim
*adede wannan gabar dole ne nayi kira ga yanuwana mata, mata! Mata!! muji tsoron Allah musani cewa duniya ba matabbata ba ce, mu gyara halinmu mu gyara zukatan mu,manzon Allah (S. A. W)dama yace mafi yawa acikin wuta mata ne, meyasa bamu aiki da ilimi da hankali meyasa wasunmu basuda imani?saboda namiji kin yarda musulunci kin tuge imaninki sister kin shirya zama cikin wuta ko? zaki iya kisa saboda namiji ,yanzu haukan har mijin kashewa ake anya anya munaso mugama da duniya lpy kuwa ?kin watsa mishi ruwan zafi kin cire mai 🍌wata ta mishi yankan rago kin yanka jariri, kinyi zina, kinyi madigo kai tirrrr wlh ,mata idan har bamu gyara ba tun anan duniya semunga sakamako, zakiiya zuwa wurin boka kisa aiwa kishiyarki kurciya ko akasheta don kisamu miji,ko mijinku yana bakin kokarinshi wurin yi muku adalci kisa a juya tunanin shi yadawo sonki ke kadai saboda zalunci kirika juyashi son rai, ko mijinku baya muku adalci kikaishi yadawo ke kadai yakeso su sauran suma yadena musu anya muna son kanmu kuwa? Meyasa bazamu rika yiwa mazajen mu addua ba? Akan surika adalci, meyasa baza muyi hakuri ba akan jarabawar da muke fuskanta kinsan ladar da Allah yake rubuta miki saboda hakurinki? Baki sani ba amma seki kwashi kafa ki tafi wurin katon kafiri neman biyan bukata kin yadda imaninki kin Yi shirka, saboda namiji shi adalci ne beyi muku ba, kuma Allah baze barshi ba seya fiddawa kowacenku hakkinta sannan ranar kiyama zetashi da paralyzed,to shifa paralyzed ze tashi daita maybe Allah ya mishi rahma ya tafi aljanna ko yasamu ceto awurin manzon rahma, kefa? katuwar kafira mushrika me hada Allah dawani direct wuta kikai hjy ,domin Allah baya yafe shirka idan kinmutu akanta sede yakan iya yafe miki in kin tuba idan yaso, to kinada tabbacin zaki kai lokacin tubar? idan kika mutu agun bokan fa kafin ma kibaro wurinsa?idan kika mutu kafin ki tuba fa? To inamiki albishir da cewa ke yar wuta ce, idan har baki tuba ba ,maza ki tuba kafin lokaci ya kure miki, maza ki koma ga Allah kafin malaikan mutuwa yazo gareki, duniya mun dauketa kamar zamu dawwama acikinta,mundena Tuna lahira munata aikata aika aika kuma kina tunanin Allah ze miki rahma dan bacewar basira, idan aka tambayeki ma huwal iman cewa zakiyi laadari,bakiiya komai daga addininki ba amma kin iya biyar malamai da bokaye,abu daya kikarike (innallaha gafurur rahimm)inbaki tuba ba fa hjy? Ko ahakan kina tunanin shiga aljannar, kishin me? duniyar kanta Nawa take dukkanta ,donme baza mu hakura mu koma ga Allah da bukatun muba shine me biyan bukata ba wani ba, Allah(SA) yace bakomai bace rayuwar duniya se lokaci kididdigagge, bakomai bace duniya se rayuwa yar kadan , yace rayuwar lahira itace rayuwa , ya kuma cewa kafirai kuji dadi kadan sanan makomar ku wuta ce kuna me dawwama acikinta*
*ya Allah kakaremu daga aikata kowane sabo ka kara mana imani da tauhidi da tawakkali ya rabbul alamin*😭
*Allah yace mutuwa zata zo muku kuna masu shagaltuwa da duniya sekuce ya Allah ajinkirta mana se yace Allah baya jinkirtawa bawa idan waadinsa yayi*
*mu tuba kafin ranar da hannuwanmu da kafafuwanmu zasu bada shaida akan abinda muka aikata,ranarda zaa bijrowa kowace rai da abinda ta aikata,aranar ne kafirai zasu rika kuka suna cewa amedosu duniya zasu aikata aikin kwarai*
*Allah yace wadanda sukai imani kuma sukai aikin kwarai zamu sakamasu da aljanna koramu na gudana daga karkashinta suna masu dawwama acikinta ladar abinda suka kasance suna aikatawa,yace sune wadanda sukayi hakuri kuma ga Allah kadai sukai dogaro*
*mudage mu zama daga cikinsu yanuwa cikin wadanda hakurinsu da dogaro da Allah ze kaisu ajanna*
Hawaye cikeda idonta batare da tabari sun zuboba tace "nabaka kwana bakwan in ma bata samu sauki ba zakaiya wuce haka na amince"
Ya fiddo ido yace "dagaske? "
Tace "eh na amince"
ya rungumeta yace "nagode Aisha Allah yakara miki hakuri yakara rage miki kishi ya barmu tare har gobe kiyama"
tace "amin" tana yatsina fuska tade amsa ne kawai amma bawai don tana so ba,
Ya fara aika mata da kisses tai lamo tana jinshi yagama kidansa da rawarsa ya rungumeta har bacci ya daukeshi ita kuwa idonta biyu takasa bacci hawayen da batai ba seda tayisu zuciyarta na zafi ta tashi ta sha magani takoma ta kwanta har bacci ya dauketa,
tunda asuba da yayi wanka ya fita masallaci yana dawowa be kara komawa dakinba ya na dakin faseelat koda yafada mata Aisha tabar mata kwana 7 yake kawai tayi amma tasan Aisha bazata iya barin mata ba hakanan dole ranta beso ba tabayar,
can da rana zazzabin ya sauka, tace"hero muje falo mana mudanyi kallo kafin zazzabin yadawo yaushe rabon da na ko leka shi "
yace "angama sarauniya acikin zuma, yawwa dan Allah atemakamin plsss yau 1month inagani sede nahade miyau tunda yanzu da sauki kidan budamin kafin jikin yadawo I'm very sure da daddare bazan samu ba"ya kwabe fuska
ta yunkura ta tashi daga kan bed din tafara tafiya majestically yabita da kallo tana cikin tafiyar takusa kai kofa tace "nagudu dan yanzunnan duk yar lpyar dana samu seka kwasheta duk ruwan dake jikina se sun kare kan kabarni.."
bata rufe baki ba taji ya rungumeta ta baya ya dagata sama yana dariya yace "niba ruwan da lpyar dazan kwasa keda zan temakawa in kara miki ruwa da fresh milk medadin gaske "
Faseelat tana dariya tace "plssss banaso kabarni nayafe dadin nan"
Aisha tazo kiran fahad lunch taji sunata gaggabar dariya,
zuciyarta na harbawa ta juya daki idonta cike da hawaye, azuciyarta take magana "wai wannan ce zaace ma marar lpy tana ta kwasar dariyarta ahakan ciwo take, sunata soyewarsu a matsayin jinya ni ina kwasar aiki da bakin ciki ,bazan iyaba tafiya ta zanyi "hawaye suka wanko mata a fuska ta kwashesu da hannu ,ta bude wardrobe tasa hijab ta fita daga gidan,
suko sunsha dariyarsu da wasanni don kan bed suka koma hardasu jefe jefen pillows da bugu da wasa,
suna gamawa suka fita shi yawuce dining ga kuloli nan amma ba Aisha yahau yashiga dakinta be ganta ba yafita har garden koina bata, yayi tsaye yarike kugu yasande tana gidan mommy to meyasa bata fadamishi ba? ya daga kafada ya koma wurin faseelat beko ci abincinba,
Aisha na shiga gidansu tafita daga mota da gudu tana kuka tashiga gida,
Mommy tai zaman dirshan kasa sadiya auta na kwance kan cinyarta Tanai mata tsifa Aisha ta shigo tafada jikin mommy tana kuka, sadiya tai wuffff ta tashi zaune,
mommy na raba ido tace "Aisha menene kuma kede matsala bata karewa daga gareki "
Aisha numfashinta na sarkewa take magana "mommy yaya yadena sona yadena kula da rayuwata, faseelat ciki ne daita yaya namin gori yana fadamin ina bakin ciki nake daita "tafashe da kuka tacigaba da kuka tace "mommy yaya yazo yace nabashi kwanaki har seta samu lpy ze dawo gareni gabadaya hankalinshi yana kan cikinta kuma lpyarta lau wlh "
Mommy ranta bace take kallon Aishar,tana dasa aya tace "ubanshi yaci uwatai ita me ciki harwani lokacin lpy ne daita, saboda tana da ciki seya ida kashemin ke, dan ubanki meyasa baki fadamin tuntuni ba seyanzu "?
Aisha tana ta kuka tace "baniso in tayarmiki da hankali ne mommy shiyasa nai shiru"
mommy tace "aiko shegen cikinnan baze zo duniya da rai ba share hawayenki kingama kukan bakin cikin shi daga yau wlh "
"Ke sadiya tashi daukomun waya ta daki",
Tatashi ta tafi sama dasauri, Aisha nata ajiyar zuciya hawaye na kara zubomata mommy tace "shi har yaisa ya miki gorin haihuwa shegen cikin ze bare kuma dole yarabu da shegiyar nan"
sadiya ta dawo da waya hannunta ,mommy ta latso number anty salma takara akunne tace "auta kishirya wurin katon boka nakeso kikaini kowani jibgegen malami wanda dana fadi bukata ta tagama biya "
anty salma tace "tofa anty lpy meyafaru? "
Rai bace tace "kome ma yafaru fahad so yake ya kashemin Aisha kawai wai dan kishiyarta nada ciki shine yake mata gori harda cewa tabarmishi kwanakinta wlh bazan bari ba wannan karan kishirya gamunan zuwa"
anty salma tatabe baki tace "ai dama zuba maku ido nayi tuntuni yakamata ace anwuce wurin base yanzu ba da Aisha tagama wahala, niko keda malaman da zan kaiku gunsu aiki kamar yankan wuka, akwai boka gumurzun duniya ya kware da aikinshi ga lasting, akwai malan halilu megani har hanji kina zuwa ze biya miki bukatunki cikin sauki "
Mommy tace "gamunan tafe nagaji wlh ni kaina abun yana affecting dina some time bana barci idan nakira likita yana fadamin jinina yahau sede munzo "takashe kiran,
Aisha najin abinda tace tai tsit ita gabadaya hankalinta ya gushe mijinta kawai takeso yadawo gareta ta kowane hali,
Sadiya datun dazun take zare ido tace "mommy bade wurin boka zakuba?"
Mommy na harararta tace "can muka nufa ko sadiya "
sadiya tace "mommy kinsan fa Wanda yaje wurin boka yayi shirka kamar hada Allah da wani ne, kuma fa bukatunku bazasu biya ba seya so, meze hana anty takara hakuri kuyita addua in ma wani asiri aka masa seya kare amma karkuje wurin boka plss mommy "
mommy tace"ke sefa munje sena kwato mata yancinta duk wa yaja inba itaba danubanta inata bata shawara taki dauka, tunda nake ko malamin zaure bantaba lekawa ba amma yau dole ne se munje wlh "
sadiya zatai magana mommy ta kai mata bugu, ta janye tana tunzuro