Showing 207001 words to 210000 words out of 212110 words
late daddy sa dangin daddy sa,dangin mommy rago,dangin Umma sa,su Ummi sa sora daya na me jego,raguna hudu daya anbarwa yanuwan ta daya na dangin Abba akabarwa Ummi daya tayi rabowa makwabta dasauransu dayan aka tambayi faseelat tace akai gidan marayu suci suyiwa babies addua🤣
(Rabonnan fa da son kai su mommy duk yawansu daya😂)
Nan fa gida yafara harmutsewa da kamshi can 12 suka sauya wanka faseelat tai shigar atamfa orange color da white taji kudi itama da different sarka dafkekiya ta zinari,tanata murmusawa abinta,
Kafin laasar sunyi shiga ukku ana laasar tabuga sabon wanka katuwar shadda dark purple taji uban aiki da white sarka tanata walainiya ba jimawa sega me pics akafara masu hotunan tarihi,
To andeyi taro an watse lpy bawani kida bawani tashin hankali,
Bayan 3 days sabeer yatafi Turkey dubo amininshi shida radiya ,
Sunje sun samu ana wanke masa kafar suka jira likitocin na fitowa ya shiga idanun fahad jawur saboda ciwo hakan behana yana ganin sabeer ba ya fara murmushi
yace "wannan surprise din fa?"
Sabeer yayi dogon murmushi yace "nasone kaganni a sama nasan zakafi murna"
Fahad yace"I'm very happy ka zauna "
Sabeer dake bakin gadon yace "firstly de ya jikin naka?"
Yana kallon kafar da hannun,
Fahad yace "nagode wa Allah inata samun sauki ,seat plsss "
Sabeer yace"OK"ya zauna.
fahad yana kallonshi yace "duk ka sauya kullum u r adding weight kanajin dadinka nida ke daddy ko inata karewa"
Sabeer yace"zaka fara ko? Dukda baka lpy bazaka hakura ba ,ai munatare da radiya tana waje wurin Umma kasan nima nakusa zama dad fatouma nada ciki ai"
Fahad yace"masha Allah Allah yaraba lpy ba rabon najima inamaka gori"
Sabeer yayi dariya yace "mutane sun amshi account number naka nasan baka sani tunda baka tareda layinka ,nima de a hannuna inada kusan 30 millions da mutane suka bada nabaka "
Fahad yayi gajeren murmushi yace "thanks"
Sabeer yace"munyi magana da manager nifa I'm leaving there company tunda basu daukar kaddara nama fara neman aiki "
Fahad yayi murmushin takaici yace"me too ai don nariga nagama yanke shawaran dana koma zanmeda musu kayansu na kwashi nawa"
Sabeer yace"hakan shine dede su samu wasu wadanda sukafi mu we don't care"
Shigowar su Umma yasa su yin shiru suka zauna radiya ta gaidashi ya kalleta so daya ya amsa ta mishi ya jiki ,
Tunda ta shigo taji kamshin dakin be mata ba ,tai shiru tanata tara miyau abaki sabeer suna labari da fahad sama sama,amai ya taho mata ta dade baki tai toilet tana sheka aman mineral da tasha a jirgi ,
Saboda Umma dake wurin yasa sabeer betashi ba ,umma tabita tana mata sannu ,
Ta gama kakarin aman ta wanke baki tafito tana fitowa tana yamutsa fuska tai hanyar kofa zata fita,
Sabeer yana ta kallonta shiko fahad so daya ya kalleta ya kauda ido,
Umma tace mata "aah ina zaki ne? baku tashi tafiya ba"
Tana ya mutsa fuska tace "zanjirashi awaje"
Umma tace "ke kadai kizo ki zauna kinji kafin kutashi tafiya"
Radiya tace"idan na zauna amai zankara yi zuciya ta ketashi saboda kamshin dakin"
Umma ta saki murmushi tace"Ashe abun arzikine to Allah yaraba lpy sabeer katashi kutafi kadawo kai daya"
Radiya ta fita batare da ta waigo ba,
Dadi yakashe sabeer yanata washe wa ,
Fahad na dariya ya mika mai hannu yace"congratulation fa duka kagama cika aiki kayi kokari"
Sabeer ya rufe baki yana dariya ,Umma tayi kamar bataji ba,
Yafita ya samu radiya zaune akan seat na kofar dakin yaje ya rungumeta yana godiya takatse shi tace"wai miye kasan de banda ciki ko last week nayi mense to miye na murna"
Ya bata fuska yace"ban yadda ba ai mata nayin alada da ciki kitaso muje muga likita"
Tace"hmmmm"tatashi yakamata suka tafi ganin likita,
Doctor ya tabbatar masu tanada ciki 3month,sabeer nata farin ciki da suka koma hotel rawar shoky yayi tayi tanata masa dariya,
Sannan ya zauna yace "kifadamin mekkso inbaki a matsayin gift?"
Ta turo baki tace"abinda kabawa fatouma mana"
Yayi dariya yace "banbata komi ba se ledar jini guda daya"
Radiya ta fashe da dariya ta leme kan bed tace"asamin tawa ledar jinin"
Yabita ya danne yana mata cakulkuli sunata dariya seda suka gaji suka sheme kan bed suna meda numfashi suna kallon juna suna sakin murmushi,
Sabeer yace"inasonki matata da halinki kinada kawaici fatouma tayi ciki ke bakida shi amma baki kishiba"
Radiya tai karamin murmushi tace"saboda me zan mata bakin ciki akan abinda Allah yabata ,kuma cikinka fa ne koba komi nima diyana ne ni murna kawai nayi maka"
Ya lumshe ido yace "nagode sosai me kukeso a matsayin gift?"
Tace"naji fatouma na complain motar ta tamata girma sannan ni inason ka sauyamun wata saboda tawan tadena burgeni"
Yace"angama kuma zan karamaku wata kyautar surprise ce se kunganta "
Tace"thanks"
Ya zaro ido ya dafe goshi yace "bankira gimbiya ba namanta shafff bari nakira amin fadan da aka saba"
Radiya tayi dariya tace"fatouma kenan"
Ya kirawo fatouma ta cika tai famm donme be kira ba tundazu kuma yanzu sundade da sauka,
Seda tai ringing biyu ta dauka murya dususu tace"meyasa kakira aida kabari se kundawo sannan "
Ya langwabe murya yace "ayya gimbiya kinsan dubiya mukazo seyanzu na samu kaina amin hakuri"
Ta rage murya tace "nima Ai ban lpyar yakamata kunaisa ni yakamata kafara nema "
Yace"to amin hakuri ya jikin"
Tace"lpy"suka danyi hira sukai bankwana radiya na zaune tana kallon ikon Allah ita tana lallabawa shikuma yana lallabar wata,
Ya kalleta yace"toya na iya kinganni nakoma bawan Allah yazanyi tunda na kwaso masifaffa"
Kwanansu biyar suka dawo,
A bangaren su khalil ma dukkansu basu saniba Jamila ta kwasa seda yayi 2month Hjy tagane bata fadamata ba ta fadawa Khalil yayi ta murna harda biyawa Hjy umara dukda shi betaba leka saudi ba,
Seda cikin yafara motsi Jamila tafara hauka duka Khalil nada 9month ga ciki wata hudu taita kuka yayi rarrashin yayi magiyar takiyin shiru ya dauketa ya kaita gun Hjy Hjy taita bada hakuri sannan ta hakura,
Babies sunata wayo se kibarsu suke yi fahad kuma nata samun sauki,faseelat kuma nata shan gyara,
Bayan 70days aka sallami fahad domin ya wartsake da temakon Allah da adduar mahaifiya,
Ranaryafadawa faseelat gobe zasu dawo ranar kuma su Ummi suka meda ta gidanta aka gyara mata shi tasss ba zama tafara shirye shiryen tarbon angonta,
Ladidi na kula da yara ita kuma tana kitchen,
Tai dambun nama tai drinks domin wanshekare da wuri zasu sauka saboda yau da dare zasu taso,
Da asuba tatashi ta cigaba da gyara da hada abinciccika hardasu Umma kamar zatai hauka ga yara ga aiki,
12:00 ta gama ta shiga tai wanka tafito tazauna shafe shafe da murje murje tana ayyana rikitawar da zatai wa hero ,
Ta gama makeup tasaka riga da sket atamfa blue da fari da baki sun matukar amsarta tasha janbaki aka feshe da turare ,
Tasa anwa babies wanka na biyu tasa musu kaya suka fito falo suna kallo ,
Karfe 12:40suka sauka daddy yaje daukarsu har yayi hanyar gida fahad na sosa gemu yace "daddy afara kaini gida tukunna ita Umma bata da matsala"
Umma tai dariya tace"kai bama zakaiya hakurin muje kadan huta ba?"
Daddy ya juya ya dauki hanyar gidan fahad yace"da gaskiyar shi tunda yanada iyali can yakamata yafara sauka"
Umma tace "hmmmm"
Aitaga inda ake kula da mace da tana ganin daddy ne karshe ashe akwai Wanda yafishi,
Suna kaishi bakin gate ya fita ya leka ta window yace"Umma kugaida gida sena zo"
Suna dariya itada daddy suka tafi sunata labarin yadda yaran suke burgesu yadda suke nunawa juna soyayya,
Da sandarshi ya shiga yana cokana kafa kamar lokacin da akafara fita dashi tattaki ,yanata sakin murmushi,
Yana zuwa bakin kofa yafara knocking lantana tazo tabude ta gaidashi ya amsa yana murmushi ,
Faseelat batai tunanin shi bane ta ganshi ta mike tsaye tana ta washe baki tana murna tana niyyar zuwa ta rungumeshi taga yafara cokala kafa yana tahowa wurinta ,takoma ta zauna ta fasa kuka,
Fahad yadanyi murmushi ya karaso wurinta ya zauna kusa daita yameda ta kan cinyarshi tadora kai akadadarshi tanata yi,
yace"menene kikewa kuka bakison gurgu ko?"
Ta dago tana harararshi tanajin haushin maganar tace "dama zaka tabayin tunanin haka? hero ba saboda kyanka nake zaune da kai ba inasonka ne saboda Allah ,ina kuka ne saboda yadda ka koma kana me kafa kadawo marar kafa shine nakema kuka bawani abu ba"
Yayi dariya yace "toki kwantar da hankalinki kafata ta dawo normal mijinki ba gurgu bane ,ina miki wasa ne dama nasan u most cry "
Ta kumbure fuska tatashi ta shige bedroom da gudu ,yabi bayanta yana dariya ,
Yana shiga ta haye saman bed tayi rufda ciki ita me fushi,
Yayi dariya yace "inason haka " yafara cire kaya ta juyo taga yana sabule wando tatashi zata fita dagudu ,ya rikota sunata dariya tace "ka sakeni tunda baka yarda da ni ba"
Ya dora hannu saman kanta yana shafawa yace "ni naisa wlh wasa kawai nakeyi inason naga in zaki kuka I trust ur love wlh "
Ta turo baki tace"inanan ina shirin welcoming mijina kai kuma kana can kana tsara yarda zanyi kuka"
Yace "I'm sorry plsss" ya juyo daita suna fuskantar juna sunata kallon juna suna sakin murmushi cikin rada yace"show me how much u missed me kinata cewa u miss my" ya Dora hannunta akan joystick dinshi,
Ta rufe ido tana murmushi tace "I want to see that from u too"
Yace"OK let me show you "
Yafara un zipping rigarta yacireta ya wurgar going to sket ya cire shi and the pant sannan ya dawo sama wurin happinesses of his life her breast ya cire bra din sun kara cika sosai fin baya ,
A rude yafara murzarsu yana kai mata kisss ta koina , ta rikice tana meda mishi martani ya sungumeta yameda kan bed suka cigaba da rikita juna,
Ya kwantar daita yafara sucking dinta abunka game shayarwa sega ruwa suna fitowa a duka 2 breast din ta danne kan daya da hannu shiko yarike gudan yanata zuka ,
Jin abun ba na tsayawa bane tace"kai!!!! hero zaka shanye masu abincifa "
Tafara janye kanshi ya dan ciro yace "plsss let me akwai dadi sosai"
Tana dariya tace "to su suci me kai kuwa ga abinci can najiranka"
Yace"I don't want the food kibarni da wannan suma zasu samu"
Faseelat tana dariya tace "zaka sa nadena cire brezia ko zamuyi sex"
Yayi dariya yace "noo nabari bari naje nasha na can tunda shi is mine only"
Ya koma under yacigaba da sucking HQ nata,
Sun rikita juna sunyi kukan dadi sunyi na farin ciki suka shiga toilet sukayi wanka sannan suka fito ita ta sauya masa kaya tasaka yar gownt suka fito dining ,
Har tafara bashi abinci yatuna da babies ummansu duk tasa ya manta yace "ummuna kinga kin rikita ni har na manta da babies dina "
Tai dariya tace"yanzu kagama cin abinci sannan kagansu suna wurin nanny"
Yace "bahaka naso ba "
Ya cigaba da cin abincinsa seda yayi natt sannan sukaje dakinsu nanny tafito tabasu wuri ya rika daukarsu one by one yana masu kissss ,faseelat nata murmushi tanata kallonshi ya dago kai yace mata "ummuna kiniya haihuwa kiniya reno dubarsu tubarkalla sunata girma suna kara kyau"
Tai murmushi kawai tanata kallonshi da burgewa,
Ya kalli agogo ya ajiye Abdul ya tashi tsaye tace "ina zaka ? Ya kamata ka zauna damu wlh muna kewar ka"
Yace "yanzu zan dawo bada jimawa ba zanje naga mommy tana can tanason ganina zanje ganin bro sabeer shima"
Faseelat ta kwabe fuska yayi murmushi ya mata Kiss's yace "sena dawo"
Ya fita hankalin na wurin mommy,
Agidan mommy yaran duk suna school se 4 ko 6 zasu dawo,
Tana kwance ta tuna da akwatin kudin da ko kallonshi batayi duk kwanakin nan ,
Ta tashi ta daukoshi ta bude tafara kidaya bandir din domin tasan yawansu ta kuma boyesu sosai don dawowar fahad,
Tana cikin kilgawa Allah ya koro tutu cikin cikinta ,ta tashi ta wuce toilet,
Fahad yana shigowa falon wayam yanata murna yana kwalawa mommy kira ya haye step yana kiranta,
Tana toilet taji yana hawowa ko tsarki bata tsaya yi ba ta tashi ta fito dasauri,
Sede is too late don har ya shigo da mommy bakinshi fuskarshi dauke da faraa ganin jikkar gabanshi yasa fuskar takoma ja faraar ta gushe,yanata kallon jikkar da kudin da ke waje da ciki,
Mommy ma abinda take kallo kenan tana hawaye tai sauri takoma toilet tana kukan nadama,
Fahad kam be yarda ba yakarasa wurin akwatin ya dauki one bundle ya jujjuya idonshi jawur jikinshi na rawa,
Tabbas kudinne to ina mommy ta samu? se yafara tuna ranar yana gidan aka kirashi akamai maganar kudin this means mommy ta turamai arm robbers'
Ya juya ya kalli toilet din yana juyo kukan mommy dake ciki,
Kafafunshi na rawa yaje bakin toilet din yana bugawa da karfi yana cewa "open the door plsss, mommy come out kice u r not the one plsss come and say I'm dreaming"
Mommy na ciki tana ta kuka zuciyarta na ciwo,she feel dama ace ta mutu before wannan rana,
Ya zame kasa ya hade kai da gwiwa yana kuka me cin rai yace"why you did this to me mommy? if u want the money why u don't ask me wlh zaniya baki duka abinda na mallaka but u choose to send gang to my house what of sun ketawa matata haddi sun kashe megadi sun kashe polices duk saboda dalilinki da yanzu na rasa kafa saboda ke mommy me namiki?what I did to you that I deserve all this from u?"
Mommy tana ta kuka ya tashi yana kuka yafita gidan zuciyarshi nata ciwo ,
Tun a mota yafara aman jini be damuba ya nufi gida ,
Ya fito dakyar dafe da zuciyarshi ya shiga ciki yana layi ,
Faseelat na bedroom tana sauya bedsheet yashigo yafada kan bed din yana tari,
Faseelat tayi kanshi tana "innalillahi wainna ilaihi rajiun !!!!!hero meya sameka meya faru ?wayyo Allah na"
Yana ta tari jini na fitowa a baki da hanci hannunshi dafe da heart dinshi,numfashin shi yafara barin jikinshi,
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
9⃣4⃣
*Allah (S.A)yace :- wal asr,innal insana lafi kusr ,illallazina amanu wa amilussalihati wa tawasau bil hakki wa tawa sau bissabr*
*Manzon Allah (S.A.W)yace kaji tsoron Allah a duk inda kake kuma kabiyar da kyakkyawan aiki akan mummuna don ya shafeshi,kuma ka muamalanci mutane da kyakkyawar dabi'a*
Jijjigashi take tana kuka shi kuma yadade da dena numfashi tana ta kuka tana tari ta dauko wayarshi tana kuka tace doctor yazo ba jimawa ya kamo hanya,
Ta koma kan fahad tana ta kuka tana cikin tarin ta kako jini tasa hannu ta duba still de jini ne zuciyarta na ciwo amma ta mijinta take,
Sabeer jin shiru fahad be zoba ya nufi gidanshi atare suka isa da doctor shide yaga likitan ya shiga gidan dasauri,
Yanata mamaki yafito yabi bayanshi,
Doctor na zuwa faseelat tatashi tana kuka tana cewa "Dan Allah katemakamin baya numfashi baya motsi"
Doctor yafara bakin kokarinsa wurin ceto rayuwar fahad,
Sabeer na shigowa cikin gidan ya samu yara nata kuka dan faseelat ta aiki ladidi gidan Umma gefe guda ga kukan ita faseelat din,
Dakin yaran ya nufa ya dauko biyu masu kukan ya sabasu akafada zuciyarshi na bugawa ya nufi bedroom dinsu,
Yana shiga fahad na farkowa ya farko da tarin jini nakara fitowa ,sabeer ya rikice jikinshi yafara rawa,
Ga itama faseelat gefe tana ta tari hannunta akan zuciyarta,
Yakarasa cikin dakin dasauri yaisa wurin faseelat dake gefen bed yace"me ke faruwa ? Me ya sameshi?"
Tana kuka tace "I don't know Dan Allah sabeer ku temakamin plsss"
Ya mika mata yaran ta amshesu hannunta nata rawa ta rasa me zatai musu,
Shi kuma yaje wurin doctor dake kara duba chest dinshi ya dora kan fahad jikinshi yanata hawaye,
Doctor yakara dubashi ya mishi duk abinda yakamata hakan yasa tarin yatsaya jinin ma amma zuciyarshi bata bar zafin ba tade rage ,hada alluran bacci akamasa amma besamu baccin ba sede idonshi daya lumshe jikinshi kuma ya saki,
Sabeer ya kalli doctor yace"meke damunsa haka ?"
Doctor yace"heart attack ,zuciyarshi tadena functioning yadda yakamata as a result of stress,ku kula da abinda bayaso da Wanda yakeso adena fadamishi mummunan labari but for now he's safe akiyaye gaba"
Faseelat tana hawaye tace "he just leave here some minutes back segashi yadawo haka I don't know meyafaru da yasa shi wannan halin"
Doctor yace"maybe yaji abinda yafi karfin brain dinsa ne kukula dashi zanje nakawo drugs"
Sabeer ya kalli faseelat yace"check on her plsss kamar jini abakinta"
Faseelat tace"noo I will be okay "
Doctor yace"no let me help you "
Dole ya dubata yanata girgiza kai,ya tafi siyo masu drugs,
Lokacin me aikin ta dawo tafara kula da yaran ita,
Sunanan aka kawo maganin tasha sabeer yabawa fahad ,
Suna nan zaune sunata kallonshi har allurar tafara sakinshi ya bude ido ya kalli sabeer yace "friend meyasa komi ke faruwa dani ne ?se yaushe abubuwa zasu dena samuna?"
Sabeer na hawaye yace "kayi hakuri fahad komi ya sameka kafi wasu jindadin rayuwa "
Fahad yayi shiru yanata hawaye ,
Mommy ta dauki lokaci toilet hawan jinin ta yataso jin tana niyyar tafiya lahira sanan tafito tasha magani tai kwance tana hawaye batare da ta kauda kudin ba sede ta watsar dasu daga kan bed din domin bata bukatarsu ko ganinsu ,
Se bayan laasar sabeer ya tafi ganin fahad din yadan samu relief ,
Suma can gida Su ramlat sundawo suka samu mommy nata kuka suka zauna tayata,
Fahad na kwance kan cinyar faseelat tana shafa sumar kanshi tana hawaye tace "abbu plsss tell me menene yasaka a wannan halin ? u left here kana farin ciki kadawo cikin mawuyacin hali plsss tell me menene?"
Hawaye masu zafi suka zubomishi yace "bakomi ciwon ne kawai yazo "
Ta tsaya da shafar sumar tace "bana ganin akwai abinda yakamata kaboyemun a rayuwarka nice fa faseelat ur wife ur secret"
Ya riko hannunta yana hawaye yace "I will tell you amma its my secret banson kowa yaji ki boyeshi kamar yadda zan boyeshi"
Tace"I promise you bazan fadawa wani ba"
Ya saki hannunta yanata motsa baki yana so maganar ta fito yasamu yace"mommy is the one that send armed robber's to me ,can u believe it mommy ce ta turo a amshi kudi awurina"
Hawaye suka wanke mai fuska yace"mommy nafa the woman that take care of me and brought me up, nakasa yadda da abinda nagani some kudin da aka dauka awurinta akan gadonta faseelat wannan wace irin jarabawa ce takesamu na ?"
Faseelat tafashe da kuka tana share mai hawaye ta rika girgiza kai don itama takasa yadda tace"mommy baza