Showing 99001 words to 102000 words out of 212110 words
magana akan sallar asubar wanda abu dawood da turmuzi suka ruwaito......
ﻭﻋﻦ ﺑُﺮَﻳﺪَﺓَ ﻋﻦ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲِّ ﷺ ﻗَﺎﻝَ : « ﺑﺸِّﺮﻭﺍ ﺍﻟﻤَﺸَﺎﺋِﻴﻦَ ﻓﻲ ﺍﻟﻈُّﻠَﻢِ ﺇِﻟﻰ ﺍﻟﻤﺴَﺎﺟِﺪِ ﺑِﺎﻟﻨﻮﺭ ﺍﻟﺘَّﺎﻡِّ ﻳَﻮْﻡَ ﺍﻟﻘِﻴﺎﻣَﺔِ » ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑُﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ
_An Kar6o daga *Buraidah* Daga Annabi Yace: *“Kuyi Bushara GA Masu Tafiya Cikin Duhun Dare Zuwa Masallaci da Haske Cikakke Ranar Alqiyama”*._
"kuma kasan ranar alkiyama duhu ne wanda mutum baze iya ko ganin tafin hannunsa ba, sukuma masu zuwa salla cikin dare manzon Allah (S. A. W) yace ayi musu bushara bazasu ga wannan duhun ba ,shine nake maka kwadayin samun wannan hasken mijina " ta langabe kai ta kamo hannunshi,
fahad yayi murmushi yace "Nagode *maratussaliha* inajin dadin gyaranki gareni ko da yaushe kikasance me nunamun mafificiyar hanya nikuma zanbi insha Allah "
Faseelat ta yiwa hannunshi kiss tace "thank you for understanding "
Fahad ya turo baki yana nuna cheek dinshi yace"u supposed to do it here fa instead "
Faseelat tana dariya ta yaye bedsheet din jikinshi tana fadin "zaka makara sekayi sauri "
Ya tashi yana mikar shakiyanci ya shige toilet,
Faseelat tai dariya ta girgiza kai ta hau carpet ta kabbara sallar rakatanil fajr,
Seda yayi brush yayi alwala yafito lokacin har tagama tana zaune tana azkhar tayi sauri ta gyara shimfidar carpet din zuwa gicce,
Ya saka jallabiya ya juyo yaga ta gyara carpet, yace "what ? Again "
Tai murmushi tace "nufi na kayi rakaatanil fajr kafin katafi inkaje inbaa kabbara ba sekayi tahiyyatul masjid kafin atada sallar "
Fahad yayi murmushi yace "angama ranki shi dade "ya kabbara sallar 3mnt ya gama ya tashi ya fita zuwa masallaci megadi de nashan mamaki koshi yasan anyi amarya,
Bayan tagama salla ta zauna tayi azkhar wadanda suka samu ta tashi ta nufi kofar Aisha,
Aisha nata bacci jin ba ko motsi faseelat ta fara knocking, Aisha ta san dakin bude yake cikin jin haushi tasan bewuce faseelat tace "waye?"da karfi,
Faseelat tace "anty ni ce dama cewa nai anyi salla "
Aisha taja dogon tsoki tace "sannu diyar liman jikanyar sheikh"
Faseelat batama tsaya jinta ba ta wuce dakin amira, amira da se bakwai, 8 take tashi wani lokaci ko sallar batayi, faseelat ta tasheta itada kanta ta kaita toilet tai mata alwala Tawuce daita dakinta,
amira tai salla faseelat ta dauko kurani tana kallon amira tace "princess wace sura kike? "
amira makarantarsu akwai ta hafeez bayan bokon kuma suna hadda tace "suratul fajri "
Faseelat tace "OK kingamata? "
Amira tace "a, a anty muna aya ta 15 zamu tashi ta sha shidda, "
Faseelat tace "OK yanzu zamuyi murajiar na baya se mu cigaba "
Suka fara karatun har ta 15 sannan faseelat ta dora mata,
Suna cikin karatun fahad ya shigo, abun really surprise and impress him yayi tsaye yanata kallonsu cikin burgewa be saba ganin amira a irin wannan time dinba suko basu dena karatun ba ,
da yanata sauri ne yazo yakara wa faseelat gajiya se kuma ya samesu ahaka ,
Cikin farin ciki ya juya ya nufi dakin Aisha,
Aisha faseelat tabar wurin amma ita batadena banbami ba "shegiya laanannar Allah wai wadda ke bin namiji da aurenta itace zatazo tana nunamun musulunci, fara me bakar zuciya...... "taitayi har ta gaji sannan ta tashi tai sallar tagama ta dawo ta kwanta gabadaya zuciyarta ta mata nauyi so kawai take ta fadawa mommy problem nata, ta dauki waya ta kirata, mommy da tai salla takoma ta kwanta bacci me dadi ya dauketa don itama bawani baccin kirki take yi ba ta dauka murya dishe ,
Aisha tace "mommy nabani faseelat zata kwacemin miji, mommy duk ya rude akanta wlh mommy bani lpya, jikina duk ya mutu baniya komai "
Mommy tuni bacin idonta ya kau taja dogon tsoki tace"banza sokuwa har seki tsaya bakin cikin kishiya ya kashe ki? Bayan fahad ba yayinki ya dena ba dan batan basira seki kwance taita yin yadda taso kenan? To bari kiji kitashi ki wartsake kifita ki kane kane da gidanki sede in ita ta tare daki, in kuma kikai sanya ita taita yadda taso ki kumshe dakin sakarai kawai, da batasan miya dace ba, ga saudat can da kishiyoyi amma ko maganar su batayi don ta masu fintinkau duk tsoronta suke se ke babbar banza se ankoya miki, seki tashi kifara hidimarki inkin ga dama "diffff takashe kiran,
Aisha tai tsit tana nazari batajin fadan mommy dan kotayi fada tana fadin mafita, tana niyyar tashi fahad ya shigo,
ta sakar mai murmushi ya meda mata hannunshi biyu acikin riga,
Tana kallonshi tace "good morning sweetheart "
Yaida isa kusa da ita ya zauna ya taba wuyanta yace "how are you feeling today"
Tace "better naji sauki "tana marmara ido
Ya sauke ajiyar zuciya yace "alhamdulillah I'm happy "
Aisha tadora hannu tana shafa sajenshi tace "thanks I missed you "
Ya lumshe ido yace "me too "
Ta sauka akan bed din tace "I'm going to the kitchen "
Yace "OK thanks you muje nima I want to sleep "
Suka fita tare,
faseelat naganin amira ta haddace don tana da kokari seta tashi tabarta tatafi kitchen don yin girki ita kuma amira ta cigaba da karatun,
Faseelat nashiga kitchen tai tsaye tana nazarin abinda zatai, ta yanke shawarar yin grilled fish da vegetable sandwich and black tea,
Shaf shaf tafara aiyukanta, Aisha na saukowa taji kamshi ta rike kugu ta shiga kitchen din taga faseelat daga ita se short tight trouser da armless riga tana ta aiki bako kallabi,
Aisha tabi bayanta da kallo cikeda kishi da balai tace "banza marar kamun kai mtswwwww "tana ta ballamata harara,
Faseelat ta juyo ta sakar mata murmushi ta kalleta up and down ta koma ta cigaba da aiki Dan bata da lokacinta ,
Aisha taja tsoki ta fita ta koma daki kamar zata fashe taita zagaye haushi takeji bataso fahad yaci abincin can,
Fahad na komawa ya samu amira nata karatu ya wuce ya haye gado ya kwanta,
Amira da kejin bacci ta tashi ta cire Arabian hijab din jikinta ta haye kan gadon ta matsa can kusa da babanta,
Fahad daketa kallonta yakara jawota jikinshi yace "har angama karatun? "
Ta daga kai tace "I'm sleepy "
Yace "OK sleep well"
Ta rumtse ido yana ta kallon fuskar ta yadda take matukar kama dashi duk duniya ba abinda yakeso kamarta ahaka shima bacci ya daukeshi,
7:30 faseelat ta gama ta harhada su a dinning table tafara aikin gyaran gidan kuma,
Se 8:00 ta shiga dakinta don ta gyarashi ta shiga wanka shi kadai ya rage mata ,
Tana shiga tagansu kwance sunata bacci ya makalkale abarshi ajiki,
Tsaye faseelat tai tana kallonsu cikin burgewa she wish amira is her daughter ta daga kai tace "Allah amin "tanata kallonsu tafara aikinta kwatakwata ma ta mance ciwon jikinta burinta gidan yayi tsafff,
Tana cikin aikin wayar fahad da baya kasheta kullum tana bude tafara ringing ,so daya ta kalli wurin ta cigaba da hidimarta,
Har ta shiga ta gyara dayan bedroom din wayar na ringing sede ringing din is very low,
Batabi takan wayar ba ta shiga toilet tana wankewa,
Shi kuma fahad umma ce keta kira, batasan zeyi aure ba se jiya kannenshi suka gani a instagram, tun lokacin taso ta kira amma dare yayi tabari har yau dukda de tasan baze dauka ba,
Har faseelat ta gama tai brush tai wanka ta gasa jikinta ta fito wayar na ringing ,cikin mamaki wake ta kira haka tana goge fuska da tawul ta matsa ta leka screen din wayar sunan da tagani yana yawo ya matukar bata mamaki *(bad woman)* keta yawo a screen din wayar, faseelat ta zaro ido waje gabanta na faduwa dukda batasan me kira ba.
*kusa nifa inbaku comments da yawa wlh barin typing zanyi har se randa nagadama don nima nagaji* eheee
[8/5, 6:09 PM] +234 815 712 7134: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
6⃣0⃣
*Dedicated to my fan's*
*Dan Allah ina cigiyar marubuciyar laifinane na manta sunanta amma tana cikin intelligent writers asso...,shiru ta boye me number dinta ya bani plssss donni fan's dinta ce*
Har kiran ya yanke ,tai shiru tana tunani to wacece kuma Bad woman? ganin batada amsa ta wuce tafara kimtsa kanta, bayan yan shafe shafe ta dauko wando pencil black color da yellow din riga da gyale black ta saka kayan ta zauna ta gyara gashinta tai styling dinshi wani ya zubo gaba ta dan kwantar dashi cikin gyalenta ta dora tana cikin fesa perfumes fahad ya bude ido ya zubasu kanta,
Tagama komi ta kara gyara daurin dankwalinta ta dan jujjuya taga komi yayi sannan ta juyo wurinsu fahad,
Fahad daketa kallonta tun dazu yana murmushi ganin yadda take ta kara gyarawa yayi sauri ya rumtse ido,
Faseelat ta isa wurinshi ta sunkuya tafara hura mishi iskar bakinta a kunne,
Dariya ta kufce mai yayi sauri ya rufe kunnenshi da kafada ,
Faseelat ta mike tsaye tana mai wani kallo tace "dama idonka biyu kenan ,oya tashi muje kayi wanka breakfast is ready there waiting for you"
Fahad ya bude ido yace "nai wanka kikace fa? Aini ke zakimin wankan "
Faseelat tai fuskar tausayi ta kalli jikinta tace "see me I already take my bath, harnayi kwalliya "
Fahad ya kalleta from head to toe ya tabe baki yace "I seen you ke bakisan kinfi kyau a tube ba? Shiyasa nakeso kimin wankan daga can seki kara kema "
Faseelat ta rufe fuska tana dariya tace "nide katashi kayi wanka "
Ya tashi ya rungumo ta ta baya yana sunsunarta yace "kinyi kyau sosai "
Tace "thanks you it's all for you "
Ya fiddo ido "haba? To bari na biya kwalliyar" ya jirkitota yafara aika mata da kisses, faseelat ta rika tureshi tana dariya take cewa "let me be I'm very tired "
Yaki denawa, dariyar su ta tada amira daga bacci ta bude ido ta tashi zaune,
Fahad yayi sauri ya Saki faseelat ya shige toilet,faseelat ta matsa wurin amira tace "princess kintashi kenan taso muje nai miki wanka muje muyi breakfast"
Taja hannun amira suka fita a dakin amira taimata wanka tasa mata kaya desame kala da nata tai mata simple makeup ta kamo hannunta suka fito,
Aisha ma gyaran daki tayi, ta zauna ta tsara kwalliya ta saka gownt ta shadda ash color ta fito ta shiga dakin amira ganin batanan yasa taja tsoki tace "wlh bakiisa ki batamin tarbiyar yarinya ba"
Ta fita ta sauka dining tana ta jin haushi, ta bude kula tai serving din kanta ta zauna tana ci don yunwa takeji saboda bataci abinci jiya ba, jin abincin yayi dadi zauu, ta ya mutsa fuska tace "a banza "
Faseelat dakin ta suka wuce fahad na gyara bottom din rigar shi Ta bude dakin, ya juyo yana kallonsu cikin burgewa, itama faseelat Kallonshi take tayi tundaga kasa zuwa sama shikuma yasaka yellow jeans da black shirt yayi matukar kyau jikin rigar an rubuta hug me darling, da yellow din rubutu,
Faseelat ta saki hannun amira taje ta rungumeshi ta dago tace "hero kayi kyau"
Yaja hancinta yace "ai ban kaiki kyau ba "
Amira ta taho tai tsaye fahad ya jawota jikinshi, zuwa can yayi breaking hug din Ya dauko waya yafara daukarsu selfie sunata farin ciki,
Bayan sun gama hannunshi rike da faseelat while amira na dauke a dayan hannun suka fito,
Aisha da take cin abinci ta dago tana kallonsu suna saukowa daga step ganin kayan jikinsu taja karamin tsoki,
Suna isowa fahad ya Saki hannun faseelat yaja kujera ya zaunar da amira yajawo ta kusa da Aisha ya zauna, faseelat ta zauna ta kusa da tashi,
Fahad ya kalli Aisha yace " nasan dole kiji yunwa dama "
Aisha tai murmushi ta kai fork baki,
Faseelat ta kalle ta tace "anty ina kwana ya jikinki? "
Aisha ta tsaya da taunar sandwich din bakinta, ta harari faseelat tace "naji sauki "ta yatsina fuska,
Faseelat tai murmushi kawai fahad daketa kallon faseelat yace "sarve us please kinyi zaune"
Faseelat ta tashi tsaye tana fadin "sorry my hero "tafara sarving nasu,
Aisha taita kallon faseelat tana mamakin ta wlh idan itace bazata taba sakin jiki ba, amma ita ko kunya bataji ta saki jiki ko nauyin Aisha bataji wai hero su Hero manja,
Ta zuba mishi ta ajiye a gabanshi ta dauko fork da knife ta dora mishi ta zuba mai black tea din ta ajiye,
Yace "thank you kinsan nakagara nafara ci don hanci na kadai ya tabbatar da dadin abincin "ya dauki fork yafara ci,
Faseelat tayi murmushi ta zubawa amira ta zuba nata ta koma ta zauna tafara ci,
tsitt wurin yayi se karar cokulla da wuka, Aisha ta kalli amira da fahad da suka dage cin grilled fish ta tabe baki aranta tace "see them plsss kamar basu tabacin grilled fish ba "
amira na taunar kifi tace "daddy! "
Yace "uhummm"bakinshi cike da kifi,
amira tace "wai nan anty Zatai ta kwana ne? "
Fahad ya kalli faseelat da take ta kallon amira suka saki murmushi,
Fahad ya meda kallonshi kan plate dinshi ya dauko tsokar kifi zai kai baki yace "siyo miki ita nai princess nan zatai ta kwana "ya kalli faseelat
Faseelat tai dariya ta kalli amira,
amira tace "daddy siye kuma? "
Yace "yess princess tariga ta zama tawa tana nan tare damu nangaba ma zata haifar miki sister "
Faseelat ta sunkuyar da kai tana dariya, fahad ya Saki murmushi, Aisha ta tashi fuuuu ta haye sama, kallo daya ya ma bayanta ya dauke ido,
Amira tace"daddy im very happy to hear that , friends nawa sunada kanne amma ni banida su nikadai ke zuwa school mommy taki tamin kanne yanzu se anty tamin,daddy ni bro nakeso "
Yana dariya yace "tell her namiji kikeso"
Ta kalli faseelat tace "anty I want brother not sister "
Faseelat daketa dariya jin dramar su tace "don't bother your self dear yan ukku zan haifo miki ke kadai, biyu maza daya mace kinji dadi ko? "
Amira tace "thank you anty I love you "
Faseelat tace "luv u much dear "
Tundazu fahad kallon kasa kasa yake ta mata jin ta kira triplet,
faseelat ta kanne mishi ido daya ta cigaba da cin abincinta .
Bayan sun gama suka wuce main pallo suka zauna kan 2 seater suna kallo amira na kan cinyar fahad,
Aisha dake daki tana charting ta fito daga kan benen ta kwalawa amira kira,
Amira ta tashi dasauri tace "naam I'm coming mommy "ta tafi da gudu,
Faseelat ta kwanta kan cinyar fahad tana lumshe eyes,tana kallonshi tasa hannu Tana shafar sajenshi ya lumshe ido yanajin sauyi ya dora tafin hanninshi kan gashinta yana massaging,
Faseelat ta lumshe ido cikin jindadi in law tone tace "Hero bacci nakeji "
Ya Saki murmushin jindadi yace "OK muje in kwantar dake"
Faseelat ta bude ido dasauri, yafara dariya yace "yess mana nima baccin nakeji "
Ta boye fuska,
Ya tashi dauke daita ya wuce room dinshi daita,
Akan bed ya kwantar daita ya tashi yafara balle boturan riga,
faseelat ta tashi dasauri zata gudu, ya cafko hannuta ya marairaice fuska "bawani abu zanyi ba zafi nakeji ne shine zan rage kayan jikina"
faseelat ta Kalli AC dake dakin ta daga mai ido tace "uhmmm akwai zafi"
Yajawota jikinshi yana dariya itako ta dakune fuska, ya rage dariyar yace "kefa kikace triplet zaki haifawa amira ba , kuma haifuwar triplet se an bada himma "
Faseelat tace "aini wasa nake mata dan Allah ka rabu dani haka ina bukatar hutu, tunda kasameni baka ragamin ba kuma ni zafi nakeji sosai "
Yace "ayya sorry sorry na yanzu baze zafi ba I promise you that "
Faseelat tace "nide a,a nagaji ban lpya "
Ya saketa yace "amma zan tafi wurin Aisha don bazan iya hakuri ba nariga na saba ina wuni ajikinta , ki kwanta ki baccinki bari naje "
Ya fara takawa ze fita faseelat ta riko hannunshi cikin zafin kishi ya juyo yana kallonta, tana turo baki tafara cire riga ya shafi sajenshi ya Saki murmushi ,
Ya rungumota yace "thank you karki ba kanki wahala bari na cire miki da kaina "
Har ta cire rigar ya balle bra din jikinta breast dinta suka fito ya hadiye miyau ya sabule mata rigar suka haye kan bed,
abun anata samun sauki bataji zafin wannan sosai ba don yabi sannu daita ,
12 :00 faseelat ta bude ido ta sauka akan bed din fahad na bacci, ta shiga toilet tagama abinda zatai ta fito ta shafa turaren fahad ta saka kayanshi ta fita kitchen tai tsaye not knowing what to cook for lunch, can de tace bari tayi alkubus da miyar ganye tafara aikinta,
Tunda jamila ta samu ciki bata kara zuwa gidan hjya ba gashi har cikinta ya kai 6 month hjya harta gaji da tambaya tayi shiru,
Yau khalil ya daukota daga asibity taje awo batare da ya mata magana ba yabi hanyar gidan hjya seda aka kusa kaiwa tagane tana yamutsa fuska tace "yaya gidan hjya zamuje? "
Yace "eh tana ta tambayarki aikin dade bakije ba "
Tace "eh gaskiya gwara muje dan danbaba ma nason ganinta "ta turo baki gaba,
Besan abinda take ba yana ta driving yace "yau zaya ganta se marece zanzo mutafi"
Tace "a, a kabari har dare please "ta harari bayanshi.
Yace "angama gimbiya "
Suna isa ta sauko tafara nishi har ya jingine mashin dinshi,
Ta mika mai Jakarta tace "yaya ka temakamin daita nagaji "
Ya anshi jikkar suka shiga yana gaba tana baya,
hjy na kitchen suka shigo ta window take kallon jamila daketa faman turo ciki dafe da kugu kamar me ciki wata tara,ga khalil rike da jikka hjya ta girgizakai tace "Allah wadaran naka ya lalace"
Khalil ya fara sallama yana kiran "hjya kinyi baki "
Hjya ta fito tana faraa tace "a, a masu ciki ne agidan yau lalle manyan baki yaushe rabo "
Khalil yace "shiyasa tazo maki wuni na musamman yau "
Hjya tace "naji dadi ko ,kushiga daga ciki"
Suka wuce ciki few minutes ya fito ya tafi wurin aiki, jamila ta zare hijab ta bude ta kardar tsiranta da suka siya bakin asibity tafara ci,
Hjya aikin kitchen ya lafa ta shigo dakin zata shiga ta